← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 144

Sashe 140

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin abunda ya fad’a d’inne kuma yasa ta mik’ewa tsaye, tare da k’arasawa gaban drawer ta d’auko hijab ta saka a jikinta.

K’arasowa wajen da Maleek d’in ke zaune tayi, tare da d’an tsayawa abayansa, daidai lokacin kuwa ya tada sallah.
Cikin nutsuwa ta bisa sukayi sallah’n, bayan sun idar da sallah’nne kuma ya kama hannunta suka fita falo.

Ganin kuma yanda take ta hamma ne yasashi gane cewar ita d’inma yunwa takeji sosai.
Akan d’aya daga cikin kujerun falon ya zaunar da ita, tare da k’arasawa gaban fridge ya d’auko musu, babban goran fresh yoghurt da kuma cups.

Bayan ya zuba musu yoghurt d’in acikin cup ne kuma, ya zauna akusa da ita, tare da soma bata yoghurt d’in abaki tana sha ahankali.
Saida kuma tasha fiye da rabin cup d’in kafun ta janye kanta ahankali, tare da karb’an cup d’in daga hannunsa, ahankali takai bakinsa kamar yanda yayi mata.

Duk da cewar kuma baiso shan yoghurt d’inba, amma ganin da yayi cewar Laylerh’nne zata basa yoghurt d’in da kanta, ya sashi bud’e bakinsa anutse ya soma sha.
Bai kuma janye kansa ba har saida duka yoghurt d’in dake cikin cup d’in ya k’are.

“Ka k’oshi?.�
Ta tayi masa tambayar alokacin da ta ke saka tissue ta goge masa bakinsa, da duk ya b’aci da yoghurt d’in.

“Eh, kefa?.� Ya dawo mata da tambayar.

“Nima.� Tafad’a asanyaye tare da ajiye cup d’in dake hannun nata, ta kwantar da kanta akan chest d’insa.

Idanunta da har yanzu ke cike da bacci ta d’an lumshe, saboda kwata kwata sam baccin da tayi d’in bai isheta ba, Dan ji yake kamar ma yanzune maganin da tasha zai soma aiki.

Shikuwa Maleek ganin yanda Laylerh’n ta lafe acikin jikinsa ne, yasashi soma shafa bayanta ahankali, saboda tun d’azu ya fahimci cewar bawai baccin da tayin ya isheta bane.

Aikuwa shafata daya soma yid’inne yasa ta sake narkewa ajikinsa, cikin k’ank’anin lokaci kuwa ta sake maida baccinta.

Shid’inma idanunsa ya d’an lumshe adaidai lokacin da yaji d’umin numfashinta na sauk’a acikin jikinsa.
Wanda kuma hakan alamace dake nuna masa cewar Laylerh’n tayi bacci.

“Ayshnoor!� Ya k’ira sunanta akasalance, jin bata amsa shi bane kuma yasa shi sake gyara mata kwanciyarta, tare da zaro waya da kuma earpiece d’insa dake cikin aljihun wandonsa, sak’ala earpiece d’in yayi acikin kunnensa, tare da kunna wak’ar Aligatie (Running on my mind) yana saurara.
Yanayin yanda yayi da idanun nasa ne kuma, yasa duk wanda ya gansa zaiyi tunanin cewar bacci shid’in ma yakeyi kamar dai yanda Laylerh’n keyi.

Ahankali Oum Ayush dake tsaye abakin k’ofar da zai sada ta da falon saman ta juyo ta kalli su Abbou Jaheed dake bayanta, wanda ayanzu sun share sama da 10minute suna tsaye abakin k’ofar suna ta doka sallama da knocking amma ba’a amsa musu ba.

“Anya suna nan kuwa?.�
Abbou Khareem ya tambaya, saboda yanda suka share tsawon mintuna suna knocking k’ofar batare da an bud’e musu ba.

“Sunanan Oum Ayush bud’e mana k’ofar falon mushiga.�

Abbou Jaheed ya fad’a atak’aice saboda ya gaji da tsayuwa awajen.

Hannu Oum Ayush tasa ta murd’a handle d’in k’ofar ahankali, tare da tura kanta cikin falon kana su Abbou Jaheed dake tsaye suka rufa mata baya.

Turus haka suka tsaya gaba d’ayansu, saboda tozali da idanuwansu sukayi musu da Maleek wanda ke zaune akan sofa ya lumshe idanunsa, Yayinda Laylerh’n ke jikinsa, da dukkan alama kuma dukansu bacci sukeyi.

Wani irin murmushi mai d’auke da tsananin farinciki ne ya bayyana akan fuskar kowannensu, musamman ma Abbou Jaheed daya kasa d’auke idanu akansu, saboda yanda yaga sunyi matuk’ar dacewa da juna, wanda ayanzu ya sake tabbatarwa kansa cewar Lallaine Maleek da Laylerh ya dace, haka itama Laylerh’n da Maleek ta dace.

Saidai kuma tuna irin tarin k’addarorin da suka fuskanta ne yasa shi jin idanunsa sun ciko da k’walla, Domin har yau ya kasa iya cire damuwar mummunan k’addarar da ta auku acikin rayuwar Maleek d’in, saidai kuma ya sani cewar Allah Baya tab’a d’aurawa bawansa abunda bazae iya ba, saboda haka yayi imani cewa komai yayi farko zaiyi k’arshe, idan kuwa k’addara ta dindince, to Allah Yakan sawa zuciyar bawa salama, tare kuma da k’arfin jure k’addarar da ta sameshi.

Oum Ayush da fuskarta ke cike da yalwataccen murmushi ne, ta k’arasa shigowa cikin falon, tare kuma dasa hannunta ahankali tad’an tab’a kafad’ar Maleek d’in, saboda duk atunaninsu bacci yakeyi.

Sab’anin gaskiyar lamarin daya kasance, idanunsa kawai ya lumshe amma bawai baccin gaske ya keyi ba, bai kuma ji knocking d’innasu bane saboda ya saka earpiece akunnensa, sannan ya kuma k’ure volume d’in wak’ar da yakeji.

Jin da yayi antab’a kafad’ansa ne kuma yasashi ware idanunsa ahankali, tare da sauk’esu akan Oum Ayush dake tsaye tana sakar musu murmushi.

Idanun nasa yad’an zaro waje tare da d’an saurin gyara zamansa.

“Oum Ayush.�
Yak’ira sunanta cikin yanayin dake bayyana mamakin ganinta.

Oum Ayush kuwa hararan wasa ta watsa masa, tare dasa hannu ta d’an buge kanshi, cikin kuma nuna masa tsananin kulawa tace.

“Wato dama ba bacci kakeyi ba, shine kanajin mu muna knocking nida su Abbou Jaheed amma kaki bud’ewa ko, to gamu mun shigo.�

Murmushin daya d’an bayyana hak’waransa yayi, tare da juyawa ya kalli su Abbou Khareem da suka k’araso cikin falon suka zauna.

Ahankali ya sakarwa Abboun nasa murmushi, tare da dawo da kallonsa ga Laylerh dake kwance ajikinsa tana bacci.

Batare kuma da yaji kunyan su Abbou Jaheed dake cikin falon ba, ya d’aura bakinsa adaidai saitin kunnenta, cikin muryarsa dake fita slowly yak’ira sunanta, tare kuma da hura mata sassanyar iskan dake bakinsa.

Ashagwab’e tad’an motsa tare da sanya hannayenta ta mak’alesa, Domin duk da kasancewar bacci takeyi amma hakan bai hanata jin sautin muryarsa acikin kunnuwanta ba.

“Ayshnoor!� Ya sake k’iran sunanta akaro na biyu, tare dasa hannunsa ya tallafo hab’arta cikin muryar dake bayyana shauk’inta akansa yace.

“Wakeup Ayshnoor nah Oum Ayush da Abbou Jaheed nefa suka zo.�

Tamkar wacce aka zabura haka ta bud’e idanunta, tare da d’an d’agowa ta kalleshi.
Da idanu yayi mata alama akan ta juya ta kalli su Abbou’n.

Da atunaninta wasa Yah M.Jay d’in keyi mata, amma kuma ganin da gaske yakeyi ne yasa tayi saurin juyowa, ai kuwa atake ta sauk’e Idanunta akan su Oum Ayush d’in, da sauri ta diro daga jikinsa, tare da fad’awa jikin Oum Ayush d’in ta rungumeta k’am, cikin muryar dake bayyana zallar shagwab’a tace.

“Nayi kewarku Oum Ayush nah.�

Murmushi Oum Ayush tayi tare dasa hannunta tashafa kan Laylerh’n, murya d’auke da farinciki tace.

“Nima nayi kewarki sosai Laylerh, amma kwana d’aya ne fa kawai tak, gashi kuma naga aure yayi dad’i har kinsaba da mijin naki.�

Saurin sanya tafukan hannayenta tayi ta rufe fuskarta, tare da zame jikinta daga na Oum Ayush d’in ta zauna akusa dasu Abbou Jaheed, tare kuma da gaishesu akunyace, saboda sosai maganan da Oum d’in ta fad’a yasata jin kunya.

Su Abbou Jaheed kuwa fuska asake duk suka amsa mata gaisuwan nata, tare da tambayarta jikinta, saboda kafun suzo Oum Ayush ta fad’a musu cewar batajin dadi.

Akunyace duk ta amsa musu gaisuwar tasu, tare da mik’ewa ta kawo musu drinks da ruwa.

Still dawowa tayi ta zauna akusa da Abbou’n, wanda suke d’an tab’a hira sama sama da Abbou Khareem.

Bayan kuma sun d’ansha drinks din da takawo musu d’inne, Abbou Khareem ya d’anyi musu Nasiha, irin wanda iyaye keyiwa yayansu idan sunyi aure.
tare da bawa Laylerh’n atm card d’in bank d’in daya sa mata sadakinta na aure aciki.

Kasancewar kuma yammaci ya danyi ne yasa basu wani jima ba sukayi musu sallama, har waje kuwa Laylerh da Maleek d’in suka rakosu, gefe Oum Ayush ta jawo Laylerh’n tare da tambayarta batun ciwon mararta, da sauki ta bata amsa, saboda tun adaren jiya ta nemi ciwon marar nata ta rasa.
wani abu me kaman chocolates Oum Ayush d’in ta bata, tare da tabbatar mata cewar kullum tasha guda d’aya, zai taimaka mata sosai.

Godiya tayiwa Oum Ayush d’in, bayan kuma sun tafi ne Maleek ya kama hannunta suka koma cikin gida.

Suna shiga cikin falon nasu kuwa wayar Maleek din ta soma ringing, ganin sunan Fou’ad akan screen din wayarne kuma yasashi saurin picking call din tare da kara wayar akan kunnensa.

Daga b’angaren Fou’ad kuwa jin Maleek ya daga wayarne yasashi d’an gyara zamansa tare da shafa sumar kansa, cikin yanayin dake bayyana tsananin farincikinsa yace.

“Kagama yangan angwancinka nima soon zan angwance malam, saboda na samu mata ajiya kawai har mun daidaita tsakaninmu Insha Allah zamuyi aure nan bada jimawa ba.�

Murmushi Maleek d’in yayi, tare da d’an lumshe idanunsa ahankali yace.

“Naji To Wacece matar?�

“Aleeyah frnd din Laylerh mana, gaskiya babe din ta hadu, yanzu ma maganan da nake maka fa harna fadawa Abbana, yace nanda 3daya zaije gidansu, kai intak’aice maka dai Insha Allah nanda 2weeks Ina da mata, nima nagaji da zama haka�

Murmushi Maleek d’in yayi, batare kuma da yace komai ba ya katse kiran, saboda yasan halin Fou’ad matuk’ar ya biye masa to zai ta damunsa da surutu ne, shikuwa ayanzun akwai abunda yakeson aiwatarwa.

Kallon Laylerh dake gefensa yayi, tare da manna mata kiss a forehead dinta, asanyaye yace.

“Bari naje wani waje Ina dawowa yanzu.�

Kai ta jinjina masa alaman to, shikuwa Cikin hanzari ya juya ya fita, ganin kuma da tayi cewar zama waje Dayan zai takurata ne yasa ta jawo sabuwar wayarta tare da soma setting d’in abubuwa Domin ayau takeson fara amfani da ita.

Ab’angaren Maleek kuwa yana fita daga cikin gidan, kai tsaye hotel ya nufa, saboda acanne yake da yakinin samun mutumin da yake nema.

*(Yau nayi yping mai yawa amma ya goge😭 yanzu kuma wallahi bacci nakeji)*

*10:06 pm*
4/13/21, 11:27 AM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting by*
fatymasardauna

*Note editing*

*CHAPTER 83*

8:30 pm daidai ya shigo cikin gidan, idanunsa ya zubawa Laylerh dake kwance akan sofa, Yayinda wayarta ke d’aure asaman chest d’inta, wanda da dukkan alama kuma amfani take da wayar bacci b’arawo ya d’auketa.

Murmushi yayi tare da k’arasowa cikin falon ya ajiye ledodin dake hannunsa.

“Ayshnoor!�
Yak’ira sunanta ahankali tare dasa hannunsa yad’an bubbuga k’afarta.
Chapter 140 · 0% Book details