← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 144

Sashe 58

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Najeeb kuwa ahankali ya murɗa handle ɗin ƙofar bathroom ɗin ya fito, yana fitowa kuwa idanunsa suka sauƙa akanta.
Yanayin yanda ta tsaya ajikin drawer'n da kuma yanda ta lumshe idanunta ne yasashi ɗan tsayawa yana kallonta from head to toe, ganin kuma ta lulluɓe jikinta da hijab ne ya sakashi sakin ɗan guntun murmushi, ahankali ya saki ƙofar bathroom din tare da takowa zuwa gareta.
Ganin da yayi har ya iso gareta bata buÉ—e idanunta bane, yasa ahankali yaÉ—an yarfa mata ruwan dake hannunsa, domin shigarsa toilet É—in Alwala yayi.
Jin sauƙan ruwa akan fuskarta ne yasata buɗe idanunta da sauri, wanda hakanne yasa ta dawowa hayyacinta, kasancewar kuma hawaye sun cika idanunta ne yasa ta kasa ɗago kae ta kalleshi, saboda awannan karon sam bataso yaga hawayenta.
Saidai kuma shiɗin ma ayanzu baiwani damu da son ganin cikin idanun nata ba, ƙatuwar sallaya ya ɗauka, kana cikin yin ƙasa da murya yace.
"Kije kiyi alwala kizo muyi sallah."
Jin abun daya faɗa ne yasa ta ɗan saci kallonsa ta ƙasan idanunta, ba tare da ta musa masa ba kuwa ta nufi hanyar bathroom ɗin.
Da kallo ya bita harta shige ciki ta turo ƙofar, wani tunani dayazo zuciyarsa ne yasashi jin wani irin tausayinta ya cika masa zuciya, take kuwa maganganun da Abbou Jaheed yayi masa suka shiga dawowa cikin kunnensa, inda yake ce masa.   "Laylerh Marainiyace bata da uwa bata da uba, ayanzu shi da yake amatsayin mijinta shi ya kamata ya zama komae nata, haƙƙinsa ne ɗauke mata duk wani damuwarta, haka kuma haƙƙinsa ne ya bata farinciki."  Murmushin daya sa kumatunsa ɗan loɓawa yayi, ahankali ya zura hannayensa acikin aljihun rigar dake jikinsa, tare da zubawa ƙofar bathroom ɗin ido yana jiran fitowarta.
Ɓangaren Laylerh kuwa tana shiga cikin bathroom ɗin, hijab din dake jikinta ta cire tare da ƙarasawa gaban sink ta soma alwala, koda tazo shafar kai haka gaba ɗaya dogon gashin kanta ya baje akan fatar wuyanta, bayan ta gama alwalanne kuma ta sake maida Hijab ɗin jikinta, ahankali ta murɗa handle ɗin ƙofar bathroom ɗin ta fito.
Fitowan nata kuwa yayi daidai da sauƙe idanunta akansa da tayi, cikin sauri tayi ƙasa da kanta, tare da tsayawa ta kasa ƙarasowa wajen da yake.
Murmushi yayi kana ahankali ya shiga takawa zuwa gareta,  ƙamshin turarensa da taji ne yasa ta gane cewar ya iso kusa da ita. 
"Nayi alwala'n." tafaÉ—a cikin sassanyar muryarta dake É—auke da craking.
Kansa ya jinjina tare da cewa.
"To muje muyi sallah." 
baijirayi komai ba ya kama hannunta suka nufi inda ya shumfuÉ—a musu sallaya.
Saida ya daidaita tsayuwarsa akan sallayan kafun ya saki hannunta, itama ta gyara nata tsayuwar.
Yanayin tsayuwar da sukayi ne yasa ya zama yana gaba ita kuma tana É—an bayansa kaÉ—an.
Kamar yanda yake ashari'ance shiya jasu sallah raka'a biyu.
Koda suka idar da sallan juyowa yayi ya fuskanceta, ahankali yakai hannunsa ya dafa kanta, tare da karanta mata addu'o'i ya shafa mata.
Tare da É—an matsowa kusa da ita, hakanne kuma yasa suka zama suna kusa da juna sosae.
Hannunsa ya É—aura akan hannayenta da tun É—azu take ta faman wasa dasu.
"Laylerh!'
Yaƙira sunanta cikin wata irin sassanyar murya, kasancewar gaba ɗaya jikinsa ya fara zama weak.
Samun kanta tayi da kasa amsa masa, dan haka takejin laɓɓan bakinta sun mata nauyi.
Jin kuma bata amsa masa bane yasa asanyaye ya jawota jikinsa.
Hannayensa yasa ya zagayeta dasu tare da yi mata wani irin runguma, ahankali ya lumshe idanunsa, tare da sauƙe wata irin katuwar ajiyar zuciya.
Laylerh kuwa kasancewar batayi tsammanin hakan daga garesa bane yasa taji ƙirjinta na wani irin bugawa,  ahankali ta soma ƙoƙarin zame jikinta daga nasa, amma saidai riƙon da yayi mata ya kasa bata daman hakan.
Shikuwa Najeeb sake matseta yayi ajikinsa, anutse ya soma kokarin cire hijab É—in dake jikinta.
Ganin hakanne kuma yasa ta ƙanƙame jikinta waje ɗaya, lura da tayi cewar da gaske cire mata hijab ɗin yakeson yi ne, yasa ashagwaɓe tace.
"Ni dai kabarmin hijab É—ina please!"
Sauƙan sautin kasalalliyar muryarta acikin kunnuwansa ne, yasashi sake jin wani irin feeling ɗinta na sake shiga jikinsa, yatsarsa ya ɗaura akan bakinta tare da yi mata alama akan  tayi shiru.
Batare kuma da ya saurari komae ba ya cire mata hijab É—in, wanda hakan yasa take dogon gashin kanta da yasha gyara, ya samu daman sake bajewa akan wuyanta, da kuma gefen fuskarta.
Jin ya cire mata hijab ɗinne yasa ta rumtse Idanunta da ƙarfi tare da ƙanƙame jikinta.
Najeeb kuwa daddaɗan ƙamshin jiki da kuma na gashinta da suka bugesa ne, ya sashi lumshe idanu, tare da shaƙan wani dogon numfashi, inda take kuma daddaɗan ƙamshin nata ya ƙara masa yawan feeling ɗinta, saboda wani irin ƙamshi ne me matuƙar daɗi jikin nata ke fitarwa.
Cikin kasalar da yake jin kansa aciki, yakai hannunsa ya ɗago haɓarta, idanunsa ya zubawa smalls lips ɗinta, yana mejin wani irin abu na yawo acikin jikinsa.
Ahankali ya shiga matso da fuskarsa dab da nata, batare da zato ko tsammani ba ya sauƙe mata wani irin kiss adaidai kusa da bakinta, wanda yasa duk taji tsikar jikinta ya tashi, da sauri tasa hannayenta ta rufe fuskarta.
Shikuwa Najeeb ganin ta rufe fuskarta ne yasashi miƙa hannunsa ya ɗauko ƙatuwar ledan daya shigo da ita ɗazu.
Buɗe ledan yayi, wanda ke cike da kayan ciye ciye, ledan chocolate ɗaya ya ɗauko tare da ɓarewa, sake gyara mata zamanta ajikinsa yayi, haɗe da ɗago fuskarta yakai ɓararren chocolate ɗin bakinta, yanayin yanda taga ya tsareta da idanun sa ne, yasa cikin yanayin sanyi ta buɗe bakinta ya samata chocolate ɗin, anutse ta soma tauna choco ɗin tana ɗan lumshe idanunta, kasancewar dama ita gwanace wajen son zaƙi, ganin tana cin chocolate ɗinne yasa shi soma warware wani poil paper wanda aka zuba pepper chicken acikinsa,  again kuma wani poil paper'n ya ƙara buɗewa, wanda shi kuma cikinsa ke ɗauke da roasted fish, wanda akayiwa haɗaɗɗen sauce.
"Chicken or roasted fish, wanne zakici acikinsu?." 
yayi mata tambayar yana me Kallon yanda take ta mamul mamul da bakinta.
"Ni chocolate kawae nakeso." Ta bashi amsa tana me kallon tarin chocolates É—in dake zube agabansa.
Kai yaÉ—an girgiza, dan sanin halinta ne dama yasashi sayo chocolate É—in da yawa.
"Saikinci abinci kafun na sake baki wani chocolate."
Yafaɗa yana me saka hannunsa acikin pepper chicken ɗin dake gabansa, ɗauko naman kazan yayi daidai wanda zai iya shiga bakinta, ya miƙa mata, sam batajin sha'awan pepper chicken ɗin, amma jin yace bazai bata chocolate ba saitaci abinci yasa ahankali ta buɗe bakinta ya samata, tana cinyewa kuwa ya sake ƙara mata.
Cikin son yi mata wayo haka ya shiga bata pepper chicken É—in abaki, bataci wani sosae ba ta kawar da kanta gefe.
Ganin ta kawar da kanta gefe ne yasashi cewa "Ƙin ƙoshi." Ya ƙare tambayan yana me juyo da fuskarta, zuwa gareshi, kai ta jinjina masa alaman "Eh."
Juice ɗin exotic ya miƙo mata, babu musu kuwa ta karɓa tasha.
Still ƙoƙarin sauƙa daga jikinsa ta somayi, saidai kuma yanayin riƙon da yayi mata yasa ta kasa samun daman hakan, ganin da tayi cewar bashi da alaman saketa ne yasa, ashagwaɓe tace. "Bacci nakeji."
Kansa ya jinjina mata alaman yaji, ahankali ya ɗan sassauta riƙon da yayi mata, tare da ɗaukan chocolate guda ɗaya ya miƙa mata.
Tana karɓan chocolate ɗin kuwa cikin sauri ta tashi daga jikinsa.
Murmushi kawai yayi batare da yace da ita komai ba, ya soma cin roasted fish É—in dake gabansa.
Ita kuwa Laylerh ganin tasamu ta ƙwace kanta daga garesa ne yasa ta shiga sauƙe ajiyar zuciya, tare da ƙarasawa kan gado, aɗan baki bakin gadon ta kwanta tare da lumshe idanunta, wani irin bugawa takejin ƙirjinta nayi, yayinda wani abu me kama da faɗuwar gaba ke ƙoƙarin ruskarta, batasan me yasa ba ayanzun takejin gaba ɗaya mood dinta na sanjawa.
Kana lokaci ɗaya taji bata ko ƙaunar chocolate ɗin daya bata, ƙanƙame jikinta waje ɗaya tayi tare da jan lallausan blanket ɗin dake aje kan gadon ta lulluɓe jikinta, yanayin kuma yanda ta kwanta shiru ne yasa wasu irin tunani suka shiga yawo acikin ƙwaƙwalwarta.

Almost 20 minute ya É—auka yana cin abincin, bayan yagama ne kuma ya É—auki tissue ya goge bakinsa.
Tattare wajen yayi tare da faka sauran abincin agefe.
Ahankali ya miƙe tsaye tare da ɗan juyowa ya kalli, inda Laylerh'n ke kwance, yayinda ta lumshe idanunta kamar me bacci.
Murmushi kawae yayi, kaitsaye kuma ya nufi toilet.
Koda ya ƙarasa cikin toilet ɗin kayan jikinsa ya rage tare da sakarwa kansa ruwa.
Bayan ya gama wankanne ya saka wani bathrobe ajikinsa, tare dayin brush, saida kuma ya kammala duk wani abun da zaiyi kafun ya fito daga toilet ɗin, hannunsa riƙe da towel yana goge jikinsa, kaitsaye ɓangaren sif ɗin kayansa ya nufa.
Wani dogon wando da kuma button shirt marar nauyi yasa ajikinsa, kasancewar kuma dare ne yasa bai saka aninayen gaban rigar duka ba.
Cool perfumed me daɗin ƙamshi ya shafa ajikinsa, tare da ƙarasawa ya rage hasken wutan dake cikin ɗakin.
Ahankali ya ƙaraso ya kwanta akan gadon.
Kwanciyar tasa kuwa yayi daidai da bugawar zuciyar Laylerh wanda dama duk wani motsinsa akan kunnenta yake, domin duk yanda taso bacci ya ɗauketa abun yaci tura, saima faɗuwar gaba da tsinkewar zuciyar dake ƙara ziyartarta.
Najeeb kuwa ahankali ya gyara kwanciyarsa, tare da juyowa ya zamana yana fuskantar Laylerh'n wanda ta riga da ta bashi baya.
Sam shikam ya kasa gane wani irin fitinannen ƙamshi Laylerh'n keyi, wanda gaba ɗaya yake sashi rasa duk wata nutsuwarsa, kasancewar har yanzu ƙamshin nata bai daina ratsa hancinsa ba, duk da kuwa cewar akwae ɗan rata atsakaninsu, amma hakan bai hanashi jiyo daddaɗan ƙamshin dake tashi ajikinta ba.
Sanadin hakanne kuma yasa yakejin wani irin hot feelings dinta na damunshi.
"Laylerh."
Yakira sunanta cikin wata irin sillent voice É—insa dake bayyana irin zallar feelings É—inta da yakeji.
Chapter 58 · 0% Book details