← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 144

Sashe 60

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Su Abbou Jaheed da Momy haÉ—i da Oum Ayush kuwa da suka fito falon tuntuni, haka suka tsaya suna kallonsu tamkar wasu statue.
Ciki kuwa harda Najeeb wanda shiɗinma tsayawa yayi yana kallon ikon Allah, ba abun da ya bashi mamaki kuwa kamar yanda yaga Laylerh da Maleek ɗin naƙara shigewa jikin juna.
Abbou Jaheed ne yayi ƙarfin halin sauƙe ajiyar zuciya, wanda take kuma maganar da Dr.Menk ya faɗa masa shekarun baya ya shiga dawo masa, musamman cewar da Dr.Menk din  yayi. "atarana abun daya faru da ita zai iya dawowa cikin tunaninta, musamman alokacin da wani namiji ke ƙoƙarin romancing ko kuma yin sex da'ita, saboda ta tsorata sosae kuma abun ya shiga jikinta."
Wani irin gauron numfashi Abbou Jaheed ɗin ya fesar, domin kuwa bama sai anyi mishi ƙarin bayani ba ya riga daya fahimci komae, saidai kuma yanayin yanda yaga Laylerh da Maleek ɗinne yasa yaji wani iri acikin zuciyarsa, duk da kuwa cewar suɗin ƴan uwane, amma irin wannan kusancin nasu ayanzu ɗauke yake da matsala babba, domin kuwa ko ba komae ayanzu akwae aure akan Laylerh'n, wani tunani kuma dayazo zuciyarsa ne, yasa shi cikin ɗan kausasa murya yaƙira sunan Maleek ɗin da haryanzu yake riƙe da Laylerh'n.
Maleek kuwa jin muryar Abbou Jaheed acikin kunnuwansa ne, yasa shi buɗe idanunsa wanda sukayi ja, yanayin yanda yaji muryar Abbou Jaheed ɗin kaɗai yasan me yake nufi, hakan yasa ahankali yasoma ƙoƙarin ɓanɓare Laylerh'n daga jikinsa, saidai kuma irin yanayin riƙon da tayi masa da ƙarfi ne yasa yakasa cireta ajikin nasa, hannayensa yasa ahankali ya tallafo fuskarta, tare da ɗan ƙura mata idanu, saboda har yanzu gata gama dawowa cikin hayyacinta ba, domin idanunta har yanzu akulle suke, still kuma lips ɗinta basu daena karkarwa ba.
Da idanunsa wanda cikinsu ke ɗauke da saƙonni kala kala yake kallonta, batare da yayi tsammani ko shiryawa ba kuwa, idanun nasa suka faɗa kan ƙirjinta, da kudan gaba ɗaya rabin breast ɗinta suka bayyana tasaman wuyan rigarta da buttun ɗinta ke watse.
Wani irin abu da yaji ne yasashi runtse idanunsa da karfi, tare da sa hannu ya dafe daidai saitin zuciyarsa, wanda lokaci ɗaya ta shiga wani irin dokawa, da ƙyar ya fusgo numfashinsa dake ƙoƙarin ƙwacewa, haƙiƙa ganin breast ɗinnata da yayi ya matuƙar sashi a shock saidai kuma, tuno da cewar Najeeb ya kalleta ahaka kamar yanda shima ya kalleta ne yasa shi jin wani ɗaci tare da ƙuna aransa, saboda sosae yake matuƙar kishin Laylerh'n.
Idanunsa yaɗan lumshe tare da soma kokuwa da zuciarsa wanda ke ƙara hasalasa, domin tabbas yasan idan ya biyewa fushin da zuciarsa ke ciki, to duk abunda zaiyi bazai zamo me kyau ba.
Yanayin kuma yanda yaji ƙuna acikin zuciarsa ne yasa take yaji har ita Laylerh'n ya soma jin haushinta, hakanan idanunsa suka rufe yake ganin kamar komae ma dake faruwa da saninta.
Ayanayin yanda yakejin ƙuna acikin zuciarsa ne yasa shi, sanya hannayensa duka biyu ya tureta daga jikinsa, tare kuma da saurin miƙewa tsaye.
Laylerh kuwa da jikinsa ya zame mata mafaka, jin ya tureta gefe ne yasa, ta riƙo ƙafafunsa ta rungume, tare da sakin sabon kuka, saboda sam batason yayi nesa da ita, dan zamansa akusa da ita ɗin, yasa taji cewar ta samu mafaka, domin tayi imani cewa matuƙar yana kusa da ita, bazai taɓa bari wani abu ya cutar da ita ba, kamar yana kuwa ya ceceta alokacin baya, haka take saran cewa ayanzuma zai taimaketa, dan gani take kamar Najeeb cutar da rayuwarta zaiyi.
Tabbas aduniyar nan zai iya jurewa komae amma kuma banda sauƙan sautin kukanta acikin kunnuwansa, domin sukan karyar masa da zuciya, sannan sukansa ka rauninsa bayyana, wannan yasa ko kaɗan bayason kukanta, domin yakanji kaman narkakken dalma ne ake ɗiga masa akan zuciyarsa.
Kowa ya sani har akullum baya iya jurewa jin sautin kukanta, to hakama ayanzun bayajin zai iya jurewa, rumtse jajayen idanunsa yayi, cikin dauriya da son karfafawa kansa guiwa ya janye ƙafansa daga riƙon da tayi masa, batare daya tsaya sauraran komae ya nufi ƙofar fita daga cikin falon.
Najeeb kuwa ganin yanda Maleek ɗin ya taho tamkar wanda baya hayyacinsa ne yasashi ɗan matsa masa daga bakin ƙofar, amma kuma duk da haka da Maleek ɗin yazo wucewa saida shoulders ɗinsu suka gogi juna.
Jin irin karfin bugun da shoulder É—in Maleek É—in yayiwa kafaÉ—ansa ne yasashi juyawa yabi bayan Maleek din da kallo.
Ahankali ya zura hannayensa acikn aljihun wandon dake jikinsa, tare da fesar da wani irin numfashi.
Ƙwarae yaji zafin abun da Maleek din yayi masa, saidai kuma amma yabarsa amatsayin bashi wanda zai rama anan kusa, wani irin murmushi yayi tare da jingina bayansa da jikin bango, ahankali ya dawo da kallonsa ga Laylerh wacce ke durƙushe jikinta sai faman ɓari yake, tamkar wanda aka watsawa ruwan sanyi.

Oum Ayush da gaba ɗaya lamarin ya rikitata sai ayanzu ta samu bakin ƙiran sunan Laylerh'n, tare da ƙarasowa ta dafa kafaɗanta.
"Lafiyanki ƙalau kuwa Laylerh me yake damunki ne, kibar kuka, ki natsu kiyi mana bayani."
Oum Ayush tafaÉ—a tana me É—an jijjiga Laylerh'n.
Faɗawa jikin Oum Ayush ɗin tayi ta rungumeta ƙam, tare da ɗan soma girgiza kanta, cikin muryarta me ɗauke da yanayin kuka, kana kuma yake bayyana zallan abun dake cikin zuciyarta tace.
"Help me Oum Ayush tsoro nakeji sosae, dan Allah Kice masa ya ƙyaleni, kada ya cutarmin da rayuwata please!!!" alokacin da ta kai ƙarshen maganan nata kuka take sosae, tare da haɗe hannuwanta biyu waje ɗaya alaman roko.
Gane abun da take nufi ne yasa cike da tsauyawa Oum Ayush ta rungumeta, ahankali taÉ—an soma shafa mata bayanta, cikin kulawa da kuma son sama mata nutsuwa tace.
"Please Laylerh kidaina kuka kinji, Najeeb Mijinki ne bakuma zai taɓa cutar dake ba, sannan gani akusa dake, ga kuma su Abbou Jaheed duk bazamu bari wani abu ya taɓaki ba, please control your self!"
Duk da kuwa cewar bata cikin nutsuwarta sosae, amma taÉ—anji zuciarta ta samu nutsuwa dajin kalaman Oum Ayush É—in.
Ganin ta É—an sassauta kukan da takeyi dinne kuma yasa Oum Ayush kamo hannunta ta zaunar da ita akan É—aya daga cikin kujerun falon, É—ago da kanta Oum Ayush É—in tayi tare dayiwa Najeeb dake tsaye alama akan ya bata ruwa.
Gane abun da take nufine yasa anutse Najeeb ya ƙarasa wajen fridgen dake cikin ɗakin, buɗewa murfin fridge ɗin yayi tare da ɗauko bottle water me ɗan sanyi kaɗan.
Zagayowa ta bayan Laylerh'n yayi yanda bazata gansa ba, ya miƙawa Oum Ayush bottle water'n.
Karɓan goran ruwan tayi tare da buɗe murfin, addu'a ta karanta abakinta tare da ɗan tofawa acikin ruwan, miƙawa Laylerh'n goran ruwan tayi, cike da kulawa tace. "Karɓa ruwa kisha."
Kamar kuwa dama jira take, har hannunta na rawa wajen karɓan goran ruwan takae bakinta.
Alokacin da ruwan ya shiga maƙoshinta kuwa idanunta ta lumshe tare da sauƙe ajiyar zuciya, sosae tasha ruwan har fiye da rabin goran, kafun ahankali ta janye goran daga bakinta, idanunta ta lumshe ahankali ta maida kanta jikin Oum Ayush.
Cikin abun da bae wuce mintuna kaÉ—an ba kuwa taji wani irin nutsuwa da kuma bacci na zuwar mata, hakanne kuma yasa tasake lafewa ajikin Oum Ayush É—in.
Abbou Jaheed da gaba ɗaya tausayinta ya cika masa zuciya, ƙarasowa wajen yayi tare dasa hannu ya shafa kanta, cikin kulawa yace. "Laylerh are you okay?."
Jin muryar Abbou Jaheed É—inne yasata buÉ—e idanunta, ahankali cikin muryarta da tayi sanyi sosae tace. "Am okay."
Murmushi Abbou Jaheed din yayi, tare da dafa kafaÉ—anta, cike da jin daÉ—in dawowa hayyacinta da tayi yace.
"Good girl, kije ki kwanta kiyi bacci kinji, namiki alƙawarin babu abun da zae sameki."
Kanta ta jinjinawa Abbou Jaheed É—in alaman to, domin dama ko bai faÉ—a ba, bacci ya fara zuwar mata.
Ganin kuma ta samu nutsuwa ne yasa Abbou Jaheed din juyawa ya koma ɗakinsa, domin sanin haƙiƙanin abun dake faruwa da Laylerh'n yasa samma babu amfanin tsayawa wani dogon magana.
Kallon babban agogon dake cikin falon Oum Ayush tayi, ganin ƙarfe shabiu harda rabi da tayi ne yasa ta miƙewa tsaye, shafa kan Laylerh'n tayi, cikin kulawa tace. "Kije ki kwanta kinji."
Batare da ta jira me Laylerh'n zatace ba kuwa ta juya ta shiga É—aya daga cikin É—akunan dake cikin falon.
Ganin kuma duk sun watse ne yasa ahankali ta miƙe tsaye, juyowan da zatayi ne kuma idanunta suka sauƙa akan Najeeb dake tsaye ya harɗe hannayensa akan ƙirjinsa, wanda kuma shiɗin ma kallonta yake, haɗa idanun da sukayi ne yasashi sakar mata murmushi, tare da buɗe mata hannayensa alaman tazo garesa.
Babu musu ko tunanin wani abu ahankali kuwa ta shiga takowa inda yake.

*5/January/2021*
1/19/21, 8:28 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Chapter 34*
Chapter 60 · 0% Book details