← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 144

Sashe 21

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Acan falon Abbu kuwa Alhaji Ahmad ne da Abbu zaune, akan lallausan darduman da ya ƙawata tsakiyan falon.
Cikin nutsuwa Abbu ya É—ago kai ya dubi Alhaji Ahmad dake ta faman aikin duba wasu files dake gabansa.
Gyara zama Abbu yayi tare da sakin ajiyar zuciya.
Cikin  muryarsa da tayi sanyi yace. 
"Nasa ka auren Laylerh nan da 1 month."

ÆŠago kai Alhaji Ahmad yayi tare da É—an sakin murmushi,cikin halin dattako yace.
"Tabbas nasan da hakan Alhaji Jaheed, saidai bansan meyasa kaketa yawan maimaita hakan ba tun É—azu."
Ajiyar zuciya Abbu ya sauƙe tare da cewa.
"Bansan Ya Laylerh zata ɗauki abun ba, saboda har yanzu ita ɗin yarinyace, tabbas nasan ba zataƙi zaɓina ba, saidai kuma bansan me yasa nakejin faɗuwar gaba agame da hakan ba inajin kamar akwai wani gurbi daban cike ba."

Murmushi Alhaji Ahmad Rufa'e yayi tare da ɗan bubbuga kafaɗan Abokin nasa cikin kulawa tare dason basa ƙarfin guiwa yace.
"Insha Allah bakayiwa Laylerh zaɓen tumun dare ba, ina me tabbatar maka da cewar kamiƙa Laylerh a inda za'a kula da ita namaka alƙawari cewa Laylerh bazatayi kuka ba, kai Uba ne nagari kuma kayi abun daya dace."

Murmushi Abbu yayi tare da miƙewa tsaye yaɗan soma zagaye falon, cikin son ƙarfafawa kansa guiwa da kuma cika alƙawarin daya ɗauka yace.
"Insha Allah nima haka nake fata."

Maleek.
Shigowarsa cikin falon kenan, kaitsaye ya nufi dining area, kujera yaja ya zauna tare da cire facing cap din dake kansa, murfin bootle water'n dake hannunsa ya buÉ—e tare da juye ruwan dake cikin goran akansa, sanyin ruwan daya ratsa sa ne ya sashi kifa kansa akan table tare da sakin ajiyar zuciya.
Laylerh fitowarta daga kitchine É—in kenan hannunta É—auke da plate É—in indomie'n da ta dafa.
Kaitsaye danning area ta nufa, idanunta akan indomie'n nata har ta ƙaraso dinning ɗin.
Ƙamshin turarensa da tajine yasata ɗaga idanunta, take kuwa ta sauƙe ganinta akansa.
Kallonsa da tayi kuwa yayi daidai da É—ago kansa da yayi.
Akaron farko kenan da tafara sa idanunta acikin nasa kusa da kusa.
Wani irin matsanancin shock ne ya shigeta asakamakon hakan, lokaci ɗaya gaba ɗaya jikinta ya fara kakkarwa, kanta ta shiga girgizawa yayinda laɓɓan bakinta suka soma vibrating, ɗan jan jikinta baya tashiga yi, aruɗe ta saki plate ɗin dake hannunta, tare da sakin wani razanannen ƙara.

*(Menene buƙatar Najeeb akan  Laylerh? sannan kuma me yakeso awajenta? wani buri yakeson cimmawa akanta? Aurenta yakeson ko kuwa wani abu yakeso awajenta na daban? WANENE MIJIN DA ABBU ya zaɓawa Laylerh? Me kuma Momy zata aikata akan Laylerh? Miye Laylerh ta gani akan fuskar Maleek daya ke ƙoƙarin fitar da ita a hayyacinta?  Lallai Tabbas akwai wani abu, BURI ƊAYA ne ke yawo da kuma gudana acikin zuciyar Laylerh da kuma Maleek. Shin Laylerh Mallakin Wayene acikin MALEEK da NAJEEB? Kada ku manta tun da farko nafaɗa muku cewa ba irin yanda kuke tunani bane, cos ba amayi komai ba, ko wasan ma ba a fara ba.)*

*Karku manta game buƙata zata turo katin MTN na 300 ko kuma ta turo 300 ta account number.*

*Whatsapp number 07017879464*

*Account number 0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Ja'iz Bank.*

*Thank You*

      *fatymasardauna*
1/19/21, 8:11 PM - Ummi Tandama:   🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
       *LAYLERH MALEEK*

     *Writing By*
*fatymasardauna*

*(Wannan littafin na kuÉ—i ne, kada ki karanta idan kinsan baki biya ba, zaki iya turo kuÉ—inki 300 ta account number 0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna. Whatsapp nomber 07017879464)*

       *Chapter 11*

Hannayenta ta sanya tare da toshe kunnuwanta, wanda hakan yasa indomie'n dake cikin plate ɗin zubewa akan ƙafanta.
razanannen ƙaran da ta saki ne yayi daidai da shigowar Abbu cikin falon.    
Yanayin yanda jikinta ke ta faman karkarwa ne yasa ƙafafunta ƙoƙarin kasa ɗaukanta, take tatafi luu zata faɗi.  
Cikin hanzari ya sanya hannunsa ya tallafota ta faɗa jikinsa, take wani irin shock ya shiga yawo ajikinsa,  kyawawan idanunsa ya sauƙe akan cute face ɗinta, tare da kai dubansa ga lips ɗinta daketa faman ɓari.     
"Hey!."  Ya faɗa cikin wata irin haɗaɗɗiyar lion voice ɗinsa, wanda dadin sauti da amonta ya ratsa cikin kunnuwanta.
Wani irin sassanyar iska ne ya shiga ratsa dukkan illahirin jikinta, sannu ahankali ta soma sakin numfashi, tare da É—an bude kyawawan idanunta wanda lokaci daya suka bayyana asali da kuma zallar kalansu na sexy eyes.
Adisashe ta soma ganin kyakkyawar fuskarsa, tare da jefa idanunta acikin nasa,  lokaci daya taji kwakwalwarta na kokarin birkicewa, tabbas wayannan idanun da take gani ayanzu sune idanun da tajima tanaso da kuma burin gani agaba daya rayuwarta, wayannan idanun sune idanun da suka zama kaman abincin ruhinta, mafarkinta da kuma dukkan fatan ta.
Wani irin zubawa tsikar jikinta ya shiga yi, hakan yasa sexy eyes dinta soma lumshewa, take kuwa hawaye suka soma gangarowa daga cikin idanun nata.
Tabbas bazata iya jurewa yanayin da takejin kanta aciki ba, haka nan takejin duniyar na juya mata.
Narkakkun idanunsa masu oily ya zuba mata, domin ya lura da tana kokarin fita cikin hayyacinta ne.     Fuskarsa dake dauke da danshin ruwa ya hade, cikin husky voice dinsa yace.
"Ke what's wrong?". Shiru tayi tare da sake sakar masa jikinta, ganin da yayi cewar batayi motsi bane ya sashi zare hannunsa dake bayanta,  wanda dama hannun nasa ne ke riƙe da ita.
Sakinta da yayine yasa tatafi luu zata faÉ—i.
"MALEEK!". 
Abbou da tun ɗazu yake tsaye yana kallonsu ya kira sunansa, jin muryar Abbou'n acikin kunnensa ne ya sashi saurin sake riƙota, hakanne yasa bata kae ga faɗuwa ƙasa ba.       
Ƙarasowa dining area ɗin Abbou Jaheed yayi, gaba daya fuskarsa babu alaman walwala.
Kallon Maleek ɗin yayi tare da kau da kansa gefe  "Me kayi mata?" Ya tambayi Maleek ɗin yana me kallon Laylerh'n.
Kyawawan fararen idanunsa yadan zaro, tare da rolling dinsu alaman
"Me nayi mata kuma?."
Fuska Abbou ya haɗe tare da cewa.  "Tabbas ruwa baya tsami banza, ni nasan cewa Laylerh bazata taɓa faɗuwa haka kawai ba, dole saidai wani abu tagani daga gareka.".             Jin hakane ya sashi sakin murmushin da shi kaɗai ya baiwa kansa sanin ma'arsa, ahankali ya ɗago ya kalli Abbou'n, kaman zaice wani Abu kuma sai ya kuma maida kansa kasa.

Laylerh da gaba daya ta Shiga shock din ganin idanunsa, jin muryan Abbou Jaheed akunnenta ne yasa ta fashewa da kuka, lokaci daya taji gaba daya zuciyarta tayi rauni.      
Ganin yanda ta fashe da kuka ne ya sashi lumshe idanunsa, lokaci daya yasa tafukan hannunsa ya rufe fuskarsa.
Hannun Laylerh'n Abbou ya kama tare da dagota tsaye cikin kulawa yace.
" Stop crying Laylerh, faÉ—amin me ya miki kike kuka?."
Kanta ta Dan shiga girgizawa tare da kokarin shanye hawayen dake idanun nata.
Hannunta Abbou ya kama tare da zaunar da ita akan daya daga cikin kujerun falon.
Kallon ƙafarta yayi wanda tuni fatar wajen ya somayin ja, saboda yanda zafin indomie'n ya kama fatar ta.
Chapter 21 · 0% Book details