Sashe 120
Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ajiyar zuciya mai k’arfi Abbou Jaheed ya sauk’e, tare dasa bayan hannunsa ahankali ya goge hawayen da suka cika idanunsa, hawayen dake d’auke da ma’anoni daban daban, saidai kuma abu mafi rinjaye na dalilin hawayennasa shine, matsanancin tausayin LaylerhMaleek d’in daya cika zuciyarsa.
Agefe guda kuwa sosai ya gamsu da kalaman Abbou Khareem, Insha Allah Kuma auren Laylerh da Maleek za’ayi shi kamar yanda Abbou Khareem ya tsara.
Acan sashin Oum Ayush kuwa, afalo Oum din ta zaunar da Laylerh’n, tare da ajiye mata plate d’in abinci agabanta.
Saidai kuma kwata kwata lomanta biyu ta ajiye spoon d’in abincin, hakan ya faru ne kuma saboda wani irin ciwon kai da takeji, ba komae ne ya jawo mata ciwon kan ba kuwa face kukan da tayi.
Lura da cewar batajin dad’ine kuma yasa bayan tayi sallan la’asar Oum Ayush ta bata maganin ciwon kai tasha, bayan tasha maganinne kuma ta wuce d’aki ta kwanta, sanin kuma da tayi cewar ba kyau yin bacci bayan Salla’n la’asar ne, yasa ta kunna karatun Al’minshawy, asanyaye ta soma bin karatun.
*Washington DC*
Sake gyara kwanciyarsa yayi akaro na barkatai, tare kuma da lumshe idanunsa wanda sukayi jajur, sosai yakejin wani irin sauyi ajikinsa, musamman acikin kwana biyun da suka wuce, duk da cewar kuwa yasan yana da k’arfin feeling amma ayanzu abunda yakeji d’in ya soma zarce tunaninsa.
Wanda har yakaisa ga fara tunanin iya jurewa abubuwa biyun dake damunsa, wanda asanadinsu yake neman zama zautacce.
Hannunsa ya d’aura akan k’irjinsa, daidai saitin zuciyarsa dake wani irin bugawa, sam baisan meyasa ayanzun yake samun kansa da rashin iya b’oye rauninsa ba, abubuwa da yawa suna damunsa, wanda idan ya tuna sai yaji zuciyarsa tayi masa rauni sosai.
Again sake gyara kwanciyarsa yayi, wanda hakan kuma ne yasa Fou’ad dake zaune k’ura masa ido, tun d’azu yana ankare da yanayin Maleek d’in, saboda ya fahimci cewa, tunda suka zo USA d’in kwata kwata hankalin Maleek ba ajikinsa yake ba, koda yaushe abu d’aya kawai yakeyi, sam shikam bai tab’a sanin cewa Soyayya nasa hauka ba, sai akan M.Jay.
Wayarsa da tayi k’ara ne yasashi janye idanunsa akan Maleek, tare da kai hannunsa ya d’auki wayar, jin kuma da yayi Abbou Jaheed ne akan layi, yasashi daidaita kansa tare da gaishe da Abbou’n.
Daga haka kuwa bai sake cewa komae ba, sai shiru da yayi yana me sauraren abunda Abbou Jaheed d’in ke fad’a masa.
Wanda ni kaina bansan abunda Abbou’n ya fad’a masa ba.
Ak’arshe dai “To.� Kawai Fou’ad d’in yace, tare da zame wayar daga kan kunnensa, fuskarsa d’auke da murmushi yasa ke kai dubansa ga Maleek.
Dake ta faman juyi akan gado.
Wani irin murmushi mai d’auke da ma’anoni daban daban yayi, batare kuma daya cewa M.Jay d’in komai ba ya mik’e tsaye, direct wajen drawer’n dake Cikin d’akin ya nufa, bud’e murfin drawer’n yayi, anutse ya soma tattare duk wani abu na Maleek daya sani, kama daga kan k’ananun kayan amfani harma dasu laptop.
Maleek kuwa dake kwance jin motsin Fou’ad d’in yayi yawa ne yasashi bud’e idanunsa ahankali ya tsaida ganinsa akan Fou’ad d’in.
Fou’ad dake zuge zip d’in jakan dake hannunsa, shima kallon Maleek d’in yayi, gane nufin kallon tambayan da Maleek d’in keyi masa ne kuma yasashi, gyara tsayuwarsa, cikin yanayin dake nuna alaman maganan da zaiyi d’in serious ne yace.
“Gobe da safe zamu bar USA hakan kuma umarnine daga Abbou Jaheed bawai daga ni ba, lallai yace mubar kome mukeyi mu koma Nigeria agobe gobe.�
Maida idanunsa yayi ya lumshe, batare kuma daya ce k’ala ba, hakanan kuma yaji bazai iya musawa tafiyar tasu ta gobe ba, duk da kuwa basu gama kammala aikin daya kawo su USA d’in ba.
Fou’ad kansa yayi mamakin ganin Maleek bai musa akan tafiyar tasu ba, saboda sanin halinsa da yayi na yawan musu da kafiya, idan kuma bai shiryawa abuba to babu wanda ya isa sakashi.
Da haka dai ya cigaba da kimtsa duk wasu abubuwansu, shi kuwa Maleek tamkar mai bacci haka yayi, saidai kuma bawai baccin yake ba.
*Washe gari.*
Tun tashinta daga baccin yau d’in takejin gaba d’aya jikinta amace, ga kuma ciwon kan da tun jiya yake damunta, duk da tasha magani kuwa har yanzu yak’i sauk’a.
Wani abun daya bata mamaki kuwa shine, lura da tayi da yanda y’an gidan keta hidima, sam kuma bata kawo aranta cewar wai hidiman aurenta da Maleek ne aka somashi tun yanzu ba, domin bata da labari ma akan antsaida ranar auren.
Ko yanzuma fitowarta daga wanka kenan, inda take zaune akan gado, daga ita sai wani mini towel a jikinta.
Turo k’ofar d’akin Oum Ayush tayi ta shigo, hannunta d’auke da wani tray, wanda samansa ke d’auke da wasu k’ananan 3cups.
Ganin Laylerh’n da tayi zaune abakin gado ne kuma yasa ta, fad’ad’a murmushin dake kan fuskarta, tare kuma da k’arasowa ta zauna a gefen Laylerh’n.
“Ina kwana.�
Laylerh’n ta fad’a asanyaye, kasancewar tun tashinta bata had’u da Oum Ayush d’in ba.
“Lafiya kalau ya ciwon kan naki, fatan yayi sauki?�
Fuskarta tad’an shagwab’e, kana cike da sakalci tace.
“Da d’an sauk’i.�
Murmushi Oum d’in tayi hade da fad’in.
“Allah Ya k’ara sauk’i, karb’i wannan kishanye.�
D’aya daga cikin cups d’in ta mik’o mata, wanda cikinsa ke d’auke da tatacciyar madarar shanu.
Idanunta ta d’an zaro waje, Kamar zata ce wani abu kuma sai ta fasa, karb’an cup d’in tayi takai bakinta, kamar yanda Oum Ayush d’in ta buk’ata kuwa saida ta shanye tas, kafun ta ajiye kofin.
Again wani cup d’in ta sake mik’o mata, shid’in ma dai wani abu me kamar pure honey ne acikinsa, kasancewar kuma yana da zak’i sosai ne yasa take ta shanyesa.
D’ayan cup d’in daya rage kuwa ajiyesa agefen bedside Oum Ayush d’in tayi, tare da ce mata tana shan maganin dake cikin kofin duk bayan 20minutes, saboda yana da k’arfi sosai nema yasa ba’aso ashanyesa nan take.
Ita dai To kawai tace, duk da akwai magana abakinta kuwa, kasa furtawa tayi, domin sam ba d’abi’arta bane, yawan tambaye tambaye.
Fita kuma da Oum Ayush tayi acikin d’akinne, ya bata daman tashi ta sakawa jikinta riga da sket na wani turkish material mai kyau, wanda suka matuk’ar karb’an jikinta.
Wayarta ta d’auka, har takai bakin k’ofar fita daga d’akin kuma sai ta dawo, cup d’in magani mai kaman yoghurt d’in da Oum Ayush ta ajiye mata ta d’auka, atsorace ta d’an lasa, wani irin zaki da kuma gard’in madarar da taji ya maye bakinta ne, yasa ta kafa kai har saida tasha Kusan rabin cup d’in kafun ta ajiye ta fita tana lashe baki.
Tana fitowa falon kuwa direct dining area ta nufa, saboda sosai takejin yunwa, harta zubawa kanta abinci sai kuma ga Oum Ayush hannunta d’auke da bowl na yankakkun kayan fruits.
Abincin dake gaban Laylerh’n ta d’auke, cikin yanayin lallami da kulawa tace.
“Daga yau kayan fruits zaki na sha, madadin wani chips and ketchup da omlet.�
Takai k’arshen maganan nata tana me ajiye mata bowl d’in fruits d’in agabanta.
Domin itakam Allah Yasani ayanzu so take ta gyara Laylerh’n sosai fiye da wanda tayi mata abaya, duk dama tasan still she’s virgin.
Laylerh dake jin yunwa kuwa babu musu, ta jawo bowl d’in fruits d’in ta soma sha.
Saida tasha fruits d’in sosai kafun taji ta k’oshi.
Dawowa cikin falon tayi ta zauna, tare da zubawa TV idanu, Tana kallon series film na Money Heist. (Lacasa De Papel)
Yayinda Oum Ayush kuwa ke zaune agefe tana waya, da dukkan alama kuma furnitures takeyin order, domin asaboda bikin, za su sanja gaba d’aya furnitures d’in gidan.
*10:00 am daidai jirginsu ya sauk’a acikin garin Abuja Nigeria, tun kafun ya gama sauk’owa daga kan matattakalan jirgin kuwa ya hangi Abbou Khareem yazo d’aukarsu, mamaki ne yad’an kamasa asakamakon ganin Abbou Khareem d’in da yayi, saidai kuma bai nuna ba, haka suka shiga motar Abbou Khareem d’in.
Aikuwa mamakinnasa bai kankama ba, saida yaga sun d’auki hanyar d’aya daga cikin gidajensa dake Wuse zone 6.
Sosai k’warai yayi mamaki, amma kuma saidai cewa da Abbou Khareem d’in yayi ana gyaran wancan gidan nasu ne, yasa shi katse mamakin nasa.
Abbou Khareem na gama daidaita parking, ya bud’e murfin motar ya fito, tare kuma da wuce wa cikin gidan kaitsaye.
Saboda dama time to time yakan zuwa gidan yad’an huta.
Abbou Khareem kuwa da Fou’ad Koda suka shigo cikin falon, basu iskeshi ba, domin tuni ya shige bedroom d’insa dake cikin gidan danyin wanka.
Saboda kafun su iso din Abbou Khareem yasa masu aiki sun tsabtace ko ina na gidan.
Food flasks na abinci kala kala Abbou Khareem ya ajiye musu, wanda musamman yasa Oum Ayush ta yisu, duka kuma favorite d’in Maleek d’inne.
Saida ya sake jaddadawa Fou’ad maganan kulawa da Maleek d’in kafun ya juya ya tafi.
Maleek kuwa koda ya fito awanka wani 3quater jeans and blue shirt ya saka, batare kuma daya tsaya yin wani abuba ya fito zuwa falo.
Inda ya samu Fou’ad ya shiga wanka.
Zama yayi akan had’add’un cushions d’in dake cikin falon, tare da jawo food flasks d’in ya bubbud’e, duk da cewar baya wani jin yunwa sosai, haka ya d’ebi abincin yaci, domin bama sai an fad’a masa ba yasan cewa Oum Ayush ne tayi girkin.
Koda Fou’ad ya fito awanka shima zama yayi yaci abincin sosai.
Bayan ya kammala cin abincinne kuma ya soma kokarin Jan Maleek d’in da hira.
Saidai shikad’ai yake ta magana, Maleek baya cewa ko k’ala, hasalima lumshe idanunsa yayi tamkar maiyin bacci, shikuwa Fou’ad dama ya saba hakan.
Acan gida b’angaren Laylerh kuwa gaba d’aya wunin yau haka tayisa, afalon Oum Ayush tana kallo, saidai idan lokacin sallah yayi takan tashi taje tayi sallah.
Akuma yau d’inne takejin labarin tafiyan Maleek da kuma dawowansa, taji hakanne kuma awajen Abbou Khareem da yake sanarwa awaya cewar Captain M.Jay d’in ya dawo.
Yayinda agame da harkar shirye shiryen biki kuwa abun keta kankama, arana d’aya kawai har sunci k’arfin shirye shiryen nasu.