← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 144

Sashe 106

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahankali kuma cikin yanayin son kawar da damuwar dake shirin duk’ar dashi k’asa ya shiga taka k’afafunsa zuwa inda Laylerh’n ke kwance.
Hak’ik’a da ace ayau kuma ayanzu zai bayyana zuciyarsa ga kowa to da dayawan mutane sai sun tausaya masa, amma kuma yasan cewa babu daman yin hakan, domin shi kansa shaidane duk yanda zuciyarsa kejin k’una, to abayan wata zuciyar take, wata zuciyar wanda ta share tsawon shekaru tana jiran cikar burinta, ta kuma samu rauni mai ciwo asanadin watsewan duk wani muradinta, zuciyar da tun asali aka halicceta da wani irin k’akk’arfan SO, wanda yake neman gusar da hankali da kuma tunanin maiyinsa.
Tabbas abunda idanunsa suka gane masa kad’ai sun isa tabbatar masa da cewa aduniya bayan wannan soyayyar babu wata, haka kuma bayan wannan muradin babu wani sauran muradi daya rage, kana idan wannan burin bai cikaba to Tabbas har abada babu wani buri aduniya nasu da zae tab’a cika.

Amatuk’ar sanyaye ya d’an ran k’wafo da kansa zuwa gareta, bayan ya tsayar da duk wani zancen zuci da zuciyartasa keyi.
Haka yakejin tausayinta tamkar zai fasa zuciya da k’irjinsa.
Hannayensa duka biyu yasa asanyaye ya d’agota cad’ak, tamakar wata y’ar baby daga kwancen da take, still kuma idanunsa wanda suke cike da ruwan hawaye na kanta, ya k’arasa da ita kan gado, tare da shumfud’eta atsakiyar gadon.
Sauk’e ganinsa kuma da yayi akan kyakkyawar fuskarsa ne yasashi kasa d’auke idanunsa daga gareta, tayayama zai iya jurewa? tayaya zai iya fasalta rad’ad’i da kuma k’unan da zuciyarsa keyi? kafun yanzu takasance wani b’arine na rayuwarsa, amma yanzun fa? shikenan ya rasata? yarasa Laylerh yarinyar da kowanni kwanan duniya sake jin sonta yake acikin zuciyarsa, tayaya zata d’auki abunda yayi mata? yasan dolene zataji zafi, saboda hakan da yayi tamkar bud’e mata sabon shafine dake cikin babban littafin k’addararta.

“I’m sorry Laylerh! I’m very sorry...!!� Ya fad’i hakan abayyane, cikin kuma muryarsa dake shaking take kuma bayyana tsananin damuwar da yake ciki.
Batare kuma da yayi aune ba yaji wani abu mai d’umi nabin fuskarsa, wanda ko tantama babu yasan cewa hawayene ke fita daga idanunsa, kasancewar kuma yayi kusa da Laylerh’n ne yasa hawayennasa ke d’iga akan fuskarta, ganin hakan da yayine kuma yasashi sake matsowa ahankali ya kawo fuskarsa gab da nata, cikin sanyi da damuwa ya d’aura bakinsa adaidai saitin forehead d’inta, batare da tunanin komae ba kuwa ya sauk’e mata wani irin hot kiss, dake bayyana condition d’in da mutum ke ciki.
Bayan yayi kissing forehead d’innata ne kuma, ahankali yad’an gangaro da kansa, wanda hakan yasa fuskarsu daidaita dana juna, har takai ga hancinsu ya had’e awaje d’aya.
Amatuk’ar sanyaye ya d’aura labb’an sa akan nata jajayen l’abban, atake kuma yayiwa lips d’innata wani irin kiss,wanda sanyi da kuma k’arfinsa yasa ta sauk’e k’akk’arfan ajiyar zuciya, saidai kuma kasancewar bacci take yasa bata bud’e idanunta ba.
Shikuwa Najeeb idanunsa ya k’ura mata yanajin sabon soyayyarta na sake shiga zuciyarsa.

Hak’ik’a ayanzu bazae tab’a iya misalta yanayin da yakejin kansa aciki ba, domin da ace yau shid’in ya kasance ajinsin mata ne ba maza ba, to da babu abunda zae masa shamaki da zama dirshan ya rera kuka har sai yaji zuciyarsa ta samu salama, amma kasantuwarsa Namiji ya zame masa tilas ya shanye hawayensa, duk da zaiyi kukan zuci amma dole ya tausashi kansa.
Janye jikinsa yayi tare da nesanta kansa daga gareta, ahankali ya soma jan jikinsa baya, saidai kuma har yanzu ya kasa d’auke idanunsa daga gareta, ahaka har ya k’arasa bakin k’ofar fita daga d’akin.
envelope d’in dake hannunsa ya yiwa wani irin rik’o tare da juyawa cikin sauri ya fice daga cikin d’akin.

*M.JAY*
Zabgegiyar kwalban wine d’in dake hannunsa yake ta faman jujjuyawa, kusan sama da mintuna 10 kenan yanzun da yake ta faman abu d’aya.
Asanyaye kuma akaro na barkatai ya sake sauk’e idanunsa akan kyakkyawan hoton da gaba d’ayansa ya cika gaban screen na laptop d’in companyn Apple dake gabansa, sosae ya k’urawa hoton idanu wanda akullum kuma akoda yaushe baya tab’a gajiya da kallonsa, sam koda da second d’ayane kuwa idanunsa basu tab’a jin gajiya da kallon kyakkyawar fuskar wanda ke jikin hoton ba, haka kuma ko wani bugun zuciyarsa da tunaninta yake tafiya.
Idanunsa masu kala da jin bacci ya lumshe tare da kai hannunsa ahankali ya shafa gefen cikinsa dake d’auke da k’awaraccen rubutu da akayisa kaman zanen tattoo.
Ci gaba da shafa gefen cikin nasa yayi yayinda kuma ahankali idanunsa keyi masa gizo da kyakkyawar fuskarta, yanayin hakanne kuma yasashi shagala dajin wani irin kasalalllen bacci.
Bisa dole haka ya kwanta flat akan had’add’en carpet d’in dake malale agaban makeken gadonsa, still kuma idanuna alumshe yana me sake shafa gefen stomach d’insa dake dauke da zanen rubutun sunanta.

Fitowarsa daga cikin part d’in nasune yasashi soma tafiya ahankali, tare kuma da aro jarumta ya sakawa kansa, gudun kada wani ya fahimci zallar yanayin damuwar dake kwance akan fuskarsa.
Isowarsa bakin k’ofar sashin Oum Ayush da yayine kuma yasashi tsayawa, tare dasa hannunsa ahankali yayi knocking k’ofar, shirun da yaji babu amsa ne kuma yasashi ci gaba da knocking door d’in.

Oum Ayush kuwa dake cikin kitchine jin ana knocking k’ofar falonne ya sata fitowa daga cikin kitchine d’in, cikin yanayi na d’an d’aga murya ta yanda za’a jiyota, ta bawa mai knocking door d’in daman shigowa.

Najeeb dake atsaye kuwa jin anbashi daman shigowa ne, yasa ahankali ya murd’a handle d’in k’ofar ya shigo.

Ganin Najeeb d’inne kuma yasa Oum Ayush dake tsaye ta fad’ad’a fari’arta, cikin sakin fuska tace.

“Najeeb sannu da zuwa, ae da ma shigowa kayi kai tsaye basai kayita knocking ba.�

Murmushin daya k’ak’alo da k’yarne ta d’an bayyana, cikin yanayin sanyi yace.

“Bansan bakya kusaba Oum Ayush shiyasa.�

Kai Oum Ayush d’in ta d’an jinjina, still fuskarta d’auke da murmushi tace.

“Badamuwa Ina kabaro Sarauniyar kuka da kuma shagwab’ar taka?�

Kansa ya sunkuyar k’asa tare kuma da kasa k’arasowa cikin falon, domin tambyar da Oum Ayush d’in tayi masa ba k’aramin karyar masa da zuciya tayi ba.

Oum Ayush kuwa jin Najeeb d’in bai amsa mata bane yasa ta d’ago kai ta kalleshi.
Lokaci d’aya kuma taji k’irjinta yayi wani irin bugawa, domin kuwa tsananin damuwa ta hango kwance akan fuskarsa dama duk wani yanayinsa.

“Najeeb lafiya kuwa? Mai yake faruwa naga duk yanayin ka ya sanja?�

Tayi masa tambayar tana meyi masa kallon tsab, yayinda kuma wani sashi na zuciyarta ke wani irin bugawa.

Najeeb da gaba d’aya gabb’an jikinsa ke rawa, asanyaye ya k’arasa shigowa cikin falon tare da neman waje ya zauna, saidai ya kasa koda d’aga ido ya kalli Oum Ayush d’in, saima shiru da yayi tare dasa tafukan hannayensa duka biyu ya rufe fuskarsa.

Hakanne kuwa yasa zuciyar Oum Ayush tsananta bugawa, hankalinta tashe tace.
“Please Najeeb ka fad’amin meyake faruwa? Ko wani abune ya samu Laylerh? dan Allah Ka fad’amin, domin yanayinka ya d’agamin hankali!�

Yanayin yanda ta k’are maganar cikin matsanancin damuwane yasa Najeeb d’an numfasawa, tare da zame hannayensa dake kan fuskarsa, araunace ya kalli Oum Ayush d’in, cikin kuma son bawa kansa k’warin guiwa da iya jure damuwa, murya asanyaye yace.

“Bansan tayaya zan iya jure k’alubalen da zae fuskanceni anan gaba ba Oum Ayush, akullum a kuma koda yaushe nasan cewa Laylerh tana da damuwa, duk da kasancewarta k’aramar yarinya kuma, amma kullum cikin kuka take, da yawan lokuta nakan gane cewar akwae abunda ke damunta, yakan hanata sukuni, sannan koda yaushe tunani take, sometimes murmushinta yakan zamo na dole ne, sannan tana da matsanancin rauni sosae, Bansan tayaya zata kalli abunda na aikata agareta ba, saidai nasan nan aikata hakan dan wata manufa ba, ahak’ik’anin gaskiya kawae nayi abunda nake ganin shine daidai!�

D’an tsagaitawa da maganganun nasa yayi ta hanyar Jan wani irin doguwar ajiyar zuciya.
Idanunsa wanda suka jajur ya rumtse tare dasa hannu ya kama chest d’insa, still asanyaye yace.

“Ina Son Laylerh sosae, saidai kuma amma yafini sonta, duk yanda nakai ga jin soyayyarta azuciyata shi fiye da haka yakeji, babu wani irin son da yake mata, domin ba wae sone na haka kawae ba, ba irin sone da kowa ya sani ba, Tabbas ni zan iya rayuwa babu Laylerh, domin ko ada daban santa ba nayi rayuwa cikin farinciki, shi kuma fa? bazae tab’a iya rayuwa babu itaba Bawae don soyayya kawae ba, no itace numfashinsa,rayuwarsa, dama zuciyarsa, duk yanda wani zai sota aduniya bayan son da yake matane, soyayyarta halittace acikin jikinsa da akayi wanda har abada bazae gushe ko goge ba, sannan halittace dake girma tana hab’aka akowanni rana bayan kuma kowani minutes, kullum zafi yakeji azuciyarsa haka itama, because zuciyoyin nasu abu d’ayane basu da banbanci da juna, mafarkinsa itace haka itama mafarkinta shine, ita cefa duniyarsa Oum Ayush, itace komae nasa, ban tab’a ganin irin wannan soyayyar ba, wanda komae zai faru da junansu sai d’aya daga cikinsu ya sani, Tabbas na yarda cewa Laylerh zanen k’addarar muce muduka biyun, amma nasa k’addarar tafi k’arfin nawa, hasalima Ba za’a tab’a had’awa ba, domin ni soyayyar Laylerh azuciyata kawae take, shi kuma soyayyartata rayuwarsace gaba d’aya, acikin jijiya da jini b’argo dama duk gangar jikinsa take, bazan iya jurewa hakanba Oum Ayush, domin sabodani kawae koda yaushe zunubi ake rubuta musu, aduk lokacin da sukayi tunanin juna, ko sukayi imagine junansu, k’warai nayarda cewa k’addara babu yanda bata juyawa rayuwar d’an adam, sannan na kuma yarda cewa komae rubutaccene kuma tsararrre, Dan haka ina fatan abunda na aikata ya zamo silar farinciki arayuwarsu!�

Ya k’are maganar cikin dauriya da kuma tsananin cijewa, asanyaye kuma ya d’an durk’usa agaban Oum Ayush wanda tunda ya fara maganganun nasa ta zuba masa ido.

“Kiyi hak’uri Oum Ayush bani da wani zab’i ne wanda ya wuce hakan, Dan Allah Na mik’a komae ahannunki kiyi k’ok’ari wajen ganin Laylerh bata sake shiga k’unci ba, Sam bansan tayaya ne zan fara fuskantarta da wannan maganan ba, Brain d’inta k’aramane saboda haka sam bai kamata na hautsuna tunaninta ba, sannan ban barta dan banasonta ba, Ina sonta sosae wallahi, koda yaushe da soyayyarta acikin zuciyata, yafini buk’atar ta sosae, domin akan fatar jikinsa ma sunantane arubuce, please Oum Ayush idan tayi kuka ki rarrasheta, domin ayanzu ita d’in batawa bace!!!�
Chapter 106 · 0% Book details