Sashe 91
Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abbou Jaheed kam jikinsa amatuk’ar sanyaye ya fita daga office na Dr. Mouhammad d’in, kaitsaye d’akin da aka kwantar da Maleek d’in ya nufa, haka yakejin duk gaba d’aya gangar jikinsa ba k’arfi, domin kuwa fargaba tausayi da kuma rauni su suka riga suka cinye masa zuciya.
Isowarsa jikin k’ofar d’akinne yasa shi soma k’ok’arin daidaita nutsuwarsa gudun kada su Abbou Khareem su gane cewar yana d’auke da damuwa, ahankali ya tura k’ofar d’akin ya shiga, bakinsa d’auke da sallama.
Oum Ayush da kuma Abbou Khareem ne suka amsa masa, sai kuma Fou’ad da ya amsa murya kasa kasa, saboda damuwar dake kwance acikin zuciyarsa.
K’asa Abbou Jaheed d’in yayi da kansa ba tare da ya yarda idanunsa sun sauk’a akan Maleek dake kwance ba, domin kuwa yasan matuk’ar ayanzu ya d’aura idanunsa akan Maleek d’in to ko shakka babu kukane me k’arfi zai k’wace masa.
Oum Ayush dake zaune Laylerh na bisa cinyarta ya kalla, asanyaye yace.
“Oum ki tada Laylerh ku koma gida, nida Abbou Khareem zamu zauna anan, kaima Fou’ad akwai buk’atar kaje kad’an huta idan yaso ko zuwa anjima saika dawo, kema Oum zaki iya dawowa anjima ko akwai wani abu da Maleek d’in zai buk’ata bayan ya bud’e idanunsa, idan ba damuwa sai a taho masa dashi.�
Numfash Oum Ayush tad’an fesar, kana asanyaye tace.
“To.� Yayinda acikin zuciyarta kuwa sam bataji tanason barin asibitin batare da taga farfad’owar Maleek d’in ba, saidai amma sam batason yiwa Yayan Mijinnata musu shiyasa.
Ahankali tasa hannunta ta d’an shiga tashin Laylerh’n, cikin sa’a kuwa Laylerh ahankali ta bud’e idanunta wanda suka kumbura suntum saboda kukan da tayi.
“Tashi muje gida ko Laylerh.� Oum Ayush ta fad’a tana me gyarawa Laylerh’n zaman lufayan dake jikinta.
Laylerh kuwa jin abunda Oum Ayush d’in ta fad’ane yasa ahankali ta girgiza kanta, saboda har yanzu bata dawo daidai ba, asanyaye cikin muryarta da ya d’an dashe tace.
“Bazan iya tafiya ba Oum Ayush, bazan iya koda fita daga d’akin nan ba, har sai naga Yah Maleek ya bud’e idanunsa yana numfashi kaman yanda mukeyi, sannan kuma yana motsa jikinsa kamar yanda muke motsa namu jikin.�
*(Dan Allah Banason yawan k’orafi, Labarin Laylerh Maleek ahaka yake, komai dake cikinsa haka yake, sannan kuma babu wani wanda yafi k’arfin karb’an tarin k’addarorin Ubangiji, da gani har kowa, abun so dai shine Allah Ya had’amu da kyakkyawar k’addara ako da yaushe.)*
*Saturday13/2/2021*
*8:37 pm*
2/16/21, 9:12 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*
*Writting By*
fatymasardauna
*Not editing*
*Chapter 52
Oum Ayush dake tsaye, wanda jin abunda Laylerh’n ta fad’a ya sa ta sauk’e wani irin sassanyar ajiyar zuciya, k’warai ta d’anyi mamakin jin hakan daga bakin Laylerh’n, amma kuma sanin hak’ik’anin abunda ke cikin zuciyar Laylerh’n, yasa babu wani amfanin mamakinnata. D’an gyara tsayuwarta tayi, tare da sa hannu ta dafa kafad’an ta, cikin yanayin tausasa murya da kuma salon da tasan zai taimaka mata wajen jawo hankalin Laylerh’n ahankali tace.
“Kiyi hak’uri mutafi gida kinji, na miki alk’awarin cewa anjima kad’an zamu dawo, ko bakyaso idan Yah M.Jay d’innaki ya bud’e idanunsa, kuma yaji yana jin yunwa yaci abinci ne? kinsan dole dae zaiji yunwa ko? saboda haka muje gida ki tayani mu dafa masa abinci mai dad’i, nasan idan ya farfad’o zaiji dad’i sosae.�
Jin hakanne yasa ta d’anyi jim, tare kuma da d’ago kanta ahankali ta kalli Maleek d’in da har yanzu ke kwance kaman gawa, yayinda wata na’ura me yanayin computer dake gefensa ke tafiya yanda ya dace, wanda kuma acikin na’urar ne ake iya ganin bugun zuciyarsa.
D’an guntun hawayen daya fito daga cikin idanunta ta share, asanyaye ta d’an karyar da wuyanta gefe, cikin muryarta da har yanzun bata dawo daidai ba tace.
“Tsoro nakeji Oum Ayush, banason bayan natafi wani abu ya samesa, yanzu ma haka nasan yanajin zafi, ki kalli jikinsa fa kiga, duk ya d’anji rauni glasses duk sun caccaka masa jiki, tayaya ma zai misalta irin wannan zafin da yakeji? ko yanzu ma me yakeji? Nasan ma....� Kasa k’arasa maganan nata tayi, sakamakon wani kuka daya so k’wace mata, wanda bisa dole hakan ya tilasta mata lumshe idanunta, take kuwa ruwan hawaye masu tsananin zafi suka sauk’a akan kumatun ta.
Wani abun mamaki kuwa kusan atare hawayen dake cikin idanun nata, da kuma wanda suke cikin idanun Abbou Jaheed suka zubo, wanda duk yanda yaso hana hawayennasa fita ya kasa, saboda tsananin tausayin Maleek d’in da yakeji yasa gaba d’aya ya kasa controlling rauninsa, hak’ik’a ayau d’in da ace shi ba babban mutum bane me yawan shekaru da sanin ya kamata ba, to da ba abunda zai hanasa zama yayi kuka sosai kamar yanda k’ananan yara keyi, saidai kuma babu yanda ya iya, ya zame masa dole ya tausashi zuciyarsa, saboda bai isa hana Allah gudanar da Ikonsa ba.
Saurin saka hannunsa yayi ya share hawayennasa tun kafun su lura da hakan, saidai kuma abunda bai sani ba shine, tuni Abbou Khareem ya ga hawayennasa, domin kusan akan idanunsa ma suka zubo.
Oum Ayush kuwa hannu takai ta sharewa Laylerh hawayen dake kwanace akan fuskarta, batare kuma da ta jira cewar kowanne daga cikinsu ba ta jawo hannun Laylerh’n tare da mik’ar da ita tsaye, anutse ta nufi hanyar fita daga cikin d’akin, ba tare kuma da ta sake hannun Laylerh’n ba, haka suka fice daga cikin d’akin.
Fou’ad dake zaune Abbou Jaheed ya kalla, cikin yin k’asa da murya yace.
“Fou’ad kuje ku huta, ka kai su Laylerh gida, zaka iya dawowa anjima kaima.�
“To.� Kawai Fou’ad yace kana asanyaye ya mik’e daga zaunen da yake, na’urar dake bayyana bugun zuciyar Maleek d’in dake kwance ya kalla, kafun ahankali ya sauk’e ajiyar zuciya tare dasa kai ya fice daga cikin d’akin.
Kamar rak’umi da akala haka Laylerh kebin Oum Ayush dake rik’e da hannunta, har zuwa wajen da sukayi parking motarsu.
Gefen me zaman Banza Oum Ayush ta bud’e mata, jikinta amatuk’ar sanyaye ya shiga ta zauna, tare da juya kanta tana me kallon cikin asibitin, hakanan takeji ajikinta kamar idan tayi nesa da asibitin wani abu zai sake samun Maleek, sam Allah Yasani har acikin zuciyarta bataso ta fiya ba, amma babu yanda zatayi.
Isowar Fou’ad garesu ne yasa Oum Ayush d’agowa ta kalleshi, asanyaye tace.
“Fou’ad Ina kuma zakaje, badai kaima tafiya zakayi ba?.�
Gajerar ajiyar zuciya Fou’ad d’in ya sauk’e, cikin kuma yanayin nutsuwa yace.
“Abbou Jaheed yace nazo nayi driving d’inku, amma ba damuwa zuwa anjima kad’an zan dawo, kafun nan ma nasan Maleek d’in ya dawo hayyacinsa.�
Kai Oum Ayush ta jinjina cike da gamsuwa, take kuwa ta mik’a masa makullin motar, tare da bud’e murfin motar ta shiga gidan baya.
Shi kuwa Fou’ad b’angaren driver ya shiga, anutse ya tada motar suka bar farfajiyar wajen.
Tunda suka d’auki hanya kuwa babu wanda yace da d’an uwansa k’ala, domin kuwa ko wannensu da abunda yake sak’awa acikin rai da zuciyarsa, musamman Laylerh da gaba d’aya ma tunaninta baya jikinta.
Ahaka dai suka k’araso gaban makeken gate d’in gidan, jin k’aran horn d’insu ne kuma yasa take mai gadi ya wangale musu wawakeken gate d’in, anutse Fou’ad ya tura hancin motar ciki, tare da neman waje yayi parking.
Kusan atare dukansu suka fito daga cikin motar, ganin yanda Laylerh’n ke layi kaman zata fad’i ne yasa Oum Ayush tayi saurin rik’o hannunta, kana cikin kulawa tace.
“Laylerh ya dai kina lafiya kuwa?.�
Kanta tad’an girgiza tare dasa hannu ta dafe daidai saitin kanta dake masifar ciwo har wani sarawa yake kaman zai rabe gida biyu haka takeji.
“Kaina ne yake ciwo sosae.�
Tafad’i hakan cikin muryarta dake shaking.
“Ayya sannu to kije kisha magani sai ki kwanta kinji, dole dama da irin wannan kukan da kikayi sai kanki yayi ciwo.�
Cewar Oum Ayush tana me k’ok’arin sake hannun Laylerh’n.
Ahankali ta soma d’an taka k’afafunta, saidai bai wuce taku uku tayi ba ta tsaya tare da juyowa ta kalli Oum Ayush d’in, cikin wata irin sassanyar muryar dake bayyana rauni tace.
“Dan Allah Oum Ayush kada ki koma kibarni idan zaki koma ki gayamin!�
Yanayin yanda ta k’are maganar cikin karyar da wuya ne yasa Oum Ayush ta sake jin matsanancin tausayinta, asanyaye tace.
“Insha Allah Zan gaya miki, kuma kema ki tabbatar da cewar kinsha magani.�
“To.�
Tace tare da juyawa cikin tafiyarta na rarrabe hanya ta nufi sashin su.
Ajiyar zuciya Oum Ayush ta sauk’e tare da kallon Fou’ad daya kafe Laylerh’n da idanu baya ko k’yaftawa, yayinda idanunsa kuwa suka zama jajur dasu.
“Fou’ad.�
Oum Ayush ta k’ira sunansa cikin tausasa murya.
Jin K’iran da Oum d’in tayi masa ne kuma ya sashi d’auke idanunsa daga kan Laylerh wanda harma ta isa sashinsu, dawo da kallonsa ga Oum Ayush d’in yayi, cikin yanayin bayyana damuwar dake cin zuciyarsa yace.
“Yanzu shikenan Oum Ayush haka rayuwar Laylerh da Maleek zata ci gaba da tafiya? sai yaushe ne zasu samu farinciki arayuwarsu? sai yaushe abunda dukkanin su ke b’oyewa zai zama kammalalle? Tabbas Ina matuk’ar jin tausayinsu, musamman Laylerh da ta kasance yarinya k’arama dudu du ko 20years bata cika ba, amma k’addara nata wasa da rayuwarta, dama duk wani burinta, lallai na gamsu cewa akwae abunda Allah Ya b’oye atsakanin Laylerh da Maleek, domin kuwa abune me girman gaske soyayyar da Laylerh keyiwa Maleek, domin na fahimci cewa bawai da iyaka zuciyarta take son shiba, harma da gaba d’aya rayuwarta, wata soyayyace ta daban atsakaninsu bawai kuma irin normal soyayya da kowa ya sani ba, soyayyace ta musamman wanda Ina da tabbacin cewa har abada bazata tab’ayin k’arshe ba.�