Sashe 67
Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Abbou Jaheed kuwa dake goge bakinsa da tissue jin gaisuwar Laylerh'n ne yasa batare daya motsa bakinsa ba, ya jinjina mata kai alaman ya amsata.
Ganin hakanne kuma yasa jikin Laylerh K'arayin sanyi duk da kuwa batasan meye ma'anar hakan ke nufi ba.
D'ago Kanta tayi ta dubi Abbou Kareem tare da gaishesa, fuskarsa amatuk'ar sake kuwa ya amsa mata, tare da nuna mata kujeran dake facing ta Najeeb, alama yayi mata akan ta zauna, babu musu kuwa taja kujeran ta zauna tana me gaishe da Oum Ayush.
Murmushi Oum Ayush tayi cikin sakin fuska tace.  "Ina fata kindai tashi lafiya?."
"Lafiya lau." Tafad'a tana me gyara zamanta akan kujeran.
Plate d'in soyayyen chips da kuma plaintain Oum Ayush ta turo mata gabanta.
Abbou Jaheed kuwa kasancewar ya gama cin abincin nasa tuntuni mik'ewa tsaye yayi batare da yace da kowansu k'alaba yabar dining table d'in.
Murmushi me d'auke da ma'anoni daban daban Momy tayi domin koba komae manufarta ya isa inda takeson ya isa.
Jan kujeran da take kai baya tayi tare da mik'ewa tsaye ta rufawa Abbou Jaheed baya.
Ganin hakane kuma yasa Abbou Kareem ma mik'ewa tsaye dan dama dukansu sun kammala cin abincin nasu.
Kusan kuma atare suka mik'e tsaye shida Oum Ayush, dan itama tanaso tabawa Laylerh da Najeeb d'in waje, duk dama bataji dad'in zuwan da Laylerh'n tayi wajen Maleek ba, domin Sam bataso zargi ya fara shigowa tsakaninta da Najeeb.
Hakan yasa batare da sunce da kowannensu wani abuba suka nufi hanyar barin falon.
Ganin haka kuwa yasa Laylerh'n ta bisu da kallo har saida suka b'acewa ganinta, sassanyar ajiyar zuciya ta sauk'e tare da maida kallonta ga plate d'in abincin dake gabanta, fork d'in dake cikin abincin ta d'auka tare da tsakalo chips d'in takai bakinta.
Jin test d'in abincin daban da wanda ta saba cine yasa ta gane cewar girkin Oum Ayush ne bana laure me aiki ba. Batare da ta gama tauna abincin dake bakinta ba, ahankali ta d'ago kai ta kalli Najeeb dake zaune suna facing d'in juna, wanda kuma har yanzu bai d'ago kansa ya sake kallonta ba, tunkuwa kallon farko daya mata, ahankali yake d'an jujjuya spoon d'in dake hannunsa, domin hakanan yaji abincin yafita aransa duk da kuwa bawai wani sosae yaci ba.
D'auke idanunta tayi daga garesa, dan kwata kwata bata fahimci yanayin nasa ba.
Azahirin gaskia abincin takeci, yayinda acikin zuciyarta kuwa tunanin M.Jay ne yayi tasiri, kana kuma shi ya maye duk wani gurbin nutsuwarta, tuna yanda kyakkyawar fuskartasa take idan yana baccine yasa ta sakin murmushi me sauti tare da d'an lumshe idanunta.
Sauti da kuma amon murmushinta da yaji ne yasa shi d'ago kansa, tare da zuba mata idanunsa wanda suka d'anyi ja, kana kuma suke bayyana zallan abun dake zuciyarsa.
Murmushin kuma daya gani kwance akan fuskarta ne yasa shi sake jin wani abu ya tokare masa k'irji.
"Mekenan me hakan yake nufi? tana farinciki ne saboda wani abu daban, wani abu dake b'oye acikin zuciyarta, meyasa bata farinciki alokacin da take tare dashi sai akasin haka?" Yayiwa kansa tambayar yana me yawo da idanunsa akanta, tabbas wani abu me kama da zargine ke neman mamaye zuciya da tunaninsa, wanda kuma yarda da hakan zai iya lalata rayuwar aurensu, because aure da zargi haramunne.
K'ok'arin daure zuciyarsa yayi ta hanyar mik'ewa tsaye daga zaunen da yake, domin yasan zamansa awajen bazai k'ara masa komai ba sai zafin zuciya.
Jin alaman tashinsa ne kuma yasa Laylerh d'ago kai ta kalleshi.
Ganin yana k'ok'arin barin dining area d'inne yasa ta tsura masa ido, domin tuni ya d'auke idanunsa daga gareta.
Kansa tsaye kuwa ya nufi hanyar fita daga falon, batare dako waiwayenta yayi ba.
Laylerh kuwa har ya fice daga falon bata d'auke idanunta daga kallon hanyar da yabi d'in ba, hakanan duk taji ta tsargu da irin mood d'in da tagani akan fuskar kowannensu.
Saidai kuma rashin son tsanantawa Kanta damuwa yasa ta share duk wani tunani dake ranta, tare da maida hankalinta ga abincin dake gabanta.
Fitarta daga cikin d'akinne yasa shi bud'e idanunsa, wanda suka d'an k'ank'ance ahankali ya sauk'e wata sassanyar ajiyar zuciya, tare da fesar da wani sassanyan numfashi ta bakinsa, duk da kuwa cewar baya cikin mood maidad'i amma hakan bai hanasa bayyana wani k'awataccen murmushi akan fuskarsa ba, tare da shak'an daddad'an k'amshinta da ya cika d'akin.
Maganganun sakalcinta da tayi ta fad'a masane suka shiga dawowa cikin kunnuwansa, wanda hakan yasa shi d'an lumshe sexy eyes d'insa.
Cikin wata irin kasalalliyar muryar dake bayyana abunda ke cikin zuciyarsa yace.
"Yeah before zuwanki am not okay Laylerh, amma yanzu da kikazo am okay!"
Ya k'are maganar yana me yun k'urin tashi zaune, duk da kuwa yana jin jikinsa very weak, hannunsa yakai ya shafi gefen wuyansa inda Laylerh'n ta tab'a.
Still murmushin da baizamo al'adarsa ba ya sakeyi, domin yasan da ace Laylerh'n tasan cewa baccinsa baiyi nisa ba da bazata tab'a sakin jiki dashi har haka ba, ganin tasaki jiki dinne kuma yasashi yin shiru tare dayin kamar bacci me nauyi ne ya d'aukesa, alhalin kuma duk abun da takeyi yana jinta.
Ahankali ya d'an yunk'ura ya mik'e tsaye, hannayensa duka biyu yasa ya kama waist d'insa,
Kallon pillown da Laylerh'n ta ajiye masa yayi, maganarta da take cewa. ya daina kwanciya ak'asa ne ya dawo masa, take kuwa sauti da amon zazzak'ar muryarta suka shiga dawo masa, tamkar alokacinne abubuwan ke faruwa, d'an murmusawa kawai yayi, ahankali ya soma rage kayan jikinsa, saida ya rage dagashi sai dogon wandon dake jikinsa kafun ya wuce bathroom dan watsa ruwa.
B'angaren Laylerh kuwa anutse ta kammala cin abincin nata, tare da d'aukan tissue ta goge bakinta.
Mik’ewa tsaye tayi tare da k’arasowa cikin falon nasu ta zauna, hankali da Kuma idanunta ta tsaida akan k’aton tv plasman dake cikin falon, tashar MBC Bollywood take kallo inda suke haska film d’in Force 2 na john abraham, kallon yanda murd’add’iyar surar JohnAbraham d’in yake ne yasa take Maleek ya fad’o mata saboda shima irin jikin John dinne dashi, saidai kuma fuskar Maleek d’inta yafi na John Abraham d’in kyau, samun kanta acikin sabon Shauk’i da tayi ne yasata lumshe idanunta tare da jingina bayanta da jikin kujeran da take kai, lokaci d’aya kuwa ta fad’a duniyar tunani.
Najeeb kuwa koda ya fita daga falon direct part d’insu ya koma, hakanan yakejin zuciyarsa duk ba dad’i shiyasa duk yaji zaman gidan ya ishesa, key d’in motarsa k’iran Benz ya d’auka kaitsaye ya fito daga part d’in nasu, babban parking space d’in dake gidan ya fito tare da bud’e motarsa ya shiga, ganinsa da maigadi yayi ne kuma yasashi wangale masa gate d’in gidan ya cilla hancin motar tasa waje, duk da kuwa cewar baiyi niyar fita yau d’inba amma dole haka zaije ya zaga gari ko hakan zaisa ya d’anji sanyi acikin zuciyarsa.