Sashe 113
Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dawowan Abdoul wajen hannunsa d’auke da cutie ne kuma yasashi tsayar da duk wani tunaninsa, bud’e murfin motar yayi tare dasa hannu ya k’arb’i cat d’innasa, lallausan gashin jikinta ya soma shafawa ahankali, kamar dai yanda ya saba yi mata akoda yaushe.
Wanda ganin hakanne kuma yasa Abdoul shiga cikin motar, batare daya tsaya wani b’ata lokaci ba kuwa yayiwa motar key, had’e dayin reverse tayanda zai fita daga cikin gidan asauk’ak’e, dan tuni maigadi ya wangale musu makeken hate d’in gidan.
Cilla hancin motar kan titi da Abdoul d’in yayi ne kuma yasashi sake maida bayansa ya kwanta ajikin kujeran motar, still har yanzu kuma cutie d’innasa na jikinsa yana shafa gashinta ahankali.
Yayinda Abdoul kuwa cike da k’warewa yake murza steering motar, kaitsaye suka nufi airport.
Kamar kuma yanda suke akan hanya haka ya kasancewa ga su Laylerh ma, saboda kuma gidan Aunty Zee d’in nada nisa sosae ne yasa basu isa da wuri ba.
Tunda suka kama hanya kuwa Laylerh bata sake koda wani k’wakk’waran motsi ba, kasancewar zuciyarta cike take da abubuwa maban banta, duk yanda Aunty Zee d’in taso janta da hira dan d’ebe mata kewa kuwa, sam takasa sakin rai da zuciyarta, Tabbas ayanzu Bawae sakin da Najeeb d’in yayi mata bane ke damunta, wani irin matsanancin kewa da takeji ne ke damunta, dan gani take kaman bazata sake had’uwa da Yah M.Jay d’innata ba.
K’aran da taji da kuma alaman cewar sun iso gidan Aunty Zee d’inne yasa ta bud’e idanunta ahankali.
Daidai lokacin kuwa maigadi ya wangale musu gate d’in gidan, Aunty Zee ta shiga da motar ciki.
Anutse ta gama daidaita parking d’in motar tata, cikin kuma fari’a da sakin fuska ta dawo da kallonta ga Laylerh’n.
“Muje ko.�
Tafad’a tana me k’ok’arin bud’e murfin motar.
Asanyaye ta jinjina kanta alaman.
“To.�
Tare kuma da bud’e murfin motar itama ta fito waje.
Sannu ahankali take k’arewa had’add’en gidan Aunty Zee d’in kallo, wanda sosae aka kashe masa mak’udan kud’ad’e wajen k’awatasa.
Trolleybag d’inta dake gidan baya Aunty Zee d’in ta ciro, ita da kanta ta rik’e trolley d’in tare kuma da kama hannun Laylerh’n sukayi cikin gidan da ita.
Da sallama abakinta suka kutsa kai cikin babban falon gidan.
Aliya dake zaune afalon tana kallon film d’in Nollywood, jin sallaman Auntynta ne yasata d’agowa da sauri, tare da mik’ewa tsaye tana fad’in.
“Oyoyo Aunty Zee sannu da dawowa.�
“Yauwa Aliya sannu.�
Aunty Zee ta bata amsa adaidai lokacin da suka k’arasa shigowa cikin falon.
Wanda kuma sai alokacinne idanun Aliya suka sauk’a akan Laylerh.
“Masha Allah ji wata kyakkyawa!�
Tafad’i haka acikin ranta, tana me sakarwa Laylerh’n murmushi.
Itama Laylerh’n murmushi tayiwa Aliya’n wanda bazata tab’a finta ashekaru ba, haka kuma itama kyakkyawace duk da kasancewarta Brown skin amma tana da kyau sosae.
Trolleybag d’in Laylerh’n Aunty Zee ta mik’awa Aliya, kana cikin kulawa tace.
“Ki kaimata trolleybag d’inta d’aki, daga yau kinsamu k’arin y’ar uwa, saura kuma ki dameta da shegen surutunki, domin Laylerh ba mai yawan son hayaniya bane.�
Murmushi Aliya tayi tare da amsar trolleybag d’in, cikin matuk’ar jin dad’i tace.
“No bazan dameta da surutu ba, ae sometimes kina bani labarinta, yau dai kam gashi Allah Yayi naga Beautiful Night da idanuna.�
Idanu Aunty Zee da Laylerh suka d’an zaro, cikin kuma yanayin mamaki Aunty Zee tace.
“Beautiful night kuma Aliya?�
Kai Aliya ta gyad’a, kana tana dariya tace.
“Eh mana Aunty Zee beautiful night, ma’anan Laylerh ai dare ne, to ita kyakkyawan dare ne mai yawan stars.�
Dariya Aunty Zee tayi, tare kuma dajan wani d’an guntun tsaki, domin kuwa idan da sabo to ta saba da halin Aleeya, always acikin shirme da yawan surutu take.
Laylerh ma murmushi tayi, saidai batace komae ba, hannunta Aleeya ta kama suka nufi d’aya daga cikin d’akunan dake k’asa wanda acikinsane d’akin Aleeya d’in yake.
Har sunkai bakin k’ofar muryar Aunty Zee ya tsaidasu inda take cewa.
“Idan sun shiga d’akin Aleeya ta shiryawa Laylerh kayanta acikin drawer, sannan kuma ta taimaka mata tayi wanka, daganan sai suzo suci abinci.�
Da “To.� Aleeya ta amsa sannan suka shige cikin d’akin, itakuwa Aunty Zee sama ta haura, Dan anan bedroom d’inta dana mijinta da kuma na two kids d’inta suke.
*M.Jay*
Shigowarsu cikin airport d’in kenan aka soma k’iraye k’irayen sallan magrib, hakan yasa Abdoul na gama parking ya bud’e murfin motar ya fito.
Saidai ma tun kafun ya gama fitowa abokan aikinsa wanda dasu za’ayi tafiyar, sukayi saurin k’arasowa wajen tare da sara masa, kasancewar dukansu shine ogansu, duk da cewar kuwa suma sunada babban matsayi amma nasa matsayin ya fi nasu, kuma akowanni tafiya shine shugabansu, haka ko awajen horarwa ma shine mai horar dasu.
Yana gama fitowa daga cikin motar tasa kuwa Fou’ad na k’arasowa wajen, wanda shima yau shirye yake tsab cikin soldiers uniform d’insa, da suka k’ara bayyana zallan kyawunsa, wanda har idan ka kallesa ba zaka ce shine wannan mai raunin ba.
Hannu ya mik’awa Maleek d’in suka gaisa, tare da soma yi masa wani irin kallo mai d’auke da tambayar.
“Har yaushe ka warke da zaka iyayin wannan tafiyar?�
Gane abunda Fou’ad d’in ke nufine kuma yasa Maleek d’auke kai daga kallonsa, murfin motarsa ya bud’e ya d’auko goran ruwa, batare daya kula kowannensu ba kuwa ya soma gabatar da Alwala’n sallan Magriba.
Ganin hakan da sukayine kuma yasa dukkaninsu kowa ya nemi ruwa yayi alwala.
Bayan dukansu sun kammala alwalan ne kuma dukansu suka had’a jam’i sukayi sallan magriba.
Daganan gaba d’ayansu suka nufi jirgi, domin tuni wasu harsun fara shiga.
Kasan shine yayi na k’arshen shiga jirgin, wanda yana shiga baijimaba kuma aka kulle k’ofar jirgin.
Kamar kuma yanda yake atsare 7:00 pm daidai jirginnasu ya d’aga zuwa sararin samaniya.
Abdoul kuwa ganin tashinsu ne yasashi komawa cikin mota inda ya tarar da kuliyar Maleek d’in nata harkokinta kamar yadda ta saba, tuna halin Captain d’innasu ne kuma yasa shi sakin murmushi, tare da yiwa motar key kaitsaye ya kama hanyarsa ta dawowa gida.
Kallon Momy Aunty Aina’u tayi fuskarta d’auke da tsananin mamaki tace.
“A gaskiya bangane abunda kike son fad’aminba Aunty Suwaeba, wai kina nufin da gaske Najeeb ya saki Laylerh, yanzu kwata kwata babu aure atsakaninsu?.�
Wani irin Murmushi mai d’auke da ma’anoni daban daban Momy dake zaune akan kujera tayi, Tabbas ayanzu ita kad’ai tasan abunda take sak’awa acikin rai da zuciyarta, domin alk’awari tayi cewar bazata tab’a bari wannan lokaci da kuma daman da tasamu su tafi abanza ba.
D’an k’walin dake kanta tad’an turo gaba, cike kuma da son bayyana gaskiyar abunda ke cikin zuciyarta tace.
“Abune da kika sani Aina’u akan wannan bazan tab’a gaya miki ba gaskiya ba, Tabbas Najeeb ya saki Laylerh, wanda kuma dasa hannuna hasalima ninayi duk wani abu dayasa ya saketa, Nina bankad’a masa sirrin da ke b’oye, har kuma nasa yaga hakan da idanunsa, yanzu kuma na samu abunda nakeso.�
Takai k’arshen maganar nata da wani irin alfahari.
Wanda yasa Aina’u zuba mata ido, domin kuwa har yanzu bata gane inda kalaman Yayartata suka dosa ba.
Saidai kuma k’aguwa dason sanin mene plan d’in yayartata na gaba yasa ta cewa.
“Yanzu Mekika shirya musu anan gaba? Sannan kuma mekika aikata haka dahar yasa Najeeb ya saketa? Saboda meyasa kuma kikayi hakan?.�
Jin tambayar da Aina’un tayi matane yasa ta mik’ewa tsaye.
Tare da d’an soma tafiya, saidai kuma ko taku uku batayi ba ta tsaya da tafiyan da takeyi d’in.
Still wani shu’umin murmushi ta sakeyi tare da had’e hannayenta waje d’aya.
Cikin muryar dake bayyanar da gaskiyar mummunan manufarta tace.
“Saboda inason na maida ita karuwarsa, tayanda zasu kusanci juna batare da aure ba, idan kuma har baki fahimci abunda nake nufi ba, to ma’ana ina nufin su aikata ZINA kenan, so nake nasa musu wani abu na daban, wanda har abada zuciyarsu bazata tab’ayin sanyi ba.�
*13/3/2021*
*8:14 pm*
3/16/21, 8:55 AM - Ummi Tandama: *L.M*
*Note editing*
*Chapter 67*
Idanu Aunty Aina’u ta d’an zaro waje, domin ita kanta mummunan fatan da kuma mugun nufin da Yar uwarta ta ke bin su Maleek d’in dashi ayanzu ya fara tsoratata, saboda ta fahimci cewa da gaske Momy’n keyi, burinta d’aya kawae shine taga ta kawar da duk wani farincikin daya shafi rayuwar LAYLERH MALEEK.
Juyowa Momyn tayi ta kalli Aunty Aina’u, wanda tayi shiru ta kasa cewa komae.
Baki ta bud’e daniyar yiwa Aunty Aina’un magana, amma kuma wani abu da ta tuna ne yasa ta fasa fad’in maganan dake cikin bakinta, juyawa tayi direct d’akinta ta nufa, tana me sakin wani munafukin murmushi.
Aunty Aina’u kuwa da idanu tabita, domin kuwa ayanzu itakan takanji zuciyarta ta karaya daga aikatawa su Laylerh’n mugunta, saboda taji awa’azi babu kyau cutar da Maraya, tana kuma tsoron abunda zaije ya dawo, dan abune dayake abayyane duk wani mai mugun nufi da aniya baya k’arewa k’alau.
Acan gidan Aunty Zee kuwa tsab Aleeya ta gama jerewa Laylerh kayanta dake cikin trolleybag zuwa drawer, sannan kuma ita tayiwa Laylerh’n jagora har tayi wanka.
Yanzuma zaune take bisa sallayan da tayi sallah’n magriba akai.
Idanunta wanda suke d’an bayyana kasala ta lumshe, Yayinda kuma sannu ahankali takejin wani irin sanyi na ratsa duk ilahirin jikinta, duk da cewar kuwa bawani sanyi sosae ake busawa ba, amma ita sanyin takeji.
Yanayin yanda ta lumshe idanunnata da kuma shirun da tayi ne, yasa idan mutum ya kalleta zai tsammaci cewa tayi nisa acikin tunani ne, wanda kuma ahak’ik’anin gaskiya bawai hakan bane.
Ta daiyi shirune kawai tana me sauraran yadda kowani bugun zuciyarta d’aya, ke mu’amalantuwa da tsananin soyayyarsa, ta yadda takejin kamar soyayyar tasa ce ke sake ruruwa acikin zuciya da gangar jikinta, Yayinda daga gefe guda kuwa takejin wani abu na musamman a kansa me kama da kewa.
D’an muskutawa tayi tare da sanya hannayenta duka biyu ta k’ank’ame jikinta waje d’aya, danji take kaman ana cakan k’ahon zuciyarta.
“Laylerh.�
Aleeya dake tsaye tun d’azu agefenta ta k’ira sunanta.
Jin muryar Aleeya’n da tayi acikin kunnuwanta ne kuma yasa tayi saurin bud’e idanunta, tare da d’ago kanta ta fuskance ta.
Murmushi Aleeya ta sakar mata tare kuma da d’an rank’wafowa ta kama hannun Laylerh’n, cikin tausasa murya da kuma nuna alaman tausayawa tace.