← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 144

Sashe 76

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

B’angaren Captain kuwa tunda suka baro gidan Alhaji Farouk d’in ya kasa sakin rai da fuskarsa, hakanan yakejin wani irin k’unci acikin zuciyarsa, yayinda gaba d’aya takaicin yarinyar da ake k’ok’arin lik’a masa dan ya aura yabi ya cika masa zuciya, domin kwata kwata baiyi tunanin cewa irin wannan zab’in Abbou Jaheed zaiyi masa ba, shin wai ma tayaya zai fahimtar da Abbou Jaheed cewar agaba d’aya rayuwarsa bayason kowacce irin mace idan ba Laylerh ba? Hak’ik’a baya mafarki da burin mallakan wata na daban arayuwarsa, so da k’auna acikin zuciyarsa guda d’aya ne kuma ya riga daya bawa Laylerh su, duk da cewar bai sameta amatsayin mata ba kuwa soyayyarta bazata tab’a fita daga cikin zuciyarsa ba, tabbas yasan cewa ayanzu cigaba da tunani ko kuma muradin Laylerh zunubi ne agaresa, amma kuma bashi da ikon hana kansa sonta, tabbas soyayyarta acikin jini da tsokansa take, haka kuma halittaciyar abace da aka halicceta tun shekaru masu yawa da suka shud’e, yayarda cewa soyayyar Laylerh k’addarace agaresa, yayarda ya d’auki hakan amatsayin k’addara, daga haka kuma baya fatan wata sabuwar k’addaran ta sake shigowa rayuwarsa. Arayuwa Laylerh yaso kuma ita zaicigaba da so har zuwa k’arshen rayuwarsa.
Jin wani irin burkin da drivern ya taka ne yasashi d’ago kansa dake duk’e, ganinsu da yayi agaban tamfatsetsen gate d’in gidan nasu ne yasashi maida idanunsa ya lumshe.
Akasalance yasa hannu ya bud’e murfin motar yafice, kasancewar tun fitowarsu daga gidan Alhaji Farouk Abbou Jaheed ya sanar dashi cewa zasu sauk’eshi abakin gate ne dan zai wuce office.
Hakan kuwa akayi domin yana fita daga cikin motar Abbou Jaheed yasa drivern yaja motar suka bar wajen.
Ahankali yasa hannu ya tura y’ar k’aramar k’ofar dake jikin gate d’in.
Maigadi kuwa dake zaune jin alaman za’a shigo cikin gidanne yasashi tashi azabure cikin fad’a fad’a yace.
“Waye haka yake tab’a mana k’ofa.....� Sauran maganganun dake cikin bakinnasa ne suka mak’ale asakamakon ganin Maleek d’in da yayi, cikin sauri ya k’ame jikinsa waje d’aya, duk da cewar kuwa shid’in ba soja bane, amma yayi hakanne dan girmamawa da kuma son kare kansa, kasancewar tunda yake agidan baitab’a ganin murmushin Maleek d’inba, wannan dalilin yasa yake masifar tsoronsa, domin yasan irinsune da idan suka tashi lokaci d’aya suke raba k’ashin mutum gida biyu, abu me sauk’ine shiga huruminsu yasa su b’abb’allaka.
“Barka da dawowa Sir.�
Ya fad’a cikin yin k’asa da murya, domin a yanda yaga fuskar M.Jay d’in amurtuk’e, lashakka zai iya bindigesa ma.
Duk da cewar kuwa baya cikin mood me dad’i, amma haka yasamu kansa da jinjinawa gateman d’in kai, alaman ya amsa gaisuwar tasa, wanda yayi hakanne kuma saboda sam wulak’anta mutane baya d’aya daga cikin halayyarsa, saidai wanda ya zubar da kansa, yasani cewa shi miskiline na k’arshe sannan babu ruwansa da rayuwar kowa, amma kuma baya wulak’anta na k’asa dashi, hakan kuma ya zame masa d’abi’a da kuma al’ada because zuciyarsa akwae rauni sosai, shi mutum ne me matuk’ar tausayi, saidai kuma amma tausayin nasa ba abayyane yake ba, yakanyi ne kawae idan yanayi yazo da hakan.
Da kallo gateman d’in ya bisa, yayinda shi kuma cikin takunsa na isa, ya k’arasa shigowa cikin gidan, kaitsaye part d’insa ya so nufa, amma kuma saidai tunawa da yayi cewar yau tun safe baiyi training bane yasashi fasa shiga b’angaren nasa kaitsaye ya juya akalan tafiyannasa zuwa inda yake aje motocinsa.
Tunkafun ya k’araso wajen kuwa ya gama yankewa kansa hukunci cewar, babbar Corolla d’insa zai hau, kasancewar tunda aka kawo masa ita sau uku kawai ya tab’a hawanta, duk da kuwa cewar motar me tsadace sosae amma baiwani damu dason shiganta ba.
Isowarsa jikin motar ne kuma idanunsa suka sauk’a akan Laylerh wanda har yanzu ke durk’ushe awajen yayinda tafukan hannunta ke kan fuskarta.
Sauk’e idanunsa akanta da yayi kuwa yayi daidai da bugawar zuciyarsa, yayinda kuma atake yaji wani irin sanyi na ratsa gaba d’aya ilahirin jikinsa, har zuwa k’asan k’afarsa, wani irin abu da yaji acikin zuciyarsa ne yasashi d’an lumshe idanunsa tare da jan wani dogon numfashi.
“Metakeyi anan?.�
Yayiwa kansa tambayar yana me sake bud’e idanunsa ya sauk’esu akanta.
“Tana da damuwa.� Cewar zuciyarsa wanda akoda yaushe take jib’antan al’amuran Laylerh’n.
Labb’ansa yad’an cije tare da zuba mata, tsumammun idanunsa, take kuwa yanayin na yanzu ya juye masa zuwa wasu shekaru dasuka wuce, wani lokaci daya saba ganinta tana zaune cikin kad’aici da k’unci, lokacin da take kuka.
Tabbas Laylerh GARKUWA take so, bawai iya miji kad’ai ba, dole kafun tasamu wanda zai sata farinciki sai tasamu wanda yasan gaba d’aya yanayinta.
Wanda yasan kukanta ya kuma san dariyarta, tabbas ya taso acikin maraici amma kuma maraicin Laylerh yafi komai tsaya masa arai, yanajin matsanancin tausayinta fiye da kowa da komai, har idan aka cire soyayya irinta So da So, to k’aunan da yakeyiwa Laylerh ta y’an uwantaka tana da matuk’ar yawa, saboda yayi imani cewa akanta zai iyaba da komai nasa, ciki kuwa harda rayuwarsa, kamar yanda baya iya manta sunansa, haka ako da yaushe baya manta kalaman da Mahaifiyarta ke fad’a masa ashekarun baya, koda yaushe cewa take zata bar masa Laylerh ya kula mata da ita, ya sama mata farinciki marar yankewa, domin Laylerh tasace har abada, ko da kuwa wata k’addara tasa ya rasata, wata k’addara zata sake had’asu.
Tabbas akullum yana tuna wannan maganganun, wanda suke sa yaji zuciyarsa tayi matuk’ar rauni sosae, yanayin idanunsa ne suka sanja launi, wanda kuma hakan alamace dake bayyana asalin hak’ik’anin abunda ke cikin zuciyarsa.
Ahankali ya sake murfin motar dake hannunsa, cikin yanayin sanyi yayi takun da baiwuce taku hud’u ba, ya iso gareta.
Tsayawa akanta yayi duk da cewar kuwa yanajin zuciyarsa na bugawa sosae, haka ya d’aure ya d’an rank’wafo kanta.
Almost 2 minute yanason had’a kalman sunanta abakinsa, amma ya kasa, hakanan yaji harshensa ya masa nauyi, cikin sabon yanayin daya samu kansa aciki, ya d’aura hannunsa adaidai kan nata hannun, ahankali cikin wata irin murya me kama da rad’a ya k’ira sunanta.
Tabbas taji motsin mutum akusa da ita, saidai kuma kwata kwata bata kawo aranta cewar shi d’in bane, duk da cewar kuwa dadddad’an k’amshinsa ya kawowa hancinta ziyara amma tayi tunanin cewa kwad’aituwa da tayi dason jin k’amshin nasa ne yasa ta jin hakan.
Sauk’an sautin muryarsa acikin kunnuwanta kuwa shiyasa duk taji tsikar jikinta sun mimmik’e, ahankali ta d’an janye tafukan hannunta daga kan fuskar nata.
Cikin sa’a kuwa tajefa idanunta acikin nasa idanun, idanun da har abada bazasu tab’a daina yi mata gizo
ba, idanun da suka zama tamkar sinadari acikin rayuwarta.
Sam bazata iya jurewa kallon cikin rikitattun idanunsa dake sauya mata tunani akoda yaushe ba, wani irin fitinannen yanayin da ta samu kanta aciki ne kuma yasata d’an lumshe idanunta, wanda hakan da tayin kuma ya bawa hawayen dake cikin idanun nata daman gangarowa kan k’uncinta.
Maleek kuwa ganin hawayen da yayi akan fuskarta ne, yasa shi rumtse idanunsa, batare kuma daya bud’e idanun nasa ba, da muryarsa wanda baya fita sosae yace.
“Me yake damunki?.�
Jin tambayan da yayi mata d’inne kuma yasa ahankali ta bud’e idanunta, masu d’auke da zallan yanayin shagwab’a, wuyanta ta karyar gefe tare da d’an soma mamul mamul da bakinta, dagani kasan ba iya ciwo ne ke damunta ba harma da zallan shagwab’a.
Ganin kuma yanda takeyi da bakinnata ne yasa shi gane irin yanayin da take ciki, ahankali ya sauk’e ajiyar zuciya me tafiya da jan numfashi.
Hakanan yaji kaman ya jawota jikinsa yayi mata kyakkyawan hugging ko hakan zaisa ta samu relief daga damuwan dake cin zuciyarta, saidai kuma bashida iko da kuma daman hakan.
Hannunsa dake kan fuskarta ya janye, cikin son daidaita nutsuwarsa yace.
“Oum Ayush na k’iranki.�
Yanayin yanda ya fad’i maganar yana me juya bayansa ne yasa ta k’ura masa ido, domin kuwa bak’aramin kyau taga yayi mata acikin sigar yanayin maganar tasa ba.
Shikuwa Maleek ya fad’i hakanne dan rage mata damuwa, musamman yasan cewa idan taje wajen Oum Ayush bazata barta ta zauna da damuwa aranta haka ba, duk da cewa k’arya ba d’abi’arsa bane, amma gashi akanta dan dolensa saida yayi.
Ko juyowa kuwa baiyiba haka ya shige cikin motarsa.
Ganin hakan kuwa yasa ta mik’e tsaye duk da cewar kuwa har yanzu tanajin ciwon marar na damunta, amma ganinsa da tayi yanzu yasa tanemi kaso 40 na daga cikin ciwon nata ta rasa, dan kafun yanzu ko mik’ewa da kyau batayi amma gashi yanzu ta mik’e.
Asanyaye ta juya tare da kama hanyar sashin Oum Ayush d’in, dan amsa k’iranta kamar yanda ya fad’a mata.
Murfin motar tasa ya mayar ya rufe tare da bin bayanta da idanunsa masu d’auke da matsanancin soyayyarta, kasancewar sai ayanzune ma ya lura da shigar dake jikinta yasashi d’an lumshe idanunsa, saboda sauk’a akan had’add’iyar surar jikinta da sukayi, yasa shi jin wani iri ajikinsa.
Take kuma wani abu me kama da matsanancin kishi ya tokare masa k’irji.
Saidai kuma babu yanda ya iya, dole haka ya ja motar tasa da reverse yabar wajen.
Laylerh kuwa direct sashin Oum Ayush d’in ta nufa.
Ahankali ta murd’a handle d’in k’ofar falon ta shiga, bakinta d’auke da sallama.
Shigowar nata cikin falon kuwa yayi daidai da fitowar Oum Ayush daga cikin d’aki tana waya.
Saidai kuma ganin Laylerhn yasa bata wani ja wayan yayi tsayi ba ta kashe.
Kallon Laylerh’n tayi cikin kulawa tace.
“Yau amarya ne kuma da yawo.�
D’an K’aramin bakinta ta turo gaba, sakamakon Jin da tayi Oum Ayush d’in ta k’irata da sunan amarya.
Saidai kuma ganin Oum Ayush d’in acikin farinciki da tayi ne yasa ta neman waje ta zauna, cikin halin nata na shagwab’a tace.
“Oum Ayush gani, amma naga kamar kina cikin farinciki sosai, Allah Yasa Abbou Kareem ne yace bazaku sake komawa wata k’asa ba anan zaku ci gaba da zama.�

Jin abunda Laylerh’n ta fad’a yasa Oum Ayush sakin murmushi, had’e da neman waje itama ta zauna, cikin nuna jin dad’in labarin dake bakin ta kuwa tace.
“Ko d’aya ba abunda kike tunani bane, domin yanzu nagama waya da Abbou’nki (Abbou Jaheed) yace Nafara had’a kayan lefe domin nanda sati biyu masu zuwa auren Yayanki yau yaje yaga yarinya ta masa kuma har anbada sadaki.�
Chapter 76 · 0% Book details