← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 144

Sashe 16

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Najeeb kuwa taro Laylerh'n da yayi ta faɗa jikinsa ne, ya sashi jin wani irin shock, take yaji gaba ɗaya tsikar jikinsa sun mimmiƙe, lokaci ɗaya wani irin yanayi ya soma ratsa ƙashi da bargonsa, hannayensa dake rawa yakai kan kyakkyawar fuskarta, cikin wata irin murya me sanyi yace.  "Laylerh! please wake up,  ki buɗe idanunki please."  Yafaɗi maganan aɗan ruɗe, dan yanda yaga idanunta na lumshewa, ya sanyashi jin faɗuwar gaba.          
Duk da cewar tana jinsa amma bazata iya amsa masa ba, saboda hakanan takejin kamar tunani da hankalinta na ƙoƙarin barin jikinta, idanunta ne suka cigaba da  lumshewa, yayinda jikinta ya sake.         
Ganin haka ne yasa Abbu tasowa hankalinsa amatuƙar tashe ya taho kan Laylerh'n, ɗago ta yayi daga jikin  Najeeb, ahankali Abbu ya shiga girgizata tare da soma ƙiran sunanta. Ganin kamar bata cikin hayyacinta ne yasa Abbu ɗago kai ya dubi Maleek wanda ya lumshe kyawawan  idanunsa, yayinda  yayi kamar baisan abun da ke faruwa ba.   
Hankalin Abbu aɗan tashe yace.   "Please M.J sake ƙiran Dr.Ishaq, Laylerh ta fara fita hayyacinta banason wani abu ya sameta.."     
Abbu bai ida maganar tasa ba Dr.Ishaq ya shigo cikin falon.
Ganinsa ne yasa Abbu sauƙe ajiyar zuciya, da kansa ya ɗaga Laylerh'n inda ya kwantar da ita akan wata luntsumemiyar kujera dake nan side din dining area'n.      
Ƙarasowa cikin falon Dr. Ishaq yayi, hannunsa riƙe da ƴar jakarsa wacce ya zuba kayan aikinsa da yasan zai ɓuƙata aciki.          
Cikin kulawa Abbu da duk ciwon Laylerh'n yasa shi cikin damuwa yace.      "Please Dr. kayi checking ɗinta, naga kaman bata motsi."           
Kai Dr.Ishaq ya jinjina alaman duk yanda Abbun keso haka za'ayi. 
Ɗan ranƙwafawa yayi tare da buɗe ƴar jakarsa ya ciro abubuwan dayasan zai buƙata.   
Cikin wasu ƴan sakanni ya gama yi mata duk wasu gwaje gwajen da zaiyi mata. 
Acikin ƴan sakannin nan kuwa idan ka kalli fuskar Abbu da kuma Alhaji Ahmad, damuwa  kawai zaka hango akwance, yayinda Najeeb kuwa ya bada duk wani attention ɗinsa akan Laylerh'n, fararen kyawawan legs ɗinta wanda suka ɗan bayyana, sakamakon doguwar rigarta da ta ɗan ɗage ya zubawa ido baya ko ƙiftawa,daga cikin zuciyarsa kuwa abubuwa da yawa yake saƙawa.               

Maleek.           
Harzuwa yanzu idanunsa alumshe suke, ga wanda baisan meke faruwa ba, idan yazo zai iyi tunanin cewa  bacci yake, saidai kuma azahirance ba hakan bane,  shi kaɗai yasan abun da yakeji acikin zuciyarsa, ahankali yake fitar da numfashi, yayinda yakejin jikinsa duk ba daɗi, lokaci ɗaya yaji kansa nayi masa ciwo,  jingina bayansa da jikin kujeran da yake kai yayi, ajiyar zuciya yake saki akai akai, daga cikin ƙirjinsa kuwa zuciyarsa ce ke beating da sauri sauri.
                      
Daga ɓangaren Dr. Ishaq ma ajiyar zuciyan ya sauƙe, dan gane abun dake damun Laylerh'n yasa komai yazo masa cikin sauƙi, kuma ciwon nata ma ba sosai irin yanda zai tsoratar ɗinnan bane.             
Wasu ruwan Injection guda biyu ya ciro acikin jakarsa tare kuma da Injection din, take yasoma haɗawa dan yasan idan yayiwa Laylerh'n su zata ɗan samu relief.           
Ahankali taÉ—an soma ware shanyayyun idanunta wanda sukayi luhu luhu, da dukkan alama tanajin ciwon ajikinta sosai.
Akan Dr. Ishaq ɗin ta sauƙe idanunta wanda ke tsaye yana haɗa ruwan alluran da zaiyi mata.         
Ganin allura ahannunsa ne yasa ta ƙarasa ware idanunta, take jikinta ya soma ɓari saboda tsoro.   
Ganin ta buɗe idanunta ne yasa Abbu ya ƙaraso kusa da ita, cikin kulawa yace. 
"Laylerh sannu ko, ya jikin naki?."      Ashagwaɓe taɗan soma girgiza kanta, cikin muryarta da ta sanja amo tace.     "Please Abbu kafaɗa masa banason allura."        
Murmushi Abbu yayi tare da shafa kanta, cikin matsanancin tausayinta yace. 
"Sorry bazai miki da zafi ba, kuma ae alluran ita zata kashe miki pain din da kikeji, kiyi haƙuri amiki alluran kinji."  Abbu yafaɗi maganar cikin lallashi.
Kai ta cigaba da girgizawa take hawaye suka cika idanunta, Allah Yasani arayuwarta tana matuƙar tsoron allura, saboda hakane ma ko ganinta batason yi.               
Ganin da gaske alluran Dr.Ishaq ke ƙoƙarin yi mata ne yasa ta fashewa da kuka, amatuƙar tsorace ta soma jijjiga kanta tare da ɗan yarfa hanna yenta, cikin sheshsheƙan kuka tace. 
"Please Ya M.Jay kace kada amin allura am scared,  pleaseeeeee .....!!" Taja maganan cikin wani irin yanayi dake nuna cewar bada iyaka bakinta takeyin maganna ba, har da zuciyarta.        

Sauƙan maganganunta acikin kunnuwansa ne ya sashi rumtse Idanunsa da ƙarfi, lokaci ɗaya wasu abubuwa suka shiga yawo acikin tunani da ƙwaƙwalwarsa, tabbas irin hakan ya taɓa faruwa, wani lokaci da take buƙatar taimakonsa kamar yanda takeyi yanzu'n, kansa ya shiga girgizawa yayinda memories din baya ke ƙokarin dawo masa, lokaci ɗaya tunaninsa ya soma juyewa, abubuwa da yawa ne suka shiga bijiro masa. lokaci ɗaya jikinsa ya soma ɓari, take jijiyoyin jikinsa suka mimmiƙe, wanda hakan yasa gargasan jikinsa ma miƙewa, bazai iya jure yanayin da yake ciki ba, kukan Laylerh ne ke ƙoƙarin haukata masa tunani, ji yake kaman ana buga masa guduma acikin kansa, idanunsa ne suka soma yi masa gizon, abun da ya faru da Laylerh'n shekarun baya da suka wuce, kansa ya soma girgizawa take gaba ɗaya mood ɗinsa ya sauya, cikin wani irin matsanancin huci haɗi da nuna zallar yanayin da yake ciki da ƙarfi ya buga table din dake gabansa, wanda hakan yajawo plates da kuma glass cup's ɗin dake kan table din suka watse, tare da tarwatsewa aƙasa.  
Ƙaaran buga table din da kuma fashewan cups ɗin da yacika falon ne yasa su Abbu atsorace suka maida hankalinsu garesa, hatta Dr. Ishaq da ke shirin yiwa Laylerh allura  tsaida komai yayi, ya zubawa M.Jay ɗin idanu.          
Har yanzu jikinsa rawa yake, yayinda ya dunƙule hannayensa waje ɗaya, yana sakin wani irin zazzafan huci.
Ganin yanda jikinsa keta faman ɓari ne yasa abun cikin yanayin sanyi yaƙira sunansa.         
Jin muryar Abbu acikin kunnuwansa ne ya sa duk wani tunaninsa tsayawa, zuciyarsa tafasa take, yayinda yakejin zuciyarsa kamar zata faso ƙirjinsa ta fito waje, kansa ya girgiza dan bayajin zai iya jurewa yanayin da yake ciki, miƙewa tsaye yayi, cikin wani irin taku dake bayyana zallan izza da kuma ikonsa haɗi da nuna cewa shiɗin tsayayyen namiji ne ya nufi ƙofar da zata sadashi da falonsa, ko gani sosai bayayi saboda yanda idanunsa suka kaɗa sukayi ja. 

Idanu su Abbu suka zuba masa har saida ya ɓacewa ganinsu, ajiyar zuciya Abbu ya sauƙe, tare da zama akan kujera yayi shiru, da yawan lokuta wani abu na haukata tunanin ɗan nasa wanda baisan ko menene ba, ba tun yauba ya fahimci cewa, Maleek ɗin nada wata damuwa acikin zuciyarsa, wanda ya kasa bayyanata ga kowa.
Lumshe idanunsa yayi lokaci ɗaya yaji zuciyarsa ta karye, haƙiƙa rashin Oum Abdiyya shiya ruguza rayuwarsu, tabbas ya sani da tana nan duk wata matsala na Maleek zata sani amatsayinta na uwa.      
Laylerh da ganin yanda Maleek ɗin ya rikide alokaci ɗaya ne yasa taji zuciyarta ta sake raunana, taso ayau din koda sau ɗaya ne ta kalli kyakkyawar fuskarsa, saidai hakan baiyi wuba, danko ayanzu bayansa kawai ta iya gani.             
Kallonta Dr.Ishaq yayi cikin son lallaɓata yace.  
"Kitsaya na miki alluran bazan miki da zafi ba."         
Kanta ta girgiza take kuma ta sake sakin sabon kuka, cikin muryarta dake rawa tace. 
"Tsoro nakeji, please Ya M.Jay tsoro nakeji."      
Chapter 16 · 0% Book details