Sashe 105
Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
D’an tsagaitawa da maganan nata tayi tare da matsowa kusa da Najeeb d’in, d’aya daga cikin hannayensa ta kamo ta d’aura akan k’irjinta daidai saitin zuciyarta.
Cikin wata irin raunanniyar murya tace.
“Yah Najeeb please koda sau d’ayane ka tab’a zuciyata, na tabbata zakaji yanda take harbawa akan kowani damuwar sa, duk wani ciwonsa azuciyata nakejin zafin, domin shine mutum na farko aduniya da tun Ina k’arama ya fara shayar dani da yawun bakinsa, kana kuma shine mutum na farko aduniya da idanuna ke yawan yimin gizo dashi, komai zai samesa sai naji hakan ajikina, ko kuma nagani amafarkina, banason wani abu ya sameshi, banason koda d’igon abu na cutarwa ne ya sauk’a akansa,
Domin saboda shine kawae nake rayuwa, Tabbas inajin ciwo sosai acikin zuciyata, amma kuma nasan nasa ciwon da yakeji ya zarce nawa zafi da rad’ad’i, ance bazae tab’a haihuwa ba, yanzu kuma ance ba za’a bashi aure ba saboda yana da lalura, nasani kwarai nasan cewar wannan masomin k’alubalen da zai ci gaba da fuskanta ne agaba d’aya rayuwarsa, Saboda wannan kawai bazai samu farinciki ba? bazai samu mai kulawa dashi koda sau d’ayane ba? shin menene laifinsa aciki dan k’addarar rashin haihuwa ta fad’a masa? kenan wannan shike nuna saboda hakan Yarasa duk wata dama nasa kenan? Bazai samu mai kulawa dashi da bashi abinci ba, bazai samu me nuna masa soyayya ba, kullum zai zauna acikin damuwar da baya iya fad’anta ga kowa, haka zaiyita jin ciwo azuciyarsa, shikenan shi bazaiyi farinciki ba, ko yaushe zuciyarsa k’uncine!!�
Idanunta ta rumtse da k’arfi, wanda kuma hakan ke bayyana abunda takeji acikin zuciyarta mai tsananin ciwo ne,
Asanyaye da kuma muryarta me rauni sosai tace.
“Please Yah Najeeb ko da sau d’aya ne ka saurari bugun da zuciyata keyi, domin acikintane kawae zaka fahimci abunda Yah Maleek yakeji acikin tasa zuciyar, wanda baki bazai tab’a iya furtawa ba, wanda kuma yake kassara masa duk wani burinsa na kowacce rana, tabbas yau naji dama ina da iko, to da na d’aukewa Yah M.Jay gaba d’aya duk wata mummunar damuwarsa, tayanda shima zaiyi farinciki kaman kowa, domin ko kad’an banason gani kojin ciwonsa, saboda nayi imani ni mai matsanancin raunine akansa!!!!
Ta k’are maganar nata tana me girgiza kanta tare kuma da kama hannayen Najeeb din duka biyu ta had’e su waje d’aya, lokaci d’aya kuma ta fashe da wani irin fitinannen kuka mai tsananin tab’a zuciyar mai sauraro, kukan dake zayyane duk wani abunda ke cikin zuciyarta, haka kuma kukan dake nuna cewar ta gaza, sannan kuma tazo last hope d’inta.
Manyan idanunsa wanda suka kad’a sukayi jajur ya lumshe tare da kamo hannunta dake kan nasa ya matse gam, wani irin ciwo mai tsanani yakeji acikin zuciyarsa, yayinda kuma gaba d’aya gangar jikinsa ya d’auki rawa, daga gefe guda kuwa gargasan dake kwance ajikinsane suka mimmik’e, yayinda idanunsa suka cigaba da runewa zuwa kalan ja.
Wani irin tsalle da zuciyartasa keyine kuma yasashi bud’e idanunsa, tare da sauk’e ganinsa akan Laylerh’n wanda take kuka sosae.
Akaron farko na tarihin rayuwarsa kenan da yaji wasu irin hawaye masu d’umi sun zubo daga cikin idanunsa, yayinda zuciyarsa kuma tayi wani irin mummunan karyewa, matsanancin tausayin kansa da kuma na Laylerh’n ne ya lullub’esa, wanda har hakan ya sashi kasa iya jurewa.
Saidai kuma gudun kada Laylerh’n ta d’ago kai taga hawayensa ne yasashi saurin kawar da kansa gefe tare da mik’ewa tsaye, cikin yanayin sauri da kuma son daidaita nutsuwarsa ya fad’a cikin bathroom.
Laylerh kuwa da zuwa yanzu kukan da take ya soma cin k’arfinta, ahankali ta zame jikinta ta kwanta akan lallausan carpet d’in dake malale asaman tiles d’in wajen, haka takejin numfashinta na fusga kaman zai bar gangar jikinta.
Najeeb kuwa yana shiga cikin toilet d’in sassanyan ruwan dake kwance acikin had’add’en jakuzzie ya d’ebo ya watsa akan fuskarsa, yayi hakanne kuma wae ko zaiji sanyi da salama na daga wutar dake cin zuciyarsa, saidai kuma sam hakan baisa yaji wani sanyi acikin zuciyarsa ba.
Ahankali ya jingina bayansa da jikin bango tare kuma da sake rumtse idanunsa.
Abayyane kana cikin wata irin murya mai dauke da rauni sosae yace.
“Tabbas zan aikata hakan koda zan kasance acikin k’unci, saboda ayanzu dolene na samawa zuciyoyin da aka ginasu akan muradi d’aya haske da kuma farinciki, ko da ace badon komae ba, idanuwana sunganemin abunda ya zama tilas d’ina!!!�
D’agowa daga jinginen da yake yayi tare da daukan towel ya goge fuskarsa.
Cikin k’arfin hali da kuma bugun zuciyar daya samu kansa aciki ya murd’a handle d’in kof’ar bathroom d’in ya fito.
Idanunsa ya sauk’e akan Laylerh da keta sakin sheshshek’an kuka, ga kuma wani wahalallen bacci daya d’auketa, wanda da’alama bata shiryawa yinsa ba sam.
Wani irin matsanancin tausayintane yaji ya k’ara narkar da zuciyarsa, tare kuma da wani sabon shauk’in sonta,
Saidai kuma amma ayau sam bashi da zab’i domin yayi imani cewa har abada ba kowani so bane yake iya zama tsuntsu.
Asanyaye ya k’arasa gaban d’aya daga cikin bedside drawer’n dake gefen gadon su, duk da yanda kirji da kuma zuciyarsa ke tsananin bugawa amma hakan bai hanashi daurewa ba, ahankali ya jawo murfin drawer’n tare kuma dasa hannunsa aciki ya d’auko wani littafi wanda samansa ke d’auke da biro.
Idanu ya tsurawa littafin dake hannun nasa kusan na mintuna 10 kafun ya dawo da kallonsa ga Laylerh wacce ke kwance ak’asa tana bacci.
Wani irin kallo yake mata wanda ke bayyana sabuwar soyayyarta dake ratsa kowani kofa na jikinsa, Tabbas yanayiwa Laylerh so mai tsanani, irin wanda a kullum yake fatan yin rayuwa da ita.
Yaya zaiyi? Tayaya zai bari saboda shi kawae komai ya lalace? Tabbas abunda yake shirin aikatawa yanzu cutarwane amma bashi da wani zab’i wanda ya wuce hakan.
Asanyeye ya janye kansa daga kallonta.
Wani irin rumtsewa yayiwa idanunsa adaidai lokacin daya d’aura hannunsa dake rik’e da abun rubuta akan farar takardan dake gabansa, ahankali ya shiga sarrafa hannunsa dake rawa wajen rubuta abundake zuciyarsa akan takardan.
Adaidai lokacin daya kammala rubutun nasane kuma wasu irin hawaye masu tsananin zafi suka fito daga cikin idanunsa tare da d’iga akan takardan.
*(Wayyo Allah Na NajeebðŸ˜ðŸ˜ kome ya aikata haka oho gaskiya I’m so sad 😞 son Najeeb yasa bazan iya karasa page d’innan yau ba. 1/3/2021 Najeeb first March abunda zaka mana kenanðŸ˜ðŸ˜)*
*8:23 pm*
3/3/21, 9:07 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*
*Written By*
fatymasardauna
#hearttouching
*Chapter 61*
Rubutun da yayi akan farar takardar ya tsurawa idanunsa wanda suka kad’a sukayi wani irin ja tamkar wanda aka watsawa garin barkono acikinsu, yayinda yakejin wani irin zafi da kuma k’una acikin zuciyarsa, lallai Tabbas yasan yayi abunda zae damesa, saidai kuma bashi da wani zab’in daya wuce hakan, k’warai yasani daga yanzun har zuwa wasu lokuta masu tsawo zai cigaba da ruskar kansa acikin bak’inciki, hak’ik’a zuciya da kuma gangar jikinsa suna matuk’ar son Laylerh so kuma ba nawasa ba, saidai akwae wani abu daya tabbatar da cewa rashin kammaluwansa babban matsalane sannan zai iya haifar da kowani irin matsala.
Janye idanunsa daga kan takardar yayi tare dasa hannunsa ya nannad’e ta, cikin wani irin rashin kuzari da kuma alhinin dake cike azuciyarsa, ahankali ya zame tare da zama abakin had’add’en gadon su, idanunsa wanda sukayi matuk’ar ja ya d’aura akan Laylerh’n wanda har yanzu ke kwance ak’asa, duk da cewar kuma bacci take, amma time to time take sakin sheshshek’an kuka, wani irin kallo mai d’auke da tsananin shauk’i ya shiga yi mata, yayinda yakejin matsanancin tausayinta na ratsa duk kowani gaba da sashi na jikinsa, zuciyarsa tayi matuk’ar karyewa, kana rauninsa ya bayyana afili, shikansa baisan cewa son da yake yiwa Laylerh’n ya girma azuciyarsa har haka ba, ya sani kuma k’warai cewa yayi babban asara, domin abune dayake abayyane cewar bazae tab’a samun mace kamarta ba, koda ma ace zai samu to da matuk’ar wahala, ba kuma sak irinta ba saidai maiyanayinta, saboda yayi imani cewa Laylerh’n ta dabance acikin sauran mata, komae nata mai kyau da tsari ne, k’warai yasan cewa zaiyi missing abubuwa da dama, musamman kallon kyakkyawan fuskarta, da kuma had’add’iyar surar jikinta, uwa uba shagwab’a da kuma yanayin yarintarta.
Hawayen da suka sauk’a akan fuskarsa batare daya san da sauk’owarsu ba yayi saurin sa hannu ya share.
Jin kuma yanda zuciyarsa ke bugawa kaman zata faso k’irjinsa ta fitone yasashi janye idanunsa daga kan Laylerh’n, asanyaye ya shiga jujjuya ninkakkiyar farar takardar dake hannunsa, wanda awajensa abunda ke rubuce ajikin takardar yafi komae d’acin ji da gani, badon kuma yakai zuciyarsa nesa ba, to fa da har abada bazae tab’a iya rubuta hakan da hannuwansa ba.
Tayaya zai fuskanci Laylerh da wannan abun daya aikata mata? baisan ayaya zata d’auki maganar tasa ba, baisan ma zata fahimta ko bazata fahimta ba.
Abu d’aya kawae yasani shine yayi iya abunda zae iya, sannan baya kuma jin zai iya fuskantar ta fuska da fuska ya gayamata abunda ke rubuce acikin takardar, saboda ita yarinyace k’arama da sam baikamata ace ta fara fuskantar k’alubalen rayuwa tun daga yanzu ba, shekarunta kad’anne hakan yasa ba komae ne zata iya jurewa ba, batasan ya abun yake ba, sannan bata kuma san ya girmansa yake ba.
Labb’an bakinsa masu kalan pink da suka bushe ya d’an taune, tare da had’iyan wani yawu mai d’acin gaske daya tsaya masa amak’oshinsa.
Cikin yanayin dauriya da kuma son k’arfafawa kansa guiwa akan abunda yayi d’in ya mik’e tsaye, tare da d’aukan wani envelope dake ajiye asaman bedside drawer’n ya zura farar takardar aciki.