← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 144

Sashe 5

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Laylerh kuwa tana fita compound ɗin gidan, ta samu drivern Momy tsaye yana jiranta,  buɗe murfin motar tayi ta shiga sannan drivern ya tada motar,  maigadi ne ya wangale musu ƙofar gate ɗin gidan.  
Koda suka kawo bakin gate ɗin, ɗan leƙa kanta tayi ta window'n motar, still har yanzu wannan soldier man ɗin na tsaye abakin gate, kamar dai yanda tabarsa ɗazu,  jingina bayanta da jikin kujeran motar tayi, tare da lumshe beautyful sexy eyes ɗinta.     "MR.SOLDIER."  tafaɗa abayyane tare da ɗan ciza ƙananan jajayen laɓɓan bakinta,   tabbas zuciyarta nason tuna mata wani abu daya wuce acan baya, saidai kuma ƙwaƙwalwarta taƙi amsa hakan, gudu take tare da ɗiban wasu ayyuka masu tarin yawa, wanda ayanda take da ƙarancin shekaru bai kamata ace hakan na kasancewa da ita ba,   dole haka ta watsar da wasu tunanin da suka kasance marassa amfani, ko da sauɗaya ne itama watarana tanaso ace takasance kamar kowa, tunanin abun da Teacher David yayi mata ne ya shiga dawowa kanta, ji tayi idanunta masu matsanancin rauni sun cika da ƙwalla, sannu ahankali hakan ke ƙoƙarin tuna mata wani abu daya faru da rayuwarta lokacin baya, cikin wani irin sanyin murya, me ɗauke da rauni tace.   *"YA M.J"*    hawayen da suka cika idanunta ne suka samu daman gangarowa, lokaci ɗaya taji gaba ɗaya jikinta yayi weak, tunanin abun daya faru abaya ne yasoma ƙoƙarin kutsowa cikin brain ɗinta, wani irin tsoro ne me tsanani ya lulluɓeta, hakan yasa gaba ɗaya jikinta ya soma rawa, cikin kunnuwanta tasoma jin wata irin murya naƙiran. *"AYSHNOOR!!"* in a slow tone, murya ce da bazata taɓa iya manta ta ba, acikin gaba ɗaya duniyarta da rayuwarta.  
Da sauri ta buɗe idanunta, sakamakon jin yanda drivern ya caka burki, har sai da taɗan wantsalo gaba.          
Idanunta taɗan zaro waje ganin saura kaɗan su buge wani ɗan dattijon mutumi da yazo tsallaka titi.   driver'n ne ya leƙa kansa waje inda ya bawa mutumin haƙuri, sannan yaja motar sukayi gaba. Sake lumshe idanunta tayi, akaro na sau ba adadi, hakan ɗabi'a ne, wanda yake gudana acikin jininta, lumshe ido da cije lips, sauda dama takan tambayi kanta meyasa takeyin hakan, saidai takan rasa amsan da zata bawa kanta, dole tabar hakan amatsayin ɗabi'arta.
Ko mintuna 7 basu ƙara ba suka iso gaban makeken gate ɗin gidan Hajia Asma'u,   abakin gate ɗin drivern ya faka, hakanne yasa ta buɗe murfin motar ta fito, gaba ɗaya duk jikinta asanyaye yake, dole haka ta aro ƙwarin guiwa da jarumta ta sakawa kanta, dan bakowa takeso ya karanci damuwarta ba.   
Ahankali ta tura ƙaramar ƙofar gate ɗin ta shiga cikin gidan,    maigadin dake zaune abakin ƙofar ɗakin da aka tanada musamman danshi, yana ganinta ya washe baki tare da tasowa ya ƙaraso gareta, baki har kunne ya shiga cewa.  
"Fara me farar aniya, Farar Alkhairi,  kaga yarinya kyakkyawa son kowa, fara me zubin larabawa, wallahi ko acikin larabawa LAYLATU  kin fi wasu da yawa kyau, tauraruwa me haske abun son kowa."          Shiru Laylerh tayi tare da sakin murmushi, tabbas idan da sabo ta saba da halin mutumin, dan idan Momy zata aikota gidan sau dubu, to ba gajiyawa zai mata kirari sau dubu,   ɗan rusunawa tayi, saboda mutumin yana da ɗan yawan shekaru, cikin sanyin murya tace.   "Ina wuni Baba."      Baki ya sake washewa tare da cewa.    "Lafiya ƙalau Laylatul Khair, wato daren alkhairi kenan ko, inji larabawa, duk yanda akayi dai a daren Laylatul Ƙadari aka haifeki, wato daren Daraja kenan."   Dariya Laylerh tayi, sannan ta girgiza masa kai, sanin cewa idan ta tsaya zaita yi mata surutu ne yasa ta wuce cikin gidan.  Shima murmushin yayi sannan ya koma ya zauna.  
Laylerh kuwa tsayawa tayi abakin babbar ƙofar da zai sadata da falon gidan, knocking tayi akazo aka buɗe mata ƙofar, Hajiya Asma'un ce da kanta ta buɗe kofar,  ganin Laylerh yasa ta saki ɗan murmushi, tare da cewa.     "Laylerh kece, sannunki da zuwa."    Tafaɗi maganan tana me bawa Laylerh hanya ta wuce.  Saida suka ƙaraso cikin falon Laylerh ta rusuna ta gaishe da Hajiya Asma'u'n, fuska asake Hajiya Asma'u ta amsa mata, tare da tambayanta su Momy.    "Lafiansu ƙalau."  Laylerh ta amsa mata, tare da miƙa mata ƴar jakan da Momy tace takawo mata, amsan jakan Hajiya Asma'u tayi tana murmushi, nan ta ƙwala ƙiran mai aikinta, ahanzarce kuwa mai aikin Hajiyan tazo, cikin isa Hajiya Asma'u tace.     "Kikawo wa Laylerh drinks da abinci."     "To" tace cikin sauri ta juya ta koma kitchine dan cika umarnin Hajiyan.                    
Bawani jimawa ta kawowa Laylerh Jallop rice nd coslow sai kuma banana drinks,    cikin kulawa Hajia Asma'u tace. "Laylerh kici abinci."       Murmushi tayi, cikin yanayin nutsuwa tace.  "Hajiya na ƙoshi bana jin yunwa."  Kai Hajiya Asma'u ta girgiza tare da cewa.  "Aa Laylerh kinsan banason halin nan naki na fulaku."  Tana faɗan haka tatashi ta wuce ɗakinta.      
Ɗan jim Laylerh tayi, bawai yunwan ne bataji ba, kawai dai bata da sakewa ne, sometimes takanji ɗar da kuma tsoron wasu mutanen na daban.  Ahankali take ɗiban abincin tana kaiwa bakinta, bata wani ci abincin sosai ba taji ta ƙoshi, kasancewar dama ita ba mutum bace me yawan cin abinci,  ruwa tasha sannan ta miƙe tsaye, daidai lokacin Hajiya Asma'u tafito daga ɗakinta.  Ganin Laylerh a tsaye yasa tace "Har kin kammala?."   Kai Laylerh ta jinjina, tare da ɗaukan tissue ta goge bakinta.         Wata ƴar ƙaramar jaka Hajiya Asmau ta bata, tare da cewa  "Gashi wannan  naki ne ki gaishemin da Momyn taku."   Ƙoƙarin girgiza kai Laylerh ta somayi, alaman bazata amsa ba, take Hajiya Asma'u ta ɓata fuska, ahanzarce tace.   "Banason musu Laylerh ki amsa kawai."    Karɓan ƴar ƙaramar jakan Laylerh tayi tare da yiwa Hajiya Asma'un godiya, daga haka tayi mata sallama sannan tafice daga cikin falon.          Saida ta shiga cikin mota, har suƙa fara tafiya, kafun ta buɗe ƴar jakan da Hajiya Asma'un ta bata, kayan meckup ne aciki sai kuma wani agogon silver me kyau, sai kuma kuɗi 5k, rufe jakan tayi tare da maida kallonta ga titi, abubuwa da yawa takeson saƙawa acikin rai da zuciyarta, amma duk yanda taso hakan abun ya kasa,  bata sani ba ko ƙwaƙwalwarta ne batayi ƙarfi ba wajen iya nazartan abubuwa.     isowansu gidane yasa ta ajiye duk wani tunani,   tana fita daga cikin motar kaitsaye babban falon gidan nasu ta nufa, bata taradda kowa ba,  ganin lokacin sallan Magrib ya gabato ne yasa  kaitsaye ta wuce ɗakinta.      Hijab ɗin dake jikinta ta cire sannan ta shiga toilet ta ɗauro alwala,      koda ta fito nan kan darduman dake shumfuɗe acikin ɗakin ta hau, ta gabatar da sallah, tana nan zaune akan sallayan har aka ƙira sallan Isha, bayan ta idar da sallan Isha ɗinne ta miƙe daga kan sallayan, gaban drawer ɗinta ta ƙarasa tare da buɗewa ta zaro wani riga da wando na bacci masu kalan blue,  doguwar rigan dake jikinta ta cire sannan ta maye gurbinsa da riga da wandon,   dunƙule dogon gashinta tayi waje ɗaya, sannan ta sanya wata hulan sanyi akanta, kasancewar ana ɗan busa sanyi kaɗan.    
Kan ɗan madaidaicin gadon nata ta hau, tare da jawo blanket ta rufe jikinta dashi,  hannunta na dama ta ɗago tare da zubawa ɗaya daga cikin yatsunta dake sanye da wani haɗaɗɗen zobe idanu, wanda ajikinsa aka rubuta (L.M)  da manyan baƙi,  zobe ne na zallan zinare me tsananin kyau da tsada,  ɗan lumshe idanunta tayi ahankali take ɗan murza zoben da hannunta, tana matuƙar ƙaunar zoben sosai, wanda yana ahanunta ne sama da 7 years, tun yana ababban ɗan yatsarta har ya dawo ƙaramar yatsarta saboda yaɗan mawa babban yatsan nata kaɗan.             Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da tura kanta acikin pillow, ita da zuciyarta kawai suke faɗin wasu kalamai wanda ƙwayan sautinsa baya iya bayyana, saidai laɓɓanta dake motsawa ahankali. 
Ahaka bacci ɓarawo ya ɗauketa. 

Washe gari.  
Chapter 5 · 0% Book details