← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 144

Sashe 31

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

MALEEK.  
Duk yanda yaso daidaita nutsuwarsa ya kasa, baisan meyasa  jin duk wata magana da ta shafi auren Laylerh'n ke matuƙar haukata masa tunani ba,   idanunsa da sukayi ja ya lumshe tare da sa tafukan hannunsa ya rufe kyakkyawar fuskarsa,  lokaci ɗaya duk wasu maganganun da Abbou Jaheed  da kuma Alhaji Ahmad ɗin keyi, suka daina shiga cikin kunnuwansa, domin gaba ɗaya zuciyarsa tatafi izuwa wani waje na daban.             
Abbou Jaheed wanda suka gama tattaunawa da Alhaji Ahmad Rufae, akan maganar auren Laylerh'n ne ya ɗago da kansa, tare da dawo da kallonsa ga Maleek wanda har yanzu bai buɗe fuskarsa dake arufe da tafukan hannunsa ba.          
"Maleek!." Abbou Jaheed ya ƙira sunansa cikin nutsuwa.              
Jin sautin muryar Abbou Jaheed ɗin acikin kunnensa ne ya sashi ɗan janye tafin hannunsa daga kan fuskarsa, idanunsa da suka kaɗa sukayi jajur ya buɗe haɗi da yin ƙasa dasu, kasancewar sam bayaso ayanzun kowa ya fahimci irin situation ɗin da yake ciki, cikin wata irin murya dake son ɓoye damuwarsa yace. 
"Na'am."    
Ɗan zuba masa idanu Abbou Jaheed ɗin yayi, ahankali ya sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa. "Sama da shekara 2 kenan yanzu dana zuba maka ido inason naga gudun ruwanka, saidai kuma na lura da cewa kwata kwata babu tunanin aure acikin ƙwaƙwalwarka, saboda haka kasa aranka cewar, kamar yanda na zaɓawa Laylerh Miji, na kuma sa aurenta lokacin ɗaya,  haka kaima zanyi maka, saboda haka ya rage naka a iya lokacin daya ragema ka nemo matar aure, idan kuma ba haka ba dakaina zan nemo maka wacce zata dace dakai."           
Jin abun da Abboun ya faɗane yasashi ɗago kansa, hakanan yaji kalaman Abbou Jaheed ɗin kaman tatsuniya, duk da kuwa yasan cewa duk abun da Abbou Jaheed ɗin yafaɗa tabbas zai iya aikatawa, amma kwata kwata bayaji ajikinsa cewar zai rayu da wata mace.        
Idanunsa ya ɗan lumshe tare kuma da sakin wani murmushi, wanda iya kansa laɓɓan bakinsa, tabbas ya yarda da cewar, muradi da kuma fata ɗaya ne acikin zuciyarsa, wanda kuma rashin samun cikar burinsa daidai yake da ƙin yin aurensa har abada.
Sama da 10 years kenan daya ɗauka yana dakon abubuwa da yawa acikin rai da zuciyarsa,  tun baisan me yakeyi ba, tun kuma baigane me yake ji ba, har hakan ya cakuɗa da numfashinsa, ya zamanto bugun zuciyarsa, duk wani zafi da yakeji ya jure, ako yaushe akuma ko wacce rana buri ɗaya ne ke yawo acikin zuciyarsa, wanda kuma ayanzu wannan fata da burin suka cika da tarin ƙaddarori masu wuyar ɗauka.   
Ahankali ya miƙe tsaye dan bayajin zai iya cigaba da zama acikin falon.     Batare daya cewa kowannensu ƙala ba, kansa tsaye ya nufi hanyar ƙofar fita daga cikin falon.
Hakanne kuwa yasa duk suka bisa da kallo.     
Saidai kuma banda Najeeb wanda ayanzu yake ƙoƙarin gaskata zargin dake cikin zuciyarsa, saidai kuma koma meye bayajin zai iya barin abun da ayanzu ya gamsu cewar lallai yanaso.             

Koda ya fita daga cikin falon kaitsaye compound É—in gidan ya nufa, inda ma aikata kota ina keta hidimomi, masu bawa flowers ruwa, da masu wanke cars duk suna aikinsu.
Direct babban parking space É—in gidan ya nufa, wanda kuma ananne tarin motocinsa ke fake.
Abdoul dake zaune ganin Ogan nasa ya fito, yasa cikin sauri ya taso tare da ƙarasowa inda yake, cikin girmamawa yace.  "Good Morning Sir."  
Kansa kawai ya iya jinjina wa Abdoul ɗin, wanda hakan ke nuna cewa ya amsa.  ƙarasawa jikin wata haɗaɗɗiyar sabuwar motarsa ƙiran Mercedesbenz CLA 35 yayi, ganin hakanne yasa Abdoul gane cewa yau ogan nasa mercedes ɗin yake son hawa.
Cikin hanzari kuwa ya ciro key ɗin motar, tare da buɗewa M.Jay ɗin murfin motar ya shiga,  shikuwa Abdoul kamar yanda ya saba, nan wajen zamansa na driver ya shiga tare da murzawa motar key, cikin ƙwarewa ya fitar da ita daga parking space ɗin, maigadi dake tsaye kuwa  yana ganinsu ya wangale masu gaba ɗaya gate ɗin gidan,  cikin ƙwarewa Abdoul ya cilla hancin motar waje, sanin inda ogan nasa yafi zuwa idan yana cikin garin na Abuja ne,  yasa batare daya tsaya wani ɓata lokoci ba ya miƙi hanyar da zata kaisu Maitama Estate.   

Ɓangaren Laylerh kuwa tun komawarsu class ta samu kanta da kasa iya aiwatar da komai, hakanan ta zama wata so silently, yayinda gaba ɗaya tunani da nutsuwarta suka ƙaura izuwa wani waje na daban, sanadin hakan kuwa yasa duk wani malamin da zai shigo yi musu lecture bata taɓa fahimtar komai akan hakan, saboda hakanan takeji kaman anshafe mata ƙwaƙwalwa.        
Yayinda acikin ranta kuwa fata da kuma burin son sanin haƙiƙanin abun dake cikin zuciyarta ne, duk ya hanata sukuni, haka kuma duk yanda Teemah taso Laylerhn ta saki jikinta kasawa tayi, duk kuwa yanda taso ta ɓoye damuwarta ta kasa.
Ahaka har aka tashe su daga makarantar, kamar kullum kuma kamar koda yaushe tare suka jero suna tafiya, ahaka har suka fito daga cikin makarantar, suna fitowa kuwa kowaccensu tasamu driver na jiranta. 
Laylerh da tatafi zata shiga mota ne, Teemah ta riƙo hannunta, wanda hakan yasa tafasa shiga motar ta juyo ta fuskanci Teemah'n.  
Idanu Teemah ta ɗan lumshe cikin sanyin muryar dake bayyana tausayin ƙawarta ta tace.  
"Please Laylerh ki daina damuwa kinji, kisa aranki cewa auren da Abbou Jaheed zai miki shine mafi alkhairi agareki, kuma nasan Abbou Jaheed bazai taɓa zaɓa miki mijin daya san zai cutar dake ba, dan Allah ki daina sa damuwa aranki kinji please!!."  
Teemah'n ta ƙare maganan tana me haɗe hannuwanta biyu waje ɗaya, wanda hakan ke nuna alaman roƙo.     Ayanayin da take ciki yasa batajin zata iya cewa Teemah'n komai, domin yanzu babu abun da takeson gani da ji, kamar M.Jay. ɗan lumshe idanunta tayi tare da jinjinawa Teemah'n kai alaman  "To."  Murmushi Teemah tayi mata, sannan ta juya ta nufi wajen da motar gidansu ke fake.   
Asanyaye ta shige motar tare da É—an kwantar da kanta asaman kujera tana maida numfashi, ahaka drivern yaja suka bar harabar makarantar.

Maitama Estate.

Tsaye yake agaban wani  haɗaɗɗen glass frizer, yayinda hannunsa ke riƙe da zungureriyar kwalban wine, sai kuma wani ɗan ƙaramin glass cup da ya riƙe a hannun damansa, ahankali yake ɗan jujjuya cup ɗin, wanda ya riga daya zuba wine ɗin aciki, yayinda gaba ɗaya tunaninsa ya tafi izuwa wani waje daban.    
Idanu wani haɗaɗɗɗen gayen dake zaune akan ɗaya daga cikin kujerun falon ya zuba masa, *Fou'ad* kenan tabbas yana mamakin hali irin na abokin nasa, ajiyar zuciya ya sauƙe akaro na barkatai, ɗan gyara zamansa yayi cike kuma da ƙaunar abokin nasa yace.   "Meyasa kake ɓoye sirrin dake cikin zuciyarka Maleek? batun yauba nasan kana ɗauke da damuwa, wanda ko da ace baka faɗa ba, gaba ɗaya yanayinka ya nuna hakan, meyasa kake ɓoye abunda ke cikin zuciya da ƙirjinka?, meyasa kake ƙoƙarin haramtawa kanka abun da Allah Ya halatta ma? ya kamata ka farka daga wannan nannauyan baccin da kake, because yanzu rayuwa ta sanja, then zurfin ciki baya kawo komai sai dana sani, meyasa ako da yaushe kake tauyewa zuciyarka haƙƙinta bayan kuma kasan ta kamu da SO matsananci?."          
Idanunsa ya ɗan lumshe  tare kuma da buɗesu alokaci guda, Ajiye kwalban wine ɗin dake hannunsa yayi, ahankali cikin nuna halin ko in kula ya ƙaraso cikin falon, kan wata kujera dake facing na Fou'ad din ya zauna, ba tare kuma da ya kalli Fou'ad ɗinba, cikin husky voice ɗinsa  yace.  "So? menene kuma SO?... its in possible, because i dont have any feeling in my mind."                

Murmushi Fou'ad yayi domin shi yariga daya san waye Maleek, ya kuma san komai agame dashi, taurin rai dana zuciya tamkar aminai suke awajensa, kwata kwata baya taɓa ɗaukan kuskurensa, always gani yake shi akan daidai yake.     
Miƙewa tsaye Fou'ad ɗin yayi tare da ƙarasawa wajen da Maleek ɗin ke zaune, hannunsa ya ɗaura akan shoulder ɗinsa, cikin kulawa yace.  "SO ne Maleek, ni nayi imani cewa akwai so acikin zuciyarka, meyasa kake ɓoyewa? meyasa bazaka iya faɗa ba? Meyasa....."        
"Enough Fou'ad, Enough is Enough please!!."  Maleek din  yafaɗi haka ta hanyar katse Fou'ad daga maganan da yakeyi.  Bayajin zai iya jurewa jin kalaman da yawancin lokuta Fou'ad ɗin ke faɗa masa, wannan dalili yasa sometimes bayason zuwa wajen Aboki kuma Aminin nasa, saboda ako yaushe so yake saiya ƙuresa.   Wayayoyinsa dake aje kan table ya ɗauka, batare da ya kalli Fou'ad ɗin ba ya juya ya nufi hanyar fita daga falon.   
Da kallo Fou'ad ya bisa har ya fice daga cikin falon. Murmushi yayi tare da komawa kan kujera ya zauna, daman ya sani ako da yaushe Maleek ɗin baya karɓan gaskiya aduk yanda tazo masa.              
Abdoul dage zaune aharabar gidan Fou'ad ɗin kuwa, ganin yanda Ogan nasa ya fito kaman afusace ne yasashi saurin tashi tsaye, cikin hanzari ya ƙarasa jikin mota, tare da buɗewa Maleek ɗi murfin motar yashiga. 
Shiɗin ma shiga yayi, yayinda tun kafun yaja motar yayiwa gateman alaman ya buɗe Musu gate ɗin zasu fita, ba ɓata lokaci kuwa gateman ɗin ya wangale musu gate ɗin gidan suka fice.     
Koda suka fara tafiya lumshe idanunsa yayi, yanamejin yanda sanyin A/C ke ratsa dum jikinsa.
kalmar "SO" da Fou'ad ya faɗa ita keta yi masa yawo acikin ƙwaƙwalwarsa,  hakanan yaji ya tsani kalmar domin yayi imani cewa abun da yakeji acikin zuciyarsa ya fi karfin aƙirasa da sunan SO, tabbas kalmar SO tayi kaɗan ta ɗauki nauyin abun daya jima yana sukar zuciyarsa.
Chapter 31 · 0% Book details