← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 144

Sashe 124

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Hakama Laylerh ta zama matarka, yanzu ita d’in mallakinka ne, zata rayune kuma ak’ark’ashin kulawarka, nasan kana ganin abun kamar amafarki ne, but ba mafarki bane da gaskene Maleek da gaskene Laylerh ta zama matarka ayau...�

Fou’ad ya k’arasa maganan da SOORAJ d’in ya soma, idanunsa cike da hawaye sam shikam ya kasa jurewa, Domin sanin k’arfin soyayyar dake tsakanin Laylerh Maleek, yasa auren nasu da aka d’aura yau, ya sanyayar masa da zuciya.

Ahankali ya matso ya rungume Maleek d’in da har yanzu ya kasa yin koda kyakkyawan motsi ne, still kuma har yanzu jikinsa bai bar b’ari ba, saboda ba k’aramin shock ya shiga ba.

Numfashinsa dake k’ok’arin k’wace masa gaba d’aya ya fusgo, tare da sauk’e wata irin ajiyar zuciyar, da tasa duk su Abbou Jaheed suka juyo suka kalleshi.

Kallo d’aya kawai da Abbou Jaheed yayi masa, take ya fahimci cewa, Maleek d’in baya cikin nutsuwarsa.
Hakanne yasa Abbou Jaheed yin k’asa da murya, tare da cewa Fou’ad ya ja Maleek d’in zuwa part d’insa dake cikin gida.

Kai Fou’ad ya jinjina tare da kamo hannun Maleek d’in, suka mik’e tsaye,

Tashin nasu ne kuma yasa mutanen dake wajen suka dinga zuwa sunayiwa Maleek d’in murna.

Shidai kam Allah Yasani ayanzu baya fahimtar komai, hakan yasa Fou’ad ne kawai ke amsa musu.

Ahaka suka fice daga cikin taron dubban jama’an.

Kaitsaye ta k’ofar baya suka shiga cikin gidan, direct kuma har sashin Maleek d’in.

Fou’ad ne ya bud’e k’ofar falon suka shiga.

Suna shiga kuwa ya sake hannun Maleek d’in, tare da dubansa suka fuskanci juna.

Y’an guntun hawayen dake cikin idanunsa ya share, tare da sakin murmushi, kana Ahankali yasa hannunsa ya bubbugi kafad’an Maleek d’in, cike kuma dason bashi k’arfin guiwa yace.

“Sama da kwanaki dubbai ka share a iya tsawon rayuwarka kana jiran zuwan wannan ranan, Tabbas komai mai zuwa da wuce wane Maleek, soyayyar daka rena acikin zuciyarsa almost 19 years yau gashi ta zama kammalalliya, Ayshnoor d’inka Maleek Ayshnoor d’in da kaketa fata da burin samu yau gashi ka sameta, yau Ayshnoor ta zamo mallakinka bayan tarin k’addarorin da sukayi wasa da rayuwarku, tabbas sau dayawan lokuta sai anfuskanci k’alubale masu tarin yawa kafun ake samun abunda akeso, ba kuma wata Nasara da take zuwa da sauk’i, ako ya ya dole sai gangar jiki da zuciya sun fuskanci k’alubale akan abunda suke so, shin ko kasan wani mutum ne mafi sa’a arayuwa? shine wanda zai iya d’auka da kuma jure kowani irin k’alubale akan k’addarorin rayuwa da Allah Ya rubuta masa, Kamar dai kai Maleek, duk da cewar akaron farko ka rasa Laylerh, amma baka aminta cewar ka zama Loser ba, zuciyarka ta tsaya akan abunda ta keso, duk da cewar akullum kanajin rad’ad’i k’una da kuma ciwo, amma still baka sanja daga soyayyar da kakeyi mata ba, domin da soyayyarta ne kad’ai kake iya gudanar da komai na rayuwarka, akwai kuma abunda kai kanka baka sani ba Maleek, idan babu soyayyar Laylerh acikin zuciya da jininka, kwata kwata bazaka tab’a iya cigaba da rayuwa ba, koda ma ace zaka rayu, To tamkar zero haka zaka zama, domin Laylerh itace gaba d’aya rayuwarka, itace macen da komin nauyin k’addara dole sai ta barku atare, again kuma itace macen da zata iya rayuwa dakai akowani irin hali, babu ruwanta da rashin lafiya ko kuma wata lalurarka, kai d’inne dai kawai acikin tunaninta, domin haka ne ma ta fad’awa su Abbou Jaheed cewar ta zab’i rayuwa dakai akan komai, saboda burinta akullum shine taganka cikin farinciki, Laylerh takace Maleek takace kai kad’ai kuma har abada!!!�

Wasu irin zafafan hawayen da suka cika idanunsa ne, suka samu daman gangarowa kan k’uncinsa.

Hakanne kuwa yasashi saurin juyawa kaitsaye ya nufi bedroom d’insa, duk da cewar ayanzun ko ganin gabansa da kyau bayayi.

Tsura masa idanu Fou’ad yayi, Yayinda ganin hawayen M.Jay akaro na farko, yasa zuciyarsa soma wani irin bugawa, take kuma tausayin Maleek d’in ya kamasa, domin ayau dole ne yayi kuka, bayan duk gwagwarmayan da yasha gashi Yau Allah ya basa Laylerh.

Shid’inma juyawa yayi ya fice daga cikin falon, tare da jawo k’ofar ya rufeta gam, saboda yasan cewa ayanzu Hutu da kuma nutsuwa Maleek d’in keso.

K’afafunsa da yakejin sunyi masa nauyi, ya soma ja ahankali tare dasa hannunsa d’aya ya turo k’ofar bedroom d’in.
Wani irin sanyi sosai yakeji ajikinsa, Yayinda bugun zuciyarsa kuwa har yanzu ta kasa dawowa daidai.

Brain d’insa kuwa tuni dama ta haukace, domin ta kasa d’aukan tunani d’aya da zata yi, abu d’aya ne kawai yasan keyi masa yawo acikin kan nasa, shine d’aura aurensa da Laylerh da akayi yau.

Baisan ta yaya, sai fara misalta irin yanayin da yake ciki ayanzun ba, abu d’aya kawai yake ta tambayar kansa, shine an d’aura masa Aure da Laylerh? hakan na nufin ya zama mijinta kenan?

Kansa ya d’an soma girgizawa ahankali, tare kuma dasanya hannayensa ya zare babbar rigar dake jikinsa, kasancewar jin jiki da kansa yake tamkar an d’aura masa k’aton dutse.

Ahankali ya shiga jan k’afafunsa har zuwa bakin k’ofar bathroom, murd’a handle d’in k’ofar yayi tare da kutsa kansa ciki.
Batare kuma daya rufe k’ofar bathroom d’inba ya k’arasa shigewa cikin toilet d’in.

Adaidai saitin shower ya tsaya, tare dakai hannunsa ahankali ya danna makunnin shower’n, take kuwa ruwa ya soma zubowa akansa, batare daya cire kaya ko takalmin dake k’afansa ba.

Sauk’an ruwan atsakiyar kansa ne kuma yasashi lumshe idanunsa, tare dasa hannunsa d’aya ya dafa jikin bango, duk da yanda jikinsa ke b’ari kuwa baiji ajikinsa cewar zai kashe shower’n ba, ayanzu so kawai yake ya dawo cikin hankali da tunaninsa.

Acan cikin gidannasu kuwa, koda labarin d’aura auren Laylerh da Maleek d’in ya shigo kunnen su Oum Ayush ba k’aramin farinciki da kuma godewa Allah sukayi ba.

Ahankali Oum Ayush ta turo k’ofar d’akin ta shigo, hannunta d’auke da plate d’in abinci.

K’arasowa jikin gadon da Laylerh’n ke kwance tayi, sam fuskarta ya kasa b’oye farincikin da take ciki, hannunta tasa adaidai kan goshin Laylerh dake kwance ta lumshe Idanunta kamar maiyin bacci.

Jin kuma babu ko d’igon zafi ajikin Laylerh’n ne yasa ta, sauk’e ajiyar zuciya tare kuma da ajiye plate d’in dake hannunta asaman bedside.

“Laylerh!�
Ta k’ira sunan Laylerh’n anutse.

Idanun nata dake alumshe ta d’an bud’e ahankali tare da kallon Oum Ayush d’in.

Murmushi mai kaman dariya ne ya k’wacewa Oum Ayush saboda, ta gama lura da cewar gaba d’aya ciwon Laylerh’n zallan sakalci da shagwab’ane.

“Tashi kici abinci, sai kiyi wanka, yau ba ranar da zakiyi ta kwanciya bane.�

D’an k’aramin bakinta ta turo gaba, kaman zata ce wani abu kuma sai ta fasa, ahankali ta yunk’ura ta tashi zaune.

Idanu Oum Ayush ta d’an zuba mata, Yayinda fuskarta ke sake wadatuwa da murmushi.

Ganin hakanne kuma yasa Laylerh’n sake shagwab’e fuska, asakalce tace.

“Nifa Oum Ayush har yanzu marana ciwo yakeyi, kuma nama k’oshi da abincin.�

Hararan wasa Oum Ayush ta watsa mata, tare da d’an had’e fuska, cikin salon bada umarni tace.

“Dolenki kuwa sai kinci abinci ko so kikeyi akaiki d’akin mijin naki da yunwa acikin ki? kin sandai waye Maleek cikinsa ma baikula ba bare naki.�

Idanunta tad’an zazzaro waje cikin yanayin mamakin da ya kasa b’uya akan fuskarta tace.

“D’akin mijina? Kuma Yah M.Jay?.�

Still wani harara Oum Ayush ta watsa mata, tare da cewa.

“Oh Allah yarinya saikace bakece da bakinki kikace a aura miki shi ba, To finally yau dai an d’aura muku aure yanzu ya zama mijinki ke kuma kin zama matarsa, idan kuma bakyaso yanzu sai nafad’awa su Abbou’nki su warware auren.�

Wani irin dokawa k’irji da zuciyarta sukayi, musamman da maganganu biyun suka fito alokaci d’aya, take kuma taji wani irin abu mai tsananin sanyi ya shiga yawo acikin gangar jikinta, wanda hakan yasa Idanunta cikowa da k’walla, yayinda akan fuskarta kuwa wani irin sahirtaccen murmushi ne ya bayyana, wanda ita kanta batasan dashi ba.

Ahankali tasa ta fukan hannayenta ta rufe fuskarta, domin wani irin shauk’i, kunya da kuma raunin zuciya ne suka lullub’eta alokaci guda, wanda har hakan yasa takejin kunyan Oum Ayush ta kalli fuskarta.

Oum Ayush kuwa gane hakanne yasa ta saki murmushi, tare da mik’ewa tsaye, cikin kulawa tace.

“Kici abincin sosai kinji Laylerh na, kinga masu meckup din dana dauko suna hanyan zuwa, idan kuma so kike akaiki wajen Maleek d’in babu kwalliya to.�

Batare kuma da ta jira me Laylerh’n zata ceba, ta bud’e k’ofar d’akin ta fice.

Laylerh kuwa jin fitar Oum Ayush d’in daga cikin d’akinne yasa ta bud’e fuskarta, wanda tuni ma harta b’aci da ruwan hawaye.

“Shikenan yanzu da gaske Yah M.Jay ya zama mijina?�

Tayiwa kanta tambayar abayyane, Yayinda azahirance kuwa takejin wani irin matsanancin soyayyarsa na k’aruwa acikin zuciyarta.

Wayarta ta dauka da sauri tare da lalub’o hotonsa dake cikin wayar, kyakkyawar fuskarsa ta tsurawa idanu bata ko k’yaftawa.

Cikin wata irin hot feeling voice dake fita slowly tace.

“Alhamdulillah Zan kasance dakai har abada My Boo, da kaine kawai Zanyi rayuwa, sannan zan jurewa duk wata k’addararka!!!�

K’arar wayarsa dake cikin aljihunsane ya dawo dashi daga cikin wata duniyar da yashiga, wanda batare daya ankara ba, har ruwan dake dukan jiki da kansa ya soma kokarin yi masa illa.

Janye jikinsa daga bakin shower’n yayi, tare dasa hannunsa ya kashe shower’n.
Gaba d’aya jikinsa ya jik’e tako ta ina, saboda tsabar sanyin daya shigesa kuwa harta hak’waran bakinsa karkarwa suke, amma da yake zuciyarsa tatafi zuwa wani waje na daban sam bayajin hakan ajikinsa.
Saima k’arasawa gaban sink da yayi ya d’auro alwala.

Bayan ya kammala alwalan ne kuma ya fito daga cikin toilet d’in, duk inda ya taka kuwa ruwan jikin kayansa ne ke d’iga awajen.

Samun kansa kuma da yayi akan Lallausan carpet d’in dake Malale a k’asan d’akinne yasa ka shi lumshe idanunsa.
Tare da zamewa ya durk’usa guiwowinsa.
Hannayensa dake ta karkarwa ya sa ya dafa k’asa, tare kuma da kai goshinsa k’asa yayi Sujjada, Lokaci d’aya kuma yaji wasu irin hawaye masu tsananin zafi sun zub’o daga cikin idanunsa.
Chapter 124 · 0% Book details