← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 144

Sashe 80

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Jin ficewar Fou’ad d’inne kuma yasa shi bud’e idanunsa ahankali.
K’ofar office d’in ya k’urawa ido, kamar me nazartar wani abu, yayinda acikin zuciyarsa kuwa tunani yake daban daban, akan auren da Abbou Jaheed ke k’ok’arin lik’a masa, saidai kuma kaman yanda yake har acikin zuciyarsa baya son auren, haka baya tunanin zai shiga koda hidima d’aya ne da za’ayi abikin hasalima ko ganinsa babu me sakeyi, daga Abbou Jaheed d’in har kowa.
Kyakkyawan idea d’in daya zo masa ne yasashi mik’ewa tsaye, ahankali ya k’arasa gaban wani d’an sif da yake aje abubuwansa masu amfani, wata bak’ar jaka ya d’auko tare da bud’e ta ya zuba duk wasu abu nasa masu amfani nasa aciki.
Wayarsa dake kan table ya d’auka, kaitsaye kuma ya fice daga cikin office d’in nasa.
Koda ya fito daga office d’in nasa duk inda ya wuce soldiers ne ke sara masa, yayinda sauran soldiers d’in da suka kasance securities d’insa suka take masa baya.
Direct babban compound d’in wajen da yake kaman camp d’insu ya fito, Abdoul dake zaune yana ganin Ogan nasa ya taho da sauri.
Saidai kafun ma ya k’araso Maleek d’in yayi masa alama akan ya tada mota, take kuwa ba b’ata lokaci ya shiga motar ya tayar.
Kamar yanda ya saba gidan baya ya shiga, bayan ya dakatar da sauran soldiers d’in dake take masa baya, ta hanyar nuna musu cewar yau d’in b’aya buk’atar rakiyar kowa.
Sanin halinsa da sukayi ne kuma yasa duk suka dakata.
Abdoul kuwa a 360 yaja motar suka bar farfajiyan wajen gaba d’aya.
Saeda sukayi d’anyi nisa atafiyar tasu kuwa kafun Maleek d’in ya fad’awa Abdoul d’in inda yakeso ya kaesa.
Kaitsaye kuwa can d’in suka nufa, wato Maitama Estate, inda acan b’oyayyen gidan na Maleek yake, wanda ko su Abbou Jaheed d’in basu san dashi ba, yayi gidanne kuma musamman dan hutawa, saboda dama shi ba mutum bane me son hayaniya, kasancewar sa soldier kuma shiyasa ako da yaushe yake matuk’ar son privacy.
Isowarsu katafaren gate d’in gidanne yasa Abdoul fitowa daga cikin motar ya wangale had’add’en gate d’in, saboda babu maigadin da zae bud’e musu.
Bayan sun shiga cikin gidan da yake kaman aljannar duniya ne kuma Abdoul ya koma ya rufe gate d’in.
Zuwa lokacin kuwa Maleek ya fito daga cikin motar.
Kallon Abdoul d’in yayi, cikin halinsa na ko da yaushe fuskarnan babu alaman dariya yace.
“Banason kowa yasan inanan, idan nace kowa kuma Ina nufin harda mahaifina, da kuma Fou’ad, sannan ka tabbatar kana kulawa da cutie yanda ya kamata, kana bata abinci sosae.�
“Okay Sir.� Abdoul ya fad’a ahanzarce yana me d’an jinjina kansa, alaman yaji.
Baisake cewa komae ba kuwa ya juya kai tsaye ya nufi cikin gidan.
Abdoul kuwa juyawa yayi ya fice daga cikin gidan baki d’aya.
K’arasowansa cikin had’add’en falon wanda ko wani kusurwa na cikinsa ke d’auke da hotunan Laylerh da yayi ne yasashi d’an lumshe idanunsa tare da sauk’e wata sassanyar ajiyar zuciya, hakanan yaji wani irin sanyi na ratsa gaba d’aya jikinsa, har zuwa tafin k’afarsa, wannan yasa
ahankali ya shiga takowa har zuwa tsakiyan falon da had’uwarsa ya zama abun burgewa.
Akan d’aya daga cikin hotunan nata ya sauk’e idanunsa, wanda take sanye da wani riga da sket na atamfa, tana zaune ne kuma ak’asan carpet, yanayin yanda fuskarta ya kasance acikin hotonne kuma yasa duk wanda ya kalla zaigane cewar tana cikin yanayin damuwa ne aka d’auki hoton.
Idanunsa ya k’urawa hoton nata baya ko k’iftawa, domin a irin yanayin da fuskar nata ke ciki haka shima yanzu yakeji acikin zuciyarsa.
Janye idanunsa daga kan hoton nata yayi, kana asanyaye ya zauna akan d’aya daga cikin had’add’un original royal cushions d’in dake cikin falon.
Hannunsa yakai yad’an shafa idanunsa, adaidai lokacin da suka sauk’a akan hoton mahaifiyarsa dake cikin falon.
Akaron farko kenan da murmushi ya bayyana akan fuskarsa, take kuma yaji zuciyarsa ta karye, hakanan yaji wani abu me kaman ruwa na neman cika masa idanu, wannan yasa shi saurin d’auke kansa daga kallon hoton, y’ar k’aramar jakar da ya shigo da ita ya jawo, tare da bud’e ta ya ciro wani Ledan cocaine.
B’ud’e ledan yayi tare dakai hancinsa ya shak’i cocaine fowder d’in ta yanda har saida yajita acikin kansa.
Haka ya lumshe idanunsa tare da ci gaba da shak’an cocaine d’in har saida yajisa acan sararin samaniya, cikin wata duniya ta daban, duniyar imagine.
Shi kad’ansa haka yayita bulayi acikin falon hardai ya zamana ma hankalinsa yabar jikinsa, inda yatafi wata duniya ta gushewan hankali me kama da bacci.

After 2 days
Acikin kwana biyun nan gaba d’aya mood d’in Laylerh ya sanja, domin tunda taji maganan auren Maleek ta kamu da wani irin zazzab’i me zafi, ga kuma ciwon maran period dake damunta, abu kaman wasa kuwa sai gashi takai ga kwanciya, acikin Kwanaki biyun kuwa Najeeb koda sau d’aya baisake zuwa mata da wata buk’atarsa ba, koda kuwa romancing d’inta ne, saidai kuma yana iyaka bakin k’ok’arinsa wajen bata kulawa.
B’angaren su Oum Ayush da Abbou Jaheed harma da Fou’ad kuwa shirin biki sukeyi sosae, hakama b’angaren gidansu amarya, sukamma abunnasu yafi na kowa, Dan tuni amarya munnira ta fara karb’an gyaran amarya, yayinda tabi kan k’awayenta tasanar musu irin mijin da zata aura, kyau da had’uwa had’i da matsayinsa duk ba wanda ta b’oye musu, hakanne kuwa yasa suka k’ara fasa mata kai, hakan yasa takejin kanta tafi kowa.
Awajen Momy kuwa har yanzu wasu makirci take shirin k’ullawa, saidai kuma jin Maleek d’in zaiyi aure ne yasa ta sauya akalan makircin nata zuwa wani waje na daban.

(Uhummm su Maleek za’a angwance 😝 Insha Allah Gobe zaku samu update saboda da yardar Allah Mungama biki yanzu Ina free, duk dama ankoma school amma hakan ba damuwa bane.)

*31January/2021*
2/2/21, 8:42 AM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*Chapter 46*
Chapter 80 · 0% Book details