← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 144

Sashe 54

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Laylerh kuwa ahankali wasu zafafan hawaye suka kwaranyo daga cikin idanunta, yayinda tuni tsayuwa ya soma ƙoƙarin gagararta, duba da irin yanda ta samu kanta acikin wani fitinannen baƙon yanayi, wanda kuma tunda take adunia bata taɓa shiga makamancinsa ba, tabbas ayanzu Maleek ya kawota wata gaɓa, wanda yasa bazata ko iya tsayawa da kafafunta ba, kasancewar kuma takai maƙura ne yasa, ahankali gaba ɗaya jikinta ya sake, take kuwa ta narke ajikinsa, tare da soma yunƙurin zube guiwowinta aƙasa.
Saidai kuma kasancewar Maleek ɗin na riƙe da ita, hakan yasa bai bari ta kai ƙasa ba, ya sake mannata da jikinsa.
Ahankali cikin yanayin sanyi ya zare bakinsa daga cikin nata, tare da haÉ—e goshinsu waje É—aya.
Idanunsa wanda sukayi jajur, suke kuma ɗauke da danshin hawaye ya buɗe, tare da sauƙe ganinsa akan kyawawan idanunta, wanda har zuwa yanzu basu daina zubar da ƙwalla ba.
Ahankali ya soma fitar da wani irin numfashi.
Cikin yanayin sanyi da kuma son daidaita nutsuwarsa, yakai hannunsa kan fuskarta, ahankali ya soma ƙoƙarin share mata hawayen dake kwance kan fuskar nata.
Jin hannunsa akan fuskarta ne, yasa ta ɗaura nata hannun akan nasa, tare da kama hannun nasa ta riƙe.
Cikin yanayin sanyin dake bayyana matuƙar rauninta, ahankali ta soma ɗan grgiza kanta, yayinda laɓɓan bakinta suka soma ɗan motsawa, da alama wani abu takeson faɗa, amma kuma ta kasa.
Ganin hakan da yayi ne kuma ya sashi ƙura mata tsumammun idanunsa, dake matuƙar rikitata.
Ƙwarai yasan akwae wani abu acikin zuciarta, wanda kuma hakanne kuma ya sashi, jafa idanunsa acikin nata baya ko ƙyaftawa, kasancewar so yake ya karanci abun dake cikin zuciarta ta hanyar kallon ƙwayar idanunta, saidai kuma yanayin yanda zuciarsa ke bugawa da matsanancin sonta, ya riga daya sashi rasa duk wata nutsuwarsa, yayinda daga wani sashe na ɓangaren tunaninsa kuwa, gani yake kamar duk abun dake faruwa bai zamanto gaskia ba, haka yake ganin komai kamar amafarki, saboda kasantuwarsa da Laylerh'n ya sashi jin wani abu na daban, kana kuma na musamman, haƙiƙa ayau zuciarsa ta riga da ta gama karyewa, domin yasan cewar ya rasa fata da duk wani muradin sa, tayaya zai iya rayuwa batare da ita ba? tayaya zuciyarsa zata iya jurewa? sama da shekaru sha ya ɗauka yana dakon wani abu azuciarsa wanda baisan ko menene ba, duk kuwa da cewar akowacce rana zafi da kuma ɗaɗaɗin abun na sukan zuciarsa amma haka yake daurewa, akullum burinsa kuma shine yasan gaskiyar abun dake zuciarsa, baisan kowa ba, bai saba da kowa ba, shi kaɗai yake rayuwarsa, idan zafi yaji shi kaɗai yake shanyewa, haka kuma idan yaji damuwa zuciarsa yake barmawa, saboda bashi da wanda zai faɗawa, sama da shekaru bakwae kenan yanzu da sanin haƙiƙanin matsalar dake damun zuciarsa, amma haka ya daure, ya kuma bawa kansa ƙarfin guiwa, akullum ji yake ajikinsa cewa bazai taɓa zama me gazawa ba, wannan yasa komae tsananin abu yakan iya jurewa, haƙiƙa amatsayinsa na Namiji kuma soldier ya shanye abubuwa da yawa, amma ayau rana ɗaya kawai komai ya ruguje, yazama Loser.
Tabbas bazai taɓa mantawa da wannan ranar ba, domin acikinta ya fara sanin meye gazawa, haka kuma acikinta ne yafara sanin haƙiƙanin ƙunci, da kuma ɗacin rayuwa, kana kuma acikinta ne kalmar Gazawa ta mamaye gaba ɗaya rayuwarsa, ya zama me RAUNI, me tsananin RAUNI.
Lallai ako da yaushe mutum yana rayuwa cikin lafiya ne idan jini yana gudana yanda ya kamata acikin jikinsa, idan akasin hakan ta faru kuma saɓanin farinciki ne yake biyowa baya, kasancewar Laylerh itace ginshiƙin numfashi, kuma jininsa me zai faru dashi kenan alokacin da tabar jikinsa? amsa guda ɗaya ce itace Mutuwa.
Haƙiƙa ya aminta cewar gaba ɗaya rayuwa cike take da ƙaddara, kuma ako yaushe sanjawa take, kamar yanda ayau wata sabuwar shafin ƙaddara ta buɗe masa, wanda kuma sanadin hakan yasa, ya zamo mutum me matuƙar rauni.
Tabbas akullum kuma ako yaushe yakan tambayan kansa, akan meyasa ƙaddara take wujijjiga rayuwarsa?.
Yau ga Laylerh tsaye agabansa amatsayin matar wani, Laylerh'n da ya rayu da sonta acikin kirjinsa sama da shekaru, Laylerh'n da kowani bugun zucia da numfashinsa ke tafiya da matsanancin sonta, Laylerh'n da yakejin ta ajikinsa kamar jini, Laylerh'n da ta kasance. AYSHNOOR É—insa, mafarkinsa, burinsa, kana kuma bugun zuciyarsa, Laylerh'n da tazamo gaba É—aya duniyarsa.
Tabbas abune me matuƙar wahala jure rayuwa babu masoyi, saidai har yanzu bazai cire rae ba, haƙiƙa zai jira, kuma ko yaushe zai zamana cikin jiranta, tabbas zai jirata har zuwa lokacin da zuciarsa zata daina bugawa, lokacin da numfashinsa zaibar gangar jikinsa, son LAYLERH ajininsa yake, daina sa abune da har abada bazae taɓa yiwuwa ba.

Idanunsa da suka cika da ƙwalla ya lumshe, tare da cije laɓɓansa da ƙarfi.
"Zanjiraki Ayshnoor, haƙiƙa zan jiraki har zuwa lokacin da numfashi zae bar jikina!..."
YafaÉ—a cikin wata irin raunanniyar muryar dake bayyana karyewar zuciarsa, wanda kuma ga dukkan alama baisan maganar tasa ta fito fili ba, dan atunaninsa azuciya yayi ta.

Ahankali ya sassauta riƙon da yayi mata, cikin sanyi ya ɗaura bakinsa adaidai tsakiar forehead ɗinta, tare da sakar mata wani irin hot kiss, wanda yasa gaba ɗaya tsikar jikinta mimmiƙewa.
Ahankali ya É—an soma janye jikinsa baya daga gareta.
Laylerh da wani sabon kuka ke shirin cimmata, da sauri ta riƙo hannunsa, kanta tasoma girgizawa, kana cikin wata irin muryar da ta taho tare da matsanancin kuka tace.
"Dan Allah Yah Maleek! Dan Allah!!!" Yanayin yanda tayi maganar cikin kukane yasa shi soma girgiza mata kai, tare kuma da ƙoƙarin zare hannunsa dake cikin nata, saboda bayajin zai iya jurewa yanayin da yakejin kansa aciki, domin idan yaci gaba da kasancewa ahaka zuciarsa zata iya tarwatsewa.
Laylerh kuwa da gaba ɗaya kukan da take yakusa shiɗar da'ita, ganin da gaske zai zare hannunsa daga cikin nata ne yasa ta fashewa da wani sabon kuka me tada hankali, wanda yasa gaba ɗaya jikinta ya soma rawa, hakanne kuwa ya bashi daman zare hannunsa daga cikin nata, ahankali ya ɗan soma jan jikinsa baya, tare da soma girgiza mata kai, yayinda kuma ya kasa ɗauke idanunsa akanta, wanda suka cika da ƙwalla.
Ganin hakane kuma yasa itama ta soma girgiza masa kae, saboda kuka yaci ƙarfinta sosai, hakan yasa bazata iya magana ba, duk da cewar kuma ƙafafunta sun kasa tsayuwa waje ɗaya, haka tashiga takawo ahankali, dan so take ta kusanta kanta dashi, domin har yanzu bai daina jan jikinsa baya daga gareta ba.
Hannunta dake rawa ta miƙo masa, cike da burin son ya kama hannun nata, cikin muryarta da ta zama over cracking tace..
"Pl....e.a...s.ee BOO don't leave me! Please!!!"
Tamkar narkakkiyar dalma haka zuciarsa ta narke, alokacin da taƙirasa da sunan BOO, sunan da yajima yana so yaji daga bakinta, sunan da yayi matuƙar kewar jinsa daga bakinta.
Take hawayen dake cikin idanunsa suka soma ƙoƙarin sauƙowa kan kumatunsa, wanda hakan yasa cikin sauri ya juya, tare da murɗa handle ɗin ƙofar bathroom ɗin dake bayansa ya shige, kafun Laylerh'n ta ƙaraso kuwa tuni ya murzawa ƙofar key.
Hakanne kuwa yasa Laylerh da ta iso da sauri, ta faɗa jikin ƙofar tare da sakin wani irin kuka me matuƙar taɓa zucia da kuma ta da hankalin me sauraro.
Jin kukan tane kuma yasa ahankali ya sulale ƙasa inda ya zauna daɓas, tare da jingina bayansa da jikin ƙofar, idanunsa ya rumtse ƙam saboda kokaɗan bayason jin kukan Laylerh'n, dan ko ayanzu haka jin zuciarsa yake na ƙuna kaman zata faso ƙirjinsa.
Laylerh kuwa zuwa yanzu, mafarkin da tayi daren shekaran jia ne ya shiga dawowa ƙwaƙwalarta filla filla, wanda hakan yasa sautin kukanta ƙaruwa, har ya kai ga numfashinta ya soma ƙoƙarin ɗauƙewa, hakanne kuwa yasa ta ta durƙusa guiwowinta aƙasa tare da jingina kanta da jikin ƙofar, ahankali cikin sheshsheƙa ta soma ƙiran sunansa.
Maleek kuwa duk yanda yaso daurewa hakan ya kasa, dan haka yakejin kaman kansa zai tarwatse, haƙiƙa kukanta shine abu na farko dake saurin karyar masa da zucia, kana kuma shike sawa yaji kaman ana sukan zuciarsa da mashi, saboda matuƙar yaji sautin kukanta, zuciarsa ɗumi take ɗauka.
Ahankali ya tashi daga jikin ƙofar, tare da arowa kansa juriya ya ƙarasa gaban jakuzzien dake cikin toilet ɗin, haƙiƙa ayanda yakejin kai da zuciarsa, yasa shi jin zai iyayin komai matuƙar zaiji salama da kuma sassauci. wannan yasa batare da tunanin komai ba ya shiga cikin jakuzzie'n dake cike da ruwa ya kwanta, tare kuma da nutsa kansa acikin ruwan, hakanne ko yasa gaba ɗaya jikinsa ya lume, take kuma ruwan ya soma shiga cikin hanci da bakinsa.
Yanayin yanda ya kwanta acikin ruwanne kuma yasa ga wanda baisani ba idan ya shigo cikin bathroom ɗin bazai taɓa tunanin cewa akwai mutum acikin jakuzzie'n ba, saboda yanda gaba ɗaya ruwan dake cikin jakuzzie'n ya haɗiyesa.

Sunday 27 december 2020
7:36 pm.
1/19/21, 8:25 PM - Ummi Tandama: *L.M*

*Chapter 30*

Oum Ayush na riƙe da hannunta suka nufi babban falon gidan, wanda yake mallakin Abbou Jaheed ne, da yawan lokuta anan yake sauƙe muhimman baƙinsa.
Koda suka ƙarasa cikin falon kuwa, zaune suka samu su Abbou Jaheed ɗin akan luntsuma luntsuman kujerun dake cikin falon .
Kaitsaye wajen Abbou Jaheed Oum Ayush ɗin ta nufa, wanda kuma har yanzu riƙe take da hannun Laylerh, akan lallausan carpet ɗin dake malale atsakiyar falon, Oum Ayush ta zaunar da ita, daidai gaban Abbou Jaheed.
Chapter 54 · 0% Book details