← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 144

Sashe 3

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana fita Teemah tayi saurin dawowa sit É—in da Laylerh ke zaune, wani duka ta kai mata tare da cewa. "Yamiki kyau uwa da uban Æ´an latti, wai ke kam Laylerh yaushe zaki daina latti ne?."
Idanunta masu kyau taɗan lumshe, tare da shafa cikinta da taji yana murɗawa, cikin zazzaƙar muryarta tace.
"Nibansan meke damunki ba Teemah, wallahi kina da takura, É—azu da kike ta damuna mezan miki ne?."
"Bansani ba É—in Æ´ar rainin hankali." Teemah tafaÉ—a tana me gyara zamanta, idanu ta zubawa Laylerh'n, dan ganin wani bushashshen hawaye kwance akan fuskarta.
Hannunta ta kai kan fuskar Laylerh'n ta shafa hawayen, asanyaye tace. "Kuka?."
Shiru Laylerh tayi, tare da sunkuyar da kanta ƙasa.
Kai Teemah ta girgiza, tare da É—aura hannunta akan kafaÉ—an Laylerh'n, cikin kulawa tace.
"Yau kuma meya sameki, harda kuka?."
Kai Laylerh ta jijjiga alaman ba komai.
Baki Teemah ta cije, tare da cewa "Hmmm kima daina ɓoyewa Laylerh damuwarki abune nayau da kullum, ya riga daya bi jikinki dole sai angane saboda haka kima daina wahalar da kanki wajen ɓoyewa, yauma bakiyi break fast ba kika fito ko?."
Still idanunta taɗan lumshe tare da jinjina kai, alaman "Eh." Ajiyar zuciya Teemah ta sauƙe, cikin tausayin ƙawartata tace.
"Ni narasa wace irin rayuwa akeyi agidanku Laylerh, bansan meyasa ake miki haka ba, babu wani mutum ɗaya da yake kulawa dake acikin gidannan, bakya taɓa jin daɗi sai Abbu na nan, suna kyararki suna miki abu kaman ke ba jininsu bace, always suna barinki kina yawo da yunwa, daidai da school wannan baza'a sa driver ya kawoki ba, sai idan Abbu na nanne ma watarana kike samun arzikin shiga mota, wallahi Laylerh ƴan gidanku basu da kirki, more especially Momy."
Saurin toshe mata baki Laylerh tayi, hawayen da suka cika idanunta ta goge, cikin raunin daya bayyana mata tace.
"Kada kice haka Teemah, bansan meyasa ba raunina baya ɓuya, ako da yaushe ni me rauni ce akan damuwa ta,kada ki bari damuwata ta dameki Teemah, because damuwata ta yau da kullum ne."

Baki Teemah ta taɓe sannan ta girgiza kai, komawa sit ɗinta tayi ta ɗauko wata food flask, wanda kuma tana zuwa da itane musamman dan Laylerh'n.
Buɗe food flask ɗin tayi sannan ta tura mata gabanta, abinci ne me rai da lafiya acikin food flask ɗin, soyayyen doya da miyan egg sai pepper chicken soup akai, ayanda takejin yunwa sosai batajin zataƙi cin abincin, dayake time break ne hakan yasa acikin ajikin taci abincin, goran ruwan swan Teemah ta miƙo mata takarɓa tasha.

Tuno da cewa Teacher David yace ta sameshi a office É—insa ne, yasa ta ce da Teemah tazo ta rakata.
Akaf duk makarantar bata da wata ƙawa wanda ta wuce Teemah, kasancewar makarantar tasu ta ƴaƴan masu faɗa aji ne, yasa kowa harkan gabansa yake, ba ruwan kowa da kowa, duk wanda ka gani yanaji da isa da kuma kuɗin babansa.

Koda suka ƙarasa bakin office ɗin, tsayawa Teemah tayi, tace ita bazata shiga ba, saboda tasan me ta aikata akan pepern ta, duk yanda Laylerh taso Teemah taraka ta ciki ƙi tayi, dole haka ta nufi office ɗin ita ɗaya.

Knocking ƙofan tayi daga ciki ya bata izinin shigowa, ahankali ta tura ƙofar ciki ta shiga.
Tsayawa tayi daga ɗan nesa dashi, cikin sanyin murya tace. "Sir gani." Ɗago kai teacher David yayi ya tsura mata idanu, tsaida idanunsa akan ƙirjinta yayi, ƙuri ya mata baya ko ƙifta idanunsa.
Ganin irin kallon da yake mata yasa ta maida hannunta cikin hijabinta, tare da ɓoye ƙirjinta.
Tasowa yayi daga kan kujeran da yake zaune, kaitsaye ya nufo inda take sai faman ƙanƙance ƙananun idanunsa yake.
Shikaɗai yake saƙa wani abu acikin zuciyarsa, tunani yake aɗazu iya hannunta kawai ya ɗan taɓa yaji wani iri ajikinsa, ina kuma ace idan ya rungumeta yasan abun da zaiji saiya kusa zautar dashi.
Ganin yana matsota ne yasa ta soma É—an jan jikinta baya, ahaka har takai jikin bango bai daina matsota ba, jinta ajikin bangone yasa ta rumtse idanunta, cikin muryarta dake rawa tace. "Sir...."
Maganan natane ya maƙale sakamakon jin ya damƙo hannunta, yana ƙoƙarin jawota jikinsa, tsoro ne ya kamata take jikinta yasoma rawa, cikin sauri ta fusge hannunta tare da sake matsawa can gefe, hijab ɗinta ya riƙo, still ƙoƙarin jawota jikinsa yasoma yi, da sauri ta fusge hijab ɗinta tare da ficewa daga cikin office ɗin, hartana jin tuntuɓe saboda sauri.

Cike da takaicin asarar daman da yayi akanta, ya cije laɓɓansa, tabbas yaso ace ya rungume ta yaji abun da yakeso yaji, batun yauba komai na yarinyar ke burgesa, musamman ma idan tana magana yanda laɓɓanta ke motsawa shiyake sawa yaji sha'awarta sosai.

Laylerh kuwa tana fita daga office ɗin nasa, ta saki wata irin ƙatuwar ajiyar zuciya.
Teemah dake tsaye ne ta riƙo hannunta tare da cewa.
"Yadai Naga kina haki kamar wanda tayi wasan tsere."

Atsorace ta kamo hannun Teemah suka bar bakin office É—in, hankalinta aÉ—an tashe tace.
"Teemah tsoro nakeji, Teacher David ɗan iskane koda na shiga wajensa ƙoƙarin kamani yayi."
Idanu Teemah ta zaro, cikin yanayin mamaki tace. "Ɗan iska? No wonder shiyasa always zaki ga yana wuƙi wuƙi da ƙananun idanunsa, munafuki muwuce class kadama yaganmu." Suna riƙe da hannun juna haka suka nufi class ɗinsu.
5:00 pm daidai kamar yanda aka saba tashinsu akowacce rana, yau ɗin ma hakanne ya kasance ƙarfe biyar daidai aka tashesu.
Gaba ɗaya compound ɗin makarantar tasu cike take da ɗalibai maza da mata, kowannensu kuwa kallo ɗaya zakayiwa fuskarsa ka nazarci halin da yake ciki, wato gajiya, da kuma yunwa, irin wanda ɗalibai suka saba dawowa dashi gida, haka take ma akan fuskar Laylerh Mahmoud Gwani, wanda itama amatuƙar gajiye take sosai, ga kuma wani irin stress dake damunta.
Atare suka fito daga cikin class É—insu ita da Teemah.
Kamar yanda yake a ƙa'idan makarantar tasu idan ankawo ɗalibi ko anzo ɗaukarsa daga bakin gate ake sauƙeshi ba ashigo da car cikin makarantar.
Hakanne yasa gaba ɗaya wajen makarantar cike yake da motoci, ƙarasowan drivern gidan su Teemah ne yasa, Teemah ta matsawa Laylerh cewar lallai sai tashiga sun yi dropping ɗinta agida. Bazataƙi ba saboda itama tana da buƙatar hakan, kuma tsakaninta da Teemah babu ɓoye ɓoye. Kasancewar basu da wani nisa me yawa tsakanin gidan su Laylerh da makaranta, hakan yasa basu wani jima suna tafiya ba suka iso, aƙofar tangamemen gate ɗin gidan suka sauƙeta, bayan ta fito daga motanne ta ɗagawa Teemah hannu alaman sai gobe. Kai Teemah ta jinjina mata sannan driver yaja motar suka tafi.

Ahankali ta tura ƙofar gate ɗin gidan nasu ta shiga, wannan karon kam ba Ɗahiru bane abakin gate, wani soldier man tagani sanye da kakinsa, fuskarnan tasa ko alaman murmushi babu, hakanan taji bugun zuciyarta ya tsananta, take wani tunani ya bijirowa ƙwaƙwalwarta, memories ɗin baya ne yasoma ƙoƙarin dawo mata, kallon soldier man ɗin takuma yi, asanyaye ta nufi katafaren ginin cikin gidan nasu.

Wata haɗaɗɗiyar farar matace zaune acikin hamshaƙin falon, sanye take da awarwaro da kuma sarkan zinare awuyanta, kallo ɗaya zaka mata kasan taji yalwan arziki, dukiya kuma sun zauna mata, wata tsaleliyar wayace ƙiran iPhone 11 pro riƙe ahannunta, sai kuma laptop dake ɗaure bisa cinyarta tana latsawa, gefe da ita kuwa wata mata ce itama tasha kwalliya, saidai ita baza'a ƙirata da sunan babbar mace ba, dan da'alama bata da yawan shekaru jikine kawai da take dashi, wayane itama ahanunta tana ta faman latsawa.
Da sallama ɗauke abakinta ta turo ƙofar falon ta shigo.
Daga cikin mata biyun nan babu wacce ta ɗago kai ta kalleta balle tasa ran zasu amsa mata sallaman nata, ƙarasowa cikin falon tayi, tare da ɗan rusunawa, murya asanyaye tace. "Momy, Aunty, barka da gida." wacce aka ƙira da Momy ne ta ɗago kanta cike da tsananin isa, bata iya amsawa ba sai jinjina kai da tayi. Idan da sabo ta saba da hakan. Ta bayansu ta raɓa ta nufi hanyar da zai sadata da ɗakinta, daidai takawo tsakiyan tangamemen falon idanunta suka sauƙa akan wani ƙaton hoto dake cikin falon, wanda aka killacesa cikin wani haɗaɗɗen glass, idanu taɗan tsurawa hoton duk dama baka iya ganin fuskar wanda ke cikin hoton dan ya bada bayane aka ɗaukesa, kallo ɗaya zakayiwa bayan na cikin hoton ka fahimci cewa cikakken Namiji ne, kuma gwarzo, dan sanye yake da kakin sojoji ajikinsa, wanda sukayi masifar yi masa kyau, ahannunsa riƙe yake da wani kwalba, da alama unexpected pic ne akayi masa batare daya sani ba.
"Laylerh."
Momy taƙira sunanta. Jin momy taƙira sunanta ne yasata ɗauke idanunta daga kan hoton tare da juyowa, asanyaye tace. "Na'am Momy."
Batare da Momy ta kalleta ba tace. "Kicire uniform É—in kizo na aikeki."

"To."
tace sannan ta shige cikin É—akinta.

Aunty Aina'u dake zaune sai yanzu ta É—ago kai ta dubi Momy, cikin kulawa tace.
"Yau naga kaman bakya cikin mood me daÉ—i meya faru?."

Numfashi Momy ta fesar tare da gyara zamanta, cikin wani irin yanayi tace. "Next week CAPTAIN MALEEK Zai dawo."
Idanu Aunty Aina'u taÉ—an zaro, cike da mamaki tace.
"What Captain M.J GWANI zai dawo? mutumin daya share kusan 7 years a U.S bai waiwayo Nigeria ba, then yanzu kuma yace zai dawo, aikine zai kawosa kenan ko me?. "

Baki Momy ta taɓe ataƙaice tace.
"I don't know."

ÆŠan jim Aunty Aina'u tayi,lokaci É—aya ta saki murmushin da ita kaÉ—ai tasan ma'anarsa.

Momy kam batasake cewa komai ba, saima ɗauƙan drinks tayi ta soma sha, zuciyarta duk ba daɗi, musamman akan dawowan CAPTAIN MALEEK.
Chapter 3 · 0% Book details