← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 144

Sashe 112

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakan da tayi d’inne kuma yasa Abbou Jaheed controlling hawayensa, ahankali ya soma shafa kanta, murya atausashe kana kuma cikin yanayin dake bayyana k’aunarsa agareta yace.
“Hak’ik’a da ana iya sauya k’addara go goge zanen abunda ya wuce da nayi hakan Laylerh, da na nesantaki da duk wasu munanan k’addarorin dake bibiyar ki, da kuma ace nasan wannan ranan zata zo, to da har abada ban bari an d’aura aurenki da Najeeb ba, duk da kuwa nasan cewar Najeeb baiyi hakan dan ya cutar da rayuwarki ba, kamar yanda nasani cewa har abada bazae tab’a iya cutar dake ba, Tabbas na zab’a miki Najeeb ne amatsayin miji, saboda ya cancanta, na kuma yi musu alk’awarin bashi aurenki tun lokacin kina k’ank’anuwa, sam ko kusa banyi hakan dan na cutar da rayuwarki ba Laylerh, domin duk da kasancewar bani na haifeki ba, amma ina miki son da nakeyiwa d’an cikina, kuma koda banine mahaifinki ba, jinin dake gudana acikin jikinki na d’an uwanane, ke d’in wata kyautace guda d’aya da Allah Ya bamu, saboda haka bazan tab’a son abunda zai cutar dake ba Laylerh...�

D’an tsagaitawa da maganganun nasa yayi, tare dasa hannunsa ya d’ago kanta, cikin son bata k’arfin guiwa da kuma nuna mata cewar tana da gobe mai kyau yace.

“Kada kiyi bak’inciki ko k’unci Laylerh domin k’addararki ce tazo ahaka, sannan kuma kada ki yiwa Najeeb mummunan zato akan abunda ya aikata, domin ko kad’an Najeeb baiyi haka dan ya cutar da rayuwarki ba, yamin bayanin komai kuma nafahimta, sannan nasan kema watarana In sha Allah Zaki fahimta, domin ni Abbou Jaheed har abada bazan tab’a yi miki zab’in da zai cutar da rayuwarki ba, sannan kuma akullum inaso kina tuna cewar komae daya faru da kuma wanda zai faru duk k’addararren al’amarine, Allah Baya tab’a d’aurawa bawansa abunda bazae iyaba, aduk kuma lokacin da kikaji k’unci ki ambacesa zae sauk’ak’amiki kinji!!�

Kanta tajinjinawa Abbou Jaheed d’in alaman gamsuwa, tare kuma da k’ok’arin b’oye duk wani abunda ke damun zuciyarta.

Ganin k’warin guiwa akan fuskarta ne kuma yasa Abbou Jaheed yaji zuciyarsa tayi wani irin sanyi.

Kanta ya sake shafawa, domin har acikin ransa yana me alfahari da ita.
Cikin kuma son jin ta bakinta yace.

“Mun yanke shawara nida Abbou Khareem da kuma Oum Ayush cewar zakije gidan Aunty Zainab kiyi iddah’n ki acan, saboda acan din zakifi samun nutsuwa, idan yaso bayan kin gama iddah’n saiki dawo, idan kuma kinaga zaki zauna anan d’in shikenan.�

K’asa tayi da kanta tare da d’an soma wasa da y’an yatsun hannunta, cikin kuma yanayin sanyi mai kaman shagwab’a daya zame mata sabo tace.
“Abbou Jaheed duk hukuncin da kuka yanke akaina daedae ne.�

Jin abunda tace d’inne kuma yasa Abbou Jaheed da kuma Abbou Khareem jinjina kai.

Daidai lokacin kuwa Oum Ayush ta shigo cikin falon, jaye da wani babban trolleybag da ta zubawa Laylerh kayan ta aciki.

Ajiye trolleybag d’in tayi, tare da kallon Aunty Zee cikin kulawa tace.

“Ya kamata kutafi domin naga magriba na k’ara shigowa.�

Hakan da tace d’inne kuma yasa Aunty Zee mik’ewa tsaye, tare da jan trolleybag d’in Laylerh’n ta nufi hanyar waje dashi.
Ganin hakanne kuma yasa Oum Ayush ta rufa mata baya.

Laylerh kuwa asanyaye ta mik’e tsaye, Abbou Khareem ne ya rik’o hannunta ya samata bandir d’in kud’i na 50/50k, had’e kuma da damk’a mata ATM CARD d’inta, wanda tun lokacin da akayi bikinta atm card din ke hannunsa, wanda ayanzu ya k’ara zuba mata kud’ad’e masu yawa aciki.

Bakinta na shagwab’a ta bud’e, saidai kuma saurin girgiza mata kai dayayi yasa dole tayi shiru.
Haka suka fito daga falon Abbou Jaheed d’in tana tsakiyarsu, har wajen da motar Aunty Zee ke fake suka rakata, bayan ta shiga motar ta zaunane kuma Oum Ayush ta mik’o mata wayarta.
Karb’an wayar tayi tare da ajiyewa akan cinyarta, kana ta jingina bayanta da jikin kujeran motar.
Idanunta da sukayi raurau ta tsayar akan had’add’en part d’insa da take hangowa, haka takejin zuciyarta na wani irin bugawa, shi kawae taji tanason gani ayanzun, domin tasan ba k’aramin kewa da kuma wahalar da ita soyayyarsa za suyi ba.
Idanunta da suka d’an ciko da k’walla ta lumshe.
Adaidai lokacin kuwa da motar Aunty Zee zata fita daga gidan, motarsa ta kunno kai.
Jin k’ara da kuma horn d’in motar tasane yasa tayi saurin bud’e idanunta, cikin sa’a kuwa ta sauk’esu akansa, inda yake zaune ab’angaren driver.
Idanunta ta tsura masa bata ko k’yaftawa, shikuwa samma bai kula dasu ba domin sauri yake sosae.
Ganin hakanne kuma yasa Aunty Zee ta matsa gefe saida ya shige cikin gidan kafun sukuma suka fita.

Fitansu daga cikin gidan kuwa yayi daidai da zubowar hawayen dake cikin idanunta.

Shikuwa Maleek da sauri ya fito ko gama daidaita parking d’in motar tasa ma baiyi ba.
Hakan yasa hankalinsu Abbou Jaheed
dawowa kansa, cikin yanayin mamakin irin saurin da yakeyi Abbou Khareem yace.

“Captain lafiya kake kuwa?�

Kansa ya jinjina, cikin kuma yanayinsa na wanda bai cika yin magana ba yace.

“Zanbar Nigeria yau, wani aikin gaggawa ya tasomin, 7:00 pm daidai flight d’inmu zai tashi.�

Cike da mamaki dukansu suka bud’e baki suna me binsa da kallo, kasancewar yayi musu maganar ne yana tafiya batare dako tsayawa yayi ba.

*5:30 pm*
3/13/21, 10:08 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*Not editing*

*Chapter 66*

Sosae jin maganan tafiyar tasa ta basu mamaki, amma kuma saidai ganin kwata kwata bai juyo ya kallesu bane, yasa suka bisa da idanu har saida ya b’acewa ganinsu.

Abbou Jaheed ne ya d’an girgiza kansa, Yayinda kuma acikin ransa yake mamakin hali irin na Maleek d’in, baidamu da kowa ba sam, shikad’ai yake son gudanar da rayuwarsa ako da yaushe, kimin damuwa da k’uncin dake cikin zuciyarsa kuwa yakan iya shanyeta, ta yadda bazae bari wani ya fahimci hakan ba.
Juyawa yayi batare daya sake cewa Komai ba ya nufi sashinsa, domin tun sanda Najeeb yaje masa da zancen sakin Laylerh yakejin zuciyarsa nayi masa wani iri, komai bayayi masa dad’i, duk da kuwa cewa Najeeb din yayi masa gamsashshiyar bayanin daya fahimta.

Tafiyar tasa ce kuma tasa Abbou Khareem dama Oum Ayush suma suka wuce sashinsu.

Ab’angaren Maleek kuwa koda ya k’arasa cikin part d’innasa direct bedroom d’insa ya wuce.
Wani d’an madaidaicin jaka irin wanda ake goyawa abaya ya d’auka, tare da zuge zip d’in jakan, anutse ya soma shirya duk wani abu dayasan zae buk’ata, saidai kuma acikin shirin nasa sam babu kaya ko d’aya, domin hakanan ya saba ko ina zaije tofa baya tafiya da kayan sawa, saidai idan yaje duk inda zashi d’in ya saya sabi.
Laptops d’insa guda biyu ya tura acikin jakar, domin kuwa yasan sosae yake da buk’atar kowannensu, domin d’aya na aikinsa ne, d’ayan kuma acikinsa yake ajiye duk wasu abubuwansa musamman privacy d’insa, hakanne kuma yasa kusan gaba d’aya sirrukansa na cikin wannan laptop d’in.

Maida zip d’in jakan yayi ya rufe, tare da d’ago kansa ahankali ya sauk’e idanunsa akan zanen kyakkyawan flower’n dake gefen gadonsa, wanda idan mutum ya kalla, azahiri babu abunda zai fahimta sai zanen flower’n, saidai kuma amma abad’ini bawae iya zanen flower’n bane kawae, ga wanda yayiwa zanen kallon tsab kuwa, Tabbas zai iya hango zanen hoton fuskar mace, wanda aka k’awata zanen flowers masu kyau akan fuskarta, wannan yasa ba kowa ne zae fahimci cewar bayan flowers akwae wani zanen fuskar mutum awajenba.
Lumsassun idanunsa dake bayyana gajiya ya d’an lumshe ahankali, kana ahankali ya shiga takawa, har zuwa inda zanen flowers d’in suke, ahankali cikin kuma wani irin sassanyar yanayin daya samu kansa aciki, ya d’aura hannunsa adaidai saitin fuskar dake jikin zanen.
Hakika sosae da sosae yakeson zanen, wannan shiya sama ya manna sa agefen gadonsa, bawai kuma yanason zanen dan mak’udan kud’ad’en daya kashe wajen yinsa bane, yanason zanen ne saboda hasken fuskar mace d’aya ya bayyana acikinsa, macen da akowanni bugun zuciya da numfashinsa soyayyarta ke k’aruwa, macen da har yau bayajin wani a zuciyarsa kamar yanda yakejinta, macen da ya d’auki sama da shekaru yana rayuwa da soyayyarta maitsanani acikin zuciyarsa, sannan kuma macen da zai iya sadaukar da komae nasa akanta, arziki dama rayuwarsa gaba d’aya, wanda baidamu ba idan shi zaiyi bak’inciki matuk’ar ita zata kasance acikin farinciki.
Sassanyar ajiyar zuciya ya sauk’e, tare da sanya hannayensa duka biyu ya d’auko zanen, da aka k’awata acikin wani glass d’in ruwan diamond.

Sassanyun idanunsa ya sake lumshewa akaro na biyu, Yayinda har acikin rai da zuciyarsa yakejin wani irin abu na ratsashi.
“I will miss you!!�
Yafad’i hakan cikin wata irin murya dake fitar da slowly sound, irin dai muryarnan dakesa mai sauraronta bacci.
Ahankali ya maida zanen ya ajiye tare kuma da juyawa ya d’auki jakansa, wanda ya gama had’a komansa da yasan zai buk’ata aciki.
Rataya jakan akan kafad’ansa na dama yayi, tare da d’aukan phones da kuma passport and ticket d’in flight d’in da zaibi.
Kamar dai yanda ya saba akoda yaushe, idan zaiyi nisa sai yayi light off na gaba d’aya wutan part d’insa kafun yake tafiya, yanzun ma dai hakanne ta kasance saida ya kashe komai kafun ya fice daga cikin part d’in nasa.

Yana fitowa cikin compound d’in gidan kuwa Abdoul wanda shine zai kaisa airport, da sauri ya k’araso ya k’arbi jakan dake kafad’an Maleek d’in, tare da bud’e masa murfin wata black car range rover velar 2019, wanda acikinta ne zaikai M.Jay d’in airport.

Shiga cikin motar yayi ya zauna, tare kuma da jingina bayansa ajikin kujeran motar, ya saki wani irin sassanyan numfashi, idanunsa ya d’an lumshe kamar yanda hakan ya zama wata d’abi’arsa, batare kuma daya bud’e idanun nasa ba, cikin halinnasa nason rashin tsawaeta magana yace da Abdoul.
“Kawomin cutie.�

“To.� Kawae Abdoul yace had’e kuma da juyawa cikin sauri ya nufi d’aya daga cikin gardens d’in dake cikin gidan, wanda ananne cat d’innasa take hutawa.

Shikuwa Maleek tafiyan Abdoul d’inne yasashi d’ago kansa tare da bud’e idanunsa, ya sauk’esu akan part d’in su Laylerh’n, hakanan yakejin wani irin abu na yawo acikin rai da zuciyarsa, duk da yasan cewar adaman abunda yakeji d’in akwae babban rauni, amma koda wasa bazae tab’a bari zuciyarsa ta cigaba da kassara ba, duk da kuwa yasan cewar zaiyi kewarta sosae.
Chapter 112 · 0% Book details