← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 144

Sashe 115

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosae kuwa ta fahimci abunda Teemah’n ke son fahimtar da ita.

Haka dae Teemah da Oum Ayush d’in suka zauna har saida dare yayi kafun suka tafi, Inda Oum Ayush da kanta tamayar da Teemah’n gida, domin dama ita taje ta d’auko ta.

*8:46 pm*

*15/3/2021*
3/18/21, 9:36 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*Not editing*

*Chapter 68*

7:00 am daidai haka k’ararrawar dake jikin babban agogon bangon dake cikin d’akin ya buga.
Daidai lokacin kuwa ta d’ago kanta ta kalli agogon, domin dama tun d’azu 7 d’in take jira ya cika, kasancewar k’arfe 8:00 am ne daidai zasu shiga exam d’innasu.
Shiyasa ma tunda tayi sallan asuba bata koma bacci ba, d’aukan takardun da Teemah ta kawo mata tayi ta soma karantawa.
Yayinda Aleeya ko keta sharar bacci, duk da cewar itama yau d’inne zasu fara exam a school d’insu, amma kuma saidai b’ata lokacin da tayi Daren jiya tana kallon film ne yasa ko sallah’n asuba da k’yar ta iya tashi tayi.

Kallonta ta mayar ga Aleeya, kaman kuma zata tasheta saita fasa, ahankali ta mik’e tsaye, tare da zare hijab d’in dake jikinta, kaitsaye toilet d’in dake cikin d’akin ta nufa.
Koda ta k’arasa cikin toilet d’in kayan dake jikinta ta cire tare da sanya shower cap akanta, kasancewar kuma yau d’in ana d’an yanayin zafi ne yasa ta k’arasawa gaban shower ta sakarwa kanta ruwa.

Bayan tagama wankanne kuma tayi brush, tare da d’aukan wani d’an k’aramin towel ta shiga tsane ruwan dake jikinta.
Ahaka ta fito daga toilet d’in, still sake kallon Aleeya dake ta faman sharara bacci tayi, yanzun kam lokaci ya d’an tafi shiyasa bazata iya barin Aleeya’n ta cigaba da bacci ba.
Hannunta tasa tad’an tab’a Aleeya’n hakanne kuwa yasa Aleeya’n tashi zaune, cikin yanayin magagin bacci tace.
“Namakara ko?�

“Kindai kusa amma kuma ci gaba da baccinki daidai yake da makaranki.� Laylerh’n ta bata amsa adaidai lokacin da take k’arasawa gaban mirror.

Body lotion na company’n Nivea ta shafa ajikinta, sai kuma powder da wani brown lipsgloss da ta shafa akan jajayen labb’anta, iya kwalli kawae ta shafa acikin idanunta, daga haka kuwa bata sake goga komae akan fuskar nata ba, direct wajen drawer’n dake cikin d’akin ta nufa, koda ta bud’e drawer’n sabon uniform d’in da Oum Ayush ta kawo mata ta ciro tare da sakawa ajikinta, sosai kuwa uniform d’in ya zauna ajikinta, sannan kuma ko kad’an bai bayyana wani shatin sura na jikinta ba, ya rufe ko ina d’inta, hatta hijab d’inma duk da cewar bashi da girma amma ya rufe guiwan hannayenta.
Wasu White socks d’inta masu tsayi ta saka, tare da wasu fararen takalma wayanda suke yanayi da sneakers shoe.
Sake d’ago kanta tayi ta kalli agogon dake cikin d’akin, wanda yake nuna 7:30 am daidai.
Face mask d’inta ta d’auka tare kuma da wasu fararen papers cikin sauri ta nufi hanyar fita daga cikin dakin, daidai lokacin kuwa Aleeya ta fito daga toilet jikinta d’auke da danshin ruwa.
Ganin da tayi kuma Laylerh’n ta shirya ne yasa itama cikin hanzari ta soma shirya kanta.

Laylerh kuwa tana fita daga cikin d’akin direct falo ta fito, inda ta samu Aunty Zee da Mijinta zaune akan dining table.

Aladabce ta gaishesu dukansu kuwa fuska d’auke da murmushi suka amsa mata, kana cikin kulawa Aunty Zee tace.

“Yanzu nake da shirin zuwa k’iranku kuyi breakfast, domin naga har takwas d’in ma ta kusa baku fito ba, Ina Aleeya’n kuma ta tsaya?.�

“Tana shiryawa.� Tafad’i hakan asanyaye, tare kuma da d’an sunkuyar da kanta k’asa.

Kai kawai Aunty Zee tajinjina domin dama ita tasan halin Aleeya badai saib’i ba.
Kujera ta nunawa Laylerh’n had’e da cewa.
“Kizo kici abinci.�

“To.� Kawae ta iya cewa duk da cewar kuwa bata wani jin yunwa sosai, saidai kuma amma sam batason cewa Aunty Zee d’in a’a, musamman ma da tafahimci cewa Aunty Zee d’in da kuma Mijinta wanda Aleeya take k’ira da Yah Jameel suna da mutumci sosae.
K’arasowa dining area d’in tayi tare da zama akan kujeran da Aunty Zee d’in ke nuna mata.

Itakuwa Aunty Zee da kanta tayi serving Laylerh’n.
Suna fara cin abincin kuwa Aleeya ta fito itama cikin shirinta.
Akujerar dake kusa dana Laylerh ta zauna, cikin sauri sauri ta soma cin abincin gudun kada tajawo musu latti, domin driver’n da zai kaisu makarantar saiya fara kai Laylerh kafun ita, kasancewar school d’in su Laylerh’n yafi kusa.

Kwata kwata kuwa ko mintuna 10 ba suyi sunacin abincin ba kuwa, kowaccensu ta ajiye spoon d’in dake hannunta.
Laylerh ce ta fara mik’ewa tsaye, domin kuwa taga time d’insu nata tafiya.
Ganin hakanne kuma yasa Mijin Aunty Zee d’in sa hannunsa aciki aljihun rigar dake jikinsa, fararen 1k ya ciro tare da bawa kowaccensu d’aya, Laylerh kam bata saba hakan ba, shiyasa tak’i k’arb’a, amma kuma ganin yanda ya had’e fuska yasa ta k’arb’a tare dayi masa godiya.

Aunty Zee kuwa addu’a da fatan samun nasara ta musu, Laylerh kuwa har takai bakin k’ofar fita daga falon, Jin da tayi kuma Aunty Zee d’in tak’ira sunanta ne yasata tsayawa tare da juyowa ta fuskanceta.

Murmushi Aunty Zee d’in ta sakar mata, cikin kuma tsananin kulawa tace.
“Ina fata baki manta maganganun da Oum Ayush ta fad’a miki ba, sannan kome zakiyi kada ki tab’a mantawa da matsayin dakike kai ayanzu, kada ki kulawa kowa saidai idan yazama dolen dole, sannan ki k’ebe kanki waje d’aya, banda yawan surutu, da zaran kunfito a exam kuma ki k’ira wayana zan turo driver ya d’aukeki, dan Allah Laylerh kikula da kanki sosae, kinga fita ma sam baikamaceki ba saidon kawae ya zamanto dole ne.�

Ahankali ta d’an jinjina kanta, cikin kuma son nunawa Aunty Zee d’in cewa ta fahimci abunda suke son nusar da ita tace.

“Insha Allah Zankiyaye.�

“Allah Yasa.�
Aunty Zee d’in tafad’a.

Itakuwa Laylerh juyawa tayi ta fice daga cikin falon, Dan tuni Aleeya tayi waje.

Koda ta fito compound d’in gidan kuwa direct inda motar da za’a kaisu makarantar ke fake ta nufa, tana zuwa kuwa ta bud’e murfin motar tashiga, akusa da Aleeya ta zauna.
Take driver’n kuwa yaja motar suka tafi.

Kamar yanda yake makarantar su Laylerh’nce afarko hakan yasa ita driver’n ya fara sauk’ewa, saida suka ga shiganta cikin skull d’in kuwa kafun suka juya suka tafi.

Tana shigowa cikin school d’in nasu kuwa ta hango Teemah, hakanne yasa ta k’arasa wajen da Teemah’n ke zaune.

Teemah kuwa dake zaune ganin Laylerh’n ta nufota ne, yasa ta fad’a d’a murmushin dake kan fuskarta, take kuma duk wani tausayin Laylerh’n da takeji acikin zuciyarta ya bayyana kansa acikin k’wayoyin idanunta.
Tabbas Allah Yasani tana tausayin Laylerh’n sosai, ko adacan ma bare yanzu da k’addara ta fad’a mata.
Wasu irin hawaye da suka cika idanunta ne yasa ta wayance.

Cikin salon tsokana tace.

“Ke kuma ya haka kin b’oyemana kyawun fuskar taki da face mask, kodai har anfara tattalawa Mr.Soldier fuskar ne?�

Hararan wasa Laylerh’n ta watsa mata tare da cewa.
“Tayaya hakan zai faru bayan kinjima kina sonshi.�

Murmushi mai had’e da dariya Teemah tayi, tare da mik’ewa tsaye ta kamo hannun Laylerh’n, Idanunta ta d’an lumshe, cikin yanayi da kuma sigar da tasan Laylerh’n zata fahimceta tace.

“Tabbas ada nayi tunanin cewa abunda nakeji a kansa sone, but amma yanzu na tabbar da cewa ba sonsa nake ba, just kawae yana burgeni ne, kuma kin dai san Namiji irin Mr. Soldier babu macen da bazae burgeba, sannan kuma hak’ik’a nikam na yarda SO d’aya ne, akuma duniyar nan gaba d’aya babu wacce zata soshi kamar yanda kike sonsa, sannan kuma ke kad’ai ce choice d’insa, saboda ke da shi d’in kun kasance MURADI d’aya ne, rabaku ayanzu daidai yake da raba mutum da rayuwa, infact ma ayanzu wanda yace zai katse wannan burin zai iya mutuwa, ko dai kinason na mutu anan kusa ne?.�

Kai Laylerh’n ta girgiza mata, tare kuma da lumshe idanunta, wanda kuma hakanne ya bawa hawayen dake cikin idanunnata, daman gangarowa kan fuskarta.
Tabbas maganganun da Teemah’n ta fad’a mata ayanzu, sunsa wani irin matsanancin soyayyar Maleek d’in ya sake motsa mata, hakanne kuma yasa ta kasa cewa komae.

Teemah kam tasan komai, da kuma irin raunin da zuciyar Laylerh’n ke dashi akan Maleek, shiyasa ma bataso sake jin wani abu daga bakinta ba.
Ahankali ta kamo hannunta, batare kuma da tasake ce mata komae ba, kai tsaye suka nufi exam hall d’in, da acikinsa ne zasu gudanar da jarrabawar tasu, inda kowannensu yake d’auke da number’n kujerarsa.

Kasancewar kuma numbers d’insu basa kamanceceniya da juna, wannan yasa koda suka shiga cikin exam hall d’in kowacce ta nufi mazauninta.

Suna zama kuwa aka soma raba musu questions papers.
Time na cika kuwa suka fara answer questions d’in.

Sosai kuwa abun yazowa Laylerh da sauk’i, domin kusan rabin questions d’in takaranta amsansu ayau da asuba bayan tayi sallah, wannan yasa bata wani sha wahala ba.
Duk da cewar kuma 1hour and 30 minutes kad’ai aka basu sugama answering questions d’in, sai gashi kuma acikin 1hour kad’ae kusan gaba d’aya students d’in sungama amsa questions d’in da zasu iya amsawa.
Ciki kuwa harda Laylerh da Teemah bayan sun gama ne kuma dukansu sukayi submit papers d’in suka fita.

Anan k’asan wata bishiya suka zauna ita da Teemah, tare da soma karatun next paper’n da zasu shiga anan gaba wanda tsakaninsa da wancan papern kwata kwata 40minute ne.
Karatu sukayi sosae mintuna 40 na cika kuwa suka sake komawa exam.

Sosae wannan paper’n ya basu wahala kasancewar sa na Geography ne.
Amma kuma cikin ikon Ubangiji sun samu sun rubutasa tare dasa ran cewa zasu samu marking mai yawa.

11:30 am daidai suka fito daga exam d’in nasu, kamar yanda Aunty Zee ta fad’a kuwa, suna fitowa Laylerh ta ciro wayarta dake kashe, kasancewar da zasu shiga exam d’in kashe wayoyinsu sukayi kana suka bada ajiya, saboda doka ne ba’a shiga exam d’in da waya.
Kunna wayartata tayi tare dayin dialing Number’’n Aunty Zee.
Bugu biyu kuwa Aunty Zee d’in ta d’aga wayar.
Gaya mata kuma da Laylerh’n tayi cewar sun gama exam ne yasa ta cewa gatanan zuwa, zata zo ta d’auketa, domin ayanzun tana kusa da makarantar su Laylerh’n.
Chapter 115 · 0% Book details