← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 144

Sashe 49

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idanunsa wanda suka kaɗa sukai jajur ya buɗe tare da tsaida kallonsa akan Fou'ad ɗin, tabbas kalaman fou'ad ɗin na ƙarshe sun tabbatar masa da cewar Fou'ad baisan zafi da rafaɗin da yakeji acikin zuciyarsa ba, domin da ace yasan koda kwatankwacin hakan bazai taɓa ce masa ya manta da baya ya fuskanci gaba ba, domin kuwa abune da har abada bazai taɓa yiyuwa ba, domin manta baya agareshi tamkar mantawa da rayuwarsa ne.
Laɓɓan ɓakinsa ya cija tare da dunƙule hannunsa, haƙiƙa dama yasan babu wanda zai fahimci haƙiƙanin abun dake cikin zuciyarsa, babu wanda zai gane me yakeji acikin ransa, zafi, ƙuna, da kuma zogi da raɗaɗin da yakeji azuciarsa duk babu wanda zai fahimta.
Ahankali ya miƙe tsaye tare da ɗaukan kayan da Fou'ad din ya ajiye masa agefensa, cikin yanayin sanyi ya nufi bedroom ɗin dake cikin falon.
Duk da yanda yakejin wani irin jiri na ɗibansa, haka ya shirya kansa cikin riga da wandon getzner'n, tare da ɗaura gare akan rigar jikinsa, wata haɗaɗɗiyar hula me kalan blue ya saka akansa, kasancewar aikin dake jikin babbar rigar tasa blue ne, tunda yake wannan shine karo na farko daya fara saka manyan kaya, bakuma ƙaramin kyau suka masa ba, yayinda suka bayyana cikar kamalansa, duk da cewar yana ɗauke da damuwa amma hakan baisa murɗaɗɗiyar surar jikinsa sauyawa ba, kyau ajininsa yake wannan yasa ako wani condition ya samu kansa kyawunsa baya tawaya.
Haɗaɗɗen black blue ɗin takalmi ƙiran company'n Italy ya sanya aƙafansa, tare da ɗaura agogon diamond ahannunsa.
Ƙwarai yayi kyau sosai, dan da ace wata mace zata ɗaura idanunta akansa cikin shigar tasa, to babu yanda za'ayi ta ɗauke kanta.
Sam baya buƙatar duba madubi wajen ganin kyawunsa, hakan yasa ahankali ya murɗa handle ɗin kofar ya fice.
Fou'ad dake zaune ganin Maleek din ya fito ne yasashi sakin baki yana kallonsa, tabbas duk da cewar shi ma Namiji ne kuma kyakkyawa, yasan cewa Maleek ajin ƙarshe ne ahaɗuwa, dan yana da tabbacin cewa irin yanayin kyawun Maleek ɗin daban yake dana kowa.
Sanin da yayi cewar idan ya tsaya yin wata magana, abune me sauƙi Maleek ɗin yace ya fasa zuwa ne yasashi gimtse bakinsa, haka suka jera atare suka fice daga cikin falon.
Koda suka fito compound ɗin gidan motar Maleek ɗin ƙirar G waggon suka shiga, yanayin yanda yake jin jiri ne yasa shi miƙawa Fou'ad makullin motar saboda bayajin ayanda yake zai iyayin driving dan ko gani sosae bayayi.

9:55 am daidai suka iso ƙofar gidan su Maleek ɗin dake cike da tarin jama'a, manya manyan malamai, ƴan kasuwa, da kuma ƴan siyasa ne cike awajen.
Yayinda Abbou Jaheed da kuma Abbou Kareem suka sha adonsu cikin shigar manyan kaya.
Najeeb na hango atsakiyarsu wanda yayi matuƙar kyau cikin shigar milk colour getzner dake jikinsa, yasha ado sosai ta yanda kallo ɗaya zakayi masa ka fahimci cewa shine angon.
Yanayin yanda mutane suka cika wajen ne yasa Fou'ad yayi parking motar daga nesa.
Duk da cewar bayason yawan hayaniya haka ya buÉ—e murfin motar ya fito.
Taku ɗaya zuwa biyu yayi yaji wani ƙaƙƙarfan jiri na neman kadashi, yayinda wani irin duhu ke ƙoƙarin mamaye ganinsa.
Kasancewarsa soldier kuma Namiji me iya shanye duk wata wahala, hakan yasashi daurewa, ya ƙarasa cikin taron jama'an, yayinda Fou'ad ke binsa abaya.
Wajen zaman da aka tanada musamman dan suɗin suka ƙarasa suka zauna.
Ganinsa awajen É—aurin aurenne Abbou da gaba É—aya zuciarsa ke cike da fargaba ya saki murmushi, saboda sae ayanzu yaji sanyi aransa.

Kamar yanda aka rubuta ajikin katin auren ƙarfe 10:00 am daedae dubban jama'a suka shaida ɗaurin auren.
*LAYLERH MAHMOUD NAI'EB da kuma angonta NAJEEB AHMAD RUFA'E* akan sadaki naira dubu É—ari biyar (500k).
Jin an É—aura aurenne kuwa yasa me shela É—aga muryarsa inda ya shiga nanatawa jama'a cewar lallai aurefa ya É—auro, Laylerh ta zamo matar Najeeb.

Ɗaura auren da akayi yayi daidai da bugawar zuciyarsa da ƙarfi, yayinda gaba ɗaya jijiyoyin jikinsa suka mimmiƙe, take wani irin matsanancin ciwon kae ya kawo masa ziyara, wanda hakan yasashi sanya hannu ya kama kansa haɗe kuma da miƙewa tsaye, duk jikinsa rawa yake, cikin dauriya haɗe da cijewa ya soma taka ƙafarsa, domin kwata kwata bayajin zai iya jurewa zaman wajen, taku ɗaya kacal yayi wani irin jiri haɗi da duhu me tsanani suka mamaye ganinsa take kuwa ya tafi luuu ya faɗi ƙasa awajen.

*(Kuyi haƙuri two days ba editing bana gama typing da wuri shiasa.)*

*Sunday 20/December/2020*
1/19/21, 8:14 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*(This book is mainly for those that pay, if you know you did'nt pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay-0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz bank. Whatsapp number 07017879464. )*

*Chapter twenty five*

Ahankali take taka ƙafafunta dake matsanancin karkarwa, sanadin hakan ne kuma yasa suke neman gaza ɗaukar nauyinta.
Yayinda kuma wani irin matsanancin ciwon kae da jiri me ƙarfi keneman rinjayarta.
Haƙiƙa abun da takeji acikin azuciyarta yau din, ya wuce duk wani tunanin me tunani, kasancewar haka takejin zuciyar tata kaman zata fasa ƙirjinta ta fito waje.
Yanzu kusan sama da 15 minute kenan da gama wankan ta, amma takasa fitowa daga cikin bathroom É—in saboda yanda kanta ke bala'in sarawa, da kuma jirin dake neman kada'ita.
Ƙarasowarta bakin ƙofar bathroom ɗinne, yasa ahankali ta ɗaura hannunta akan handle ɗin ƙofar, tare da buɗeta asanyaye ta fito.
Wani ɗan ƙaramin towel ne ɗaure ajikinta, wanda tsawonsa ya tsaya a iyaka cinyarta, sannan kallo ɗaya zaka mata ka ga zallan raman da tayi, wanda ya bayyana kansa ɓaro ɓaro. Yayinda dagon gashin kanta dake jiƙe da ruwa ya kwanta lub akan baya da kuma wuyanta.
Lumshe idanunta wanda ke cike da ƙwalla tayi, ahankali tasa hannu ta dafe daidai saitin zuciyarta dake bugawa da sauri sauri.
Hawayen dake cikin idanunta ne suka gangaro kan fuskarta, haƙiƙa rana irin ta yau takasance ɗaya daga cikin ranakun da bazata taɓa mantawa dasu ba acikin rayuwarta, dan ayau tarasa duk wani fata da burinta, sannan farinciki da kuma nutsuwar zuciya, a yau duk wani tunaninta ya tsaya cak, haka takejin zuciarta na mata wani irin matsanancin ciwo, tabbas ayau ta yarda cewa samun abun da kakeso aduniar nan yafi komae daɗi, haka kuma rasashi yafi komai ciwo, kana kuma samun abun da kakeso abune me matuƙar wuya, tabbas ayau ta sake yardarwa kanta cewar tana matsanancin SON SA, sannan taji ajikinta cewar lallai tarasa Yaya, farinciki kuma jigonta, hakan yasa takejin wani irin suka da kuma raɗaɗi me zafi acikin zuciyarta, haƙiƙa bazata iya jure rashinsa da kuma yanayin da take ciki ba, domin zuciyarta bata da wannan ƙarfin.

Turo ƙofar ɗakin da akayi ne yasa ahankali ta buɗe idanunta.
Teemah da shigowarta É—akin kenan ganin hawaye kwance akan fuskar Laylerh'n ne yasa ta É—an zaro idanunta waje, cikin yanayin mamaki tace. "Kuka kuma Laylerh? meke damunki?."
Ayanayin da take ciki yasa batajin zata iya amsawa Teemah'n, tabbas so take tayi kuka sosae ko hakan zaisa taji sauƙin abun dake sukar zuciyarta, so take tayi kukan da shi kaɗai ne zai iya rarrashinta.
Ahankali ta soma ƙoƙarin sulalewa ƙasa tare da sakin wani irin kuka me tsananin taɓa zuciya.
Ganin haka yasa Teemah tayi saurin ƙarasowa gareta, tare da sa hannayenta ta ɗago Laylerh'n.
Jin Teemah'n akusa da ita ne yasa ta faɗa jikinta tare da rungumeta ƙam, kuka take sosai irin kukan nan dake bayyana zallar damuwar dake zuciyar me yinsa, yanayin yanda take kukan ne yasa tsoro da kuma fargaba suka shiga zuciar Teemah, domin kuwa a iyaka saninta da Laylerh bata taɓa ganinta tana irin wannan kukan ba, ga kuma yanda lokaci ɗaya duk jikinta ya ɗauki ɓari.
Cikin sanyin jiki ta rungume Laylerh'n, kana cikin karyayyar muryarta tace. "Please Laylerh ki daina kuka, ki faɗamin meyake damunki, ko zazzaɓin ne ya saki kuka haka? dan Allah Kifaɗamin saboda kinsa gaba ɗaya zuciyata ta karye, stop crying please......"  Yanayin yanda Teemah taƙare maganar cikin sanyin murya da kuma karyewar zuciya ne yasa idanunta cikowa da ƙwalla, kwarai tausayin ƙawarta ta ya kamata.
Laylerh kuwa yanayin yanda take rusa kuka sosai ne, yasa numfashinta soma sarƙewa, hakanne kuma yasa lokaci ɗaya jikinta ya saki, take kuwa  numfashinta ya ɗauke, wanda hakan yasa ta sulale daga jikin Teemah ta faɗi ƙasa.
Ganin da Teemah tayi Laylerh'n ta zube aƙasa bata numfashi ne yasa ta fasa wani irin ƙara, amatuƙar razane ta juya da gudu ta fita daga cikin ɗakin dan ƙiran Oum Ayush, akan tazo taga halin da Laylerh'n ke ciki.

Cikin yanayin damuwa haɗi da zallar rashin hankali Fou'ad dama sauran jama'an dake cike awajen sukayi kansa, durƙusawa agabansa Fou'ad yayi tare da kamo kafaɗunsa ya soma jijjigawa, amatuƙar ruɗe kuma cikin tsoro haɗi da zallar fargaban daya rufesa ya soma ƙiran sunansa.
Cikin sauri da tashin hankali su Abbou Jaheed suka ƙaraso wajen da Maleek ɗin ke yashe.
Durƙusawa Abbou Jaheed yayi, hankalinsa amatuƙar tashe ya soma ƙiran sunan Maleek ɗin, tare da girgiza shi.
Ko motsi Maleek É—in baiyi ba, kasancewar tuni ya jima da fita a hayyacinsa, yayinda gaba É—aya numfashinsa ya bar gangar jikinsa.
Fou'ad da idanunsa suka ciko da ƙwalla ne yasa hannunsa adaidai hancin Maleek ɗin, shirun da yaji ba alamar fitar numfashi ne yasashi zaro idanunsa waje, da sauri yakai hannunsa ya dafa ƙirjin Maleek ɗin daidai saitin zuciyarsa.
Jin zuciyar Maleek ɗin na harbawa kaɗan kaɗan ne yasashi sauƙe wata nannuyar ajiyar zuciya, cikin sanyin da jikinsa yayi ya ɗago kae, ya kalli Abbou Jaheed wanda yake cikin tashin hankali, cikin muryarsa dake ɗan rawa yace.
"Taɓa zuciyarsa kaji Abbou bata beating da kyau, komae nata yana zama low, please Abbou aƙira doctor kada mu rasa shi.!"
Abbou Jaheed da gaba É—aya ya ruÉ—e kasa koda motsa jikinsa yayi, domin idan yace zai nemo wayartasa ma baisan ta inda zai fara ba.
Abbou Kareem ne yayi saurin ciro wayarsa, cikin tashin hankali ya dannawa abokinsa Dr.Hafeez ƙira, bugu uku kuwa Dr.Hafeez ɗin ya ɗaga.
Cike da tashin hankali Abbou Kareem ya labartawa Dr.Hafeez É—in abun dake faruwa.
Yanayin yanda Dr.Hafeez yaji muryar Abbou Kareem É—in aÉ—an ruÉ—e ne yasashi cewa gashinan zuwa.
Chapter 49 · 0% Book details