← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 144

Sashe 43

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin alamar fitanta daga cikin É—akinne yasa ahankali ya buÉ—e idanunsa wanda suka sauya launi daga kalan fari zuwa ja, yayinda kuma suka rikiÉ—e suka koma zallar sexy eyes wanda suke É—auke da zallar wutar sha'awa acikinsu, kana kuma suka bayyana da kuma fallasa asirin dake cikin zuciyarsa.
Hanyar da tabi ya zubawa ido, haka yakejin tsikar jikinsa na ci gaba da tashi, yayinda kuma gargasan jikinsa ke ƙara miƙewa, the first time kenan da yaji wata irin mahaukaciyar sha'awarta na neman fasa masa mara.
Domin kuwa tun shigowarta falonsa yaji motsin mutum, kana kuma har ta shigo cikin ɗakin idanunsa biyu, duk wani abu da ta aikata ta kuma faɗa yana jinta, saidai rufe idanunsa da yayi yasa ta ga kamar bacci yakeyi, tabbas baƙaramin juriya yayi ba, domin alokacin da ta ɗaura hannunta akan tsakiyar bayansa, wani irin masifaffen shock ne ya shiga jikinsa, take kuma jarababbiyar feelings dinsa ta motsa, lallai ya daurewa hakan, domin yanayin yanda take wasa da ƴan ƴatsun hannunta akan bayansa baƙaramin ruguza masa lissafi yayi ba,  saidai kuma azuciyarsa cike yake da mamakin abun da zai kawota ɗakinsa acikin daren,  tabbas ayau lallai ya yarda cewa da So da kuma sha'awa mataki mataki ne, saboda ya fahimci cewa aso da kuma sha'awar Laylerh ya tafi zuwa wani mataki na daban, babban mataki wanda bakowa ke iya hawansa ba.
Sannan Ayau ya sake tabbatarwa da kansa cewa shi me matuƙar Rauni ne akanta, sannan kuma duk wani fata da burinsa akanta ne, ayayinda jini ke guda ajikin kowa shi ƙaddararsa da ta Laylerh ce ke gudana acikin jikinsa.
A karon farko na gaba É—aya tarihin rayuwarsa kenan dayaji zuciyarsa ta karye da gasken gaske.
Idanunsa dake neman fallasa zallan ɗaci da kuma raɗaɗin dake kwance acikin zuciyarsa ya rumtse da ƙarfi, tare kuma da haɗiye wani yawu me ɗaci da ya tsaya amaƙoshinsa.
Tunowa dayayi cewar Abbou Jaheed ya hanasa komawa USA ne yasa shi jin wani sabon abu ya tokare masa maƙoshi, haƙiƙa ƙaddarori sun kewaye rayuwarsa, saidai ako da yaushe yana fata da kuma burin cimma nasara, domin kuwa har yanzu yana nan akan bakansa cewar bazai taɓa zama Me kasawa ba akullum akuma koda yaushe.
Akaron farko kenan daya fara ƙokarin saka kansa baccin dole, duk da kuwa cewar baccin ya ƙauracewa idanunsa tuntuni, saidai ya zame masa dole ya ƙaƙalo baccin matuƙar yana son tseratar da rayuwarsa daga bugawar zuciya.

Laylerh.
Kanta tsaye tafita daga falon nasa, koda ra fito kuwa anan cikin babban falon gidan ta samu kanta, batare da ta damu da dubun da ya mamaye falon ba ta nufi É—akinta.
Ganinsa yasata jin zuciyarta ta mata sanyi, yayinda duk wani damuwa dake kwance acikin zuciyarta ya yaye.
Tabbas tayi imani cewa. M.Jay É—in daban yake da kowa.
Locking ƙofar ɗakin nata tayi sannan ta koma ta kwanta.
Kasancewar zuciyarta cike take da farinciki hakan yasa bata wani jima ba bacci ya sake É—aukanta.

*(Note editing)*
1/19/21, 8:14 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*(This book is mainly for those that pay, if you know you did'nt pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay-0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz bank. Whatsapp number 07017879464. )*

                 *Chapter 23*

Maleek.
Sama da 20 minute ya ɗauka yana ta faman juyi akan gado, duk yanda ko yaso bacci ya ɗaukesa ya kasa, haƙiƙa  shigowarta cikin ɗakin nasa yasa yayi losing duk wata nutsuwarsa, yayinda ahankali yakejin wani nannauyan kasala na sauƙar masa, again ga kuma  wani sabon hot feelings ɗinta dake sukar duk wata kafar sadarwa na jikinsa, wanda kuma sanadin hakanne ya sashi kasa rumtsawa.
"Yah Maleek."
Sautin amon sassanyar muryar da taƙira sunansa da shi ne ya shiga dawowa cikin kunnensa,   ahankali ya soma tuna yanda take zagaye ƴar yatsar hannunta akan  fatar bayansa, wannan yasa batare daya sani, ko shiryawa hakan ba ya saki wani ƙawataccen murmushin daya bayyana zallar kyawunsa, ahankali ya ɗan lumshe idanunsa, dan so yake bacci ya ɗaukesa tunkan tunaninsa ya koma ga wani fanni na daban.
Duk da cewar zuciyarsa na ƙoƙarin raya masa wani abu na daban, ƙin bata daman hakan yayi saboda ayanzun yafi buƙatar bacci fiye da komae.  Cikin abun da bai wuce 15 minute ba kuwa yayi sa'a  bacci ya ɗaukesa.

Washegari.

9:00 am
Daidai ahankali ta buɗe idanunta wanda suka cika da yanayin bacci, miƙa tayi tare dayin hamma, kana  cikin nutsuwa ta zuro da kyawawan ƙafafunta ƙasa.
Idanunta dake ɗan gane mata dishi dishi ta murza, ahankali ta sauƙo daga kan gadon tare da miƙewa tsaye.
Yanayin yanda taji jikinta ya zama very weak sosai ne ya sa ta ɗan lumshe idanu, tare dasa hannu ta dafe kanta dake ɗan sarawa kaɗan kaɗan, wanda  kuma tuni hakan ya zame mata sabo, dan kusan ko wacce rana idan ta kwanta da ciwon kai take tashi.
Kaitsaye bathroom ta nufa, dan tasan idan tayi wanka zata daina jin ciwon kan.
Ahankali ta murɗa handle din ƙofar bathroom ɗin ta shiga, cikin nutsuwa ta cire rigar baccin dake jikinta, tare da ƙarasawa gaban shower, akasalance ta sakarwa kanta ruwa. Jin sauƙan ruwan shower'n ajikinta ne yasata sauƙe ajiyar zuciya, take kuwa
moment ɗinta na daren jiya ya shiga dawo mata, tunawa da kyakkyawar fuskarsa da tayi ne yasa ta sakin murmushi har saida fararen haƙwaranta suka bayyana, tabbas yanayin na jiya yayi mata dadi sosai,
domin sanadinsa ne yasa takejin zuciyarta wasai, haka kuma acikin kaso É—ari na damuwarta tayi loosing kaso hamsin.
Yanayin yanda ɗumin ruwan shower'n ke sauƙa ajikinta ne yasata lumshe idanunta akaro na barkatai takuma sauƙe ajiyar zuciya.
Yayinda takejin wani ɓangare na zuciyarta, na ƙoƙarin aikawa ƙwaƙwalwarta wasu tunani ma ban banta. Sanin da tayi cewar idan ta biyewa tunanin zata matuƙar ɓata lokacinta ne, yasa take ta soma ƙoƙarin zeroying mind ɗinta.
Wanda hakan yasa tayi wankanta cikin nutsuwa.
Koda ta kammala wankan wani light peach colour ɗin bathrobe tasa ajikinta, saboda  yanayin weather'n garin yasa ana ɗan busa sanyi kaɗan, wani ɗan ƙaramin farin towel ta ɗauka tare da naɗe dogon gashin kanta wanda ke jiƙe da ruwa, anutse ta ƙarasa gaban sink din dake cikin bathroom ɗin, brush tayi haɗe da sake wanke fuskarta, kana cikin nutsuwa ta fice daga cikin toilet ɗin.
Koda ta fito daga cikin bathroom É—in
akan Agogon dake saƙale jikin bangon ɗakin ta sauƙe idanunta
9:30 am daidai da ta gani ne yasa taɗan zaro idanunta waje, don kwata kwata bata kawo aranta cewar ta ɓata lokaci abaccin nata har haka ba, saboda tunda ta tashi tayi sallan asuba ta sake komawa wani sabon bacci, bata tashi ba sae yanzu.
Ganin babu wani wadataccen lokaci ne yasata ɗaukan towel cikin nutsuwa ta shiga goge jikinta, tana gama goge jikin nata kuwa ta ƙarasa gaban dressing mirror.
Wani body lotion me sauƙin ƙamshi ta shafa ajikinta, tare kuma da feshe jikinta da body spray ɗinta me daɗin ƙamshi, wanda ƙamshinsa ke matuƙar samar da nutsuwa, dan irin ƙamshin nan da baifiye tashi bane dashi, dan sometimes ba me jin ƙamshin har sai idan mutum ya samu kusanci da ita sosai ne zai iya jiyo ƙamshin.
Dama kwallia ba aikinta bane, hakan ne kuma yasa bata wani tsaya shafa powder da jambaki ba direcÉ— ta nufi wajen drawer'nta.
Koda ta bude drawer'n wani riga da sket ɗin material me kalan baƙi ta ciro, wanda aka ƙawata gaba ɗaya jikinsa da adon fararen duwatsun
white stones.
Anutse ta sanya kayan da yayi matuƙar amsar jikinta, dan kuwa baƙaramin kyau material ɗin yayi mata ba, yanayin yanda kayan ya lafe ajikinta ne yasa cikakkun hips ɗinta bayyana.
Dogon gashinta dake bin bayanta ta tubke da wani babban ribbom, sake komawa gaban dressing mirrorn  tayi tare da zubawa kanta idanu.
Ita kanta tasan tayi kyau sosai, hakanne ko yasata sakin murmushi,  ita kanta tana mamakin yanda kowani kaya tasa saiya mata kyau, ɗan kwalin material ɗin nata ta yafa akanta, kasancewar kuma yana da ɗan girmane yasa shi sauƙowa har bayanta.
Tun tashinta takejin cikinta na kukan yunwa,  wannan yasa tana gama kimtsa kanta bata tsaya wasa ba ta zura wasu flat shoe masu kalan fari aƙafanta, zuciyarta cike da ɗokin ganin Mr. Beautyful Eyes ɗinta, ta murɗa handle ɗin ƙofar ta fita.

Zaune suke dukansu akan dining table É—in cikinsu kuwa harda Najeeb.
Wanda shigowarta cikin falon yayi daidai da ɗago kansa da yayi, take kuwa ya sauƙe idanunsa akanta.
Wani irin kyau'n da yaga tayi masa ne ya sashi dan lumshe idanunsa tare da sauƙe ajiyar zuciya.
Laylerh kuwa ganinsa da tayi ne yasa ta sauƙar da kanta ƙasa, tare da ƙarasowa kan dining table ɗin.

Ganin Laylerh'n ne yasa Oum Ayush sakin murmushi, cikin kulawa tace.  "Laylerh kin tashi?."
Murmushine ya bayyana akan fuskarta, ahankali taɗan jinjina kai alaman "Eh" ɗago kanta tayi tare dakai dubanta zuwaga su Abbou Jaheed dake zaune, cikin nutsuwa ta gaishesu, inda suka amsa mata fuska asake, Abbou Kareem ne ya ɗago kai ya dubeta, cikin yanayin tsokana yace. "Sarkin shagwaɓa har antashi?."
Murmushi me kama da dariya tayi  cikin nutsuwa da kuma bayyana  farincikin dake ranta tace.  "Eh Abbou nah na tashi, saidai kuma kwana nayi ina mafarkin chocolate ɗin dakace kakawomin.."    Dariya sukayi dukansu, cikin kulawa Abbou Kareem ɗin yace.  "To bari mugama cin abinci saina ɗauko miki." 
"To." tafaɗa cikin jin daɗi, dan tasan chocolate ɗin dayake kawo matan daɗinsu na musammne 

Juyowa tayi tare da gaishe da Oum Ayush, fuska ɗauke da murmushi Oum Ayush ta amsa mata, tare da tambayarta yanda ta kwana, da "Lapia." ta amsa mata kana ta juya ta gaishe da Momy,  ganin su Abbou Kareem ɗinne yasa Momyn ta amsa mata cikin sakin fuska.
Chapter 43 · 0% Book details