← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 144

Sashe 82

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

2:30 am
Matsanancin gumi ne ke ketowa daga kowani sashi na jikinta, yayinda kuma alokaci d’aya duk gaba d’aya jikinta ya d’auki rawa, cikin matsanancin firgita had’i da razana tafasa wani irin k’ara me tada hankali wanda kuma acikin sautin k’aran nata ta ambaci sunan MALEEK da wata irin murya, wanda hakan yasa Najeeb dake kwance tashi arud’e, daidai lokacin kuwa itama ta tashi azabure daga baccin da takeyi cikin kid’ima da tashin hankali marar misaltuwa.

*1February/2021*

8:00 pm
2/4/21, 8:44 AM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*
*Writting By*
fatymasardauna

*Chapter 47*

“LAYLERH!�
Najeeb wanda gaba d’aya k’ara da kuma sautin ihun nata yasa shi tashi afirgice ya k’ira sunanta cikin yanayin d’an d’aga murya tare dasa hannunsa ya soma k’ok’arin kama nata hannun.
Saidai kuma yanayin yanda gaba d’aya jikinta ke b’ari yasa shi kasa yin hakan, musamman da yaga ta dunk’ule hannayen nata waje d’aya, da d’an k’arfi take jijjiga kanta, yayinda lokaci d’aya hawaye suka shiga zirya akan fuskarta kaman an kunna famfo, cikin yanayin tsoro da kuma firgicin da ta samu kanta tasoma k’ok’arin dirowa daga kan gadon.
Ganin haka yasa cikin sauri Najeeb ya rik’o hannunta, hankalinsa ad’an tashe yace.
“Lafiyanki k’alau kuwa Laylerh? What’s wrong with you?� Yayi mata tambayar yana me d’an girgiza kafad’unta daya rik’esu da hannayensa.
Kai ta soma girgizawa tare da soma yunk’urin ya kice hannayensa dake kan kafad’anta, saboda a yanda yanayin nata yake ayanzu bazata iya ce masa komae ba.
Gane hakan da yayi da kuma fahimtar cewa bata cikin hayyacinta, yasa shi matsowa kusa da ita ahankali, ya shiga shafa bayanta, cikin muryarsa me d’auke da yanayin kwantar mata da hankali yace.
“Please Laylerh ki nutsu kinji, ki dawo cikin hayyacinki, babu abunda zai sameki gani atare dake, kuma bazan tab’a bari wani abu yazo ya cutar dake ba, kidawo hayyacinki kinji!!� Ya k’are maganan yana me kamo hannayenta, da har yanzu suke b’ari.
Fuskarta ya k’urawa ido, saboda yanda yaga labb’an bakinta na motsawa duk da karkarwan da sukeyi da alama wani abu take son fad’a.
Tabbas kuwa abunda ta gani amafarkin nata takeson bayyanawa, saidai kuma hakanan taji harshenta yayi mata nauyi, da k’yar cikin wata irin murya me d’auke da shaking tace.
“Yah M.Jay ne, ina tunanin wani abu ya sameshi, wata mota ta buge shi na gansa da jini ajikinsa, baya numfashi, komae nasa ya tsaya, wayyo Yah Najeeb dan Allah kabarni naje na dubashi, Inaso na gansa, Inaso naga ko yana lafiya, banason wani abu ya same sa banasoo!!!!� Ta k’are maganan nata cikin wani irin matsanancin kuka, me tada hankali da kuma bayyanar da gaskiyar abunda ke cikin zuciyarta.
Idanu Najeeb d’in ya zuba mata cike da mamakin jin abubuwan da take fad’a.
“Anya kuwa Laylerh bata da aljanu?�
Yayiwa kansa tambayar da dagashi sai zuciyarsa da ta sak’a masa hakanne suka sani, azahirance kuwa wata irin sassanyar ajiyar zuciya ya sauk’e, ganin yanda Laylerh’n ke kuka sosaine kuma yasashi jawota jikinsa, inda ya d’aura kanta akan faffad’an chest d’insa, tabbas kalaman da ta fad’a akan Maleek d’in ya daki zuciyarsa, wanda hakan yasa yaji wani abu me kama da kishi, take ya wanzu acikin ransa, saidai kuma amma ko kad’an bayason yanda Laylerhn ke nuna damuwa akan d’an uwannata yake damunsa, har yakai ga ya haifar masa da mummunan zargi acikin zuciyarsa, duk da cewar kuwa yana iyaka bakin k’ok’arinsa wajen gujewa zargin hakan, amma kuma yasan wani lokaci zuciya bata da k’ashi, komae yazo cikinta turawa k’wak’walwa take.
K’ok’arin sha re gurb’ataccen tunanin dake cikin ransa yayi, ahankali cikin sassanyar murya yace.
“Babu abunda ya samu Maleek Laylerh, saboda haka ki daina kuka, ko kin manta cewa da yawan mafarki ba gaskiya bane? ba lallaine abunda kika gani amafarki ya zama gaske ba, haka ko anan gaba ba lallaine hakan ya faru ba, da yawan mafarki baya tab’a zama gaskiya, ki kwantar da hankalinki kinji nasan Maleek yana lafiya!�
Ya k’are maganan yana me d’an shafa bayanta da hannunsa.
Kanta tad’an girgiza, still cikin muryan sheshshek’a tace.
“Inajin tsoron kada wani abu ya faru da shi, nagani dagaske, naga wata mota ta bugeshi, nasan mafarki ba gaskiya bane, amma wannan mafarkin inajin tsoro kada......�
“Shiii!!! kiyi shiru babu abunda zae faru, ki sakeyin addu’a ki koma ki kwanta kinji.�
Ya fad’i hakan ta hanyar katseta daga maganan da takeyi, domin sam bayason koda jin ta ambaci sunan Maleek d’inne, saboda fad’an hakan da kuma nuna damuwarta akan Maleek d’in, yana sawa yaji k’unci acikin zuciyarsa.
Jin abunda ya fad’a yasa ta d’ago kai da idanunta wanda suka cika tab da k’walla ta kalleshi, cikin yanayinta na abun tausayi da kuma kukan dake cinta ta bud’e baki da niyar sake yi masa wani magiya akan yabarta taje wajen Maleek d’in.
Cikin cracking voice tace.
“Dan Allah....�
Saurin sa hannunsa yayi ya toshe mata baki, tunkafun ma ta ida fad’an abunda zata fad’a d’in, lokaci d’aya kuma yanayin fuskarsa ya sanja, sake ta yayi tare da sauk’owa daga kan gadon, direct wajen k’ofar d’akin ya nufa, batare da tunanin komae ba kuwa ya murzawa k’ofar key, sanin kuma dayayi cewa idan yabar key d’in ajiki zata iya bud’ewa ta fitane yasashi zare key d’in ya rik’e a hannunsa, dawowa kan gadon yayi ya kwanta, irin kwanciyar nan ta rub da ciki, tare da rumtse idanunsa.
Laylerh kuwa ganin abunda yayi d’inne yasa ta k’ara sautin kukanta, had’e da matsawa can gefe ta takure jikinta waje d’aya, da iya k’arfinta ta shiga rera masa kukan da gaba d’aya yaso haukata masa tunani.

Adaidai lokacin kuwa ya bud’e idanunsa wanda suka kwashe tsawo awanni suna rufe, ahankali ya d’an yunk’ura ya tashi zaune daga kwancen da yake, cikin wani irin sabon yanayin daya samu kansa aciki yasa hannu ya dafe daidai saitin zuciyarsa dake bugawa da k’arfi.
D’an cije labb’an bakinsa yayi, domin kuwa ayanayi guda d’ayane yakejin irin wannan bugun zuciyar, shine idan yakasance Laylerh na cikin damuwa, ko kuma idan yaji sautin kukanta, tabbas hakan yakansa yasamu kansa cikin bugun zuciya, ko yana kusa ko baya kusa kuwa idan Ayshnoor d’insa na cikin damuwa yakanji yanayinsa ya sauya.
“Acikin wannan daren me yake damun Laylerh?�
Zuciyarsa tayi masa tambayar da Allah Ne kad’ai masanin amsarta.
Idanunsa yakai kan agogon dake aje gefen gadon.
3:00 am daidai idanunsa suka nuna masa, hakanne kuwa yasashi soma yunk’urin sauk’owa daga kan gadon, ahankali ya aje k’afafunsa ak’asa, koda yazo mik’ewa tsaye kuwa saida ya rumtse idanunsa kafun ya iya mik’ewa, domin kwana biyunnan duk bayajin dad’in jikinsa, ko abinci baya ci daga drinks sai tea kawai yake iya sha, baya fita ko ina daga d’aki sae falo, daga gefe guda kuwa ya kashe gaba d’aya wayoyinsa, yayi hakanne kuma gudun kada su Abbou Jaheed su sake tunkararsa da maganan jarababben auren da suke son lik’a masa.
Addaddafe ya k’arasa toilet, duk da cewar kuwa ana d’an sanyi hakan bai hanashi sakarwa kansa ruwan shower me sanyi ba.
Ak’alla kuwa sama da 20minute ya d’auka ruwan na dukan jikinsa, har saida ya d’anji zuciyarsa ta samu relief kafun ya kashe shower’n kana ya d’auro alwala.
Bayan yafito daga toilet d’in kuwa wata navy blue jallabiya yasaka ajikinsa, tare da shumfud’a sallaya ya tada sallah, domin so yake ya rok’i Allah Ko hakan zaesa ya samu sassaucin abunda ke azalzalan zuciyarsa babu dare ba rana.

Acan B’angaren su Najeeb kuwa, tsawon mintuna 20 Laylerh ta kwashe tana ta faman aikin kuka, tabbas ada yaso yin k’ok’arin jure kukannata saidai kuma jin yanda take k’ok’arin shid’ewa ya sashi kasa jure hakan.
Ahankali cikin sanyin da zuciyarsa tayi ya juyo da kallonsa zuwa gareta.
“Laylerh!�
Yak’ira sunanta cikin sassanyar murya me d’auke da rarrashi.
Laylerh kuwa duk da cewar tajisa amma haka ta cigaba da kukanta, me d’auke da abubuwa da dama, shagwab’a, sakalci, da kuma tsoron faruwar abunda tayi mafarki akai d’in, saboda ba yanzune karo na farko da take mafarkin Maleek d’in acikin mawuyacin hali ba, ay’an kwanakinnan acikin mafarkinta duk haka take ganinsa acikin damuwa.
Najeeb ko ganin da yayi bata kulasa bane yasa shi tashi zaune, asanyaye ya matso kusa da ita, cikin murya me kama da rad’a yace.
“Am very sorry My Wife, am so sorry kiyi hak’uri kinji, kuma kiyarda cewa Maleek yana nan lafiya, sannan ban hanaki zuwa wajensa haka kawae ba, yanzu fa tsakiyar dare ne, ke kanki idan zakiyi tunani baidace ace kinje wajensa awannan talatainin daren ba, amma I promise you gobe da safe zakije ki dubasa, but nasamma yana lafiya, amma kiyi hakuri kinji, kizo mukwanta, banason jin kukanki ko kad’an.�
Ya fad’i maganar yana me kamo hannayenta duka biyu, ya jawota jikinsa, ahankali ya shiga share mata hawayen da duk suka mata dama dama da fuska.
Ko kad’an kuwa batayi yunk’urin hanasa ba domin dama kukan da tayin yasa mata wani irin fitinannen ciwon kae.
Kwanciya tayi akan gadon tare da juya masa baya, ahankali take sakin sheshshek’an kukan da ya zame mata dole.
Cike da tsoro da kuma fargaban abunda kunnuwanta zasu jiye mata gobe bacci yasake d’aukarta.
Jin yanda take ta faman sauk’e ajiyar zuciya ne, yasa Najeeb matsowa kusa da ita sosae tare da jan blanket ya rufa musu.
Da tunani kala kala acikin ransa shima bacci ya d’aukesa.
Chapter 82 · 0% Book details