← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 144

Sashe 47

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

"Eh mana masu lalle, ko kin taɓa ganin inda aka bar amarya haka ba lalle ajikinta?." Oum Ayush tafaɗa tana me nufar ƙofar bathroom dan so take ta haɗawa Laylerh'n ruwan wanka.
"Amarya.!" Ta maimaita kalmar da Oum Ayush ɗin tafaɗa, dan hakanan taji kalmar abakinta kamar sabuwar kalma, ganin bata da lokacin tunani ne yasa ta sanya hannayenta ta mutsutstsuke idanunta, da suke gane mata dishi dishi, ahankali kuma ta zuro da kyawawan ƙafafunta ƙasa daga kan gadon.
Daidai nan Oum Ayush ta fito daga cikin toilet ɗin, towel ɗin dake hannunta ta miƙawa Laylerh'n, tare da ce mata ta karɓa tasa.
Babu musu kuwa ta karɓi towel ɗin ta ɗaura ajikinta.
Ganin haka ne yasa Oum Ayush fita daga É—akin, kana kuma cikin minti biyu ta dawo hannunta É—auke da wani cup wanda cikinsa ke É—auke da madarar shanu.
"Kitabbatar kin shanyesa tas kafun kishiga wankan." Oum Ayush ta faɗa tana me miƙawa Laylerh'n kofin madarar.
Ganin madara ne acikin kofin yasa ta karɓa, tare da kafa kanta ta shanyesa nan take ta ajiye cup din.
Juyawa Oum Ayush din tayi ta fita, wanda hakanne kuma ya bata daman shigewa toilet É—in kaitsaye.
Yau ma kamar jia ruwan wankan da Oum Ayush ɗin ta haɗa mata acikin bathtube din wankan, sai tashin daddaɗan ƙamshi yake, cikin marari ta shiga cikin ruwan ta kwanta, tare da lumshe idanunta.
Tunawa da mafarkin nata na yau da tayi ne yasa taji gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, take kuma taji zuciyarta ta karye, duk da cewa bata da yaƙini akan mafarki, amma tanaji ajikinta cewa lallai wani abu zai shigo cikin rayuwarta, wanda zai mata shamaki da duk wani muradin zuciyarta, tabbas taji ajikinta cewa wata sabuwar ƙaddara na neman kutso kai cikin rayuwarta, wanda kuma hakan daidai yake da salwantar farincikin ta.
Cikin rashi kuzari da kuma ƙarfin jiki tayi wankan. koda ta fito daga cikin toilet ɗin, zaune ta taradda Oum ayush akan gado, gefenta kuwa Aunty Zee ce, wanda takasance ƙanwa ga Oum Ayush ɗin.
Ganin Aunty Zee ɗinne yasa ta ɗan doka tsalle, cikin sauri ta ƙaraso ta faɗa jikin Aunty Zee ɗin, cikin farinciki tace. "Oyoyo Aunty Zee." Murmushi matashiyar matar da aƙalla bazata haura 31 years ba tayi, tare da shafa kan Laylerh'n cikin kulawa tace. "Oyoyo Laylerh amarya."
Jin Aunty Zee ɗin ta ƙirata da amarya ne yasa ta ɗan turo ƙaramin bakinta gaba ashagwaɓe tace. "Nifa ba amarya bace."
Dariya Oum Ayush da kuma Aunty Zee din sukayi, saboda dukansu sunsan cewa akwai ƙurucia acikin sha'anin Laylerh'n.
Wasu ɗinkin riga da sket na atamfa, wanda yana ɗaya daga cikin kayan da suka karɓo jiya awajen tailor Oum Ayush ta bata tace ta saka.
Koda ta sa kayan kuwa sosai ɗinkin ya amshi jikinta yayinda hips ɗinta suka bayyana kaman zasu fasa sket ɗin, kasancewar kuma Oum Ayush ta turawa telan da yayi ɗinkin hoton Laylerh'n ne yasa shi yi mata ɗinkin daidai da jikinta, wanda kuma tasaya kayayyakin ne a Dubai musamman saboda Laylerh'n tasa alokacin bikin ta, saboda tafi kowa sanin irin ƙiyyayar da Momy ke nunawa Laylerh'n, wannan yasa lokacin da Aunty Zee takai musu ziyara ta bata wasu daga cikin kayan tace takawo nan Nigeria aɗinka.
Kasancewar Aunty Zee ƙwararriyar me meckup ne yasa ta zaunar da Laylerh'n tayi mata light meckup akan fuskarta.
Masha Allah kuwa sosai fuskar Laylerh'n tayi raÉ—au da ita, yayinda wani fitinannen kyau ya bayyana akan fuskar Laylerh'n, take kuwa ta fito a siffanta na amarya.
Oum Ayush da kanta ta kama hannunta zuwa falo, wanda yake cike da jama'ar Oum Ayush, dan acewarta auren gata za'ayi Laylerh'n saboda hakane ma ta gayyato ƙawayenta da kuma danginta na kusa dan tundaga yau takeson bikin ya soma, inda yau za'ayi sakun lalle, gobe kuma shine za'ayi walima, sannan kuma zasuyi mothers night da dare, yayinda jibi insha Allah Za'a shafa Fatiha.
Ganin taron jama'a acikin falonne yasa Laylerh taji duk ta takura,yayinda gaba É—aya jikinta yayi sanyi, saboda ayanzu ne ta sake tabbatarwa da kanta cewar lallai Aurenta da Najeeb ba fashi.
Kilisa aka mata na musamman ta zauna, take wacce zatayi mata zanen Lallen ta fara aikinta.
Haka ma dae yauɗin Kusan wuni sukayi suna abu ɗaya, yayinda akayiwa Laylerh'n zanen jan lalle me matuƙar kyau, kasancewar kuma tana da hasken fata ne yasa zanen lallen fitowa raɗau ajikinta, yayi mata kyau.
6:00 pm daidai ta wanke lallen tare da yin wanka tayi sallah, tana nan zaune akan sallayan har aka kira sallan isha, bayan ta idar da sallan ne ta haye saman gadon Oum Ayush, saboda yanda taji lokaci ɗaya zazzaɓi na ƙoƙarin sauƙar mata, da kwanciyan nata kuwa ko minti 20 ba tayi ba bacci ɓarawo ya ɗauketa.
Washegari.
Da wani irin zazzafan zazzaɓi ta farka wanda har yakai ga da ƙyar ma take iya mota gaɓɓan jikinta.
Ganin yanda jikin nata yayi tsanani sosae ne yasa Hankalin Oum Ayush ya tashi, take tayiwa Abbou Jaheed waya ta sanar dashi cewar Laylerh'n bata da lafiya, hankalin Abbou Jaheed atashe ya ƙira family Doctor ɗinsu.
Cikin abun da baiwuce 30 minute ba kuwa Dr. din yazo.
Zuwa lokacin kuwa zafin jikin Laylerh'n ya ƙara tsananta, allurai biyu dr ɗin ya mata, tare da bata magani, duk da kuwa cewar tanajin ciwon ajikinta bata sha maganin ba saida Oum Ayush ta lallaɓata sannan tasha maganin, kasancewar kwata kwata batason magani.
Kasancewar alluran da dr. Ɗin ya mata nada ƙarfi sosae ne yasa take bacci ya ɗauketa. Ganin kuwa ta samu bacci ne yasa Oum Ayush komawa cikin jama'arta suka ci gaba da hidimominsu.
Chapter 47 · 0% Book details