← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 144

Sashe 78

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

“LAYLERH!�
Najeeb dake tsaye tun d’azu acikin falon ya k’ira sunanta, da muryarsa wacce tayi sanyi sosae, domin tun shigowarta cikin falon yake tsaye abakin dining table, saboda dawowansa shima kenan, ganin kuma food flask d’in abincin daya ajiye mata a yanda ya barshi ne, yasashi k’arasowa wajen ya duba dan yaga ko taci abincin.
Jin amo da kuma sautin muryarsa acikin kunnuwanta ne yasa tayi saurin bud’e idanunta wanda suka b’aci da hawaye, saboda kwata kwata bata kawo aranta cewar akwae wani acikin falon bayan itaba
Ahankali ta janye idanunta daga kallon da yake mata, tare da sunkuyar da kanta k’asa.
Shikuwa Najeeb anutse ya shiga takowa zuwa gareta, har ya k’araso inda take kuwa bata sake d’ago kae ta kalleshi ba.
Isowarsa kusa da ita ne kuma yasashi d’an durk’usawa agabanta, cikin yanayin sanyi yasa hannayensa ya d’ago hab’arta, hakanne kuwa ya bashi daman kallo full face d’inta.
Ahankali yasa d’ayan hannunsa ya shafi gefen fuskarta.
“Me yake da munki?�
Ya fad’a asanyaye tare dasa hannayensa ya share mata hawayen dake mak’ale atsakankanin eye lashes d’inta.
“Babu.� Ta fad’a da k’yar cikin muryar ta dake fitar da sheshshek’a.
Ahankali ya maida hannayensa kan kafad’unta ya d’agota saboda dama yasan cewa ba lallaine ta fad’a masa gaskiya da kuma hak’ik’anin abunda ke damunta ba.
K’ok’arin mik’ar da ita tsaye yayi ta hanyar rik’o hannunta, ahankali yajawota zuwa tsakiyar falon.
Zama yayi akan d’aya daga cikin kujerun falon, still kuma hannunsa na rik’e da nata ya jawota ta fad’a jikinsa.
Hannayensa duka biyu yasa yayi hugging d’inta.
Ahankali ya kawo bakinsa daidai saitin kunnenta, cike da kulawa yace.
“Meyasa har yanzu bakiyi breakfast ba, kodai baki ga kayan breakfast d’in dana ajiye miki bane?�
Yanayin yanda yayi mata tambayan cikin rad’a ne yasa ta sake shagwab’e fuska, y’an yatsun hannunta ta shiga murzawa cikin muryarta da bata fita sosae tace.
“Nak’oshi ne.�
“Me kikaci da har yasa kika k’oshi haka? bakisan cewa rashin cin abinci yana sa mutum ya kamu da ulcer ba? koda yake ma duk ba wannan ba, meyasa meki kike kuka? saboda na tabbata bazakiyi kuka haka kawae babu wani daliliba, fad’amin idan kuma bankai na sani bane shikenan.�
Jin abunda ya fad’a d’inne yasa ahankali ta d’ago kai ta kalleshi, ganin kuma shid’in ma ita yake kallo ne yasa tayi k’asa da idanunta, tabbas baicancanci shariya ko k’arya awajen ta ba, amma kuma saidai wani lokaci bisa dole ake aje gaskiya ayi k’arya, musamman idan akayi duba da cewar fad’an gaskiyan kan iya ruguza komai.
“Marana ne yake ciwo.� Ta fad’a atak’aice domin gudun kada ya gano cewa ba gaskiya ta fad’a masa ba.
“Meya samu marar naki yake ciwo?�
Ya jefo mata tambayar da sam batayi tsammanin jinta daga garesa ba, hakan yasa ta kau da kanta gefe, Dan ayanzu kam bata da amsar da zata basa.
Gane hakan da yayine kuma yasa baisake tambayar taba, saima tashi da yayi ya k’arasa gaban dining table d’in, da kansa ya had’o mata breakfast d’in acikin plate.
Zuwa yayi har gabanta ya zauna, tare da sata agaba dole saida yaga ta d’anci abincin kafun ya k’yaleta.
Itakuwa Laylerh anan cikin falon ta kwanta, haka zuciyarta ta dinga sak’a mata abubuwa da yawa acikin ranta, cikin mintuna k’alilan kuwa bacci b’arawo ya d’auketa.
Tunda tafara baccin kuwa Najeeb ya tsura mata mayun idanunsa, baya ko k’iftawa, tunani daban daban kawai yake tayi acikin zuciyarsa, shima ahaka bacci ya d’aukesa.
Har yayi baccin nasa ya farka kuwa Laylerh bata tashi ba, wanka ya je yayi tare da sake shirya kansa cikin shiga me kyau, batare kuma da ya ta she ta ba ya fice daga cikin gidan na gaba d’aya, saboda ya lura zamansa atare da Laylerh’n shine ke k’ara haukatar dashi yayi ta jin feelings.
Laylerh kam bacci tayi sosae dan sai wajajen 3 tatashi, hakanan taji duk duniyar batayi mata dad’i.
Wanka ta sakeyi inda ta shirya kanta cikin kaya marassa nauyi.
Atak’aice dai haka ta k’are gaba d’aya wuninta na wannan rana batajin dad’in yanayinta, domin kuwa da zaran tatuno cewar Maleek zaiyi aure nanda 2 weeks saitaji komae ya tsaya mata.
Ahaka har dare yayi, yau dai kam Najeeb ko kusa da ita baizoba akan doguwar kujeran dake cikin d’akin yayi kwanciyarsa saboda ya lura dagaske cewa Laylerh’n batajin dad’i, idan ya matso kusa da ita kuwa ba k’aramin azabtuwa yakeyi ba, wannan dalili yasashi samawa kansa nutsuwa ya kwanta akan kujera.
Laylerh kuwa sosae taji dad’in hakan saboda yau d’in duk adagule take.

Washegari.
Awayewan garin na yau ne kuma su Abbou Jaheed da Oum Ayush suka tashi da shirye shiryen auren Maleek haik’an, inda Oum Ayush ta shiga shirye shiryen abubuwan da ya kamata ayi, b’angaren kayan lefe kuwa tunjiya ta bada order’nsu wa k’awarta Hajiya Nana dake can k’asar Dubai, wanda kuma nan da kwana hud’u kayan zasu iso.

(kuyi hakuri muna biki bansamu zama ba shiyasa, wannan page dinma atsatstsaye nayi ba editing.)
29January/2021
2/1/21, 3:27 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*
*Writting By*
fatymasardauna

*Chapter 45*
Chapter 78 · 0% Book details