← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 144

Sashe 122

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau ma d’indai sosai jikinta yasha gurza, saidai kuma ita kanta idan ta shak’i k’amshin dake fita ajikinta, sai taji wani irin hot feeling ya ratsa ta.

Almost 1hour da shan maganin nata ne kuma, taji wani irin ciwon Mara na d’an taso mata, saidai kuma sanin da tayi cewa bawai period d’inta ne zaizo ba, yasa bata wani damu sosai ba.

Koda aka gama yi mata gyaran jikin ma d’aki ta koma ta kwanta, saboda ta lura tun safe bak’i ke zuwa cikin gidannasu, gashi sai hidiman canja furnitures da kuma gyare gyara ake tayi agidan,wanda duk ita batasan na meye ne hakan ba.
Tana kwanciya kuwa ba jimawa bacci ya d’auketa.

Only 20mn kuwa acikin baccin nata taji wani irin azababben ciwo na tashi daga cikin mararta, wanda yayi sanadiyar bud’e idanunta.

Ahankali ta tashi zaune tare dasa hannu ta dafe marar nata dake yi mata wani irin ciwon da bata tab’a jin irinsa ba.

Santala santalan legs dinta ta zuro k’asa daga kan gadon, tare da yunk’urin mik’ewa tsaye, saidai kuma bata kai ga k’arasa mik’ewa tsayen ba, ta saki wani irin azababben k’ara tare da saurin komawa ta zube akan guiwowinta.

Daidai lokacin ne kuma Oum Ayush da Aunty Zee harma da Aleeya suka shigo cikin d’akin.
Jin ihunta da sukayi ne kuma yasasu k’arasa shigowa cikin d’akin da sauri.

Oum Ayush ne tayi hanzarin rik’ota, hankalinta atashe tace.
“Lafiyanki k’alau kuwa Laylerh, me yake damunki?�

Kanta ta d’an shiga girgizawa, tare kuma da soma yarfa y’an yatsun hannunta, kasancewar zuwa yanzu sosai marar nata ta tsananta ciwo, ko tsayuwa mai kyauma ta kasa yi.

“Marana Oum Ayush, marana ciwo yake inajin kaman zai fashe!!�

Tayi maganan cikin muryar kukan daya k’wace mata, tare kuma da sake ci gaba da yayyarfa yatsunta.

“Subahanallah!�
Dukansu suka had’a baki wajen fad’a, cikin yanayin tausayawa kuma Oum Ayush dake rik’e da ita ta zaunar da ita akan gado, hannunta d’aya tasa ta d’an danna saman marar Laylerh’n, Jin kamar marar ta kunbura ne kuma yasa Oum Ayush saurin d’agowa ta kalli Laylerh’n, fuskarta d’auke da tarin damuwa tace.

“Ya ilahi Laylerh me kika sha haka, kodai period time d’inki ne yayi?�

K’ara volume d’in kukanta tayi, tare kuma da d’an girgiza kanta alaman “A’a ba period d’inta bane.�

Kwantar da ita Oum Ayush tayi, tare da d’anyin Jim tana me son nazartar yanayin Laylerh’n, aikuwa take wannan maganin ya fad’o mata arai, Da sauri ta kamo hannun Laylerh’n tare da fad’in.

“Ina maganin dana baki jiya da safe, wanda nace kina shan kad’an kad’an?.�

Duk da azababben ciwon dake cinta kuwa, saida taji k’irjinta ya buga alokacin da Oum Ayush ta tambayeta maganin, ad’an tsorace kana kuma da muryar sheshhek’an kuka tace.

“Nashanye!.�

Idanu Oum Ayush ta zazzaro waje cike da tsananin mamaki, da kuma tsoron abunda zai biyo baya.

Hankalinta amatuk’ar tashe tace.

“Why Laylerh? Why? Meyasa zaki shanye shi duka? Koda na kawo miki saida na fad’a miki yanda zaki na sha, amma saboda shegen son zak’i irin naki, kin shanyesa lokaci d’aya, kin san k’arfinsa kuwa? Meyasa kikayi haka Laylerh? Wallahi ko tantama banayi shiya saka miki wannan azababben ciwon maran da bashi da magani anan kusa.�

Idanunta dake tsiyayar da hawaye ta rumtse da k’arfi, had’e da sakin wani azababben nishin wahala.
Sam kwata kwata ma ita bataji fad’an da Oum Ayush d’in keyi ba, saboda zuwa yanzu ciwon nata k’aruwa yake bayan kowani second.

Ganin yanda take ta mik’ewa ne kuma yasa Oum Ayush tashi tsaye, zuciyarta cike da danasanin bawa Laylerh maganin, ta fice daga cikin d’akin.

Kaitsaye d’aki ta wuce tare da d’auko wayarta, tayi dialing number’n family Dr d’insu.
Bayanin ciwon Laylerh’n ta masa, take kuwa yace gashinan zuwa.

Duk da tasan cewar maganin hospital bazaisa Laylerh’n ta daina jin radad’in ciwon ba, koda ma ace ta samu maganin ciwon maran, To fa feeling din da zatakeji bazai tab’a barinta ba dole sai Namiji yayi sex da ita kafun ta samu cikakken relief, Thank God Ma yanzu aurenta da Maleek d’in saura 3days.

Ruwa maisanyi Oum Ayush d’in ta kai mata tasha, still har yanzu kuma kukan ciwon marar take.

Mintuna 15 kacal tsakani Dr ya k’araso, checking d’inta yayi da kyau, gane kuma da yayi cewar akwai feeling mai k’arfi ajikinta ne yasashi yi mata alluran relief da kuma wanda zai sata bacci, domin yasan yawan feeling ma na d’aya daga cikin best abunda ke jawo ciwon mara.

Aikuwa yana yi mata injections bacci ya d’auketa, wasu pain relievers ya bata sannan ya tafi.

Ganin ta samu bacci ne kuma yasa su Oum Ayush fita waje suka jawo mata k’ofar.

Aranar yau d’in gaba d’aya hidima sosai sukayi, domin ayau ne ma’aikatan OJC Concept suka zo suka sanja musu gaba d’aya furnitures d’in falukan gidan, furnitures masu kyau da tsada aka zuba musu.

Acan b’angaren Laylerh kuwa tunda Dr yayi mata injections, bacci take bata farka ba, har saida aka yi sallan Isha.
Koda ta tashi haka taji duk jikinta babu k’wari, hatta awajen yin wanka saida Oum Ayush ta taimaka mata, bayan kuma ta biya sallolin dake kanta ne, Oum Ayush ta kawo mata kayan fruits tasha, ko mintuna 30 ba ayiba kuwa still ta sake komawa wani baccin.

Wani babban abun mamaki kuwa shine kamar yanda Laylerh’n ta wuni tana bacci, haka ma Maleek dake can gidansa, shima yau d’in wuni yayi yana abu d’aya, saboda tun cocaine d’in daya sha daren jiya har yanzu bata gama sakeshi ba, kasancewar cocaine d’in nada k’arfi sosai.

The following day

Thursday.
Tabbas komai aka sawa lokaci sai yazo, Kamar dai yanda yakasance yau auren saura kwana biyu.

Gaba d’aya yanzu gidan nasu acike yake da jama’ar Oum Ayush wanda yawancinsu k’awaye da kuma y’an uwanta ne, saidai kuma awannan karon harda mutanen Egyft suma sunzo, wanda suke matsayin y’an uwansu Abbou Jaheed.

Sosai aketa hidiman biki, duk da cewar ba za’ayi program ko daya ba, amma hakan bai hana jama’a cika acikin gidan ba.

Saidai kuma rashin lafiyar Laylerh’n gaba d’aya yasa jikin su Oum Ayush yayi sanyi, saboda har yanzu marar nata bai daina ciwo ba, tana dai samun relief ne kawai idan tasha maganin baccin da Dr ya bata, daga zangar ta tashi abaccin kuwa amfanin maganin na k’arewa ciwon zai dawo, ga wani matsanancin feeling d’in da yake neman haukata mata lissafi, wanda akoda yaushe hakan ke sawa taji kaman tayi kuka, wannan dalilin yasa bata ko fitowa yanzu gyaran jikin ma an d’an lafa mata dashi.

Acan b’angaren su Abbou Jaheed ma sam basu zauna ba, Dan tuni sun gama raba invitations cards wa jama’arsu.
Ciki kuwa harda Fou’ad wanda shine ya tsaya akan komai da komai na bikin, hatta kayan da Ango zai sa yariga daya tsara komai.
Yayinda ya tura invitations card ga kowa, kama daga kan friends d’insu harma da abokan aikinsu.

Ab’angaren Maleek kuwa ya lura da yawan zirga zirgan da Fou’ad d’in keyi, saidai kasancewarsa ba mutum ne me yawan shisshigi ba, shiasa bai tambaya ba, hasalima gaba d’aya wunin yau a office d’insa yayi, saboda ayyuka sun d’anyi masa yawa, shi yasama bai dawo gidan ba sai 11pm, koda ya dawo kuwa bai kula da abunda yaga Fou’ad din nayi ba, kaitsaye bedroom d’insa ya wuce ya kwanta.

*Friday*

Alhamdulillah yau Koda ta tashi bata ji ciwon marar nata ya tsananta kamar yanda ya sabayi mata akwana biyun da suka wuce ba.

Samun k’arfi ajikinta da tayi ne kuma yasa ta fito zuwa falo.

Sosai kuwa su Oum Ayush sukaji dad’in ganin jikin nata, hakan nema yasa Oum Ayush ta k’ira meyin zanen Henna ta zana mata, wani irin kyau’n da Laylerh’n tayi kuwa har d’auke idanun jama’a yake, musamman da zanen red henna d’in ya kwanta akan skin d’inta.
Ita dai kam har yanzu ta kasa fahimtar komai, dake faruwa acikin gidan.
Saidai ayau d’in tasa aranta cewar zata tambayi Oum Ayush dan sanin hak’ik’anin abunda ke faruwa.

Hakanne kuwa ya kasance domin tana idar da sallah’n Isha ta mik’e tsaye, direct bedroom d’in Oum Ayush ta nufa.

Oum Ayush dake zaune akan gado tana Ware wasu Sabin clothes din da aka kawo mata d’inki, ganin Laylerh’n da tayi ne kuma ya sata sakin murmushi.
Tare da cewa.

“Laylerh bakiyi bacci ba?.�

Kanta tad’an jinjina alaman “Eh.�

Asanyaye kuma ta zauna agefen Oum Ayush d’in, cikin muryarta dake tafiya very slowly tace.

“Oum Ayush wai waye zaiyi aure? naga gaba d’aya anata hidima.�

D’an dakatawa daga duba clothes d’in Oum Ayush tayi, tare da juyowa ta kalli Laylerh’n, fuskarta d’auke da murmushi tace.

“Auren wa kike tunanin za’ayi agidannan Laylerh idan ba naki ba? Kodai baki shiryawa yin auren bane?�

Kanta ta d’ago da sauri, tare da zaro idanunta waje, murya na rawa tace.

“Aure na kuma Oum Ayush?�

Jinjina mata kai Oum Ayush tayi, tare da kamo hannayenta ta rik’e Cike kuma dason bata k’warin guiwa tace.

“Abunda zuciya keso ne zata samu Laylerh, sannan kuma muradin dake yawo acikin zuk’ata biyu ne ke son cika, Insha Allah Ayanzu babu wani abu dazai dakatar da farincikin ku, saboda haka kwanta kiyi bacci, domin gobe da sassafe za’a shiryaki..�

Baki idanu harma da hanci ta bud’e tana kallon Oum Ayush, da kalamanta suka sa taji ta tamkar ta zama wata statue, domin gaba d’aya tunaninta tsayawa yayi, abu d’aya ne kawai ke kai kawo acikin Brain d’inta shine AURE’n da Oum Ayush tace za’a mata.

Saidai tunanin nata baije ko ina ba, haka bisa dole ta katse shi, alokacin da taji Oum Ayush d’in na cewa.

“Ta kwanta anan d’akin, ita zata je wajen Abbou Khareem.�

Har Oum Ayush d’in kuwa ta fice Laylerh bata d’auke idanu akanta ba.

Gaba d’aya ma tarasa tunanin me zatayi.

Hakan yasa ahankali ta sulale ta kwanta akan gadon, tare da lumshe idanunta, ga mamakinta kuwa ji tayi wasu irin k’walla masu sanyin gaske na bin gefen fuskarta.

K’wallan da ita kanta batasan na menene ba.

Lokaci guda kuma taji wani irin sanyi na ratsa cikin tafin k’afanta dama zuciyarta.

Hakan kuwa shi yasa ta dunk’ule jikinta waje d’aya, tare da soma sauk’e wani irin ajiyar zuciya.

*M.Jay*

*12:30 am*
Chapter 122 · 0% Book details