← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 144

Sashe 48

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ƙarfe uku daedae ta farka daga baccin nata sakamakon hayaniyan daya cika gidan.
Ahankali ta buɗe idanunta da sukayi mata nauyi, jin motsi da kuma ƙaran danna waya agefenta ne yasa ta ɗan juyo da kanta.
Ganin Teemah zaune agefen gadon ne yasa ta ɗan waro idanunta, cikin yanayin mamaki haɗi da muryarta da bata fita da kyau ta ƙira sunan Teemah.
Jin muryar ta ne yasa Teemah dake danna wayarta ta ɗago da sauri, ganin Laylerh'n ta buɗe idanunta ne yasa cikin sauri ta hawo saman gadon tare da kamo hannun Laylerh'n ta riƙe, cikin kulawa tace. "Sannu Amarya ya jikin naki, nayi mamaki sosai da Oum Ayush ta tura driver har gida ya ɗauko ni, ashe kin fara jinyan amarcin ne tun yanzu, tun kan akashe boss!."
Yanayin yanda ta ƙare maganar cikin tsokana ne yasa Laylerh da taɗan yunƙura ta tashi, ta watsawa Teemah'n harara.
Dariya Teemah tayi tare da matsawa kusa da Laylerh'n, cikin yin ƙasa da murya tace. "Gaskia Angon nan naki zai kwashi garaɓasa, ji yanda kike ƙamshi kaman anmiki wanka da turare, bayan haka kuma kalli yanda skin ɗinke keta sheƙi like diamond, awwn sunan wani abu wae so sweet!."
Teemah tafaÉ—i haka tana me É—an rungume Laylerh'n.
Ayanayin yanda takejin kanta yasa bata tunanin biyewa shirmen Teemah'n, dan har yanzu bawae zazzaɓin ya gama sauƙa ajikinta bane.
Shigowar Oum Ayush cikin É—akinne yasa Teemah ta saki Laylerh'n, cikin salon tsokana tace. "Yauwa Oum Ayush amaryar tamu ta farka." Murmushi kawae Oum Ayush tayi, kasancewar tasan halin Teemah'n da tsokana.
Ruwan wanka Oum Ayush ɗin ta haɗawa Laylerh, tare da zuwa ta kamo hannunta, da kanta ta kaita har cikin toilet, ganin jikin Laylerh'n babu ƙarfi sosae ne yasa Oum Ayush din da kanta tayi mata wanka, bayan ta fito daga wankanne kuma aka turare mata jikinta da turaren wuta me dadin ƙamshi.
Aunty Zee ne ta shiryata cikin wani haÉ—aÉ—É—en yadi me kalan blue da kuma golding, wanda aka masa É—inkin riga da sket, sosai kayan suka amshi jikinta sannan suka bayyana hasken fatarta, meckup me kyau Aunty Zee É—in ta mata, saidai sanin cewa laylerh'n bata da ishashshen lapia ne yasa bata tsawaita meckup É—in ba.
Dogon gashinta Aunty Zee É—in ta kama inda ta nannaÉ—e mata shi da wani blue É—in ribbom, da babban É—an kwalin kayan tayi mata É—aurin turban.
Haɗaɗɗen sarƙan gwal da kuma awarwaro Aunty zee ɗin tasa mata, wanda hakan ya ƙara ƙawata adon nata, wani golding colour laffaya me tsananin kyau da tsada Aunty Zee din ta naɗa mata, tare da bata wasu haɗaɗɗun takalma masu kalan golding ta saka aƙafafunta, bakaɗan ba Laylerh'n tayi kyau, duk dama yanayin rama ya bayyana akan fuskarta saidai hakan baihana kyawunta bayyana ba.
Ganin yanda Laylerh'n tayi kyaune yasa Teemah ta shiga yi mata pics masu kyau.
Kasancewar tuntuni jama'a sun hallara a hall ɗin da za'ayi waliman ne yasa Aunty Zee kamo hannun Laylerh'n dake ta faman baza ƙamshi suka fice daga cikin ɗakin, yayinda Teemah ke biye dasu abaya saiyi wa Laylerh'n vedio take, duk da kasancewar yanayin yanda aka ɗan sa mata laffaya ya rufe rabin fuskarta.
Koda suka fito compound É—in gidan, cikin wata haÉ—aÉ—É—iyar Range Rover Aunty Zee ta saka Laylerh'n tare da zama akusa da ita, Teemah kuwa gaban motar ta shiga, kasancewar dama tuntuni su drivern ke jira, suna shiga kuwa yaja motar suka bar compound É—in gidan.
4:30 pm daidai suka isa katafaren hall din da aka ƙawatasa da decoration, yayinda tuni mutanen da Oum Ayush da kuma wanda momy ta gayyata sun cika wajen.
Zuwan su Laylerh'n ne yasa malamar da aka gayyato ta fara wa'azi akan yanda mace zatayi rayuwa me kyau da tsabta acikin gidan aurenta.
Babu laifi kuma sosai Malamar tayi wa'azi me ratsa zuciya.
Ƙarfe 6 daidai aka tashi daga walimar, nan fa aka soma ciye ciye, bayan kuma anci ansha ne Oum Ayush ta raba kyaututtuka na burgewa ga duk wacce ta halarci waliman.
Ɓangaren Laylerh kuwa gaba ɗaya ta kasa sake jikinta, kasancewar bata saba da yawan shiga jama'a ba, hakanne kuma yasa hayaniyar mutanen ya ƙara mata ciwon kai, wannan yasa jikinta ya sake ɗaukan zafi.
7 daidai suka dawo gida, kasancewar akwai gajiya da kuma ciwo ajikinta ne yasa tana idar da sallan isha ta kwanta anan kan sallayan bacci ya É—auketa.
Shigowar Oum Ayush cikin ɗakinne ta sauƙe idanunta akan Laylerh'n dake kwance akan sallaya.
Ajiyar zuciya Oum Ayush ɗin ta sauƙe tare da kafe Laylerh'n da idanu, wani irin matsanancin tausayin Laylerh'n ne ya cika mata zuciya, wanda hakan yasa take taji idanunta sun ciko da ƙwalla, cikin dauriya ta shanye ƙwallan dake idanun nata, ahankali ta ƙaraso inda Laylerh'n ke kwance, ɗan durkusawa tayi tare da shafa kan Laylerh'n, cikin sanyi da kuma matsanancin tausayin Laylerh'n tace. "Nasan matsalan dake damun zuciarki Laylerh, kuma insha Allah Idan da rai da rabo watarana zaki rayu da Maleek, zaki zauna a ƙarƙashin inuwarsa zama na har abada, saboda ku ɗin fata da buri ne haɗe awaje ɗaya, insha Allah zaku kasance atare da juna." Hannu tasa ta share ɗan guntun hawayen daya sauƙa akan fuskarta, tare da ɗaga Laylerh'n caɗak ta kwantar da ita akan gado, jin jikin nata da zafi sosai ne yasa Oum Ayush ɗin ta rufa mata blanket, tare da rage mata gudun A/C kaitsaye ta fice daga cikin ɗakin.

Washegari.
Tabbas Rana bata ƙarya, duk kuma abun da Allah Ya tsara faruwarsa sae ya faru, kamar yanda ranar yau ɗin ta kasance asabar kuma acikinta ne za'a ɗaura auren Laylerh'n.

Kallon Agogon dake saƙale ajikin bangon ɗakin Fou'ad yayi, wanda ya nuna masa ƙarfe 9:30 am daidai. Ajiyar zuciya ya sauƙe, kana akaro na bartakai yakai dubansa ga Maleek wanda ke zaune akan kujera, yayinda idanunsa ke alumshe. Gefe dashi kuwa wani haɗaɗɗen yadin getzner ne wanda akayiwa ɗinkin riga da wando da kuma babban gare.
"Maleek.!"
Fou'ad ya ƙira sunansa cikin yanayin dake bayyana zallar damuwar dake kwance acikin zuciyarsa.

Samun kansa yayi da kasa amsawa Fou'ad ɗin duk da cewar kuwa yaji ƙiran da yayi masa.
Yanayin yanda yakejin zuciyarsa na harbawa akai akai ne ya sashi sanya hannu ya dafe daidai saitin zuciyar tasa, wanda yakejin tanayi masa ƙuna da kuna suka, yayinda yakejin wani abu me tsananin ɗaci na game maƙoshinsa.
Kwana uku kenan daya kasa rumtsa idanunsa da sunan bacci, sanadin hakan kuwa yasa gaba É—aya yafita hayyacinsa, yayinda kallo É—aya zaka masa ka karanto zallan damuwa kwance akan fuskarsa.
Tabbas atsakanin jiya da yau shi kaɗae yasan me yakeji azuciyarsa, domin kuwa zafi da raɗaɗin dayake bazai taɓa misaltuwa ba, dukkuwa ga yanda yaso daurewa sai yaji abun na neman fin ƙarfinsa, wannan yasa ya barwa kansa komai domin zuwa yanzu zuciarsa ma bazata iya ɗaukar ƙunan da yakeji ba, ada yayi tunanin cewa har abada bazai taba bari rauninsa ya bayyana ba, saidai ayanzu ya riga daya fahimci cewa, RAUNINsa bame ɓuya bane, saboda duk wani sirrin zuciyarsa yanzu rubuce yake akan fuskarsa.

Fou'ad daya tsura masa ido ganin bae amsa ƙiran da yayi masa din bane yasashi miƙewa tsaye tare da ƙarasowa inda Maleek ɗin ke zaune.
Tabbas ya fahimci irin yanda Maleek ɗin keji azuciyarsa, saboda gaba ɗaya fuskarsa ta bayyana matsanancin Rauninsa, haƙiƙa koda yaushe azuciyarsa yake ɓoye duk wani sirrinsa, saidai kuma ayau zuciyar tasa takasa juran cigaba da ɓoye abun dake cikinta.
Tabbas wannan shine karo na farko da Fou'ad ɗin ya fara ganin Maleek ɗin acikin irin wannan halin, ahankali ya sanya hannunsa ya dafa kafaɗan Maleek ɗin cikin son ƙarfafa masa guiwa yace.
"Shiru da zurfin ciki basa taɓa kawar da damuwa M.Jay, tabbas na fahimci irin yanda kakeji azuciyarka, saidai kuma kasani ako da yaushe muna tafiya ne da Ƙaddaran mu, ƙaddaran mu da bamu da ikon sanjata daga mummuna izuwa kyakkyawa, sau dayawa ba komae da kake so kake samu ba, haka kuma ba kowani buri ne ke cika ba, sau da dama mukan rasa hope ɗinmu, kuma amma hakan baya nufin cewa har abada zamu ta rasa hope ɗin mu bane, lallai watarana burin mu zai cika, saboda idan mun rasa anan zamu samu acan, Allah Shi yake duk wani tsarinsa babu kuma wanda ya isa ya wargaza, saboda haka ka sawa zuciarka jarumta, dan Allah Na roƙeka akaro na uku katashi kasa kaya mutafi wajen ɗaurin auren nan, kada fa kamanta Laylerh ƙanwar kace, kuma ako da yaushe burinka shine rayuwarta tayi kyau, meyasa bazaka kwaɗaitawa kanka halartar ɗaurin aurenta ba? ka tuna koba komai itaɗin ƙanwace agareka, kuma ita ɗin wani ɓangare ne na zuciyarka, saboda idan akace ayau Abbou Jaheed ya kwanta dama kaine komae nata, sannan kayi tunanin rashin zuwanka wajen ɗaurin auren nata me zai haifar? baza'a fasa abun da Allah Ya tsara ba, haka kuma Abbou Jaheed bazaiji daɗin bakan ba, idan ya tambayeka dalili wace amsa zaka bashi?, nasan baka da ita, saboda haka ka manta baya Maleek ka fuskanci gaba please!."
Chapter 48 · 0% Book details