← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 144

Sashe 110

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Abbou Jaheed ya k’ira wayarki baki d’auka ba.�

Hannu tasa ta d’an dafe kanta, cikin nuna rashin saninta tace.

“Subahanallah gaba d’aya na sha’afa nabar wayartawa acikin d’aki bari naje na d’auko.�

Mik’ewa tsaye tayi da sauri tare da juyawa ta nufi hanyar bedroom d’inta.

Saidai ko taku hud’u batayi ba ta tsaya cak tare da juyowa ta kalli Maleek d’in, da abubuwan dake cikin zuciyarsa suka bayyana akan fuskarsa.

Shikuwa Maleek falonnata ya soma bids kallo, ganin babu wata alama da zuciyarsa keyi masane yasa shi dawo da kallonsa ga Oum Ayush din, wanda tayi saurin dawowa ta d’auki farar envelope d’in da ta bari akan kujera.

Envelope d’in hannun nata ya zubawa ido, kamar wanda zai nazarci wani abu kuma sai ya fasa ahankali ya juya, taku biyu kacal yayi ya tsaya tare da juyowa ya fuskanceta.

“INA AYSHNOOR?.�

Ya tambaya
cikin wata irin murya da ita kanta Oum Ayush d’in batasan yana da ita ba.

Sanin kuma da tayi cewar Laylerh’n yake k’ira da Ayshnoor ne yasa ta tsuke fuska, cikin son rashin bashi daman ganin Laylerh’n tace.

“Batanan.�

Idanunsa ya d’an lumshe tare da bud’e jajayen labb’ansa, magana yasoyi amma kuma sai ya fasa, madadin hakan sai ya d’an juya tongue d’insa, batare daya sake cewa komae ba kuwa ya juya ya fice daga cikin falon.

Hakanne kuwa yasa ta bisa da kallo, ganin ficewarsa yasa ta sauk’e wani irin ajiyar zuciya, idanunta ta d’an lumshe kana asanyaye tace.

“Daga yanzu har zuwa wani lokaci mai tsawo bazaka sake ganin Laylerh ba Maleek wannan alk’awarine!!!�

*(ALHAMDULILLAH two days na d’an shiga busy, amma yanzu komae normal zanyi kokari wajen baku update kullum, saboda na gama duk wasu tests d’ina💃💃 littafi yazo gangara mutanen Maleek how far😉)*

*7/March/2021*

*6:14 pm*
3/9/21, 4:53 PM - Ummi Tandama: *LaylerhMaleek*

*Writting by*
fatymasardauna

*Chapter 64*

“Daga yanzu har zuwa wani lokaci mai tsawo ba zaka sake ganin Laylerh ba Maleek wannan alk’awarine.�

Cewar Oum Ayush da har zuwa yanzu ta kasa d’auke idanunta daga kallon hanyar da Maleek d’in yabi ya fice.
Ak’alla kuma saida ta d’auki almost 5minutes tsaye awajen kafun daga bisani ta juya ta nufi d’aya daga cikin bedroom d’inta wanda kuma anan cikinsa ta manto wayartata.

Laylerh.
Akaro na barkatai kenan da take ta so da kuma k’ok’arin daidaita nutsuwarta amma abun yaci tura, duk yanda taso tsagaita tunaninta kuwa abun na neman gagararta.
Tabbas amatsayin bak’o takejin komae dama duk yanayin.
Sannan kuma hak’ik’a zuciyarta acike take da fargaba, wanda takasa tantance k’arfinsa da kuma yanayinsa, ayau d’in akuma wannan lokacin shine karo na farko da ta fara jin wani abu akan Najeeb, wanda yasa gaba d’aya hawayen dake cikin idanunta kasa daina gangarowa kan fuskarta.
Sake rumtse idanunta dake aikin zubar da k’walla tayi, tare da mirginawa ta gyara kwanciyar da tayi akan makeken gadon Oum Ayush.
Sannu ahankali kana cikin wani irin sassanyan yanayi gaba d’aya rayuwar da tayi da Najeeb d’in suka shiga dawowa cikin kanta filla filla, yayinda take ganin fuskarsa nayi mata gizo acikin idanunta.
Tabbas Najeeb Ya isa Namjin da kowacce mace zata soshi, yana kulawa da ita matuk’a, ko da kad’anne kuma bayason ganin damuwar ta, akoda yaushe idan tana cikin k’unci yakanyi k’ok’ari wajen ganin ya magance mata duk wani damuwarta, koda kuwa baya cikin mood mai dad’i yakanyi k’ok’arin wanzar da murmushi akan fuskarsa matuk’ar yana gabanta, bai damu da hakk’insa ba matuk’ar zatayi farinciki, sannan yakan iya danne duk wani abu dake zuciyarsa wajen ganin ya mu’amalance ta yanda bazata ga komae na b’acin ransa ba.
Idanunta ta kuma rumtsewa, wanda sanadin hakan suka fitar da wani irin hawaye mai zafi, ahankali tasa hannunta ta dafe daidai saitin zuciyarta dake d’an bugawa da k’arfi.
Tabbas tasan Najeeb yayi halacci agareta duk da bata da masaniya akan dalilin dayasa ya saketa.
Matsanancin kukan dake shirin k’wace mata ta shanye tare da jawo wani pillow tayi hugging d’insa, still har yanzu maganganun Najeeb d’inne ke dawowa cikin brain d’inta, musamman ayau d’in dayake fad’in cewa.
“Yafini buk’atarki Laylerh, domin ni da zuciyata kawai nake sonki, shi kuma ke d’ince rayuwarsa gaba d’aya.�

Kalmarsa na “I love you� daya furta mata da ta tuno ne yasa ta fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya, cikin kuma wata irin muryarta mai d’auke da tsananin rauni tace.

“I’m sorry Yah Najeeb, I’m very sorry, banyi maka abunda ya dace nayi maka ba tuntuni, sanadin hakan kuwa gashi ayanzu bansan me kakeji acikin zuciyarka ba.
Lallai Tabbas da ace inada dama da ikon sauya k’addara dana sauya tawa k’addarar, duk da nasan cewa rayuwa babu soyayyar Yah M.Jay abune agareni da har abada bazae tab’a yiwuwa ba, so da k’aunarsa acikin jiki da jinina suke, babu wani second ko minute da zai wuce batare da naji soyayyarsa acikin jinina ba, hasalima ina rayuwane da sonsa, bansan tayaya zan iya jurewa hakan ba, domin ako da yaushe sonsa shi yake maye gurbin duk wani tunanina.�

D’an tsagaitawa da maganan nata tayi, saboda yanda zuciyarta ke wani irin tsalle, numfashinta kuwa haka yake yi kamar zae d’auke, hakan ya farune kuma saboda kukan da tayi sosae.
Sake gyara kwanciyarta tayi had’e da nutsa kanta acikin pillow, take kuma ta shiga sauk’e wani ajiyar zuciya akai akai, wani irin sanyi ne takeji na ratsa duk ilahirin jikinta, wanda hakan shiya tilasta mata, jan babban blanket d’in dake kan gadon ta rufe gaba d’aya jikinta dashi.
Sake takure kanta waje d’aya tayi, tare kuma da sanya hannayenta duka biyu ta toshe kunnuwanta, tayi hakanne kuma saboda muryar Najeeb da takeji na yawo acikin kunnuwanta, wanda kuma hakan shike sanya mata jin fad’uwar gaba maitsanani, musamman idan ta tuna da cewar azamansu koda sau d’ayane bata tab’a bashi hakk’insa na aure dayake kanta ba.
Wannan abu shike k’arasawa taji hawaye sun tsananta zuba daga cikin idanunta,
Tabbas awani sashi na zuciyarta taso ace ta rayu da Najeeb d’in ko da na d’an k’ank’anin lokaci ne, musamman ayanzu da k’addara ta fad’awa Maleek, ta yanda zata iya jure duk wani wahala wajen ganin ta haifi d’a ko y’ar da zata bawa Yah M.Jay d’in nata kyauta na har abada.
Asanyaye ta share hawayen da suka zubo mata, tare kuma da soma ambaton sunan Allah acikin zuciyarta, domin kuwa zuwa yanzu ta kawo wani matakin da zuciyarta ta riga da ta gama karyewa, hasalima ayanzun so takeyi tayi bacci ko hakan zaisa ta d’anji sauk’in abunda ke damun zuciyarta.
Cikin ikon Ubangiji kuwa ko mintuna 15 bata share ahakaba wani irin bacci mai nauyin gaske ya d’auketa, wanda cikinsa ke d’auke da tarin mafarkai kala kala.

Acan b’angaren Maleek kuwa koda ya fito daga part d’in Oum Ayush d’in kaitsaye nasa part d’in ya nufa, saidai yanayin yanda zuciyarsa ta kasa nutsuwa waje d’aya ne yasa duk yaji zaman gidan ya ishesa.
Yanaji ajikinsa cewar lallae Tabbas akwae abunda yake faruwa, amma kuma menene shi abun ya kasa sani, duk da kasancewar kunnuwansa sun jiye masa abunda Abbou’n nasa ya fad’a da kyau, amma sam ko kusa ya kasa aminta da abunda zuciyarsa ke gaya masa akan hakan.

Akan wata had’add’iyar sofa dake gefen gadonnasa ya zauna, tare kuma dasa hannu ahankali ya dafe kansa da yakejin yanayi masa wani irin sarawa, atake kuma ganin da yayiwa wannan farar envelope d’in dake hannun Oum Ayush ya fad’o masa.
Wani irin abune yaji ya daki k’ahon zuciyarsa, wanda har saida hakan kuma ya tilasta masa zabura.
Lallai ne Tabbas yanason sanin gaskiyar abunda ke faruwa.
Idan kuma har da gaskene cewa Najeeb ya saki Laylerh to yana da buk’atar sanin dalili da kuma hujja.

Idanunsa da sukayi ja ya sake rumtsewa da k’arfi, wani irin tafasa zuciyarsa keyi, domin lokaci d’aya tunaninsa ya basa cewar Najeeb d’in ya auri Laylerh’nne dama dan kawae ya tozartata, maybe ya samu abunda yakeso awajenta shiyasa yake k’ok’arin tozartata, wanda shi kuma Allah Yasani bazae tab’a iya jurewa hakan ba, har abada bazae tab’a barin wani abu na damuwa mai tsanani ya samu Laylerh ba.
Raya hakan da yayi acikin ransa ne kuma yasashi d’an soma girgiza kai, tare kuma da dunk’ule hannayensa waje d’aya, lokaci d’aya idanunsa sukayi wani irin ja tamkar wanda aka watsawa garin barkono, yayinda jijiyoyi da kuma gargasan dake jikisa suma duk suka mimmik’e.
K’una sosae yakeji ak’irjinsa wanda ke d’auke da matsanancin b’acin rai.
Hakanne kuwa yak’ara sawa yaji komae bayayi masa dad’i.
Kaitsaye wajen da yake ajiye car keys d’insa ya nufa, key d’in wata had’add’iyar BMW 5201 k’iran 2018 navy blue colour ya d’auka, tare da d’aukan wayoyinsa, kai tsaye ya nufi hanyar fita daga cikin d’akin, duk da cewar sam bayajin dad’in jikinsa ko kad’an, amma yana da yik’inin cewa fitansa daga cikin gidan yafiye masa zamansa.

Koda ya fito compound d’in gidan, Abdoul dake zaune yana hango Ogan nasa ya tashi tsaye da sauri tare da k’arasowa wajen Da Maleek d’in yake.

Cikin girmamawa yace.

“Barka da fitowa Oga, ya jiki?.�

Da kai kawae ya iya amsawa Abdoul d’in, batare kuma da yace komae ba ya sa key ya bud’e murfin motar.

Idanunsa da suka sauk’a akan cutie cat d’insa dake ta shawagi acikin babban compound d’in gidan ya d’auke, tare da shigewa cikin motar b’angaren driver ya zauna.

Ganin hakanne kuma yasa Abdoul d’an rank’wafowa cikin yin k’asa da murya yace.

“I’m sorry Sir bai kamata ka fita kai d’aya ba, kodan gujewa abunda ya faru...�

Kasa k’arasa maganan Abdoul yayi saboda wani irin kallo da yaga Maleek d’in yayi masa.

Bisa dole haka yaja bakinsa yayi shiru tare da d’an Jan jikinsa baya.

Shikuwa Maleek rufe murfin motar nasa yayi, tare da danna wani irin horn da ya saka maigadi wangale masa makeken gate d’in tun kafun ma ya k’araso.

Da wani irin speed ya cilla hancin motar tasa waje, ko sauraron mai gadi ma da yakeyi masa adawo lapia baiyiba yasa kai ya fice.

Da wani irin isa yake murza kan steering motar nasa, duk da cewar kuma yanajin k’asan mararsa nayi masa ciwo amma haka ya cijewa fitan, kaitsaye CASH and CARRY ya nufa.
Chapter 110 · 0% Book details