Sashe 74
Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Tunda suka kama hanyan unguwan na Wuse Zone 3, idanunsa ke kan titunan da suke ta wucewa, tabbas azahirance kuwa idan ka kallesa zakayi tunanin cewa gaba d’aya hankali da nutsuwarsa naga titin ne, saidai kuma sam bahaka abun yake ba, tabbas idanunsa titunan suke kallo, amma tunaninsa da kuma zuciyarsa ba’anan suke ba, domin tun fitowansu daga gida abu d’aya ne ke yawo acikin tunaninsa, shine maganar Auren da Abbou Jaheed d’in yace zai masa.
Sam zuciyarsa bata gaya masa gaskiya akan auren, yayinda ajikinsa kuwa yakejin kamar wata sabuwar k’addara ne ke shirin tunkarosa, k’addaran da zata sauya masa gaba d’aya rayuwa.
Babban abunda yake tambayar kansa kuwa shine. “Agaba d’aya rayuwarsa tayaya zai fara zama da wata mace amatsayin matarsa? tayaya zai iya had’a shumfud’a da wata ta daban?�
Sam bayajin yiwuwar hakan, saboda yasan so ana ginasa ne azuciya, idan kuma yayi k’arfi sai ya mamaye dukkan sassan jiki, tabbas auna mizanin abunda ka taso kanaso daban yake da wanda zakazo agaba ko kuma ayanzu, sannan kuma kowani irin soyayya takan iyayin tsuntsuwa tatashi amma Banda soyayyar da aka halittata acikin jini da tsoka, wannan so d’in baya tab’a fita har abada.
Auna mizanin son da yakeyiwa Laylerh kuwa abune, me matuk’ar wahala, saboda ya gina gaba d’aya rayuwarsa ne akan soyayyarta, Hak’ik’a ya raini sonta acikin zuciyarsa tun tana k’arama, tsari yanayi dama body structure d’inta yayi masa yanda yakeso, saboda haka bayajin cewa akwae wata mace aduniyarnan da zaigani ya kwad’aitu da ita ko kuma tashiga ransa idan ba Ayshnoor d’insa ba.
Idanunsa ya lumshe adaidai lokacin da yaji driver’n na danna horn d’in motar, wanda kuma hakan alamane dake nuna cewar sun iso inda zasu je.
Ko minti 1 ba ayiba kuwa aka wangale musu babban gate d’in gidan dayaji had’uwa, wanda dagani kasan cewar gidan attajirin maikud’i ne.
Anutse driver’n ya kutsa hancin motar cikin gidan.
Jin tsayuwar motar ne kuma yasa shi bud’e idanunsa wanda suka d’an sanja kala.
Daidai lokacin kuwa Alhaji Farouk wato abokin Abbou Jaheed ya k’araso wajen motar tasu da gaggawa, fuskarsa d’auke da murmushi kana kuma cikin mutuntawa ya bud’ewa Abbou Jaheed murfin motar ya fito, mik’a masa hannu Abbou Jaheed yayi sukayi musabaha.
Ganin hakanne kuma yasa Maleek d’inma bud’e murfin motar ta b’angaren da yake ya fito.
Kallonsa Alhaji Farouk yayi cikin sakin fuska da walwala yace.
“Captain Maleek Gwani sannu da zuwa.�
Sanin cewa Alhaji Farouk d’in abokin babansa ne, kuma mutum me mahimmanci ne awajen Abboun sa yasashi d’an bayyana murmushi akan fuskarsa, cikin muryarsa da ako yaushe take tafiya da aji yace.
“Yauwa barka da gida.�
Murmushin fuskar Alhaji Farouk d’inne ya fad’ad’a, cikin halinsu na y’an boko bawani surukunta ya mik’owa Maleek d’in hannu suka gaisa.
Cikin son nuna zallan farincikin dake ransa, da kuma murnar ganinsu agidan nasa yace.
“Masha Allah Bismillah mu isa daga ciki.�
Babu musu kuwa suka rufa masa baya, saidai kuma Maleek kam ko kad’an baiso hakanba, sanin da yayi cewa idan sun shiga ciki d’in surutu su Abboun zasu tayi, shikuma Sam Ko kad’an bayason damuwa, amma gudun kada ya b’ata ran Abbou Jaheed yasashi rufa musu baya.
Kaitsaye babban falon Alhaji Farouk inda yake sauk’e bakinsa na musamman suka nufa.
Koda suka k’arasa cikin falon kuwa sake gaisawa sukayi, inda kuma Buzuwa wato matar Alhaji Farouk d’inkenan ta shigo suka gaisa, tun shigowarta kuwa ganin Maleek d’in yasa take ta sakin murmushi, domin dama Alhaji Farouk ya fad’a mata komai agame da had’a auren Maleek d’in da tilon Y’arsu, wanda kuma hakan bak’aramin nasara da d’aukaka zai jawo musu ba, domin sun san had’a zuri’a da Alhaji Jaheed Gwani ba k’aramin girma da k’ima zai k’ara musu awajen mutane ba.
Bata kuma sake yarda da hakan ba sai ayanzu da tayi ido hud’u da Maleek d’in, wanda ta tabbatar cewa idan y’arta tasamu daman aurensa to bak’aramin sa’a tayi ba, ko shakka babu kuwa sai y’arta tazama autar mata, sannan kuma lokacin arzikin yarinyar nata ya soma, dan musamman tasa akayi mata bincike akan Maleek d’in da kuma irin tarin dukiyar da ya mallaka wanda shi kansa baisan iya adadinta ba, tabbas ya had’a komae na more rayuwar duniya, ga kyau ga to kud’i.
Shikuma Maleek ganin matar da take matsayin wai uwar wacce zai aura, yasa lokaci d’aya yagano wani irin zab’ine Abbou Jaheed d’in yayi masa.
Fuskarsa ya kwab’e tare da tab’e bakinsa, acikin zuciyarsa yace.
“Banji ajikina cewar zan rayu da wani tsatso na gidannan ba, because a irin gidannan ba asamun choice d’ina.�
B’angaren Buzuwa kuwa jikinta yana b’ari tasa aka cika gaban su Captain Maleek d’in da kayan sha dana ciye ciye.
Saidai Maleek ko ruwa bai shaba bare ma yace zaikai wani abu bakinsa.
Abbou Jaheed kuwa sanin abunda suka shirya shida abokinnasa ne yasa su mik’ewa tsaye suka fice daga cikin falon.
Inda suka bar Maleek d’in zaune, M.Jay kuwa ganin sun barsa shi kad’aine yasashi zaro wayarsa k’iran iPhone12pro dake cikin aljihunsa ya soma dannawa.
After 10 minutes.
Ahankali aka turo k’ofar falon aka shigo, wata matashiyar budurwace wanda bazata wuce 23 years bane ta shigo, sanye take cikin wani tsadadden atamfa wanda yaji d’inkin riga da sket, ak’afanta kuwa wani uban takalmi ne me tsini, duk da cewar kuma tana da tsayi amma takalmin ya k’ara mata tsayi, yanayin yanda kayan jikinnata suka kamata ne kuma yasa d’an k’aramin surar jikinta bayyana, kaitsaye za’a iya k’iranta da fara amma ba irin farinnan na turawa ko larabawa ba farin buzaye, akan fuskarta kuwa meckup ne kwance wanda dagani kasan anb’ata lokaci ana zana shi, bata da wasu manyan ido, sannan kuma bata da tsayin hanci sosae, haka kuma bata da babban baki, tabbas ga wanda baisan kyauba idan ya ganta zai iya k’iranta da kyakkyawa, amma kuma abad’inance ba haka abun yake ba, domin kyaun nata bawani kyau bane, saidai kawae tana da yanga.
Munnira kenan y’a d’aya tilo awajen Alhaji Farouk, yarinya mejin kanta da wayewa kasancewar a k’asar syprus tayi karatunta na degree.
Tabbas ayangance ta shigo cikin falon tana me taunar chewing gum abakinta, yayinda take ta faman baza k’amshi, saidai kuma sam babu wani mayafin kirki ajikinta.
Shigowarta cikin falon da kuma sauk’e idanunta akansa da tayi ne, yasa ta tsayawa cak yayinda taji wani irin abu mekama da shock ya shiga jikinta.
Sallaman da take k’ok’arin yine ya mak’ale abakinta adaidai lokacin daya d’ago kansa, Dan ganin ko waye ya shigo cikin falon.
Kusan fad’uwa Munnira tayi saboda tozali da tayi da kyakkyawar fuskar da aduniya take mafarkin ganinta face to face, fuskar da sau d’aya ta tab’a ganinta ajikina jaridar Daily Trust, fuska mafi tsadan gani da kyau, tabbas zata iya cewa tunda take aduniya bata tab’a ganin Namiji me kyau da had’uwarsa ba.
“Handsome� Tafad’a acikin zuciyarta saidai kuma batasan cewa maganar nata ya fito fili ba.
Kallo d’aya kawai yayiwa tsigau fiyau d’in da yagani agabansa ya kau da kai, tare da cigaba da latsa wayarsa, cikin zuciyarsa yace.
“Allah kasa ba wannan tsigau fiyau’n Abbou Jaheed ya kawoni na aura ba.�
Munnira kuwa ganin da tayi ya d’auke kansa daga kallonta ne yasa, ta k’arasowa cikin falon, cike da d’okin ganin had’add’en Namijin dake gabanta, da k’yar ta had’o kalaman bakinta wajen fad’in
“Sannu da zuwa.�
Shiru yayi tare da shareta yayi kamar baiji abunda ta fad’a d’inba.
Ganin haka kuwa yasa duk saitaji guiwowinta sunyi sanyi, saidai kuma amatsayinta na gwanar rawan kai kasa yin shiru tayi cikin son jin muryarsa tace.
“Ina wuni�
Again shareta yayi bai d’ago kansa bama bare ya amsa mata.
Still kuwa Munira bata daddara ba, zama tayi akan kujeran dake facing nasa, cike dason nuna masa ita wayayyace tace.
“Please say something kodai bakajin Hausa ne, nayi maka magana da English?�