Sashe 35
Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zaune yake acikin babbar motar tasa ƙiran Prado LandCruiser, yayinda ya sanja shigar jikinsa zuwa wani tsadadden yadi me kyau, time to time yake ɗan duba agogon dake ɗaure atsintsiyar hannunsa, ɗago kansa da yayi ne ya bashi daman hangota, wanda fitowarta daga falon kenan, lokaci ɗaya ya zuba mata mayun idanunsa baya ko ƙyaftawa, kasancewar kuma garin yaɗan ɗau sanyi ne yasa shuke shuken bishiyoyin da ke compound ɗin gidan soma kaɗawa, hakanne kuma yabawa doguwar rigar dake jikinta daman buɗewa, sanadin hakanne yasa kayan jikinta fitowa fili, tare kuma da bayyana shape ɗinta.
Idanunsa da suka sauƙa akan shape ɗin cikinta da kuma hips ɗinta ya ɗan lumshe, tare da jan wani dogon numfashi, dan kuwa har cikin ransa ya yaba da kyau da kuma tsarin halittar ta, lokaci guda kuwa yaji wani irin hot feeling na jansa zuwa gareta, numfashi me zafi ya fesar tare kuma da sake kafeta da ido, ko acikin ransa yasan cewa haƙiƙa samun ta amatsayin mata babbar nasarace ga kowani Ɗa Namiji, haka kuma rashinta daidai yake da duk wani ƙuncin rashin samun nasara.
Samun kanta acikin compound É—in gidanne yasa ta cigaba da daidaita nutsuwarta, kyawawan idanunta ta zubawa gaba É—aya cars din dake cikin compound É—in gidan, kasancewar akwai tarin motoci agidanne yasa ta kasa tantancewa kanta wace mota ce Najeeb din ke ciki.
Murmushi yayi domin daga ganin yanda take ta kalle kalle ya fahimci cewar bata gane wace mota yake ciki ba, kasancewar baya son wahalar da'ita ya sashi danna horn É—in motar.
Jin horn ɗin mota agefenta ne yasa ta dawo da kallonta inda taji ƙaran, hangosa tayi zaune agaban motar ɓangaren driver ya tsura mata idanu baya ko ƙyaftawa, ganin irin kallon da yake matane yasa ta sadda kanta ƙasa, tare da soma takawa cikin nutsuwa ta ƙarasa wajen da motar nasa ke fake.
Daga ciki yasa hannunsa ya buÉ—e mata murfin motar wanda hakan ya bata daman shiga ciki ta zauna, ahankali ta maida murfin motar ta rufe tare da É—an lumshe idanunta.
"Kin shanyani da yawa."
YafaÉ—ayana me kai dubansa gareta.
Jin abun daya faɗa ɗinne yasa ta ɗago ɗara ɗaran idanunta ta kalleshi, kana lokaci ɗaya kuma ta sadda kanta ƙasa. Ganin hakane ya sashi zuba mata idanunsa cike da son karantar yanayinta, saboda yaga gaba ɗaya mood ɗinta ya sanja.
"Laylerh!." Yaƙira sunanta cikin yin ƙasa da murya.
Samun kanta tayi da kasa amsa masa haɗe kuma da kasa ɗago kai ta kalleshi, kwata kwata batason ya fahimci rauni haɗi da damuwarta, wanda tasan ko daga cikin muryarta zai iya fahimtar hakan, domin ayanzu idan tace zata tsananta magana tabbas kuka zai iya ƙwace mata.
"Laylerh!!."
Ya kuma ƙiran sunanta akaro na biyu. Yanayin yanda taji muryarsa tayi sanyi sosae ne yasa ta ɗago kai ta kalleshi.
Idanunsa acikin nata ya sakar mata murmushi, tare da soma yi mata wani irin shu'umin kallo, cikin son ƙarfafa mata guiwa haɗe da gusar da duk wata damuwa dake kan fuskarta yace. "Ba yau ba, ba kuma kullum ba sam damuwa bata kamaci kyakkyawar fuskarki ba, zai fi kyau ako da yaushe ki faɗi abun dake cikin zuciyarki akan ki ɓoyeshi, kisani ita damuwa tana gushewane kawai idan kasamu ka fitar da abun dake cikin ranka, sannan kuma barinta azuciya kwata kwata baya kawo mafita, sometimes saidai ya sake jefaka acikin wani hali, inaso ki gusar da damuwar dake kan fuskarki ta hanyar faɗaɗa murmushinki, kina da kyau saboda haka murmushi yafi dacewa dake ako da yaushe, ko wani bai taɓa faɗa miki cewar kina da kyau ba ne?."
Idanu ta tsura masa saboda har acikin zuciyarta so take ta fahimci inda kalamansa suka dosa, kasancewar ayanzu komin ƙanƙantar hanyar da zaisa ta fahimci abun dake cikin zuciyarta nemansa take.
Ganin yanda take kallonsa ne yasashi sakin murmushi tare da É—auke kansa daga gareta, domin yasan idan ya cigaba da kallonta to bazai iya controlling É—in kansa ba, anutse yayiwa motar key tare da É—anyin reverse, ganin hakane yasa maigadi wangale masa wawakeken gate É—in gidan ya cilla hancin motar tasa waje.
Idanunsa da sukayi matuƙar ja ya rumtse, tare da sakin curtain ɗin window'n dake riƙe ahannunsa, ahankali ya juyawa window'n baya, yayinda yakejin wani irin raɗaɗi da kuna na sukar zuciyarsa, wani irin abu me kama da zallan kishi ne ya tokare masa ƙoshi, har zuwa yanzu abu ɗaya ne ke yawo acikin idanunsa, wato ganin da yayiwa Laylerh'n tare da Najeeb riƙe da hannun juna, wanda yanzu ma again akan idanunsa yaga ficewarsu daga cikin gidan, kansa da yakejin ya masa nauyi ya riƙe, tare da ware idanunsa wanda suka ƙara zama jajur kaman wanda aka watsa musu jan barkono, tafasan da zuciyarsa keyi ne yasa hatta sautin fitan numfashinsa ma saida ya sauya. Lallai ba ƙaramin asara bane rasa abun da yakasance kamar fata da buri agareshi, tabbas arayuwa akwai ƙaddarori masu tarin yawa acikinta, saidai wata Ƙaddaran tafi gaban kwatance, domin zafi da kuma ƙunarta takan iya raunata gaba ɗaya rayuwa. Hannayensa ya zuba acikin aljihun wandonsa, tare da fesar da wani zazzafan numfashi, ɗan jingina bayansa da jikin window'n yayi, saboda bayajin zai iya barin wajen batare da yaga dawowan Laylerh'n cikin gidan ba, domin yaune karon farko daya fara jin cewa yayi mistake na ɓoye gaskiyar abun dake cikin zuciyarsa, wanda sanadin haka gashi yana neman rasa duk wani muradi da kuma ƙwarin guiwarsa, tabbas bazai iya jurewa ba matuƙar Ƙaunar daya jima yana kiwonta acikin zuciyarsa ta watse alokaci guda.
Æangaren Laylerh kuwa jin sun hau tsakiyar titi ne yasata jingina bayanta da jikin kujeran motar, tare da maida gaba É—aya kallonta zuwa kan titi tana kallon yanda ababen hawa keta zirga zirga, wanda azahirin gaskia kuwa hankalinta ba akan ababen hawan yake ba, tunani da nutsuwarta ne kawai ke Æ™oÆ™arin tafiya zuwa wani waje na daban. Tabbas tasan babu wani abun Æ™i atattare da Najeeb, kama daga kan halayya É—abi'unsa dama yanayin tsarin halittarsa,saidai kuma koma yaya zuciyarta ta karkata ne izuwa wani waje na daban. "Inasonki!." Maganar da Najeeb din ya faÉ—a É—azu kenan da ke ta yi mata yawo cikin Æ™waÆ™walwarta, ahankali taÉ—an lumshe idanunta, kana kuma acikin rai da zuciyarta yanda babu me iya ji ko karantar yanayinta tace. "Tayaya Najeeb ya fahimci cewar yana sona kuma har ya iya gayamin? hakan na nufin cewa yasan alamomin so da kuma wanda ba so ba kenan? haka kuma furta kalman SO ga wanda kake so, bai zamanto abu me wahala ba kamar yanda ta É—auka, lallai tabbas tana da buÆ™atar wanda zai gaya mata ya kalan nata SO É—in yake." ÆŠan nisawa tayi tare da sauÆ™e ajiyar zuciya akaro na barkatai, tabbas tana da buÆ™atar sanin amsan duka waÆ´annan tambayoyin dake cikin ranta, nan ta yanke shawarar cewa zata tambayi Najeeb, kuma bata damu ba koda kuwa zai gane cewa bashi take so ba.
Momy
Safa da marwa take tayi atsakiyan katafaren ɗakinta, babu komai acikin zuciyarta kuwa face son ganin cikar burinta. Wayarta dake aje kan bedside ne ta soma ƙara, alaman shigowar ƙira, hakanne kuma yasata tsayawa daga tafiyan da take tare da kai dubanta inda ta ajiye wayar tata, ɗan jim tayi tana tunanin wanda zai ƙirata adaidai lokacin, jin ƙiran wayar na neman katsewa ne yasa da ɗan sassarfa ta ƙarasa wajen da wayar take, ganin sunan Aina'u akan screen ɗin wayar ne yasa cikin sauri tayi picking call ɗin, batare kuma da ta jira Aunty Aina'un tayi magana ba tace.
"Bani da wadataccen lokaci Aina'u, ayau nakeson ruguza rayuwar Laylerh dama duk wani farincikin daya rage mata ta hanyar amfani da babban Rauninta wato Maleek!."
Jin Abun da Momyn tafaÉ—a ne yasa Aunty Aina'u sakin murmushi, cikin son fahimtar da Æ´ar uwartata tace.
"Rusa ƙauna me tsanani kamar wacce ke tsakanin Maleek da Laylerh ba abu bane me sauƙi kamar yanda kika ɗauka Hajiya Suwaeba, lallai dole muna buƙatar nutsuwa kafun aiwatar da komai, domin yin abu cikin gaggawa zai iya jawo mana tonon asiri, kuma kinsan dukanmu bazamu so hakan ba."
ÆŠan jim Momy tayi cikin rashin fahimtar kalaman Aina'un tace. "Me kike nufi, ban fahimci kalamanki sam."
Murmushi Aunty Aina'u tayi cike kuma da son bayyana abun dake ranta tace.
"Baikamata plan ɗinmu ya faraci daga yanzu ba, tabbas ada munyi tunanin cewa Alhaji Jaheed, Maleek zai aurawa Laylerh, sai kuma yazo ya ɓata mana tunani, ta hanyar bawa Najeeb aurenta, kuma hakan da yayi damace ya bamu me kyau, wanda zamu ɓata rayuwar Laylerh ta hanyar ɗansa Maleek, sanadin hakan kuma zai jawo tsana me tsanani tsakanin Maleek da Laylerh har ma kuma dashi Alhaji Jaheed ɗin kansa, domin nayi imani cewa matuƙar yafahimci cewa Maleek na bibiyan Laylerh bayan kuma tana da aure abun bazai taɓayin kyau ba, ba kuma mu da yanda zamuyi wanda ya wuce mu bari Maleek ya nemi Laylerh da aurenta."
Jin abun da Aina'un tafaɗa ne yasa Momy lumshe idanu, tare da sakin wani shu'umin murmushi, lallai tayarda ƙanwarta Aina'u tafita kaifin hankali da kuma tunani haɗi da iya shirya mugunta, gashi yanzu take ta samu kanta acikin farinciki da kuma zallan nishaɗi.
fashewa da wata irin dariya me ɗauke da tunanin samun nasara tayi, sai kuma da tayi dariyan sosai kafun taɗan tsagaita cikin yarda da shawarar ƙanwartata tace.
"Tabbas kinyi magana me ma'ana Aina'u, zan kuma bita ayanda ta dace, saidai kada ki manta aƙwarine na ɗaukarwa kaina cewar sai Maleek ya zamanto silar lalacewar rayuwar Laylerh, bansan meyasa ba nakejin wani abu adangane dasu, lallai barinsu su biyun zai iya kawomin matsala ako da yaushe, tabbas zan bari Laylerh ta auri Najeeb domin hakan ma wata damace dazan samu, wanda kuma nasan abu mafi munin baƙin ciki shine Maleek ya kusanci Laylerh da aure akanta, tabbas zanso hakan domin mafari ne na hargitsewar rayuwarsu!."
Dariya suka saka su dukansu, daga bisani kuma suka yi sallama.
Ajiye wayar Momy tayi tare da yin murmushi, tabbas burinta ne ta ƙuntatawa rayuwar Laylerh da kuma ta Maleek, cikin isa da kuma bayyanar da abun dake cikin zuciyarta tace.
"Dole saina tono sirrrin dake ɓoye, sannan kuma kuskure ɗaya kayi arayuwarka Maleek, da ka bari nasan cewa Laylerh itace Rauninka."