Sashe 77
Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*(Chab gaskia akwae biki ashe yarinyar ma ta masa amma bamuda labari😹 team Maleek kunshirya kuwa? Gaskia yau comment nake bukata dan inason sanin ko kun shiryawa hakan)*
1/31/21, 9:06 PM - Ummi Tandama: *L.M*
*Writting By*
fatymasardauna
*Note Edit*
*Chapter 44*
A wani irin yanayi taji sauk’an kalaman Oum Ayush d’in acikin kunnuwanta, wanda kuma hakanne yasa tayi saurin d’ago kai ta kalli Oum d’in, domin hakanan taji kaman kunnuwanta basu jiye mata gaskiyar abunda Oum Ayush d’in ta fad’a ba.
Lokaci d’aya kuma tasamu kanta cikin tsinkewar zuciya, da kuma tarin fargaba, had’i da k’unan k’irji, yanayin yanda take kallon Oum Ayush d’inne yasa itama Oum d’in tsayawa tana kallon ta.
Cikin muryarta wanda yayi sanyi sosae tace.
“Aure kuma Oum auren waye?�
Jin tambayan da Laylerh’n tayi matane yasa ta sakin murmushi, batare kuma da ta lura da halin da Laylerh’n ta shiga asakamakon jin maganan nata ba tace.
“Auren Maleek mana kodai bakiji abunda na fad’a da kyau bane, ko bayan shi kina da wani yayane?.�
D’an tsagaitawa da maganan tayi ta hanyar d’aukan fruit juice d’in dake gabanta ta d’anyi sipping kad’an, fuskarta d’auke da murmushi tace.
“Tabbas naji dad’in wannan al’amarin domin kuwa batun yau ba nafahimci cewa, rashin mace akusa da Maleek shiyasa duk ya zama wani k’aton miskili, baidamu da kowa ba, bayason kowa yasan damuwarsa, koda kuwa zai shekara acikin k’unci bazai tab’a furtawa ba, shi kad’ai yake shanye duk wata damuwarsa komin d’acinta, da yardar Allah Yanzu komae zaizo da sauk’i, saboda ko ba komai matarsa zata zama k’awa kuma abokiyar d’ebe masa kewa.�
Idanunta wanda suka ciko da k’walla ta rumtse, ahankali kuma ta had’e labb’an bakinta waje d’aya ta taune su, hak’ik’a sosae maganganun Oum Ayush d’in suka daki zuciyarta, yayinda kuma sukayi fatali da duk wata nutsuwarta.
“Zaiyi aure? hakan na nufin cewa lallai tilas zai rayu da wata kenan amatsayin matarsa? shin dagaske ne kuma abunda Oum Ayush ta fad’a na cewar ya amince da wata tazamo mata, kuma abokiyar rayuwarsa?.�
Abunda zuciyarta ta tambayeta kenan wanda ahak’ik’anin gaskiya bata da amsar sa.
Lallai shigowarta cikin barayin Oum Ayush d’in ya jawo mata tashin hankali, domin kuwa maganganun da taji daga bakin Oum Ayush ba k’aramin gigita mata tunani sukayi ba, wanda har hakan yasa hawayen dake cikin idanunta kasa control d’in kansu, saida suka gangaro kan k’uncinta, lokaci d’aya kuma taji wani irin masifaffen sanyi na shiga jikinta, yayinda kuma har yanzu bugun zuciyarta ya kasa dawowa normal.
D’ago kai Oum Ayush dake faman danna wayarta tayi, asakamakon jin Laylerh’n tayi shiru ne yasa ta d’an gyara zamanta, cikin kulawa ta k’ira sunanta, tare dason ganin fuskar Laylerh’n kasancewar ta d’an bata baya kad’an.
Laylerh kuwa jin da tayi Oum Ayush d’in ta k’ira sunanta ne, yasa cikin sauri ta kai hannu ta share hawayen dake kwance akan fuskarta, ahankali ta juyo da kanta ta fuskanci Oum Ayush d’in, saidai kuma duk da cewar ta goge hawayen nata hakan baihana Oum Ayush fahimtar cewa Laylerh’n kuka tayi ba.
D’anjim tayi tare da kafe Laylerh’n da ido,domin kuwa so take ta fahimci wani abu daga gareta.
Ganin hakanne kuma yasa Laylerh yin k’asa da kanta, asanyaye ta soma wasa da y’an yatsun hannunta.
Murmushin da yake iya kan labb’an baki Oum Ayush tayi, domin dama tasan dole hakan zai iya faruwa, wannan dalilinne ma yasa tafad’awa Laylerh’n cewa Maleek ya yaba da zab’in da Abbou Jaheed yayi masa, domin ta hakanne kad’ai take ganin cewa Laylerh’n zata saduda ta cire Maleek daga cikin ranta, saboda ci gaba da rayuwa da sonsa acikin zuciyarta babban haramci ne saboda tana da aure.
“Tunanin me kike?.� Oum Ayush ta fad’a ta hanyar katseta daga tunanin da take.
“Babu.� Ta fad’a asanyaye tana me wasa da y’an yatsun hannunta.
“To yayi kyau, amma meyasa kika baro Najeeb shikad’ai kika taho nan?�
Oum Ayush ta fad’i hakan tana me sake zubawa Laylerh’n idanu.
Shagwab’abbiy’ar fuskarta ta kwab’e cikin muryarta dake d’an rawa tace.
“Bayanan bansan inda yake ba, kuma ba Yah M.Jay ne yace nazo kina k’irana ba.�
Idanu Oum Ayush ta zaro waje, cikin yanayin mamaki tace. “Ni nace ina k’iranki?.�
“Eh mana haka Yah M.jay ya fad’a.� Ta fad’i hakan tana me d’an mammatse cinyoyinta, saboda yanda taji ciwon marar nata na neman dawowa.
Shiru Oum Ayush tayi ta kasa cewa komae, saboda Jin abunda Laylerh’n ta fad’a ya d’an sata mamaki kad’an, saidai kuma rashin sanin dalilin da yasa Maleek d’in yayi hakan yasa, ta sauk’e ajiyar zuciya.
Gyara zamanta tayi had’e da fuskantar laylerh’n cikin yanayin sanyi ta k’ira sunanta tare da kamo hannayenta, anutse ta yanda ta tabbatar da cewa Laylerh’n zata fahimceta tace.
“Kada ki bari koda wasa damuwa ko k’unci suyi tasiri acikin rayuwarki Laylerh, tabbas nasan halin da kuke ciki dukanku keda Maleek, amma hakan bawai yana nufin akoda yaushe kuyita biyewa son zuciyarku bane, hak’ik’a nasan zuciyarki na sak’a miki abubuwa da yawa akan d’an uwanki Maleek, amma komai zai faru dake Laylerh ki daure, kada wani abu na daban ya hanaki kulawa ko bawa mijinki hakk’insa, domin yin hakan zaisa Allah Yayi fushi dake, sannan kuma nasan zakiji ba dad’i saboda Maleek zaiyi aure, amma inaso kusani aduniya babu wani d’an Adam da yake da ikon yin abu dan kansa, komai Allah Ne ke tsarawa bawansa, sannan babu wani me iya canja k’addara, abunda Allah ya tsara kuma ya hukunta shine kawai ke faruwa, sannan ako yaushe ki rik’e cewar saudayawa bako wani abu da kakeso kake samu ba.�
D’an numfasawa da maganan nata tayi, kana kuma cikin sakeyin k’asa da murya tace.
“Babu buk’atar na tsaya tambayanki akan hakk’in Najeeb dake kanki, shid’in Mijinki ne, idan har baki basa hakk’insa dake kanki ba watace daban zata basa? Tabbas Najeeb Namiji ne me nutsuwa, dan Allah Laylerh kada kiyi gangancin rasa Namiji me nagarta kaman Najeeb, domin samun kamarsa acikin sauran maza ba abu bane me sauk’i, saboda haka ki tashi ki koma d’akin ki, ki kuma aikata duk abunda Najeeb ya umarceki dashi, matuk’ar bai sab’awa Allah ba, ya kamata kuma kisan cewa yanzu ba lokaci ne da zaki tsaya kuka ko damuwa ba, kamata yayi kimanta komai, domin damuwarki bazae tab’a sanja komae ba.�
Takai k’arshen maganan nata tana me d’an bubbuga kafad’un Laylerh’n, wanda tuni sabin hawaye sun sake cika idanunta.
K’asa tayi da kanta ahankali tare dasa hak’waranta ta datse labb’anta, hak’ik’a ayanzun ita kad’ai tasan abunda takeji acikin zuciyarta, so take tayi kuka sosae dan rage rad’ad’i da kuma zafin abunda takeji acikin zuciyarta.
Saidai kuma awannan karon sam bataso Oum Ayush tasake ganin hawayenta, dan faruwar hakan alamace dake nuna gazawarta, sam ita kuma bata fata hakan yakasance.
Ahankali kuma cikin yanayin sanyi ta zare hannayenta daga cikin na Oum Ayush d’in.
Sanin da tayi kuma cewa idan tace zatayi magana wani sabon kukane zai zo mata babu controll yasa ta jan bakinta tayi shiru, asanyaye ta mik’e daga zaunen da take, batare kuma da ta kalli Oum Ayush ko ta sake cewa wani abuba kaitsaye ta nufi hanyar fita daga cikin falon.
Da kallo me d’auke da tsananin tausayi Oum Ayush ta bita, harta fice daga cikin falon kuwa bata d’auke kanta ba.
Ajiyar zuciya ta sauk’e tare dasa hannayenta ta tallafi hab’arta, sam takasa gano wace irin soyayya ce haka, me k’arfin gaske da ke tsakanin Laylerh da Maleek d’in, saboda zuwa yanzu al’amarin nasu sosai yake bata mamaki, ita dai addu’a da kuma fatanta d’aya shine kada Allah Yasa watarana Najeeb yafahimci hakan, harta kaisa ga rabuwa da Laylerh’n ko kuma ya fara yi musu mummunan zargi.
Laylerh kuwa tun fitowarta daga sashin Oum Ayush d’in tafiya kawai take tana jefa k’afafunta batare da tasan inda take takawa ba, hak’ik’a abu d’aya ne keyi mata yawo acikin ranta shine auren Maleek, hakanan taji duk wata nutsuwarta ta k’aurace mata tunda taji batun auren nasa, yayinda a gefe guda kuwa kalaman Oum Ayush ne ke yawo acikin k’wak’walwarta.
Da tunani kala kala acikin ranta haka ta iso part d’in su.
Ahankali ta tura k’ofar falon tashiga, kamar kuwa dama hawayen dake cikin idanunta jira suke ta shigo cikin falon, take suka soma gangarowa kaman ana turosu.
Maida k’ofar tayi ta rufe, ahankali kuma ta zame ta zauna abakin k’ofar dab’as.
Tayaya ma zata iya jure duk way’annan matsalolin? Tayaya zata iya cire soyayyar Maleek acikin jikinta? Soyayyar da ta zame mata kamar numfashi, soyayyar da ta zama itace gaba d’aya rayuwarta, lallai tayi imani cewa koda kashe ta za’ayi har abada bazata tab’a iya daina so da tunanin Maleek ba, domin saida tunaninsa kad’ai take samun nutsuwa, tunaninsa ne abincin ruhinta, yayinda kuma akullum idan ta ganshi take k’ara jin matsanancin soyayyarsa na k’ara shiga zuciyarta.
Asanyaye sautin sheshshek’an kukanta ya fara fitowa, saboda takai wani matakin da bazata iya jurewa ba.