← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 144

Sashe 142

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Inaso ki auri Najeeb Teemah, Domin ke kad’ai ce macen da na aminta cewar, zaki basa ingantaccen farinciki, nasan zaki goge masa duk wani damuwa dake cikin zuciyarsa, wallahi Teemah Najeeb bashi da makusa ko kad’an, sannan yana da kyau da nagarta, da kuma kyawawan halaye, shid’in Namiji ne kuma abunso ga kowacce mace, lallai tabbas nasan idan kika auresa zaku samawa juna farinciki, Insha Allah kuma zakuyi alfahari da kasancewarku atare, ina me rokonki kada kice aa Teemah, kada kuma kice wai dan ya tab’a aurena ke bazaki iya aurensa ba, kinsani babu abunda ya tab’a shiga tsakanina dashi, bai tab’a kusantata ba, kuma koda ma ace ya tab’a sanina amatsayin ya mace bana tunanin wannan zaisa ki ki aurensa, Domin nidake ba ya da kanwa bane, kuma koda ace har yau ina nan amatsayin matarsa, To aurenki dashi ba haramun bane halaltacce ne, dan Allah Teemah Kada kice aa.�

Idanu Teemah’n tad’an zaro waje tare dasa hannu ta dafe kirjinta, cike kuma da mamakin abunda Laylerh’n ta fad’i ayanzun tace.

“Anya kuwa Laylerh kinsan me kike fad’a? cewa fa kikayi ma auri Najeeb, tsohon mijinki, Chab gaskiya bazai yi wuba, bandamu ba koda akwai abunda ya shiga tsakaninku, nidai gaskiya bazan aureshi ba, bayan haka ma nifa sam banason second din Namiji sabo nakeso.�
Tak’are maganan tana me d’an murgud’a bakinta.

Wanda kuma hakanne yasa Laylerh da Aleeya sakin murmushi, saboda duk sun San halin Teemah’n tana da kafiya sosai.

Again kafadun Teemah’n Laylerh ta dafa, tare da kwantar da muryarta yanda tasan Teemah’n zata fahimta, cikin sanyi tace.
“Dan Allah Teemah ki amincewa auren Najeeb, ki kawar da duk wani tunanin dake cikin rai da zuciyarki, Insha Allah zakiyi farinciki da hakan, kinga Aleeya yanzu ta amince da Fou’ad za kuma ayi bikinsu nan bada jimawa ba, mun riga da mungama secondary school Teemah, kada ki manta ako da yaushe ke kike fad’amin cewa, idan dama ta sameka kada ka tab’ayin kuskuren wasa dashi, yanzu dama ta sameki Teemah why zakiyi watsi da ita? sannan awannan rayuwar tamu Kinsha fad’amin cewar, rufin asirin kowacce mace budurwa dake tasowa shine yin aure, saboda alokacin da tayi sake ta haurawa shekaru 20 batare da tayi aure ba, samun irin future husband d’in da take da muradi zaiyi mata wahalar samuwa, sam kada ki bari hakan ta kasance dake Teemah, ki mori k’uruciyarki ta hanyar yin aure yafi ki k’are k’uruciyarki awaje ba tare da aure ba, Tabbas aure lokaci ne amma idan naka lokacin yazo kada kayi wasa dashi, saboda watarana zaka so lokacin ya dawo, amma kuma yayi Nisan da juyowansa zaiyi wahala.�

Idanu Teemah’n ta d’an lumshe tare da jinjina kanta, Tabbas tasan duk maganganun da Laylerh’n ta fad’i haka suke, za kuma taso ace itama tayi aure da yarintarta.
Saidai kuma daga wani sashi na zuciyarta tanajin nauyin abun, kanta tad’an sunkuyar k’asa tare da murza yatsun hannunta cikin sanyi tace.

“Na amince da maganganunki Laylerh but bansan tayaya Najeeb zai daukeni ba, saboda bani da tabbaci akan cewar yana sona ko a’a.�

Murmushin tsananin jin dadi Laylerh’n tayi, tare dasa hannayenta duka biyu ta rungume Teemah’n, cikin kuma nuna tsananin farincikinta tace.

“Nagode sosai Bestie Tee kuma Insha Allah Najeeb bazai tab’a kinki ba, saboda ke macece irin wanda kowani namiji zaiso samu, Insha Allah Kuma zakiyi farinciki da hakan.�

Murmushi sukayi dukansu, cikin kuma farincikin da ya mamaye gaba d’aya zuciyarsu suka ci gaba da hira.

Sunanan atare kuwa har 4 su suka taimakawa Laylerh’n tayi abinci, bayan ta fito daga wankane kuma suka sake zama wata hirar.

Jin ana knocking kofar falonne kuma yasa Laylerh’n tashi taje ta bud’e, aikuwa tana bud’ewa idanunta sukayi tozali da Fou’ad, saidai kuma wanda ta gani abayan Fou’ad dinne yasata d’an zaro Idanunta waje, Cikin yanayin mamakin ganinsa tace.

“Yah Najeeb.�

“Na’am LaylerhMaleek.�
Najeeb din ya amsa mata fuskarsa dauke da murmushi.

Itadinma murmushin tayi tare Kuma da matsawa ta basu hanya suka wuce cikin falon.

Ganinsu dinne kuma yasa Teemah saurin sadda kanta kasa.

Itakuwa Laylerh direct ruwa da drinks ta tafi kawo musu.

Adaidai lokacin da Najeeb din ke kokarin zama ne kuma idanunsa suka sauka akan Teemah, hakanan kuma at the first time daya samu kansa da kasa dauke idanunsa akanta, cikin yanayin tsokana ne kuma yace.

“Teemah ba’a ji da ganinki sai awajen bestie’n ki ko.�

Jin abunda ya fad’a dinne kuma yasa Teemah’n ta saki murmushi tare da gaishesa.
Fuskansa asake ya amsa mata, daidai lokacin kuwa Laylerh ta cika musu gabansu da kayan drinks dana ciye ciye.

Sake sabon gaisawa sukayi, cikin kuma yanayinta na shagwab’a tace.

“Da fushi nakeyi dakai Yah Najeeb, but yanzu komai ya wuce.�

Murmushi yayi tare da d’an shafa sumar kansa, k’asa k’asa kuma yake kallon Teemah.

Ahaka dai suka dan sha drinks din da Laylerh’n ta kawo musu bayan Fou’ad ya sanarwa Laylerh’n cewa tun d’azu tare suke da Maleek, saidai jin zasu taho nan dinne yasashi wucewa wajen da yakeyin gym.

Hira sukayi sosai dukansu, acikin hirar tasu ce kuma Laylerh take fadawa Najeeb cewar ta kama masa Teemah amatsayin mata.

Ga mamakinsu kuma sai gani kawai sukayi Najeeb d’in yayi murmushi, tare da cewa.

“To na amince Allah yasanya alkhairi.�

Da “Ameen.� Suka amsa su dukansu, tare da d’an ci gaba da tab’a hira.

Saidai kuma ganin yamma na dad’ayine yasa Najeeb yace su Teemah’n su tashi su sauk’esu agida.
Hakan kuwa akayi har waje Laylerh’n ta rakosu, bayan taga tafiyarsu ne kuma ta juya ta koma gida.

Acan b’angaren su Najeeb kuwa, tun acikin mota shida Teemah suka daidaita kansu, tare da yin exchanging phone number.

Bayan sun sauke Teemah dinne kuma suka biya suka sauke Aleeya agida.

Acan gidan Laylerh kuwa ana kiran sallan magriba Maleek ya dawo, haka Laylerh’n ta cika masa cikinsa da abincin da ta dafa, koda dare yayi kuwa yau dinma soyayyarsu suka sha, wanda dadinta yasa duk suka zautar da juna.

Washegari kuwa suna zaune afalo sukaji ana musu knocking door, Maleek da kansa ya bud’e kofar saidai wacce ya gani dinne kuma yasashi hade fuskarshi.

Momy da Aunty Aina’u dake tsaye kuwa gaba daya jinin jikinsu suka sha, duk da cewar dama sunsan zasu fuskanci hakan.

Laylerh kuwa ganinsu Momyn da tayine yasata d’an fad’ad’a murmushi’nta, cikin nuna jindad’in zuwan nasu tayi musu iso, tare da kawo musu drinks.

Akunyace haka dukansu sukasha drinks din, cikin kuma yin k’ank’an dakai Momy tashiga neman yafiyan Laylerh da Maleek d’in, tare da nuna musu cewar abubuwan da tayi abaya bata kyauta ba, musamman akan Laylerh, sannan kuma da bakinta ya fad’a musu cewar itace tayi sanadiyar da Najeeb ya saki Laylerh, saboda kiransa da tayi awaya, ta masa kwatancen gidan Maleek dake Asokoro inda yaje yaga duk wani sirri akan soyayyar Laylerh da Maleek d’in yake b’oyewa, sosai ta nuna musu cewar tayi nadama.

Shidai Maleek kallonta kawai yakeyi batare da yace komai ba, saboda dama yawan magana ba al’adarsa bace.

Laylerh kuwa ganin hawaye a idanun Mom dinne yasa ta cewa ta yafe mata, dama ita Momyn batayi mata komai ba, tunda bata tab’a yi mata wani babban abu na cutarwa gaba da gaba ba.
Maleek kuwa duk yanda Momyn taso yace wani abu kincewa yayi, saidai acikin zuciyarsa ya raya cewa ya yafe mata.
Haka Momy da Aunty Aina’un suka tashi suka tafi, saidai sun d’anji sanyi acikin zuciyarsu saboda Laylerh’n da sukafi zalunta tace ta yafe musu.

A kuma ranar ne Alhaji Ahmad da Abbou Jaheed suka je suka nemawa NAJEEB auren Teemah, saboda kuma da mutumcinsu ne kuma yasa take mahaifin Teemah’n ya amince, Cikin aminci kuma suka nemi da asaka musu lokacin biki ba kuma sason lokacin yazo da tsawo, dayake kuma mahaifin Teemah’n attajirin gaske ne, take yace ya yanke biki nanda sati biyu.
Godiya sosai su Abbou Jaheed sukayi masa, atake kuma suka bada kudin aure domin dama su already ashirye suke.
Ahaka dai suka baro gidan su Teemah’n zuciyarsu babu ko digon damuwa.

Kamar kuwa yanda aka tambayowa Najeeb din auren Teemah yau, haka aka tambayowa Fou’ad auren Aleeya kuma duk ayau d’in, inda nan ma aka yanke biki nanda sati biyu masu zuwa.

Tun a washegarin ranar ne kuma grooms din suka soma
Shirye shiryen biki.

Yayinda ab’angaren Laylerh da Maleek kuwa wani irin sabo mai tsananin k’arfi da soyayya ne ta sake tsakaninsu, wanda kuma ayanzu har Laylerhn ta saba da yanayin feelings din Maleek dinnata, Domin ya koyar da ita kuma ta dauka, saboda hakanne ma kuma yasa akoda yaushe suke cikin feeling din junansu.

Two weeks
Tabbas rana bata k’arya kome akasa sai lokacinsa yazo, Domin yau ta kasance ranar Asabar kuma ayau d’inne aka d’aura auren Najeeb da amaryarsa Teemah, sai kuma Fou’ad da amaryarsa Aleeya inda dukkaninsu suka biya makud’an kud’ad’e amatsayin sadaki.

Bayan an d’aura aurenne kuma akayi walimah, yamma nayi kuwa aka d’aiki kowacce amarya aka kaita gidanta.

Inda aka kai Teemah had’add’en gidan Najeeb dake Wuse zone 2 sai kuma Aleeya inda aka kaita gidan Fou’ad dake asokoro.

Koda dare yayi kuwa kowani groom ya shiga d’akin bride d’insa, tare da nuna mata irin nasa salon da kuma kaunar da yakeyi mata.

Ab’angaren su LaylerhMaleek kuwa aranan suma amarcinsu suka ci, Domin kullum Maleek d’in sake jin Laylerh’n nasa yake sabuwa fil.
*** *** ***

After 2months.

Acikin watanni biyun abubuwa da yawa sunfaru, wanda kuma yawancinsa zallan k’auna da soyayya ne dake gudana atsakanin Laylerh da Maleeek d’in.
Acikin kuma watannin ne results dinta suka fito, wanda kuma duk acikin biyun babu wanda ta fad’i.

Sosai tayi farinciki da hakan, inda a b’angaren Maleek kuwa tuni ya gama yi mata duk wani abu daya dace tare da sama musu visa, saboda so yake su koma London da zama, dan acan yakeson Laylerh’n ta k’arasa gaba d’aya karatunta.

Wanda kuma yaune zasu tafi London d’in, Domin da k’arfe 4pm daidai jirginsu zai tashi.

Tuni kuma ya gama had’a musu komai nasu da yasan zasu buk’ata, yanzun ma kuma shida kansa ya kai Laylerh gida, Dan yiwa su Oum Ayush bankwana, Domin yana da tabbacin idan suntafi suntafi kenan, ba abunda zaike kawosu Nigeria sai ziyara.
Chapter 142 · 0% Book details