← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 144

Sashe 126

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Oum Ayush kuwa k’afar Laylerh’n ta kamo, anutse ta zura mata wasu had’addun grey shoes masu kyau da tsini.
D’an madaidaicin grey vail mai d’auke da adon duwatsun white stones Oum Ayush ta rufa mata, akai zuwa jikinta, yanayin yanda Oum Ayush d’in ta rufa mata vail d’inne kuma yasa kusan rabin fuskarta ya zamana arufe.

Hakanne kuwa ya k’ara bayyana asalin matsayinta na had’add’iyar amarya.

Turaruka masu dad’in k’amshi Oum Ayush ta fesa mata, tare kuma da kamo hannayenta ta rik’e acikin nata.

Fuskarta d’auke da tsananin farinciki tace.

“Masha Allah Laylerh kinyi kyau sosai, lallai yau ko Maleek idan ya ganki sai yayi da gaske kafun zai iya ganeki.�

Murmushi gaba d’aya Aunty Zee da su Theemah sukayi, domin su kansu sun yaba da irin kyaun da Laylerh’n tayi.

Mik’ar da ita tsaye Oum Ayush tayi, cikin nutsuwa kuma suka shiga takawa har suka fice daga cikin d’akin.

Kaitsaye d’akin dake gefen na Oum Ayush d’in suka shiga, kan wani lallausan kujera Oum Ayush ta zaunar da ita, kana itama ta zauna akusa da ita.

Hannayenta ta sake kamowa, cikin nuna tsananin farinciki da kuma nuna godiyarta ga Allah Tace.

“Alhamdulillah hakika kowani tsanani yana tare da sauk’i, sannan babu wani k’unci ko kuma bak’inciki da yake d’orewa acikin wannan duniyar, ba kuma lallaine idan ka rasa abu, ya zama ka rasa shi ba kenan har abada, sannan acikin rayuwa fad’uwa da nasara na bibiyarmu akullum akuma koda yaushe, watarana mai nasara zai zamanto ak’asa, wanda yake k’asa kuma ya zamanto asama, rasa abunda kakeso afarko bawai shike nuna cewar har abada bazaka tab’a samun abunda kakeso ba, lallai idan kayi hakuri watarana zaka samu..�

D’an numfasawa tayi, had’e da sake gyara zamanta, hannayen Laylerh’n dake cikin nata ta rik’e da kyau, cikin yanayin tausasa murya, da kuma nuna k’aunarta ga Laylerh’n tace.

“Laylerh yau Allah Yayi kinzama mata ga Maleek, wanda hakan ke nuna cewar wani babban nauyi ya rataya awuyanki ke dashi, yana da hakk’i akanki haka kuma kema kina da hakk’i akansa, wajibinki ne kuma ki aikata duk wani abunda ya saki, matuk’ar bai kaucewa addinin musulunci ba, wajibinkine kulawa da ci da shansa, haka kuma hakk’inkine kulawa da kuma basa farinciki, Laylerh kinfi kowa sanin cewar Maleek mai rauni ne, duk da kuwa cewar a idanu shid’in cikakken jarumine, amma har acikin rai da zuciyarsa shid’in mai raunine, musamman akanki, domin duk wani masomin rauninsa kece Laylerh, amadadin komai nasa kece, ke kuma d’ince dai kad’ai zaki iya jib’anta al’amuransa, kasancewarsa d’an uwa kuma Yayah agareki, sannan dole sai kinyi hakuri kin kuma jurewa, duk wata jarrabawa da zata fuskanto ku, domin kasantuwarku amatsayin ma’aurata yanzu ya goge duk wani Nisan dake tsakaninku, ayanzu zaku kasance tamkar abu d’aya ne, dole buri da kuma fatanku zasu kasance atare da juna.
Nasan kuma kinyi kokari sosai Laylerh, domin duk da irin k’addarar da ta same da, baki guje masa ko sanja tunani ba, haka kika amincewa aurensa, lallai Tabbas Allah Ne kad’ai zai baki ladan abunda kika aikata masa, na kuma yi imani cewar koda da second d’aya har abada bazaki tab’ayin danasanin kasancewar Maleek amatsayin mijinki ba, nasani k’warai cewar zai baki farinciki marar yankewa, da izinin Allah Kuma zakuyi rayuwa mai dad’i, rayuwar da babu munanan k’addara acikinta, rayuwar da zaku mantar da junanku cewar kud’in marayune, sannan rayuwar da haskenta zai haskaka kowa insha Allah....�

Dakatawa da maganan nata tayi, tare kuma dad’an sanya hannu ahankali ta share hawayen daya cika idanunta, wanda batare kuma da ta saniba har ya gangaro kan fuskarta.

Saurin share hawayen nata tayi, gudun kada Laylerh’n taga hawayen, murya atausashe tace.

“Tashi muje tun d’azu Fou’ad da abokansa suka zo d’aukarki, Tabbas amma nasan zanyi kewarki sosai Laylerh na!!�

Wasu irin siraran hawaye ne suka tsiyayo daga cikin idanunta, domin itama tasani tabbas zatayi kewar Oum Ayush da kuma su Abbou Jaheed, k’warai zatayi kewarsu sosai.

Hannunta Oum Ayush ta kamo tare da mik’ar da ita tsaye, ahankali kuma cikin nutsuwa ta shiga takawa da ita har suka fice daga cikin d’akin.

Koda suka fito cikin babban falon gidan kuwa, gaba d’aya kallo kansu ya dawo, musamman yanda mayafi da kuma shek’in suturar Laylerh’n ke d’auke idanu.
Duk da cewar kuwa Rabin fuskarta arufe yake, amma hakan bai hana mutane da yawa soma yi mata video ba.
Hannun Laylerh’n Oum Ayush ta mik’awa Aunty Zee, tare da yi mata alama akan taje tasa Laylerh’n amota.

“To.� kawai Aunty Zee d’in tace, tare kuma da kama hannun Laylerh’n kamar yanda Oum Ayush ta buk’ata, haka suka fito daga cikin falon, Aunty Zee na rik’e da Laylerh wanda take d’an sakin sheshshek’an kuka, abayanta kuwa Theemah da Aleeya ne, wanda sune zasuyiwa Laylerh’n rakiya, sai kuma y’an uwansu dake Egyft wanda suka zo.

Fou’ad wanda ya d’ebo abokanansa suka zo d’aukan auren, batare da Maleek d’in ma ya sani ba, shida kansa ya bud’ewa Laylerh’n k’ofar had’add’iyar White Range Rover car, Aunty Zee ta sanyata aciki, tare da shiga itama ta zauna.

Ganin hakanne kuma yasa y’an tsirarun mutanen da zasuyiwa Laylerh’n rakiya suka shiga sauran motocin, saboda kuma tsabar yawan motocin da Fou’ad d’in ya kawo ne yasa kowacce mota mutum d’aya ne kawae ya shigeta, sauran kuwa haka suka zauna empty babu kowa acikinsu, domin koda ma ace mutanen suna da yawa, To dole akwai cars d’in da zasu koma empty.

Fou’ad dake k’ok’arin driving motar da Laylerh’n ke ciki ne, idanunsa suka hango masa Aleeyah wacce ke shirin shiga wata mota ta daban, idanunsa yad’an tsaida akanta, tare kuma da soma k’arewa gaba d’aya halittar jikinta kallo, saboda lokaci d’aya yaji wani feeling akanta, Tabbas yarinyar tayi mishi sosai, domin tana da irin structure’n da yake matuk’ar so awajen Mace, kasancewarta brown skin kuma shine ya k’ara sawa yaji zuciyarsa ta narke akanta sosai.
Har ma yaji ajikinsa cewar inama da ace motarsa ta shiga ba na wani can daban ba.

Saidai kuma tunawa da yayi cewar duk guri d’aya zasuje ne, yasashi jin sanyi acikin zuciyarsa, anutse ya tada motar.
One by one kuwa haka cars d’in suka soma fi cewa daga cikin gidan.

Adaidai lokacin da suka mik’a kan titi ne kuma Laylerh, da kejin wani irin bacci na fusgarta Ahankali ta kwantar da kanta akan cinyar Aunty Zee.

Hakanan bata san meyasa ba takejin wani irin abu mai kama da fargaba, tsoro da kuma fad’uwar gaba na yawan tunkararta, wanda har hakan yasa zuciyarta ke beating fast fast, awani bak’on yanayi na musamman takejin kanta, yanayin da sam bataji makamancinsa alokacin da aka d’aura mata aure da Najeeb ba.

Gaba d’aya tunaninta ya tafi ga yanda zata fuskanci Maleek d’in amatsayin mijinta, har yanzu ganin abun takeyi tamkar amafarki.

Batare kuma da sunyi tafiya mai tsawo ba duk motocin suka tsaya, adaidai lokacin da suka iso tsakiyar Maitama, agaban wani makeken gate mai masifar kyau da tsari, sauran cars d’inne sukayi parking awaje, Yayinda matashin maigadin gidan, ya wangale gate d’in, Fou’ad kuwa da Laylerh’n ke cikin motarsa anutse ya tura hancin motar cikin makeken gidan, da had’uwarsa ya zarce duk wani misali.

Kasancewar kuma compound d’in gidan nada girma sosai ne, yasa saida Fou’ad ya d’anyi tafiya maitsawo kafun yayi parking motar, agaban wani katafaren dogon gini dake cikin compound d’in gidan.

Yana gama daidaita parking d’in kuwa, ya fito tare da zagayowa cikin sauri ya bud’ewa su Aunty Zee k’ofar motar.

Anutse Aunty Zee ta kamo hannun Laylerh, wacce zuwa yanzu sautin kukan nata ya tsaya, saidai hannunta na dama dafe yake da saman mararta.

Ahaka suka fito daga cikin motar Aunty Zee na rik’e da hannunta, kaitsaye suka nufi wannan had’add’en ginin.

Aunty Zee ne ta bud’e had’add’en k’ofar babban falon tare da cewa Laylerh tayi bismillah sannan kuma ta shiga da k’afar dama.

Hakan kuwa akayi cikin zuciyarta tayi bismillah’n tare da saka k’afarta na dama acikin had’add’en falon da kaitsaye za’a k’iransa da sunan Aljannar duniya, musamman yanda aka k’awata cikinsa da 2021 Austin classic sofas masu matsanancin kyau da tsada.

Two bedroom ne acikin falon, sai kuma stairs d’in da zaka taka wanda zai kaika sama, kasancewar kuma asaman d’akin Laylerh’n yake, hakan yasa direct Auny Zee ta wuce saman da ita.

Again kuma wani babban falon suka Tatar asaman, wanda shima aka k’awata cikinsa da kayan furnitures masu kyau, saidai kuma sofas d’in dake cikin falon sun banbanta dana falon k’asa, kasancewar su way’annan d’in Culliana Victoria’n sofa ne.
Kamar kuma yanda yake two bedrooms afalon k’asa haka ma ya kasance acikin falon saman, d’akin da yake ana biyu Aunty Zee ta nufa da ita, wanda kuma shima aka k’awata cikinsa da furnitures masu kyaun gaske.
Ko ina dake cikin falo da d’akin kuwa daddad’an k’amshin turaren wuta ne ke tashi, sai kuma sanyin A/C’n dake tashi.

Kan lallausan bed d’in dayasha bedsheet na alfarma Aunty Zee ta zaunar da Laylerh’n, tare kuma da gyara mata rufin mayafin dake jikinta.

Daidai lokacin kuwa aka soma k’iraye k’irayen sallan magriba.

Kallon su Theemah dake ta santin kyau da kuma had’uwar gidan Laylerh’n Aunty Zee tayi, tare dayi musu alama akan suje falo su jirata, babu musu kuwa haka suka juya ita da Aleeya suka fice daga cikin d’akin, Theemah kuwa da gaba d’aya bakinta ya kasa rufuwa, kallon Aleeya tayi cikin yanayin zumud’i tace.

“Lallai Yau akwai show agidannan, da ace Ina da dama to da yau na zama sauro ta yanda zan morewa idanuna, Domin kuwa ko nayi imagine this night abun nasan sai yafi tunani na�

Dariya Aleeya tayi tare da d’an girgiza kanta, domin ad’an sabon da sukayi da Theemah’n ta fahimci cewar, Theemah’n irin mutanen nanne da basa iya b’oye gaskiyar abunda ke cikin rai da zuciyarsu.

Acan cikin d’akin kuwa hannun Laylerh’n Aunty Zee ta kamo, cikin kulawa tace.

“Mu zamu koma please Laylerh ki kula da kanki da kuma Mijinki kinji, duk abunda ya buk’ata awajenki kada kice masa a’a, domin komai dake jikinki halal d’insa ne, ke d’in yanzu mallakinsa ne, sannan kuma basa ingantacciyar farinciki ayanzu yana wuyanki ne, please Laylerh ki kula kinji Allah Ubangiji ya baku zaman lafiya!!�

Hawaye masu sanyine suka fito daga cikin idanunta, lokaci d’aya kuma taji kuka mai sauti na shirin k’wace mata.
Chapter 126 · 0% Book details