← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 144

Sashe 97

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hannunsa yakai ahankali ya shafa saman marar sa inda yaga jini kwance, d’aya daga cikin yatsar hannunsa da ta dangwalo jinin ya d’ago tare da d’an k’urawa jinin nasa idanu.
Akasalance ya d’an lumshe idanunsa tare da sauke wata irin b’oyayyar ajiyar zuciya, tabbas duk da baisan cewa jinin na meye bane, amma yaji hankalinsa ya d’an tashi kad’an, saboda dai yasan baiga ciwo akan marar tasa ba, amma wani abun al’ajabi kuma ga jini, wani tunani kuma daya fad’o ransane yasashi share duk wani abundake zuciyarsa, tissue d’in dake aje agaban sink ya d’auka had’e da goge saman marar tasa, kana kuma yasa ruwa ya wanke wajen.
Gaba d’aya jikinsa yabi da kallo, wanda hakanan yakejin wani irin abu duk babu dad’i, ayanzu kam babu abunda yakeson yi face wanka, Dan hakanne kad’ai zaisa yajisa ya k’ara zama normal, duk da cewar toilet d’in da yake cikin nada tsabta sosae saidai bayajin zai iya sakewa acikinsa har yayi wanka.
Duk wani sashi na jikinsa da yasan akwae najasa saida ya wanke tas kafun ya d’auro alwala.
Ahankali ya bud’e k’ofar toilet d’in ya fito, zuwa lokacin kuwa har su Oum Ayush sun idar da nasu sallah’n.
Ganin jikin Maleek d’in d’auke da danshin ruwane yasa Fou’ad dake zaune gane cewar Maleek d’in alwala yayi.
Babban ledan daya shigo da ita tun zuwansa na farko ya d’auko tare da bud’ewa ya zaro wani riga da wando, wanda suke sabi k’al k’al, domin musamman ya sayosu awani Big super market saboda Maleek d’in idan ya farfad’o ya samu kayan da zaisa.

Mik’a masa kayan Najeeb yayi, shikuwa batare da wani dogon tambaya ba ya amshi kayan tare da juyawa ya koma cikin toilet d’in.
Bajimawa kuwa sai gashi ya fito sanye da kayan ajikinsa, wanda suka matuk’ar yi masa kyau, kasancewarsu kuma kalan bak’i shiyasa suka k’ara bayyana hasken fatarsa.

Laylerh kuwa da har yanzu take zaune akan sallayan da tayi sallah, kyawawan k’afafunsa ta zubawa ido, ba abundake d’aukar hankalinta agaresa kuma kamar yanda yake taka k’afafunnasa ahankali.
Isowarsa kusa da itane kuma yasa tayi saurin lumshe idanunta, tare dajin wani irin bugun zuciya wanda bata tab’a jin irinsa ba.
Shikuwa Maleek kaitsaye ta gefenta ya rab’a ya wuce ya d’auki sallayan da Oum Ayush tayi sallah akansa, shumfud’a sallayan yayi tare da fuskantar gabar ya tada sallah.

Ganin haka yasa asanyaye tatashi daga zaunen da take tare kuma da nannad’e sallayan da take kai ta ajiye agefe.
Daidai lokacin kuwa su Abbou Jaheed suka dawo daga tafiya masallacin da sukayi.
Kallon Oum Ayush Abbou Khareem yayi cikin kulawa yace.
“Likita yace bazai sallamemu yau ba sai zuwa gobe, saboda haka ni zan kwana da Maleek d’in, ku kuma zuwa yanzu ya kamata ku koma gida, domin dare na k’ara yi.�
Jin abunda ya fad’a d’inne yasa Oum Ayush ta d’an jinjina kanta, tare da mik’ewa tsaye, domin dama itama harta fara jin bacci, koba don haka bama ya kamata ace sun koma saboda ayanzu tasan duk inda Najeeb yake to yana buk’atar dawowar Laylerh gida, hakanan kuma bazasu tauye masa hakk’insa ba.

Fou’ad dake zaune agefe kuwa jin Abbou Khareem yace shi zai kwana a asibitinne yasashi kafewa akan cewar lallai shi zai kwana tare da a Maleek d’in idan yaso su Abbou Khareem d’in dukansu sai su koma gida.
Abbou Khareem kam yaso cewa aa amma kuma sai Abbou Jaheed yace ba damuwa abar Fou’ad d’in ya kwana.
Haka dai suka tsaida magana akan cewa Fou’ad d’inne zai kwana.

Laylerh kuwa tunda taji ance sutafi duk ta k’ara sururucewa, sam hakanan taji batason koda fita daga d’akinne balle ma daga cikin asibitin gaba d’aya, amma kuma sanin da tayi cewar babu yanda zatayine yasa ta gyara rufin mayafin dake jikinta.
Asanyaye ta saci kallonsa ta gefen idanunta, domin kuwa har yanzu sallah yakeyi bai idar ba, kasancewar yana ramakon sallan azahar da kuma na la’asar ne da ake binsa, wanda lokacin da akayi su baya cikin hayyacinsa.

“Muje ko.�
Muryar Oum Ayush ta katseta daga d’an guntun tunanin da takeyi.
Haka dole batare da ranta ya soba tabi bayan Oum d’in da har ta isa bakin k’ofa suka fice.
Koda suka fito compound d’in asibitin kai tsaye wajen da Oum Ayush tayi parking motar ta suka nufa.
Asanyaye Laylerh ta bud’e murfin motar ta shiga.
Cikin d’an yanayin sauri kuma Oum Ayush taja motar suka tafi.
Har sukayi nisa da tafiyan nasu kuwa babu wanda yace da d’an uwansa k’ala, kowannensu da irin abunda yake sak’awa acikin zuciyarsa, yayinda acikin zuciyar Laylerh ya kasance tunanin Maleek ne zallan, Oum Ayush kuwa mamaki da kuma tunanin abunda ya hana Momy zuwa hospital d’in take.
Da wannan tunanin nasu ahaka har suka iso gida.

Acan asibiti kuwa Koda ya idar da duka sallan da ake binsa bai tashi akan sallayan ba har saida ya sallan Isha.
Bayan ya idar da sallanne kuma ya d’auki magungunan da Dr. Mouhammad ya kawo masa yasha, tare da komawa saman gadonsa ya kwanta, domin kuwa wani irin ciwo yakejin jikinsa da mararsa nayi masa, ga kuma wani irin bacci mai k’arfi dake fusgarsa, hakan kuwa yana da nasaba da allurar da Dr. Mouhammad yayi masa d’azu, saboda alluran tanabin jikin mutum ne da sannu saita saka macewar jiki da kuma bacci.

Ahankali Fou’ad ya turo k’ofar d’akin ya shigo, dawowansa daga masallaci kenan, yayinda su Abbou Jaheed kuwa suna idar da sallah’n Isha suka wuce gida shida Abbou Khareem.
Ganin Maleek d’in da yayi kwance akan gadone yasashi k’arasowa cikin d’akin tare dajan kujera ya zauna akusa da M.Jay d’in wanda yasa hannayensa duka biyu ya dafe mararsa, duk da kuwa cewar idanunsa alumshe suke, amma Fou’ad yasan cewa ba bacci yakeyi ba, domin duk wani kwanton b’aunan Maleek d’in babu wanda baisani ba.

Idanu ya zuba masa nad’an wasu sakanni kafun daga bisani ya kawar da kansa gefe, cikin tausasa murya yanda yasan Maleek d’in zai fahimcesa yace.
“Bai kamata ace har yanzu kabar zuciyarka taci gaba da son Matarwani ba, Laylerh fa matar wani ce Maleek kuma kasan hakan, kana kasan zunubin dake cikin hakan amma kuma kake aikatawa, meyasa ba zakayi k’ok’arin cireta acikin rayuwarka ba? ko kamanta cewar ba lallaine abunda kakeso shi kake samu ba? Kada kayi tunanin wai don kanason Laylerh watarana dole saika sameta, Tabbas nasan kanajin k’una da kuma radad’in rashinta amma hakan bawai shi yake nufin cewa bazaka rayu idan ba itaba zakayi rayuwa cikin farinciki da inganci Idan har kaso hakan, Dan Allah Captain M.Jay kamanta da Laylerh ka k’yaleta tayi rayuwa da mijinta, saboda ta sanadiyarsa ne zata samu aljannarta, shin tayaya kake tunanin Laylerh zata iyayin zaman aure matuk’ar tana ganinsa akusa da ita? sannan kuma idan kana bibiyarta hakan bazae tab’a yiwuwaba, na tabbata ganin da nayi muku d’azu da ace Mijintane yayi muku da zuwa yanzu labari ya sanja salo, shin kanason Najeeb yafara zargin Laylerh da aikata fasik’anci da aurensa ne? Kasani basai na fad’a maka ba Laylerh yarinyace k’arama duk abunda aka koyar da ita dashi zata tashi, kada ka koyar da Laylerh wannan d’abi’ar Maleek sam kada ka fara.�

Idanunsa wanda suka rune sukayi ja kaman Jan barkono ya bud’e, tare dajan wani irin dogon numfashi, ahankali ya kamo hannun Fou’ad dake gefensa ya d’aura akan kirjinsa daidai saitin inda zuciyarsa take.

Sauk’an hannun Fou’ad akan saitin zuciyar Maleek d’inne kuma yasashi zaro idanunsa waje, cike da mamaki had’i da tsoro yake kallon k’irjin Maleek d’in.
Asakamakon wani irin mummunan bugawa da yaji zuciyar Maleek d’in nayi fast fast kaman zata faso k’irjinsa ta fito.

“Yin shiru zaifi sauk’i Fou’ad akan kacemin na daina son Laylerh, bakasan ya nakeji ba aduk kwanan duniya idan na tuna cewar Laylerh tana ak’ark’ashin inuwar wani sai naji zuciyata tana k’una kaman ana gasamin ita, Ya nakeji me nakeji babu wanda ya sani Fou’ad saini kad’ai, cire soyayyar dake yawo acikin gangar jiki da jini ba abu bane me sauk’i, nayi imani cewa da soyayyar Laylerh acikin zuciyata zan mutu, so yakan tashi ya k’aura zuwa wani waje na daban amma ba irin soyayyar da nakeyiwa Laylerh ba, wannan soyayyar daban take, soyayyar Ayshnoor tafi gaban kwatancen kowa, ta wuce hasashe Fou’ad, ba kuma zata tab’a misaltuwa ba, halittace da bazata tab’a mutuwa ba, domin kuwa koda babu rai ajikina soyayyar Ayshnoor bazata daina rayuwa ba!!�

D’an tsagaitawa da maganan nasa yayi, saboda yanda yaji k’irjinsa na rik’ewa, Sam yawan magana ba d’abi’arsa bace, wannan dalilin yasa sanadin maganan da yayi yanzun yaji k’irjinsa ya rik’e.
Idanunsa wanda suka cika da ruwan hawaye ya mayar ya lumshe, tare da sakin hannun Fou’ad dake kan k’irjinsa, gyara kwanciyarsa yayi tare da juyawa ya bawa Fou’ad d’in baya.

Fou’ad kuwa hawayen da suke kokarin zubowa daga cikin idanunsa ya shanye, asanyaye ya zubawa bayan Maleek d’in idanu.
K’warai sosai tsananin soyayyar da Maleek keyiwa Laylerh ke basa mamaki, wacce irin soyayyace wannan da k’arfinta yake neman zarce hankali? shikam Allah Ya sani zuwa yanzu tsoron soyayyar LaylerhMaleek d’in yakeyi, domin kuwa soyayyace Bawae mai hankali ba.
Sanin cewa sha’anin su Layerh’n yafi k’arfinsane yasa baisake cewa komae ba, jingina bayansa ajikin kujeran da yake kai yayi tare da lumshe idanunsa.
Chapter 97 · 0% Book details