Sashe 88
Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kyawwwan idanunta ta runtse da k’arfi wanda hakan ya bawa hawayen dake cikinsu daman gangarowa kan fuskarta, cikin matsanancin tsoron da ya shigeta ne kuma, ta soma girgiza kanta ahankali, yayinda take kuma lokaci guda jikinta ya soma b’ari, tamkar wacce aka jonawa shocking, ahankali labb’an bakinta suka soma d’an motsawa, da’alama kuma wani abu take son fad’a daga bakinnata, amma takasa.
Ganin hakanne kuwa yasa Oum Ayush da gaba d’aya jikinta ya riga da yayi sanyi tasa hannu ta dafa kad’an Laylerh, cikin muryarta dake bayyana zallan tausayin ta tace.
“Ki kwantar da hankalinki Laylerh, domin kuwa Ina da yak’inin cewa da izinin Ubangiji mai sama da k’asa babu wani abu da ya samu Maleek, koda ma kuwa ace yana cikin wani hali na rashin dad’i, ayanzu addu’ar mu yake da buk’ata bawae kuka ko firgicewa ba, ki tashi mu k’arasa cikin asibitin kinji, Dan Allah Karki ce zakiyi kuka.�
Tak’are maganan nata tana me yunk’urin mik’ar da Laylerh’n tsaye, wanda tuni hawaye sun wanke mata fuska, yayinda wani hawayen na korar wani.
D’agota Oum Ayush d’in tayi, wanda hakan kuwa yasa tsab ta mik’e tsaye kamar yanda Oum Ayush d’in ta buk’ata, saidai kuma ko kad’an ta kasa iya daidaita nutsuwarta, wani irin tsalle k’irji da zuciyarta keyi kaman zasu fito waje, domin kuwa ta sake samun kanta acikin k’arin fargaba da kuma tashin hankali, asakamakon jin da tayi cewa M.Jay d’inta ne bashi da lafiya.
Cikin wata irin muryar dake shaking, kana kuma wanda take bayyana tsananin tsoron dake cikin zuciyarta, murya ararrabe tace.
“Tsoro Nakeji Oum Ayush, Wallahi tsoro nakeji, nasani dama tunjiya nakeji ajikina cewar wani abu zai sameni, nayi mafarki cewar Yah M.Jay yayi accident, amma kuma da na fad’awa Najeeb sai ya k’aryatani, nasani dama da yawan mafarkaina akansa gaskiya ne, wayyo Allah Na tayaya zan iya d’aukar wannan k’addaran? Tayaya zan iya jurewa? Tabbas nasan cewa aduniya babu wanda zaisan me nakeji ajikina aduk sanda wani abu na cutarwa ya samu Yah M.Jay, wallahi nayi imani cewa akansa zan iya mutuwa, Oum Ayush ki tab’a zuciyata kiji, Wallahi gab take da rabewa gida biyu, menakeji wazai san me nakeji babu, babu wanda zai gane hakan sai ni kad’ai, tabbas K’addarorin Ubangiji sun cika rayuwarmu ....� kasa k’arasa maganan nata tayi, saboda wani irin kuka daya so kwace mata.
Hakanne kuma yasa Oum Ayush tayi saurin sanya hannu ta toshewa Laylerh’n baki, domin kuwa itama tuni idanunta sun ciko da kwalla, yayinda wani irin matsanancin tausayin Laylerh’n ya cika mata zuciya, k’warai tasan cewa akwae wata soyayya me tsananin zafi dake tsakanin Laylerh da Maleek d’in, amma sam batasan da cewar k’arfin d’i maucewar Soyayyar tasu har takai haka ba.
Cikin son arawa kanta jarumta da kuma bawa Laylerh’n k’arfin guiwa tace.
“Ya isa haka Laylerh, kuka da fad’an wasu maganganu ba naki bane, muje ciki kawae.�
ta k’are maganan agajarce tana me kuma kama hannun Laylerh’n batare da ta jira ta bakinta ba suka kutsa kansu cikin asibitin, domin dama tuni Abbou Khareem yayiwa Oum Ayush d’in kwatancen d’akin da aka kwantar da Maleek d’in kuma ta gane, shiyasa ma bata tsaya tambayar kowa ba, kaitsaye suka nufi sashin da zai sadasu da d’akin, duk da cewar wajen privet waje ne babu yawan hayaniyan mutane da kuma sawunsu.
K’warai da gaske Laylerh bata gamsu da cewar akwae wani abu wai shi tsoro, fargaba da kuma bugun zuciya ba saida ta ga sun tsaya adaidai bakin wata k’ofa wanda take akulle gam, ahankali tasa hannu ta dafe daidai saitin zuciyarta dake wani irin bugawa akaron na barkatai, lokaci d’aya kuma taji numfashinta nayin sama da k’asa cikin yanayin fusga tamkar wanda zae d’auke gaba d’aya.
Daidai lokacin ne kuma Oum Ayush da ita kanta jikinta ke ta faman tsuma tasa hannu ta bud’e k’ofar d’akin, ahankali ta kutsa kanta ciki, yayinda bakinta ke d’auke da sallama.
Su Abbou Khareem dake zaune akan wasu fararen kujerune suka amsa mata, ciki kuwa harda Najeeb wanda da zuwansa asibitin zuwa yanzu da yake cikin d’akin bai wuce 14 minutes ba, kasancewar lokacin da Abbou Khareem ya k’iarasa ya fad’a masa yana kusa da asibitin shiyasa bai wani d’au lokaci ba ya taho.
Turus haka Oum Ayush d’in taja ta tsaya adaidai lokacin da idanunta suka sauk’a akan Maleek dake kwance flat akan gado kamar gawa.
Cikin muryarta da tayi sanyi sosai, kana cike kuma da tausayin Maleek d’in tace.
“Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un!�
Kalmar da ta fad’a kenan wanda ya sa zuciyar Laylerh dake waje sake harbawa da k’arfi.
Wanda kuma sanadin jin hakan ne ya bawa hawayen dake cikin idanunta daman gangarowa kan k’uncinta, ahankali cikin wani irin yanayin da ita kanta bazata tab’a iya fassarasa ba, ta soma d’an jan k’afafunta dake rawa zuwa cikin d’akin.
K’afarta ta fara sakowa cikin d’akin kafun kanta ya biyo baya, tana shigowa kuwa idanunta wanda ganinsu ya d’an disashe saboda hawayen dake cikinsu, suka sauk’a akan mutumin dake kwance, wanda tayi imani cewa koda makancewa tayi Indai yana kusa da ita to babu abunda zai hanata iya zayyano halittar kyakkyawar fuskarsa dama murd’add’iyar surar jikinsa dake cike da matsanancin kwarjini.
Hawayen dake cike a cikin idanunnata ne suka samu daman soma yi mata ambaliya akan k’uncinta, hakanne kuwa yasa ganinta ya sake disashewa, yaza mana bata iya tantance yanayin tsarinsa.
Ahankali ta d’aga k’afafunta wanda take jinsu kamar an sark’e mata su da igiyan kaca, cikin yanayin dake bayyana zallan rashin nutsuwa da kuma firgicin da take ciki, ta shiga takawa kaitsaye zuwa inda Maleek d’in ke kwance, tayi hakan kuwa batare da ta iya rarrabe inda take jefa k’afafun nata ba.
Jin sautin tafiyan nata ne kuma yasa duk hankalin su Abbou Jaheed ya dawo kanta, ganinta acikin mawuyacin hali yasa suka zuba mata ido, saidai kuma dukansu kaman an kulle musu baki. babu wanda ya iya koda k’iran sunanta ne, haka suka zuba mata idanu.
Laylerh kuwa tunkafun ta k’arasa kusa dashi taji wani irin jiri mai k’arfi na neman kada ita, saidai sam a irin yanayin da take jin kanta aciki batajin zata iya bawa wani abu daman katse mata hanzarinta nason zuwa garesa.
Isowarta jikin gadon nasa da tayi kuwa yayi daidai da sauk’an wasu hawaye masu tsananin zafi akan fuskarta.
Ahankali kana kuma cikin rawan da hannayenta dama duk jikinta keyi, ta matso gab dashi, hannunta takai ahankali ta d’aura akan kyakkyawar fuskarsa da ko d’igon tabo ko kwarzane babu akanta.
Batare kuwa da tasan me takeyi ba ta soma d’an yawo da hannun nata akan kyakkyawar fuskarsa harzuwa kan faffad’an chest d’insa dake abayyane, kasancewar doctors d’in sun cire masa rigar dake jikinsa, domin duk ta b’aci da jini, kuma akwai y’an kananun raunuka da yaji, wanda dole sai sunyi treating d’in wajen, shiyasa ma gaba d’aya suka rabashi da rigarsa.
Isowar hannunta da har yanzu keta faman b’ari daidai kirjinsa inda zuciyarsa take ne yasa gaba d’aya ilahirin jikinta ya sake d’aukan rawa, har yakai ga hak’waranta na kartan juna is....
Da k’yar cikin wata irin murya me d’auke da wani rikitaccen amo, sannan kuma mai fitar da shaking sound d’in dake d’auke da matsanancin raunin zuciya tak’ira sunansa, in a slowly tone.
“Y...A...H M...J...A...Y!!�
Yanda sauti da kuma amon muryar nata ya fita ne yasa su Abbou Jaheed kafesu da ido basa ko k’yaftawa.
“Y...A...H M...JAY......!!!�
Still Ta sake k’iran sunan nasa, saidai kuma awannan karon amon muryar nata yafi na farko fitarda rauni.
Again bud’e labb’an nata tayi,da niyar sake k’iran sunansa saidai kuma awannan karon harshenta bazae tab’a iya motsa kansa ba, domin kuwa takai wani stage da yin maganarta zai iya haifar mata da d’aukewar numfashi.
Ahankali ta sauk’e tattausan tafin hannunta akan nasa hannun, batare kuma da tunanin komai ba ta d’ago hannun nasa tare da kawosa daidai saitin bakinta, labb’an bakinta ta d’aura akan lallausar fatar hannun nasa, cikin wani irin yanayi ta fashe da wani kuka me tsananin ban tausayi da kuma tsayawa arai, duk da cewar kuwa har yanzu jikinta na b’ari, amma hakan bai hanata rik’e hannun nasa da k’arfi, ta shiga rera wani irin kuka me sauti da kuma tsuma zuciya ba, tabbas kukan da ya amsa kuka Laylerh’n keyi, ma’ana irin wanda ke fitowa daga cikin zuciyar mutum me d’auke da matsanancin rauni, haka zalika kuma kukane dake bayyana yanda wanda keyinsa yakeji acikin rai da zuciyarsa, sannan kuma kukane da zautattun mutanen da zuciyarsu ta narke acikin zazzafan soyayya keyi, Kuka take irin wanda bata tab’a yinsa ba aduniya, kukan da ya firgita zuciyar su Abbou Jaheed, kukan daya saka kowannensu acikin matsanancin shock, har ya kai ga sun tsaya kallonta tamkar gumaka babu wanda yake motsi acikinsu.
Laylerh kuwa kukanta take sosae wanda gaba d’aya sautinsa ya cika d’akin, yayinda kuma har yanzu take rungume da hannun Maleek, wanda tayi masa wani irin rik’o, tun tana fitar da sheshshek’a kuwa acikin kukan nata har ya zamana ta fara shid’ewa, yayinda numfashinta ya shiga ja baya yana me k’ok’arin d’aukewa.
Ganin hakane kuma yasa Oum Ayush da tuni hawayen tausayin Laylerh Da Maleek d’in sun zubo kan k’uncinta, cikin rawan murya ta k’ira sunan Laylerh’n, da ko kad’an bataji k’iran Oum Ayush d’in ba.
“LAYLERH.�
Oum Ayush ta sake k’iran sunanta akaro na biyu, tare da soma k’ok’arin danne kukan da ya zo mata.
Still Laylerh bata amsa taba, bata kuma tsaya da kukan nata dake nuna musu zaucewarta ba, haka kuma har yanzu tana rik’e da hannun Maleek d’in bata sake ba.