← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 144

Sashe 7

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin takunsa na isa ya gama ƙaraso cikin falon,  zama yayi akan ɗaya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun da suka ƙarawa falon kyau, sannan suka ƙara ƙawata shi,  facing cap ɗin dake kansa ya cire, hakanne ya bawa asalin kyakkyawar fuskarsa bayyana.  
Wanda yake Kyakkyawane bana wasa ba, yayinda yake da wasu irin fitinannun eyes masu kyau, da ɗaukar hankali, duk da kasancewar idanun nasa basu da girma sosai, amma suna da yalwar lashes asamansu,  sannan ga kuma gashin eye brow ɗinsa dake ashirye tsab sai sheƙi suke,  yana da dogon hanci, da kuma small lips masu ɗauke da kalan pink, akan fuskarsa kuwa babu alaman wasa, ko murmushi, sam fuskar tasa bata ɗauke da yanayin dariya, bata kuma ɗauke da tsumewa, hakanan nature ɗinsa yake, yana da wani irin kwarjini naban mamaki, yayinda lafiyayyen sajen dake kwance akan kumatunsa ke ƙarawa fuskar sa kyau,  yana da wani irin lafiyayyen tulin gashi akansa,  wanda yasha gyara sai shining yake.      
Ajiye facing cap ɗin nasa yayi tare da miƙewa tsaye, direct jikin wata ƙofa dake cikin falon ya nufa, ahankali ya murɗa handle ɗin ƙofar, sannan ya kutsa kansa ciki.                      

Ɓangaren Laylerh kuwa, gaba ɗaya ganinsa ya so birkita mata lissafi, ɗaukan flask da kuma cup ɗin tayi ta mayar kitchine, anan gaban sink ta tsaya tare da kunna fanfo, ruwan dake gudunatasa hannu ta tara, tare da watsawa akan fuskarta, hakanan taji zuciyarta na tsananta bugawa,  idanunta da suka sanja launi ta lumshe, tare da sakin wata ƙakƙarfan ajiyar zuciya,   tabbas ganinsa da tayi ayanzu  yana neman tuna mata abubuwan da suka wuce tun tana ƴar ƙaramar yarinya,  ganinsa yasa memories ɗinta na baya na ƙoƙarin dawo mata,  duk da cewar ta kwashe shekaru masu yawa batare da ta sake sanyashi a idanunta ba, amma koda sau ɗaya ne zuciyarta bata taɓa bugawa batare da wani nau'i na tunaninsa ba, haka zalika sauyawan kamanni da jikinsa baisa ta kasa ganeshi ba, lallai shiɗin ne, koda ace idanunta zasu kasa tantance mata, to banda zuciyarta.   
Jin kaman motsin za a shigo cikin kitchine ɗin ne, yasa  ahankali ta buɗe idanunta, tare da ƙoƙarin daidaita nutsuwarta,  anan cikin kitchine ɗin ta haɗa tea ɗin tasha.

Samun kansa da yayi acikin makeken bedroom ɗin nasa ne, yasa shi soma ƙoƙarin cire rigar jikinsa,  hannunsa yakai ya shafi gefen cikinsa, wanda ke ɗaure da bandage,  ɗan rumtse idanunsa yayi, da alaman ciwon dake wajen nayi masa zafi,  ƙarasawa gaban madubin dake jikin bangon ɗakin yayi, take yayi ido biu da murɗaɗɗiyar surar jikinsa da kuma buɗɗaɗun muscles ɗinsa,  manya manyan 6 packs ne kwance acikinsa, wanda kallo ɗaya zaka masa ka tabbatar da cewa shiɗin ma'abocin motsa jiki ne, kusan ma ya maida hakan babbar ɗabi'arsa,  still sake kai hannunsa gefen  cikinsa  ta ɓangaren dama yayi, wanda akayi masa   zanen tattoo awajen, ɗan shafa zanen tattoo ɗin yayi, tare da lumshe idanunsa,   wanda yake har  hannayensa akwai zanen tattoo ajiki, saidai zanen tattoo ɗin nashi basu da yawa, wanda yake kuma kowanni zane da akwai abun da yake nufi, kamar zanen dake kwance akan cikinsa, azahirin gaskiya idan ka kalli zanen zaka ɗauka adone kawai akayi awajen, saidai ba hakan yake ba, dan idan mutum me fahimta ya ƙurawa zanen ido, zai iya fahimtar cewa suna ne aka rubuta, sai dai anjuya harufan sunan tayanda baza suyi sauƙin karantuwa har akai ga gane me aka rubuta ba, saidai idan mutum nada zurfin ƙwaƙwalwa, zaiyi saurin gane abun da aka rubuta da tattoo ɗin.
Cikin nutsuwa ya zare dogon wandon dake jikinsa, ƙarasawa gaban makeken drawer glass ɗin dake cikin ɗakin nasa yayi, wanda komai dake cikin drawer'n ana iya gani daga waje, wani sabon towel ya ciro daga cikin drawer'n, tare da ɗaura towel ɗin akan waist dinsa, agogon dake hannunsa ya soma koƙarin cirewa, bayan ya kammala ne ya ƙarasa jikin wata ƙofa, wanda da dukkan alama ƙofar toilet ne, murɗa handle din ƙofar yayi ya shige kaitsaye.
Tabbas kuwa nan ɗin toilet ne kaman yanda nayi hasashe, amma saidai ya banbanta da sauran toilet ɗin da kuka sani, domin komai dake cikin toilet ɗin na original royal glass ne, hatta bath ɗin wanka kewaye yake da royal glass me ɗaukan idanu,  ƙarasawa gaban shower yayi tare da sakarwa kansa ruwa.      
Haka ya É—auki sama da 30 minute yana wanke jikinsa, koda ya gama alwala yayi sannan ya É—aura bathrobe ajikinsa.
Koda ya fito daga toilet É—in gaba É—aya jikinsa É—auke yake da danshin ruwa, musamman ma gashin kansa wanda har É—igar da ruwa yake.

Agaban dressing mirror ya zauna tare da ɗaukan wani ɗan ƙaramin towel ya shiga tsane gashin kansa,  yana kammalawa kuwa yasa handrayer ya busar da gashin kannasa, wani haɗaɗɗen body lotion ya murza ajikinsa, tare da shafe jikinsa da wani fitinnanen turare. 
Ƙaran horn din motan dake tashi acikin compound ɗin gidan ne, ya shiga ratsa kunnuwansa, ɗan lumshe idanunsa yayi saboda sam shi bayason yawan hayaniya, agogon dake saƙale ajikin bangon ɗakin ya kalla, ganin cewa 12:30 pm daidai, ya sashi gane cewa Abbu ne ya dawo, dan dama yace masa yau zai dawo.  

Cikin nutsuwa ya ƙarasa gaban drawer ɗinsa, wasu tsadaddun riga da wando ya ciro, kamar yanda ya saba dayin komansa cikin nutsuwa, haka yanzun ma anutse ya saka kayan, wanda suka matuƙar fito da kwarjini da kuma faffaɗan jikinsa, sosai kayan sukayi masa kyau kasancewar fatarsa na da haske sosai, black jeans ne da wata jar riga wacce take da adon baƙi da fari agabanta, sai kuma wata blue ɗin denim jacket daya ɗaura asaman rigar, tare da saka wasu tsadaddun white sneakers shoe aƙafansa, sosai shigar tasa tayi kyau, kwarjininsa kuwa ya sake bayyana,  wata farar facing cap me ratsin baby pink colour ya ɗaura akansa. 
Masha Allah Yayi kyau sosai, dan babu wata macen da zata masa kallo ɗaya ta ɗauke kai, baga mace ba harma ga kowa, CAPTAIN MALEEK JAHEED GWANI kenan, matashin saurayin da aƙalla bazai ɗarawa 31 years ba, kyakkyawa ne shi na gasken gaske, sannan yana da abubuwan burgewa masu tarin yawa, duk da cewa bashi da tsawo sosai, amma tsarinsa da kuma murɗaɗɗiyar surar jikinsa, na matuƙar jan hankalin mata da dama, idan ka ganshi kai tsaye bazaka ƙirasa da sunan ɗan Nigeria ba, koda ga yanayin farin fatarsa, idan mutum ya kalla, zai gane cewar shiɗin ba asalin ɗan Nigeria bane, kana kuma shiɗin  yakasance wani irin   murɗaɗɗen mutum, wanda ba a iya gane gabansa da bayansa, miskiline  na ƙarshe, sannan bai fiye yawan  magana ba, saidai yana da zafin nama sosai akan komai musamman ma aɓangaren aikinsa, hakanne yasa sunansa ke yawo ako ina.            
Wayarsa ƙirar iPhone 11 pro max ya ɗauka, cikin takunsa na isa kuwa ya nufi hanyar fita daga cikin ɗakin, murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin yayi, tare dasa kai ya fice.        

Kaitsaye babban falon gidan ya nufa.  Fitowarsa daga sashinsa yayi daidai da shigowar ALHAJI JAHEED GWANI  (Abbu )cikin falon,  ganin M.J ɗin ya saka Abbu sakin murmushi, cikin kulawa yace.   
"Wellcome back Captain M.J"     

Akaron farko kenan MALEEK ya ɗanyi murmushi, wanda iya kanta kan laɓɓan bakinsa, saidai kuma abun da baisani ba, murmushin ya matuƙar ƙarawa fuskarsa kyau, haka zalika akaron farko daga dawo wansa zuwa yanzu da sautin muryarsa ta bayyana, yace.
"Thank you Abbu."   

Hannu Abbu ya miƙa masa tare da cewa.  
"Naji daɗin dawowanka Maleek, saboda kwata kwata hankalina baya kwanciya da zamanka a US ɗin nan, then 7 years fa kenan bakazo Nigeria ba."      
Musabaha sukayi shida Abbu'n nasa, sannan ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun falon.      

Momy da ganin Abbu yasa fuskarta ta faɗaɗa da fari'a tace.   
"Your wellcome Alhajina."   

Murmushi Abbu yayi tare da ɗan jinjina mata kai, cikin sakin fuska yace.  "Thank you."     

Zama yayi akan kujeran dake facing ɗin ta Maleek,  take kuwa Momy tasa aka cika musu gabansu da kayan ciye ciye dasu drinks,   ƙawayen Momy dake zaune ne sukayi wa Abbu sannu da dawowa, wanda dama dan yi masa sannu da dawowan Momy ta tarasu, kasancewar yaune birthday ɗin Abbu'n shiyasa ta gayyacesu dan suzo sutaya ta murna.              

Ko tsinke bai ɗauka daga cikin abun da aka ajiye masa ba, jin surutun ƙawayen Momy na neman Affecting ɗinsa ne, ya sashi miƙewa tsaye ya nufi hanyar fita daga cikin falon. 
Da idanu Abbu da Momy suka rakashi, har ya fice daga cikin falon.   

Miƙewa Abbu yayi shima ya nufi sama dan yanaso yaɗan huta, take kuwa Momy ta rufa masa baya.             

Yana fita daga cikin falon,  kaitsaye compound ɗin gidan ya nufa, inda motarsa ke fake ya ƙarasa, soldiers ɗinsa da ke ta kai kawo acikin gidan nasu, suna ganinsa kowa ya shiga sense ɗinsa, duk suka ƙame awaje ɗaya, buɗe murfin motar yayi ya shiga,  shigansa cikin motar kuwa yayi daidai da tashin cute cat ɗinsa, wanda yake ƙira da sunan  cutie,  itaɗin tazama kamar wata baby ɗinsa ce, dan mafi yawancin lokuta yana tare da ita, yanason cat din tasa sosai, haka itama tayi matuƙar sabo dashi, hayewa saman jikinsa cat ɗin tayi, saman bayanta ya ɗan shafa,  tare da ɗaukan kwalin madararta dake cikin motar ya shiga bata abaki tana sha, time to time yake shafa screen ɗin wayar dake hannunsa, da'alama wani abu me mahimmanci yakeyi.

Koda ya gama bawa cutie ɗin nasa madara, soldiers ɗinsa yayiwa alama akan su taho akwai inda zasuje, take kuwa duk suka shiga mota, drivers ɗinsa yaja suka fice daga cikin gidan.                    
Chapter 7 · 0% Book details