← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 144

Sashe 52

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ÆŠaya daga cikin doctors É—inne ya kalli agogon dake É—aure a tsintsiyar hannunsa, wanda ke nuna 3 minute kacal ya rage musu, akasin haka kuwa zasu iyayin losing É—insa.
Duk wani iya ƙoƙari da basirarsu sunyi amma shiru, saidai kuma ganin da sukayi cewa, da gaske zasu iya rasashi ne yasa suka ƙara dagewa wajen ganin dawowan numfashinsa, dan ta hakane kaɗai bugun zuciyar tasa zata daidaita.
Wani na'ura da suka ɗaura masa akan aƙirjinsa ne yasa shi jan wani dogon numfashi me ɗauke da yanayin nishi.

Amamakance jin yanda yaja dogon numfashin ne yasa su maida idanunsu ga wata ƴar ƙaramar abu me kaman computer dake gabansu.
Ahankali suka ga numfashin nasa na ƙoƙarin dawowa, yayinda take zuciyarsa fara ɗan motsi da harbawa.
Ajiyar zuciya suka sauƙe su dukansu, domin hakan alamace dake nuna zallan nasara, dan ba kaɗan ba shawo kan matsalar tasa ya basu wuya.
Handglobes É—insu suka soma cirewa yayinda wasu daga cikinsu suka turo gadon da Maleek din ke kwance zuwa wani special room.

Acan waje kuwa hankalin su Abbou Kareem amatuƙar tashe yake, kasancewar dukansu basu san awani hali Maleek din ke ciki ba.
Aɓangaren Abbou Jaheed kuwa ko zama ya kasayi, kallo ɗaya zaka masa kafahimci cewa yafi kowannensu shiga tashin hankali, yayinda aransa yake ta fata da kuma addu'an samun sauƙin ɗannasa, kasancewar shi kaɗai ne ɗan daya ke dashi guda ɗaya aduk faɗin duniya, saboda haka bazai taɓa son wani abu da zai cutar dashi ba.

Dr.Hafeez da kuma Dr.Al-bashir wanda fitowarsu daga emergency room ɗin kenan, ganin su Abbou Jaheed atsaytsaye cikin tashin hankali ne yasa suka ƙaraso garesu.
Ganin Doctors É—inne yasa su Abbou Jaheed zuba musu ido, kowannen su zuciyarsa cike da tarin fargaban abun da kunnuwansa zasu jiyemai.
Ganin yanda tashin hankali ya bayyana ƙarara akan fuskokinsu ne yasa.
Dr.Hafeez sakin murmushi, cikin son ƙarfafa musu guiwa yace.   "Alhamdulillah ku kwantar da hankalinku, domin da izinin Allah Nida abokan aikina munyi nasarar ceto rayuwar Maleek."

Tamkar sauƙan ruwan sanyi haka su Abbou Jaheed sukaji kalaman Dr.Hafeez, sanadin hakan kuwa yasa suka sauƙe wani irin ƙatuwar ajiyar zuciya, da ke bayyana tsananin jin daɗinsu.
Take kuwa cikin tsananin zumuÉ—i da zallar farinciki Abbou Jaheed yace.
"Alhamdulillah Allah, Yanzu Dr.Hafeez ina Maleek É—in yake? ya buÉ—e idanunsa kuwa?."

ÆŠan girgiza kai Dr.Hafeez yayi, inda Dr.Al-Bashir ya gyara tsayuwarsa, kana cikin kulawa yace.
"Munkaisa É—akin hutu na musamman, saidai har yanzu bai buÉ—e idanunsa ba, amma hakan bazai zamo wani abun damuwa ba, insha Allah koda yaushe zai iya buÉ—e idanunsa, ya kuma dawo cikin hayyacinsa."

"Alhamdulillah!!."
Dukansu suka haÉ—a baki wajen faÉ—an hakan, domin ba kaÉ—an ba sukaji dadin kyakkyawan labarin da su Dr.Hafeez É—in suka kawo musu, wanda hakan yasa zuciyoyinsu yin sanyi.
"Amma kana ga zamu iya ganinsa yanzu kuwa Doctor? "
Abbou Kareem ya tambaya.

Kai Dr.Hafeez ya girgiza cikin kulawa yace.
"Agaskia yanzu yana buƙatar hutu sosai, duk dama bai gama dawowa hayyacinsa ba, so inaga zaifi kyau ku bari sai nan da cikakken 1 hour, kafun nan brain ɗinsa ta sake hutawa, saboda sai brain ɗinsa ta samu nutsuwa sosai, kafun bugun zuciyarsa zai cigaba da tafia daidai."
Jin hakanne yasa su jinjina kae, cike da gamsuwa da kalaman Dr.Hafeez É—in.
Duban Abbou Jaheed Dr.Hafeez yayi, anutse yace.   "Please Alhaji ina son ganinka a office."
Da "To"
Abbou Jaheed ya amsa, nan kuwa su Dr.Hafeez É—in sukayi gaba shi kuma ya rufa musu baya.
Yayinda Abbou Kareem da Alhaji Ahmad da kuma Fou'ad suka samu guri suka zauna, anan kan wasu bench zuciyoyinsu cike da nutsuwa.

Abbou Jaheed kuwa kaitsaye Office ɗiɓ Dr.Hafeez suka wuce.
Koda suka ƙarasa cikin office ɗin kujeran da aka tana da musaman dan zaman baƙi, Dr.Hafeez ya nunawa Abbou Jaheed, alaman ya zauuna.
Gane abun da Dr.Hafeez É—in ke nufi ne yasa Abbou Jaheed jawo kujeran ya zauna, tare da maida dubasan ga Dr.Hafeez.
Gyara zama Dr.Hafeez yayi haɗe da sauƙe ajiyar zuciya.
Wani file ya ɗauko yayu rubutu aciki, bayan ya gama ne kuma ya ɗago ya kalli Abbou Jaheed cikin nutsuwa yace. 
"Please Alhaji dama Maleek yana É—auke da wata damuwa ne, wanda ta jima tana damunsa?."
Kai Abbou Jaheed ya girgiza, kana cikin sanyin jiki yace.  
"Agaskiya Dr. Bana tunanin haka, saboda a iya sanina da shi, baya sakewa da jama'a bare kuma har damuwarsu ta dameshi."
Ajiyar zuciya Dr.Hafeez yayi, kana yace.
"Babu wata damuwa Insha Allah Zai samu sauƙi, saidai kuma agaskiya yana da buƙatar kulawa sosai, dan akwai buƙatar hanasa yawan tunani, domin matuƙar yana sa damuwa aransa da kuma yawan tunani to fa wani abunne na daban zai iya kamasa, wanda magancesa bazai zo mana da sauki ba, sannan ya kamata aguji ɓata masa rai, domin samun kansa acikin bacin rai shima abune da zai iya jawo masa babbar matsala."
Kai Abbou Jaheed ya jinjina tare da faɗin. 
"Insha Allah zamu kiyaye."
Hannu Dr.Hafeez ya miƙa masa sukayi musabaha, tare da tabbatar musu da cewar akowani lokaci Maleek ɗin zai iya dawowa hayyacinsa, duk dama sunyi masa allurai masu ƙarfi, saidai ganin yana da ƙarfin jini yasa suka sa tsammanin cewa zai iya dawowa hayyacinsa anan kusa.
Koda Abbou Jaheed ya fito daga office É—in Dr.Hafeez, direct wajen daya bar su Abbou Kareem ya nufa.
Kallon Abbou Kareem da kuma Alhaji Ahmad, harma da Najeeb wanda ya iso wajen bada jimawa ba yayi, ganin kaman akwai damuwa akan fuskarsu ne ya sashi nemo ƙwarin guiwa ya azawa kansa, cikin kulawa ya dubi Fou'ad dake zaune wanda ya zuba tagumi. 
"Fou'ad."  Yaƙira sunansa, hakanne yasa Fou'ad din ɗago kai ya kalli Abbou Jaheed ɗin.
"Ka zauna dashi, mu zamu koma gida kasan munbar mutanen gidan cikin tashin hankali, ga kuma Laylerh itama ba lafiya ne da ita ba."
Cike da gansuwa Fou'ad ya jinjina kai alaman "To."
Abbou Kareem kam har acikin ransa baiso tafiya ba, saidai ganin Abbou Jaheed din dakansa ne yace su tafi yasashi amincewa, nan suka shiga motarsu suka kama hanyar dawowa gida.

Gida.
Ahankali ta soma ɗan buɗe idanunta wanda sukayi luhu luhu, kana kuma suka ƙanƙance, jin kaman an ɗaɗɗaure mata jijiyoyin jikinta ne yasa ahankali ta soma ƙoƙarin motsa hannunta.
Oum Ayush dake zaune agefenta ganin ta fara motsi ne yasa ta zuba mata ido, ahankali cikin sanyin murya ta ƙira sunanta.
Jin muryar Oum Ayush acikin kunnenta ne yasa ta ƙarasa buɗe idanunta, ƙoƙarin amsa ƙiran da Oum Ayush ɗin tayi mata take, saidai kuma ta kasa, saboda yanda taji laɓɓan bakinta sunyi mata nauyi.
Ahankali ta soma ɗan jan jikinta, kasancewar so take ta tashi zaune, duk da kuwa batajin wada taccen ƙarfi ajikinta.
Ganin tana yunƙurin tashi ne yasa Oum Ayush kamo kafaɗunta tare da taimaka mata ta ɗan jingina bayanta ajikin gadon.
Cikin kulawa Oum Ayush ɗin tace.  "Sannu ko ya jikin naki?."
Kanta ta jinjina alaman da sauƙi, gefen fuskarta Oum Ayush ta shafa, cike da tausayinta tace.   "Yanzu ina ne ke miki ciwo?."
Kai ta ɗangirgiza ahankali takai hannunta daidai saitin ƙirjinta, wanda da dukkan alamu nan ɗinne ke mata zafi.
Fahimtar cewa ƙirjin nata ne kaɗai ke mata ciwo yasa Oum Ayush duban Aunty Zee cikin kulawa tace.  "Zee haɗo mata tea yanzu tasha please."
"to" Aunty Zee ta faÉ—a take kuwa cikin gaggawa ta fice daga cikin É—akin.
Mintuna 5 tsakani ta dawo cikin É—akin hannunta É—auke da mug wanda ta haÉ—a tea din aciki.
Ƙarasowa jikin gadon tayi tare da miƙawa Oum Ayush mug ɗin.
Karɓan mug ɗin Oum Ayush tayi tare da kamo hannun Laylerh, cikin kulawa tace.  "Tashi kisha tea kinji, nasan zaki ɗan samu ƙarfi ajikinki."
Jin abun da Oum Ayush ɗin tafaɗa ne yasa ta shagwaɓe fuska, saboda kwata kwata bata sha'awar komai, "Naƙoshi."
TafaÉ—a akasalance, tare da jan blanket ta rufe jikinta, dan bawani rigar kirki bane ajikinra, nan ma Oum Ayush É—inne tasa mata rigar.
"Kiyi hakuri ki sha kinji, saboda likita yace sai kinci abinci kafun kisha magani, dan akwai yunwa ajikinki, karbi kishi kinji Laylerh na." Oum Ayush ta faÉ—a cikin rarrashi.
Haƙiƙa acikin yanayin da takejin kanta batajin zata iya ɗaukan rarrashi, saboda ayanzu ma zuciyarta bugawa take da sauri sauri, yayinda tarin tambayoyi ke kwance acikin ƙirjinta, kallon Oum Ayush ɗin tayi, cikin karyayyar muryarta me ɗauke da matsanancin rauni tace.  
"Nasan zuwa yanzu Abbou Jaheed ya É—auramin aure ko Oum Ayush?."
Jin tambayar nata ne yasa matsanancin tausayinta ya rufe zuciar Oum Ayush,  hannunta takai ta dafa kafaɗun Laylerh'n, cikin sigar lallashi haɗe da sanyin murya tace. 
"Haka Allah Ya tsarawa rayuwarki Laylerh, kuma inaso kisani kowa baya wuce ranarsa, domin aure kaman Mutuwa ne, ranar da Allah ya tsayarwa mutum ko za'ayi yaya bazai wuce saba, kisawa zuciyarki salama, domin fatan mu ako da yaushe shine Allah Yabaku zaman lafiya da kwanciyar hankali azaman aurenki da Najeeb, domin ayanzu ya riga daya zamo mijinki, wanda kuma nan da anjima kaɗan zamu miƙa mishi ke amatsayin mata."
Chapter 52 · 0% Book details