← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 144

Sashe 53

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Jin abun da Oum Ayush ɗin ta faɗa ne, yasa ta lumshe idanunta wanda suka ciko da ƙwalla, ahankali taji bugun zuciyarta na ci gaba da tsananta, yayinda wani irin abu me kama da maɗaci ya tsaya amaƙoshinta.
"Shikenan yanzu ta zama matar aure?" tayiwa kanta tambayar, take kuwa hawayen da suka cika idanunta suka samu daman gangarowa kan fuskarta.
Daidai lokacin ne kuma aka turo ƙofar ɗakin, wanda hakan yasa su Oum Ayush suka maida kallonsu ga ƙofar.
Ganin Abbou Jaheed da kuma Najeeb dake biye dashi abayan ne yasa Oum Ayush sauƙe ajiyar zuciya.
Ƙarasowa cikin ɗakin Abbou Jaheed yayi, wanda ganin Laylerh'n a ɗan kishingiɗe yasa shi jin sanyi aransa.
Da ɗan sauri ya yaraso jikin gadon yana me ƙiran sunanta.
Jin muryar Abbou Jaheed akunnenta ne yasa tayi saurin buɗe idanunta, take kuwa wasu sabin hawaye suka shiga sauƙa akan kumatunta.
Ganin hawaye afuskarta ne yasa Abbou Jaheed shafa kanta, cikin kulawa yace.  "Sannu ko Laylerhtun Abbou Jajeed ya jikin naki?."
Shagwaɓe sick face ɗinta tayi, cikin muryarta dake ɗauke da rauni tace "Da sauƙi."
Kai Abbou Jaheed ɗin yanjinjina, tare da duban Oum Ayush cikin kulawa yace.  "Taci abinci kuwa?."
Kai Oum Ayush ta girgiza alaman "A'a"  tare da nuna masa mug ɗin tea ɗin dake hannunta. 
Karɓan mug ɗin yayi haɗe da miƙawa Laylerh'n, cikin kulawa yace.  "Karɓi kisha kinji."
kai ta girgiza alaman "A'a." domin har acikin zuciyarta yanzu babu wanda takeson gani sama da Maleek.

Najeeb.
Ahankali ya sauƙe ajiyar zuciya tare da tura duka hannayensa cikin aljihun rigar jumper'n dake jikinsa, duk da cewar kwana huɗu kawai yayi baisata a idanunsa ba, amma hakan bai hanashi ganin kyau da kuma hasken da ta ƙara ba,  ba abun daya fi ɗaukar hankalinsa atattare da ita kuwa, kaman cute innocent face ɗinta, da kuma jajayen lips ɗinta.
Idanunsa dake cike da mayen soyayyarta ya lumshe, ahankali ya fesar da wani numfashi, yayinda yakejin kamar yaje ya rungumeta acikin jikinsa.musamman ma yanda yaga tana zuba zallar shagwaɓa, wannan yasa shi jin gaba ɗaya tsikar jikinsa sun mimmiƙe.

Abbou Jaheed kuwa ganin da gaske Laylerh'n taƙi karɓan tea dinne yasa shi ajiye mug din haɗe da miƙewa tsaye, kallon Oum Ayush da kuma Aunty Zee yayi, cikin nutsuwa yace. "Mutafi wata ƙila idan Najeeb ya mata magana zata sha." 
Jin hakanne kuwa yasa Oum Ayush da Aunty Zee harma da Teemah suka miƙe, jin an anbaci Najeeb ne kuma yasa Teemah sake kallon haɗaɗɗen gayen dake tsaye cikin milk colour ɗin shadda, wanda dama tun shigowarsa take kallonsa.
Murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, acikin zuciyarta tace.
"Gaskiya Najeeb handsome guy ne, shine wannan ƴar rainin hankalin zata wani ce bata sonshi." ƙwafa tayi tare da ƙudurtawa aranta cewar sai tayiwa Laylerh'n tsiya, da zaran tasamu sauƙi saita tsokane ta.
Kasancewar kuma Teemah'nce ta zamo ta ƙarshen fita daga ɗakin, hakan yasa ta jawo ƙofar ɗakin ta rufeta gam.

Laylerh kuwa ganin su Abbou Jaheed sun fita daga cikin ɗakinne yasata maida idanunta ta rumtse su ƙam, lokaci ɗaya kuwa ƙirjinta ya soma bugawa, akaron farko cike da tsoron Najeeb ɗin ta ƙanƙame jikinta waje ɗaya.

Najeeb kuwa da bai motsa daga tsayuwan nasa ba, har yanzu idanunsa akanta suke, saboda yanda yaji idanun nasa basu ƙoshi da kallonta ba, ganin kuma yanda take ta kakkame jikinta ne yasashi takowa ahankali ya ƙaraso jikin gadon.
Ƙamshin turarensa da ya shiga ratsa cikin hancinta ne ya sata gane cewar ya iso kusa da ita.
"Laylerh.!!"
Yaƙira sunanta cikin wata irin murya, me ɗauke da wata irin amo.
Hakanan ta samu kanta da kasa amsa masa, tare kuma da kasa buɗe idanunta ta kalleshi, saboda abu ɗaya ne ke yawo acikin zuciyarta, kuma shi kaɗai take so, shi take son gani da ji, shi kaɗai ne kuma zai iya rarrashinta har zuciyarta ta samu nutsuwa, haƙiƙa MALEEK shine saɓin zuciarta.

*(Sorry guys jia banyi update ba, saboda naga dayawanku fushi kuke da auren Laylerh shiasa nima nace bari na huta.😃)*

*24 December 2020*
1/19/21, 8:25 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*(This book is mainly for those that pay, if you know you did'nt pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay-0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz bank. Whatsapp number 07017879464. )*

*Chapter twenty eighth*

Sauƙan harshensa acikin bakinta ne yasa bugun zuciya, da nunfashinsu soma ƙoƙarin ɗaukewa, musamman saboda yanda sukaji wani irin abu me tsananin ƙarfi ya shiga cikin jikinsu, wanda hakan yasa suka samu kansu acikin wani irin yanayi me matuƙar wahalar fassaruwa, irin yanayin kuwa da dukkaninsu basu taɓa sanin cewar akwaishi acikin duniya ba, yanayin daya gusar musu da hankali haɗi da nutsuwarsu, kana yanayin da yasa gaba ɗaya rauninsu bayyana, tabbas ayau dukansu sun shaida cewar su ɗin muradi da kuma BURI ƊAYA ne, domin haɗewar su waje ɗaya yasa wani irin matsanancin shauƙi da kuma zazzafan ƙauna ya shiga yawo acikin jininsu, tare da haukata duk wani nau'in tunanin dake yawo acikin ƙwaƙwalwarsu, wanda sanadin haka yasa gaba ɗaya jikinsu ya soma ɓari.
Tabbas ayau bashi da ikon control ɗin kai da kuma zuciyarsa, kasancewar ayau ne duk wata soyayyar dake ɓoye acikin zuciyarsa ta bayyana kanata afili, haƙiƙa rasa Laylerh awajensa tamkar rasa rayuwarsa ne, domin kuwa ayau ya sake tabbatarwa da kansa cewar itace bugun zuciya da numfashinsa.
Tabbas wannan yanayi ne da ya zamo baƙo agaresu, saboda haɗuwar saliva ɗinsu waje ɗaya ba ƙaramin gigita musu tunani yayi ba, musamman Laylerh wanda ɗanɗanon yawun bakin Maleek ɗin yasa ta fara ƙoƙarin manta kae da kuma duniyar da take, kasancewar a iyaka tsawon rayuwarta, wannan shine karo na farko da wani namiji ya fara sanya bakinsa acikin nata, kuma wannan shine karo na farko da ta fara jin ɗanɗano da kuma launin saliva ɗin sa.
Maleek kuwa da gaba ɗaya jikinsa ya ɗauki rawa, ahankali cikin matsanancin shauƙin dake ɗibansa, ahankali ya sake tura harshensa acikin bakinta, amatuƙar sanyaye yasa laɓɓansa ya kamo ƴan ƙananan lips ɗinta, da aka shafawa sweat lipgloss, hannayensa yasa ya sake matseta ajikinsa, adaidai lokacin da yayiwa lips ɗinta wani fitinannen sucking ɗin daya sa lokaci ɗaya numfashinta ya soma ƙoƙarin ɗaukewa, haƙiƙa kasantuwar hakan shine karo na farko agaba ɗaya tarihin rayuwarsu, shin tayaya zasu misalta yanayin, da kuma faɗarsa?.

Tabbas ba zata iya jurewa yanda yake tsotsan bakinta da jajayen laɓɓansa masu masifar taushi ba, domin har aƙasan ƙafarta takejin wani abu na yi mata yawo, yayinda gaba ɗaya tsikar jikinta suka mimmiƙe, jin yanayin nasu take kamar amafarki, kasancewar ko da wasa bata taɓa kawo tunanin hakan aranta ba. Yanayin yanda yake juya harshensa acikin bakinta ne, yasa harshensu haɗewa waje ɗaya.
Wanda hakan yasa cikin fitinnannen yanayin da ta samu kanta aciki ta sake shigewa jikinsa, haɗe da manna ƙirjinta da nasa, wanda kuma tayi hakanne saboda bata cikin hayyacinta, kasancewar garɗi da kuma daɗin saliva ɗinsa, yasa tuni ta manta matsayita, da kuma sanin wacece ita.
Aɓangaren Maleek ma hakan take, dan kuwa kamar yanda Layler'n ta zauce haka shima ya fita hayyacinsa, yayinda gaba ɗaya ya manta wacece ita awajensa, zazzafan soyayyar da yake mata yasa shi manta cewar ita ɗin matar wani ce, kana halaliyar wani, kuma mallakin wani.
Saboda ayanzu gaba É—aya zuciyarsa ta cika da matsanancin son nunawa Laylerh'n irin yanda yajima yana muradin ta.
Yanayin yanda yake shan bakinta amatuƙar zauce ne yasa shi mata wani irin runguma, wanda har sai da ƙashin jikinta yayi ƙara, saboda yanda ya matseta sosai ajikinsa, haka yakejin kansa kamar mayunwacin zaki, yayinda kuma yakejin kamar ya ciro zuciyarsa ya damƙa mata atafin hannunta, ko hakan zai sa ya samu sassauci na daga abun da yakeji, saboda ayanzu yakai ƙololuwar zautuwa akan soyayyarta, haƙiƙa son da yake mata ya wuce duk wani tunanin me tunani.
Chapter 53 · 0% Book details