← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 144

Sashe 128

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idanunsa ya zubawa kyawawan yatsun k’afan nata baya ko k’yaftawa, yayinda daga gefe guda kuwa yakejin wani irin sanyi na ratsa duk ilahirin jikinsa.
Asanyaye yasa hannunsa ya d’ago k’afarta na dama, tare da ajiye k’afar nata akan cinyarsa, igiyan dake jikin shoes d’in ya soma warwarewa, wanda hakanne kuma ya bashi daman cire mata takalmin daga k’afarta.
Ahankali ya saka duka tafukan hannayensa ya rik’o k’afafun nata, tare kuma da d’ago kansa ya k’urawa mayafin dake jikinta idanunsa wanda lokaci d’aya suka koma kalan bacci.

Sassanyan k’amshin turare da kuma wani daddad’an sanyin da taji yana shiga cikin tafin k’afarta ne yasa ta d’an bud’e idanunta ahankali, domin dama baccin da takeyi d’in baiyi nisa ba, saboda yanayin yanda mararta ke murd’awa akai akai, sam ya kasa barin bacci mai k’arfi ya d’auketa.
K’afanta dake cikin tafukan hannayensa tad’an motsa, asakamakon jinsu da tayi acikin wani abu mai laushin gaske.

Atake kuma zuciya da k’irjinta sukayi wani irin bugawa saboda k’amshin turarensa, da taji ya cika mata hanci, wanda kuma hakan alama ce dake nuna mata cewar, lallai Maleek d’in yana cikin d’akin.
saurin maida idanunta tayi ta lumshe, tare dasa hannunta ta dafe daidai saitin zuciyarta dake bugawa, matsanancin fargaba takeji sosai akan daren nasu na yau.

Maleek dake durk’ushe akan k’afafunsa kuwa ganin da yayi tad’an motsane yasashi.
Sake matsowa kusa da ita.
Ahankali ya zare hannayensa daga k’asan k’afafunta.

“AYSHNOOR!!!� Yak’ira sunanta cikin wata irin kasalalliyar muryar dake bayyana, asalin rauni da kuma abunda ke cikin zuciyarsa...

Cak bugun zuciya da tunaninta suka tsaya adaidai lokacin da taji sauk’ar muryarsa acikin kunnuwanta, Yayinda taji wani irin abu maikama da tsoro ne ya lullub’eta.

“AYSH......NOOR!!!� Ya sake k’iran sunanta akaro na biyu, tare da d’aura tafukan hannunsa akan nata hannun, wanda suka sha gold rings, saidai kuma ayanzu yanayin amon muryartasa ta banbanta da wanda taji afarko.
Ayanzun ya k’ira sunanta ne da murya mai bayyanar da rauni.

A yanayin yanda yakejin kai da zuciyarsa kuma bayajin zai iya tsayawa har sai Laylerh’n ta amsa masa.
Ahankali yasa hannayensa yayi k’asa da mayafin dake jikinta.

Take kuwa kyakkyawar fuska, da kuma idanunta wanda suka ciko da k’walla suka bayyana.

Kusan atare suka lumshe idanunsu, saboda wani irin daddad’an yanayin da suka samu kansu aciki marar misaltuwa.

Sake tank’washe k’afafunsa yayi akaro na biyu, tare da kamo soft hands d’inta ya rik’e acikin nasa, duk kuma da irin shocking d’in da rik’e hannun nata ya jawo masa hakan baisashi sakin tattausan hannayen nata ba.
Idanunsa da sukayi ja sosai ya lumshe, tare da d’an matsowa kusa da ita sosai, wanda har hakan yasa guiwowinta suka shiga gogan chest d’insa.
Hannayenta dake cikin nasa ya d’an matsa Ahankali, cikin kuma wata irin raunanniyar murya, dake bayyana gaskiyar abunda ke cikin zuciyarsa yace.
“Why? Meyasa Ayshnoor? meyasa zaki zab’i rayuwa da mutumin da yake amatsayin nakasasshe? Meyasa zaki tauyewa kanki farinciki saboda ni kawai? Me yasa kika zab’i zama da mutumin da bazai iya baki d’a ko y’a daga jikinsa ba? Me yasa kika zab’i mutumin da zama dashi bazai amfaneki da komai ba? Bazan iya amfanar dake ba Laylerh, sure ba zaki samu zuri’a daga gare ni ba, ni mai raunine Laylerh, Tabbas hakika ni Mai Raunine, mai raunin da baicancan ci samun wata mace ya aura ba, tayaya zaki bada duk wani hope d’inki akaina Ayshnoor? Akullum burina shine kiyi farinciki, sannan burina ako da yaushe shine na nesantaki da munanan k’addarorina, sam banason kiji zafi asabo dani, domin kowani rauni d’aya naki acikin zuciyata nakejinsa...�

Kanta ta d’an soma girgizawa cikin sauri tare dasa hannayenta ta toshe masa baki.
Lokaci d’aya kuma wasu irin siraran hawaye masu zafin gaske suka shiga gangarowa daga cikin idanunta.
Yayinda gaba d’aya duk jikinta ya d’auki b’ari. Saboda wani kuka ne na gaske ke k’ok’arin k’wace mata.

Ganin hakanne kuma yasa shi durk’usa guiwowinsa akasa, ahankali ya d’aura kansa akan k’afafunta.
Sanadin hakanne kuma yasa shi, jin wani irin feelings mood na yawo acikin jikinsa.
4/1/21, 9:10 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*Note editing*

*(This page is dedicated to you My Sweetheart Munu Glams ILYSM Bae🖤🥀🥰)*

#Love

*Chapter 77*

Idanunsa da sukayi ja sosai ya lumshe, alokacin da sassanyan k’amshin dake fita ajikinta ya shiga ratsa cikin hancinsa, wani irin k’amshine mai tsananin dad’i, ga kuma taushin skin d’in k’afafun nata da suka sauk’ar masa da kasala.

Har yanzu yanajin tamkar abubuwan dake faruwa ba gaskiya bane, har yanzu yana ganin kaman idanu wansa gizo sukeyi masa, yanajin tamkar bashine da Laylerh’n acikin d’akin ba.

Ahankali ya sauk’e wata irin k’akk’arfar ajiyar zuciya, tare da d’an janye jikinsa baya, idanunsa ya d’ago ya kalli Laylerh’n da har yanzu wasu siraran hawaye basu daina bin k’uncinta ba.
Akaron farko daya tsura mata idanu baya ko k’yaftawa, domin shikad’ai yasan meyakeji acikin zuciyarsa ayanzun, k’arfin yanayin da yakejin kansa aciki ya wuce ya fassara sa, abunda zuciya da kuma gangar jikinsa ta jima tana buri da fatan samu, yau itace agabansa kuma amatsayin mallakinsa.
Lallai ya yarda cewa babu wata k’addara mummuna ko kuma mai tawaya da zata tabbata, babu kuma wani abu wanda har abada bazai wuce ba.

Again tsumammun idanunsa wanda yakejin ruwa acikinsu ya lumshe, tare da d’an janye guiwowinsa, daga durk’uson da yayi ya mik’e tsaye.

Tafiya ya d’an soma yi Ahankali har zuwa gaban babban drawer’n dake cikin d’akin.

Hula da agogon dake d’aure a tsintsiyar hannunsa ya cire, had’e kuma da zare babbar rigar dake jikinsa, ya ajiye akan wani original gothic chair dake cikin d’akin.

D’an durk’usawa yayi anutse ya zare takalman dake sanye a k’afafunsa.

Cikin kuma takunsa dake bayyana nutsuwarsa, kai tsaye ya nufi bathroom d’in dake Cikin d’akin.
ahankali ya murd’a handle d’in k’ofar bathroom d’in, tana bud’ewa kuwa ya shige ciki tare da kullo k’ofar.

Laylerh dake zaune kuwa jin alaman ya shige cikin bathroom d’inne yasata zamowa k’asa ta durk’ushe akan guiwowinta, d’aya daga cikin hannayenta ta d’aura adaidai kan mararta dake yi mata wani irin ciwo, mayafin dake kan nata ta d’an yaye tare da ajiye bayanta ajikin gadon, ta lumshe Idanunta, sassanyan k’amshin turarensa dake matuk’ar kashe mata jiki ta ci gaba da shak’a, wanda hakan yasa takejin kanta acikin wata duniya ta daban, duk da kuma ciwon da takeji ak’asan mararta, amma hakan bai hanata Jin wani irin abu na musamman akan Yah M.Jay d’in ba, yanayin da batasan dame zata k’irasa ba, kasancewar duk yanda tunaninta ya d’auki al’amarin ya wuce nan, jin abun take acikin gangar jiki da jininta.

Ruwan daya taro acikin tafukan hannayensa ya watsa akan kyakkyawar fuskarsa, lokaci d’aya kuma ya saki wani irin ajiyar zuciya, tare dajan dogon numfashi.
Kwantattun gargasan dake jikinsa wanda ayanzu suka mimmik’e tsaye ya zubawa ido.
Tamkar dai wani mai nazartar wani abu.
Saidai kuma azahirance bawae nazartan wani abun yakeyi ba, shiru da kuma nutsuwar da yayi, alamace dake nuna cewar gangar jikinsa na amsar abunda zuciya da kuma brain d’insa ke aika masa.

Ahankali ya janye jikinsa daga gaban classic glass bathrobe d’in, tare da juyawa ya k’arasa gaban sink, hannayen riga da kuma k’afan wandonsa ya d’an nad’e, anutse ya soma gudanar da Alwala, bayan kuma ya gama alwala’nne ya juya Ahankali ya nufi hanyar fita daga cikin toilet d’in.
Bud’e k’ofar toilet d’in yayi ya fito, tare kuma da soma takowa ahankali zuwa gareta.
Ganinta da yayi a durk’ushe ne kuma yasa shi, d’an tsaida Idanunsa da suke lumshewa akanta, tare dasa hannunsa ahankali ya d’an janye mayafin dake kanta.

“Ayshnoor kije kiyi alwala.�
Ya fad’a cikin wani hot unique voice d’insa, daya sanya tsikar jikinta mimmik’ewa.
Duk da cewar kuwa bata kallonsa amma saida taji wani irin nauyinsa ya lullub’eta.
Hannunta dake kan mararta ta zare tare da mik’ewa tsaye, ahankali cikin kuma yanayin sanyin daya zame mata sabo ta nufi k’ofar da take tunanin cewa nanne toilet.

Daidai takai tsakiyar d’akinne kuma vail d’in dake jikinta ya zame ya fad’i k’asa.
Batare kuma da ta ankara da hakan ba, ta cigaba da tafiya harta shige cikin toilet d’in.

Kasalallun idanunsa ya lumshe tare dajan wani dogon numfashi, hakan ya faru ne kuma saboda sauk’e idanunsa da yayi akan tsararren shape d’in jikinta, kasancewar d’inkin riga da sket d’innata ya bayyana komai da komai.
Wani tunani na daban kuma daya shigo cikin k’wak’walwarsa ne yasashi zama abakin gado, tare da sanya hannayensa ya rufe fuskarsa.

Laylerh kuwa koda ta shiga cikin toilet d’in baki ta bud’e tana k’arewa cikin toilet d’in kallo, domin had’uwarsa ya wuce duk yanda take tunani, gudun kuma kada ta b’ata lokaci ne, yasa ta k’arasa gaban sink ta d’auro alwala kamar yadda ya umarceta.
Saidai kuma sam batasan meyasa har yanzu bugun zuciyarta ya kasa zama daidai ba.
Gaba d’aya amatakin wani irin take kallon komai.

Bata kuma tashi sanin cewar vail d’in da ta rufu dashi baya jikinta ba, sai yanzu da ya kammala alwala, shagwab’abb’iyar fuskarta ta d’an kwab’e, sanin babu yanda zatayi ne kuma yasa ta zame d’ankwalin dake kanta ta yafa ajikinta.
Ahankali ta bud’e k’ofar bathroom d’in ta fito.
Tana fitowa kuwa idanunta suka sauk’a akanshi, saidai kuma ganin ba ita d’in yake kallo ba ne, yasa tayi saurin k’arasawa gefen gadon ta d’auki Hijab d’in da tayi sallah dashi d’azu ta saka ajikinta.

Maleek kuwa tun fitowarta daga cikin toilet d’in yana lure da ita, duk da kasancewar idanunsa ba akanta suke ba, amma zuciya da tunaninsa na gareta, shiyasa ko da ace idanunsa basu sauk’a akanta ba, To hakan bawai yana nufin baya kallonta bane, domin duk wani abu daya shafeta da idon zuciya yake kallonsa, kuma kallo bawai Lallai dole saida idanu ba, sometimes ma hankali shine gani.

Mik’ewa tsaye yayi tare da juyowa ya fuskanceta, wanda hakan yasa tayi saurin sadda kanta k’asa.
Wani irin bugawa kuma zuciyarta ta shiga yi adaidai lokacin da ta ga ya nufo Inda take
Wanda har saida hakan ya kasa b’uya, domin zai iya cewa duk taku ae dake dad’a kusanto shi gareta sai yaji sautin bugun zuciyarta.

Lokacin daya k’araso kusa da ita d’inne kuma ya tsaya cak, tare da daidaita tsayuwarsa akan wani babban darduma dake gefen gadon, wanda kuma akansa ne Laylerh’n take.
Chapter 128 · 0% Book details