← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 144

Sashe 139

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

K’warai takan ga kasantuwarta da Maleek d’in kamar amafarki, haka kuma zamantowanta mata agaresa tamkar al’amara, saidai kuma abune da yake abayyane cewa k’arfi da kuma ikon Ubangiji ya wuce komai, Allah Ne kad’ai keyin komai alokacin da yaso, ya hanaka alokacin da kake buk’ata, ya kuma baka alokacin da kafi tsananin buk’ata.

Idanunta da suka ciko da hawaye ta d’an lumshe, tare da sake hugging d’in Maleek d’in sosai, ahankali kuma ta dawo da kanta dake kan k’irjinsa, daidai saitin inda zuciyarsa take, yanayin yanda taji zuciyar tasa na bugawa anutse ne kuma yasa akasalance ta saki murmushi, kasancewar itama maganin da tasha d’in ya somayi mata aiki, dan tuni ta farajin yanayin bacci na satarta, da yake kuma dama akwai gajiya ajikin ta, shiyasa ko mintuna 10 ba arufa ba itama bacci ya d’auketa.

***

Aunty Aina’u dake zaune zugum akan sofa ne, tayi saurin d’ago da kanta ta kalli Momy wacce ita d’inma take zaune duk yanayinta babu dad’i.

Gyara zama Aunty Aina’u tayi tare kuma da sake kallon Momy’n, cikin kuma nuna sak’ewar guiwanta akan abun tace.

“Nikam gaskiya nagaji da way’annan abubuwan da suketa faruwa, yanzu fa almost 2years kenan da mukeson ganin bayan Captain Maleek da wannan shegiyar Laylerh’n amma abun ya kasa yiwuwa, duk wani plant d’in da muka tsara saiya warware, first kin tsara cewar Maleek zainemi Laylerh’n da aurenta amma bamu cimmawa hakan ba, har Najeeb ya saketa, fine naji plant dinki daya yayi aiki, wanda kikasa Najeeb yaje d’aya daga cikin gidajen Maleek ya ga sirrukan soyayyar Laylerh da yake ta b’oyewa tsawon shekaru, saboda haka nema yasa ya sauwak’e mata, bayan nan kuma kince zakisa Maleek ya maida Laylerh’n karuwarsa, amadadin hakan sai gashi ya maida ita matarsa ta sunnah, why duk way’annan abubuwan suke faruwa? hakan na nufin cewa kenan mu bamu da sa’a kwata kwata arayuwa, ga dukiya munaji muna gani amma mallakarta na nema ya zame mana bala’i, koda yake dama anfad’amin cewa har abada bazamu tab’a yin nasara akan LAYLERHMALEEK ba, amma nak’iji, To yanzu kam na tabbatar, kuma Insha Allah Zan cire hannuna akan wannan lamarin saboda yanzu duniya abun tsoroce, baka bi wani da sharri bama yaka k’are....�

Harara Mom da ta cika tayi fam ta watsa mata tare da cije labb’anta, Tabbas ayanzu ita kad’ai tasan tafasar da zuciyarta keyi akan al’amarin, saboda kwata kwata ma yanzu Abbou Jaheed ya daina sata acikin duk wani al’amura nasa, ya daina fad’a mata komai daya shafesa, domin hatta auren Laylerh da Maleek d’in sai ana Gobe za’a d’aura ta sani, k’warai taji babu dad’i akan hakan, saidai yanzu babban abundake damun zuciyarta shine burinta da har yau yak’i cika, abu mafi tashin hankali kuma da take tsoron faruwarsa, itace ranar da Abbou Jaheed zai san gaskiyar abunda taji ma tana k’ullawa y’ay’ansa.
Lallai tasan awannan ranar komai nata yazo k’arshe, saboda Abbou Jaheed bazae tab’a yarda yaci gaba da zama da ita ba, sannan kuma ba haihuwa tayi dashi ba balle tasa ka ran samun wani kaso daga cikin tarin dukiyarsa.

Tabbas ayanzu mafita d’ayane ke gareta, kodai tayi regreting abunda ta aikata ko kuma ta sanja taku, saidai abu mafi sauk’i agareta shine yin regreting, Domin da hakan zuciyarta tafi aminta, abune kuma da tasani cewa Allah Yana jin k’an bayinsa masu tuba, matuk’ar kuma ta nemi yafiyan Maleek da Laylerh to tasan Allah Ma zai yafe mata, lallai wannan shine abu mafi sauk’i agareta, saboda tamkar ceton kanta tayi, matuk’ar ta share duk wani mummunan tunani da kuma k’udirin dake cikin zuciyarta, sannan ta kuma gamsu da duk abunda Aunty Aina’u ta fad’a, gaba d’aya duniya ba komai bace saidai idan kaine ka d’auketa wata abar girmamawa, nan kuma gaba d’aya rayuwarka zata k’are awahala da yawan buruka wanda har abada bazasu tab’a cika ba.

Jikinta amatuk’ar sanyaye ta kalli Aunty Ayna’u, tare dasa hannu ta d’an matse hawayen dake cikin idanunta, saboda ayanzu ta sakejin gamsuwar cewar idan har ta cutar da Laylerh Maleek har abada Allah bazae tab’a barinta ba.

Hannun y’ar uwarta Aina’u ta kamo, cikin muryarta da tayi sanyi sosai tace.

“Insha Allah Aina’u bazan sake cutar da rayuwar Laylerh da Maleek ba, kamar yanda bazan sakeyi musu mummunan fata ba, zan kuma nemi yafiyarsu, amma kafunnan dole saina gyara tsakanina da Ubangijina da kuma Mijina, duk da cewar ya watsar dani ayanzu, amma bazan gajiya ba Insha Allah zanyi k’ok’ari wajen ganin na gyara kura kuran da nayi masa, tun ada bansan Meyasa na zamanto Mace mai tsananin son zuciya ba, idanuna sun rufe harta kai ga ina abu kaman ba Musulma ba, na manta cewar Allah Ne keyin yadda yaso, kana na manta cewar idan bai tsara abuba, har abada baya tab’a yiwuwa, lallai Tabbas zan gyara kuskurena, zanyi kokarin zama ta kwarai ko badan kowa ba, kodan saboda kaina da kuma karshena.�

Rungume Mom d’in Aunty Aina’u tayi saboda, ita dama tuntuni zuciyarta ta jima da karyewa, saboda wani wa’azi da taji, kuma Insha Allah zata nemo wa’azin ta sakawa y’ar uwarta, wanda tayi imani hakan zai sake sawa zuciyar Momyn tayi sanyi, kuma dama tuncan sunsani cewar, duk wani abu da zakayi wanda zai cutar da d’an uwanka ba abu bane maikyau, kuma sannan Allah baya yafe laifin dake tsakanin bawa da bawa, saidai har idan har wanda ka zalunta d’in ne ya yafe maka, To Allah Ma zai yafe maka, duk sun san hakan amma son zuciya da dukiya suka rufe musu ido, sam suka kasa nazartar abunda zai amfanesu.

*3:00pm*
Daidai ya soma bud’e idanunsa da suka d’an k’ank’ance saboda baccin daya share sama da awanni yanayi.

Jikinsa dake had’e dana Laylerh ya zare, tare da zuro k’afafunsa ya sauk’o daga kan gadon, agogon dake sak’ale ajikin bango ya kalla, ganin da yayi kuma lokaci ya d’anja har 3:2 pm ne yasashi mik’ewa tsaye, tare da d’an dafe kansa dake sarawa, sam baisan haka magungunan da suka sha d’in keda k’arfi sosai ba, saboda tun kwanciyarsu da k’yar ya iya tashi yayi sallah’n azahar, koda ya tashi Laylerh’n ma kukan shagwab’a ta saka masa, tare da cewa ita bacci bai isheta ba, haka dai ya lallab’ata tayi sallah’n, bayan ta idar da sallah’nne kuma suka sake komawa wani bacci’n, ba shi ne ya farka ba kuma sai yanzu da la’asar ta kusa.

Still kuma ya tashi ne bawai dan baccin ya ishesa ba, saidan yunwan dake damun cikinsa, wanda ya kuma san cewar bashi kad’ai ne yakejin yunwan ba harda Laylerh’nsa.

Hannunsa ya daura akan handle din kofar toilet d’in, tare kuma da tura k’ofar kana ya kutsa kansa ciki, kaitsaye gaban babban jakuzzie’n dake cikin toilet d’in ya nufa.

Adaddafe ya had’a musu duk wani abu dayasan zasu buk’ata, tare kuma da juye wani turaren wanka mai dadin kamshi acikin ruwan jakuzzie’n.

Bayan ya kammala komae ne kuma ya dawo cikin d’akin, tare da zare long jeans d’in dake jikinsa.

Direct gaban gadon ya nufa, tare da bud’e hannayensa duka biyu ya d’auki Laylerh’n da har yanzu ke bacci, kaitsaye toilet d’in ya nufa da ita.

Still kuma tana jikinsa, ya shiga cikin jakuzzie d’in, kwantar da ita yayi akan chest d’insa tare da lumshe idanunsa, yana mejin yanda ruwan ke ratsa duk jikinsu.

Haka kuma d’umin ruwan daya ratsa cikin jikinsu d’inne yasa ta bud’e idanunta akasalance, ta sauk’e ganinta akansa.

“Boo!!�
Tak’ira sunansa ashagwab’e tare da sake manna kanta da jikinsa.

“Ummm Shugarnoor!!!�
Ya amsa mata, da wata irin muryar da dadinta yasata d’an lumshe Idanunta, tare da d’an lasan lips d’in bakinta, cikin yanayin dake nuna jin dad’in mood d’innasu ne kuma ta juyo ta fuskancesa.

Idanunsa dake alumshe yad’an bud’e tare da yi mata wani irin kallo’n dayasa duk taji tsikar jikinta ya zuba, Daga cikin ruwan kuwa hannayensa yasa ahankali ya had’e waist d’insa da nata.
Atare suka fitar da wani sexual eraction sound.
Saboda wani irin abu da sukaji ya ratsa duk ilahirin jikinsu.

Harshensa yad’an zaro waje tare da bud’e bakinsa, ahankali yace.

*”I LOVE YOU Shugarnoor!!� *

harshenta ta d’aura akan Lips d’insa daya d’an bud’e su tare, da lumshe idanunta, saboda yanda kalmar tasa ta shigeta sosai, cikin kuma muryarta dake shaking tace.

*� I LOVE YOU too Boo!!!�*

*(Love you all guys)*

*10:20 pm*
4/12/21, 7:52 AM - Ummi Tandama: *82*

Lumsassun idanunsa ya bud’e saboda yanda yaji amo da kuma sautin muryar nata, ya sake hautsuna tunaninsa tare dajin wani irin kasala na musamman.

Tabbas yanayin maidad’ine agaresu, irin kuma dad’in da misalta shi keda wahala, saidai ga duk wanda ya kallesu, zai gane hakanne kawai ta yanda suke sake shigewa jikin juna.

Sake rungumeta yayi sosai tare da d’aukan soap ya soma goga musu ajikinsu.
Sannu ahankali cikin yanayi’n nutsuwa kuma, yayi musu wankan atare.
Tare da d’aura towel akan waist d’insa ita kuma ya saka mata bathrobe a jikinta, kama hannunta yayi har zuwa gaban sink suka d’auro alwala.
Still kuma yana rik’e da hannunta haka suka fito daga cikin toilet d’in.

Yanzun ma shi da kansa ya shafa mata body lotion a jikinta, kamar dai yanda yayi mata da safe.
Bayan ya gama shafa mata mai d’inne kuma da kansa ya bud’e wardrobe d’inta ya ciro mata wata net tight pencil gown marar nauyi, mik’a mata rigar yayi tare da yi mata alama akan tasa, kana ya juya shima ya soma kimtsa kansa.

Laylerh kuwa ganin ya juya mata bayane yasa ta shirya kanta atsanake tare da zura rigar daya bata d’in a jikinta, saidai kuma kasancewar rigar ya kamata sosai ne yasa duk wani shape d’in jikinta bayyana.

Dogon gashinta daya kwanta agadon bayanta ta d’aure, tare da neman waje ta zauna, Idanunta ta tsayar akan Maleek d’in daya gama shirya kansa cikin wasu had’add’un riga da wando.
Kamar yanda kuma komai yasa ajikinsa yana yi masa kyau, haka wannan kayan d’in ma sun amshi jikinsa sosai.

Juyowan da taga Yayine kuma yasata yin k’asa da kanta tare da kama y’an yatsun hannunta ta shiga murzawa.

“Zo muyi sallah.� Ya fad’a adaidai lokacin daya gama daidaita tsayuwarsa akan darduma carpet d’in dake shimfud’e agefen gadonsu.
Chapter 139 · 0% Book details