← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 144

Sashe 117

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idanunsa dake kan wayar tasa wanda suka sakeyin jajur, ya rumtse da k’arfi, tare dasa hannunsa d’aya ya katse k’iran.
Sam ba zae iya jurewa abunda yakeji ba, saboda ayanzun zuciyarsa tayi rauni sosai, har yakai ga yanajin wani abu mai kaman ruwa na yawo acikin idanunsa.
K’warae bashi da bakin da zai iyayi mata magana, saboda kowani magana d’aya da zaiyi mata, zai zama tamkar b’allewan bugun zuciyarsa ne.

Acan b’angaren Laylerh kuwa jin an katse k’iran da akayi mata d’inne, yasa ahankali ta zare wayar daga kan kunnenta, kamar wanda ke na zarin wani abu kuwa haka ta k’urawa screen d’in wayarta ta idanu.
Saidai kuma sam ta kasa fahimtar komae.
Domin hatta tunaninta ma tsayawa yayi, saidai kuma still har yanzu bata dae na jin wannan sanyin na ratsa cikin jikinta ba.

“Laylerh mekikeyi anan tun da muka fito paper nake ta nemanki, amma ban ganki ba.�

Muryar Teemah dake k’arasowa wajen ya katse mata duk wani yanayi da take ciki.

Ahankali ta d’ago kai ta kalli Teemah’n, Kamar kuma zata ce wani abu saita fasa, saboda hakanan taji duk jikinta yayi sanyi, Yayinda wani irin mood ke fusgarta.

Teemah kuwa idanu ta d’an k’urawa Laylerh’n domin ta fahimci kamar tana cikin damuwa.
Saidai kuma sanin da tayi cewar ako da yaushe, labarin da kuma damuwar Laylerh’n bata wuce ta Maleek shiyasa bata tambayeta agame da abunda ke damunta ba.

Saima kamo hannun Laylerh’n da tayi ta mik’ar da ita tsaye.

Kallon Laylerh’n tayi sosae kafun tad’anyi k’asa da muryarta, cikin siga da kuma salon tsokana irin nata tace.

“Tun d’azu Aunty Zee tazo d’aukanki, gashi kuma yau dai munyi final exam saboda haka sai munzo bikin L&M I mean LaylerhMaleek kenan.�

Teemah’n takai k’arshen maganan nata tana d’an kashewa Laylerh’n idanu.

Wanda hakan yasa Laylerh’n zuba mata idanunta dake bayyanar da abubuwa kala.

Teemah kuwa sam bata damu da shirun da Laylerh’n ba, because hakan Bawae bak’on abu bane awajenta, itama bata sake cewa komae ba taja hannun Laylerh’n suka tafi.

Direct wajen da motar Aunty Zee ke fake suka nufa.
Koda suka k’arasa Aunty Zee d’in murmushi tayi, tare da tambayan Laylerh’n ya jarrabawa.

Da “Alhamdulillah!� kawae ta amsa daga haka ta bud’e murfin motar ta shiga, bayan sunyi sallama da Teemah akan cewar next week zata zo gidan Aunty Zee d’in.

Still yauma kuma saida Teemah’n taga fitansu acikin school d’in kafun ta koma wajen sauran students din makarantar suka ci gaba da celebration.

Acan gidansu Laylerh’n kuwa
Abbou Jaheed da kuma Abbou Khareem ne ke zaune akan d’aya daga cikin had’addun royal chairs d’in dake cikin falon, idanu suka zubawa Oum Ayush dake zaune.
Wanda da dukkan alama kallo d’aya zakayi mata kafahimci cewa akwae magana abakinta.

Duk da cewar hakanne kuma amma yanzu tsawon 10mn kenan da zamansu awajen takasa cewa komae.

Abbou Khareem wanda ya gaji da zamanne ya sake d’ago kae ya kalleta, cikin kuma yanayin k’osawa yace.

“Ayush kince akwae muhimmiyar maganan da zaki fad’a mana amma kuma naga kinyi shiru, kodai wani abu ya faru ne?, ki fad’i koma meyene duk ke muke saurare.�

Ahankali Oum Ayush ta d’an sunkuyar da kanta, Tabbas duk da cewa batasan a yanda zasu fahimci maganar nata ba, ya zama tilas ta fad’a musu, domin kuwa ita tasan tayi nakanne
Bawae da mummunan manufa ba, Idanunta ta d’an lumshe tare da tausasa murya, cikin kuma son bayyanar da gaskiyar abunda ke cikin ranta tace

“Kuyi hak’uri domin akwae abunda na b’oye ban sanar muku ba, ban kuma yi hakan da wata manufa ba, saidan duba cancanta da kuma dacewar hakan, hakika duk da cewar bani ce na haifi Laylerh ba amma har acikin zuciyata, inajin soyayyarta kamar y’ar ciki na, kasancewar ta yarinya k’arama kuma yasa dole tana da buk’atar samun nutsuwa, musamman idan muka duba irin k’addarar daya sameta ayanzu, akwae buk’atar musa ma mata Hutu, da kuma yin abun da zai sanyaya zuciyarta, aciki kuwa harda nesan ta ta da gidan nan, domin kuwa matuk’ar tana zaune cikin agidannan dole ne rayuwar da tayi da Najeeb zai dinga dawo mata, hakan kuwa zai iya shafar karatun ta.�

D’an tsagaitawa da maganan nata tayi, wanda hakan yasa Abbou Khareem cewa.

“Har yanzu dae baki fad’i abunda kikeson fad’ad’in ba, sannan kuma mu sam bamu fahimce ki ba, ba mu kuma gane abunda kike nufi ba.�

Jin abunda Abbou Khareem d’in ya fad’ane, yasa ta sauk’e ajiyar zuciya, cikin kuma confidence d’in abunda ke cikin zuciyarta tace.

“Abunda nake nufi shine kwata kwata Laylerh bata da Iddah akanta, saboda wata mu’amala ta aure bata tab’a shiga tsakaninta da Najeeb ba, ma’ana Najeeb bai tab’a kusantarta ba, saboda haka babu Iddah akanta, nasan hakanne kuma aranar da Najeeb d’in ya sake ta, koda na tambayi Najeeb d’in kuwa shima ya tabbatar min da hakan, saboda haka
Laylerh bazatayi Iddah ba, na b’oye muku maganar ne kuma saboda, sai ta dalilin yin iddah’n ne kad’ae zata nesanta da gidannan, wanda hakan zae sa tayi karatun exam d’inta anutse, gashi kuma Alhamdulillah yau sun kammala exam d’in, dan haka ko ayau kuka buk’aci dawowanta gidannan zata dawo batare da wani miki ko ciwo acikin zuciyarta ba, sannan kuma
Ko agobe za’a iya d’aura mata wani sabon AURE.�

Wani irin nannauyan ajiyar zuciya gaba d’aya su Abbou Jaheed d’in suka sauk’e, asakamakon jin maganganun da Oum Ayush d’in ta fad’a musu, Yayinda fuskonkinsu kuwa suka cika da tarin mamaki da kuma al’ajabin faruwar hakan, domin acikinsu babu wanda ya tab’a kawo tunanin cewar wai Najeeb bai tab’a kusantar Laylerh ba.

*(Sorry page din yau ba yawa, just na samu time ne kawae nace bari na yi)*

*19/3/2021*

*7:43pm*
3/22/21, 7:59 AM - Ummi Tandama: *LAYLERHMALEEK*

*(Page d’in yau dai sai kun had’a da hakuri gaba daya ina busy ban zauna na nutsu ba)*

*Chapter 70*

Gyara zama Abbou Jaheed yayi tare kuma da sake sauk’e wata sabuwar ajiyar zuciya, Tabbas maganganun da Oum Ayush d’in ta fad’a sun matuk’ar shiga jikinsu, kana kuma sun sauya tunaninsu.
Domin kuwa abune da dukkansu basu tsammata ba.
Saidai kuma sam basuga laifin Oum Ayush akan b’oye musu gaskiyar al’amarin da tayi ba, saboda koba komai hakan da tayi d’in ya bawa Laylerh’n daman yin karatunta cikin nutsuwa.

Still ajiyar zuciya Abbou Jaheed d’in yayi, cikin kuma nuna cewar ya fahimci abunda Oum Ayush d’in ta aikata yace.

“Tabbas nafahimceki Ayush, na kuma san bazaki tab’ayin wani abu da zai cutar da rayuwar Laylerh ba, na kuma ji dad’in hakan k’warae, domin kuwa koba komae Laylerh zata samu nutsuwa acan gidan, saidai kuma aanzu duk wani abunda ya faru ya riga daya wuce, ko akwai Iddah akan Laylerh ko babu, yanzu babban abunda ya kamata mu fara fuskanta shine rayuwar da Laylerh’n zatayi anan gaba, duk da kuwa munsan cewa Allah Ne ke tsarawa bawansa komai da komai na rayuwa, amma ya kamata ace muma munyiwa rayuwar da zata fuskanta ayanzu kyakkyawan tanadi, domin so nakeyi kulawar da zata samu ayanzu daga garemu ya zarce na ko yaushe, ko badan maraicinta ba, Kodan saboda k’addarar da ta fuskanta da kuma tsananin biyayyarta.�

D’an tsagaitawa da maganan nasa yayi, tare kuma da numfasawa.
Kana yaci gaba da cewa.

“Tun bayan mutuwar aurenta, na tsara cewar baza mu sake d’auko mata maganar aure da wuri ba, har sai bayan ta kammala karatun degree d’inta, domin result d’inta na fitowa zan turata karatu k’asar syprus, acan nakeso tayi degree d’inta, zuwa lokacin da zata kammala kuma nasan tasan duk wani abu daya shafi rayuwar duniya, da ma sanin ciwon kai, sab’anin yanzu da ba komai ne ta gama sani ba, saidai kuma kafun na aikata hakan dole Ina buk’atar amincewar ku, domin kasancewarta agabana, Bawae yana nufin cewa ni kad’ai nake iko da ita ba, kuma d’iyarku ce kuna da iko da ita.�

Gaba d’aya falon shiru ya d’auka saboda jin abunda Abbou Jaheed d’in ya fad’a, Lallai tabbas tanadin da yayiwa Laylerh’n me kyaune, dukkaninsu kuma zasu yi fatan ace hakan ya kasance.

Saidai kuma banda zuciyar Oum Ayush da take sak’a mata wani abu na daban, saboda sam gangar jikinta bai bata cewar abunda Abbou Jaheed d’in keso zai yiwu ba.
Saidai kuma gudun kada wani abu ya sake faruwa da rayuwar Laylerh’n kamar yanda ya faru abayane yasa ta d’an gyara zamanta, tare da d’ago kai ta fuskanci Abbou Jaheed d’in, cikin yanayin kuma da tasan zai fahimceta tace.

“Tabbas fatan da ka yiwa Laylerh maikyau ne, kuma dukan mu zamu so ace hakan ya kasance, saidai kuma akan komai daya shafi rayuwarta dole muna buk’atar jin ta bakinta, domin ba Lallai abunda muka zab’a mata ya zama shine zab’inta ba, watak’ila tana da wani hope d’inta na daban, saidai kuma kasancewarta yarinya mai biyayya hakan yasa kome muka zo mata dashi bazata k’i amincewa ba, koda kuwa tana da nata ra’ayin.�

D’an tsagaitawa da maganan nata tayi, tare kuma da sake duban su Abbou Jaheed d’in.
Murya atausashe kana kuma cike da tausayi tace.

“Dan Allah awannan karon mubar Laylerh ta zab’i abunda takeso, mubari muji zab’inta daga bakinta, domin zai iya kasancewa bayan karatu akwai wani abu da takeso, wanda kuma take mafarkin cimmasa, saboda haka mu b’ata zab’i akan rayuwarta tanan gaba!!�

Yanayin yanda ta k’are maganar nata murya asanyaye ne yasa, duk su Abbou Jaheed suka sauk’e ajiyar zuciya.

Cikin yanayin gamsuwa da kalaman Oum Ayush d’in kuwa Abbou Jaheed, yace.
“Insha Allah zamuyi hakan, saidai kuma ayau inason Laylerh’n ta dawo, domin dama Iddah ne ya kaita to yanzu kuma babu shi, sannan sun kammala jarrabawar tasu, saboda haka Oum Ayush kije ki d’aukota ta dawo, ban kuma yarda asauk’eta akowanni sashi ba sai naku.�

Kai Oum Ayush da Abbou Khareem suka jinjina cike da gamsuwa, Yayinda Oum Ayush kuwa taji wani irin sanyi na ratsa zuciyarta, domin kuwa duk da batasan wani abune zai biyo baya ba, tanasa rai da kuma fatan cewa Alkhairi ne Insha Allah.

Mik’ewa tsaye tayi cikin kuma yanayin sakin fuska ta juya ta fice daga cikin falon.

Nan tabar su Abbou Khareem na tattaunawa, ita kuwa kaitsaye sashinta ta wuce tare da soma kimtsa kanta, saboda sam batason b’ata lokaci awajen d’auko Laylerh’n.
Chapter 117 · 0% Book details