← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 144

Sashe 50

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahankali Fou'ad yasoma ƙoƙarin ɗaga Maleek ɗin, saidai kuma yanayin yanda jikin Maleek din ke asake ne yasa Fou'ad ɗin kasa ɗaga sa shi kaɗai, ganin hakane yasa Najeeb wanda isowarsa wajen kenan cikin matsanancin damuwa ya sa hannu suka ɗaga Maleek ɗin.
Direct cikin gida suka nufa dashi, saidai kasancewar farfajian gidan cike yake da mutane ƴan biki dake ta hada hada, yasa suka bi ta ƙofar baya, wanda direct ya kaisu har zuwa  sashinsa.
Kaitsaye bedroom É—insa suka wuce dashi, tare da kwantar dashi akan makeken gadonsa, wanda yaji bedsheet na alfarma.
Su Abbou Jaheed da suka biyosu ne suka tsaya sukayi jigum jigum, kallo É—aya zakayiwa fuskar Abbou Jaheed ka fahinci cewa yana cikin tashin hankali da kuma tsananin damuwa.
Abbou Kareem daya cire hulan kansa ya soma fifita dashi ne ya ɗago kai ya kai dubansa ga Fou'ad wanda ke tsugune agaban gadon, cikin muryarsa data bayyana tsananin damuwarsa yace.    
"Fou'ad meke damun Maleek ne, dama tun can bashi da lafiya har haka, amma ba wanda ya sani?."

Fou'ad ko jin tambayar da Abbou Kareem ɗin yayi masa ne yasashi fesar da wani gauron numfashi, cikin yanayin damuwa yace. 
"Bani da masania akan wannan rashin lapiyan nasa Abbou Kareem, hasalima lafiya ƙalau muka fito daga gida, bansan meyake faruwa dashi ba, aƴan kwanakin nan gaba ɗaya bana gane masa, domin yau kwana biyu kenan da muke tare dashi, amma ko abinci bayaci, abun dana lura dashi kawai shine baya cikin farinciki, lallai akwae abun dake damunsa." 
Yafaɗi hakan yana me ƙoƙarin danne zuciyarsa, domin ahaƙiƙanin gaskia ingiza sa take akan yafaɗi haƙiƙanin abun dake damun Maleek ɗin, saidai kuma sanin da yayi cewar faɗan gaskiyar lamarin bazai haifar da komae ba ne yasashi rufe bakinsa, domin tuntuni aikin gama ya riga daya gama, bayyana sirrin zuciyar Maleek ɗin ba abun dazai haifar sai rugujewar mutumta ka, da kuma ɓata alaƙa, dan Allah Yariga dayayi tsarinsa.
Jin abun da Fou'ad din ya faɗane yasasu yin shiru, tare da zubawa Maleek ɗin dake kwance idanu, wanda kuma sai alokacinne suka lura da yanda ya rame, amma kuma fatarsa ta ƙara haske sosae.
Abbou Jaheed dake tsaye jin idanunsa sun ciko da ƙwalla ne yasashi lumshe su, tare da jingina bayansa da jikin bango, ahankali yake sauƙe ajiyar zuciya, yayinda aransa yake addu'a da fatan samun lafiyar ɗannasa, tabbas yasan idan wani abu ya samu Maleek to sakacinsa ne, kuma Allah Sae ya kamashi saboda hakan, dan shi kansa yasan baya bawa ɗannasa kulawa yanda ya kamata.

Wayar Abbou Kareem da ta soma ƙara ne yasa kowannensu dawowa daga duniyar tunanin da suka faɗa.
Ganin sunan Oum Ayush na yawo akan screen É—in wayarne yasa Abbou Kareem ya É—auki wayar cikin sauri.
Jin abun da take faÉ—a ne yasashi rumtse idanunsa, lokaci É—aya kuma ya buÉ—esu tare da kai dubansa ga Najeeb dake tsaye.
Ajiyar zuciya ya sauƙe batare daya ce komae ba ya kashe wayan.
Kallonsa ya mayar ga Abbou Jaheed dake tsaye.
Ganin yanayin Abbou Kareem É—in ya sauya ne yasa Abbou Jaheed yace. "Lafiya meke faruwa?."
Ajiyar zuciya Abbou Kareem ɗin ya sauƙe, kana cikin sanyin muryar dake bayyana sabuwar damuwar da ya samu kansa aciki yace.  "Laylerh ce  ba lafiya, wai tafaɗi bata ko numfashi."
Idanu dukansu suka zazzaro waje, cikin yanayin tashin hankali haɗi da damuwa.  Abbou Jaheed yace.  "Subahanallahi yanzu ina Laylerh'n take, sannan wani hali take ciki?." Abbou ya haɗewa Abbou Kareem duka tambayoyin awaje ɗaya.
Ɗan jim Abbou Kareem yayi, kana cokin sanyi yace "Tana sashin Aysha, sannan akwae buƙatar likita ya dubata cikin gaggawa, wannan wani irin tashin hankaline haka? ace atake yara dukansu biyu basu da lafiya, sannan kowannensu baya cikin hayyacinsa, Ya Allah Kabamu ikon jurewa hukuncinka." cewar Abbou Kareem daya ƙare maganar yana me ɗaga hannayensa sama alaman roƙon Allah.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da lumshe idanunsa wanda suka ɗanyi ja, haƙiƙa jin cewar Laylerh'n bata da lafiya ya sanyaya masa guiwa sosai, tunawa da cewar yau kwanansa huɗu kenan baisanyata a idanunsa ba, yasa yaji ya kwaɗaita dason ganinta, domin dama bai nisanta kansa daga gareta da wata manufa ba, kawai dai yanaso sai ta zamo mallakinsa ne, saboda ako yaushe yasa ta acikin idanunsa, ji yake kaman ya jawota ya rungumeta, dan sosai yake da feeling me ƙarfi akanta.
Ahankali ya ware idanunsa tare da ɗan soma jan jikinsa baya, batare daya sani ba ya buge wani ɗan ƙaramin table dake bayansa, sanadin hakanne ko yasa wani abu me kaman box dake ɗaure asaman table ɗin an lulluɓesa da wani farin yadi me kyau ya faɗo ƙasa.
"Oh My God!." YafaÉ—a alokacin dayake juyawa dan É—aga abun daya ture É—in ba tare da saninsa ba.
ɗaukan box ɗin wanda afaɗuwar da yayi yasa abun dake cikinsa suka zubo ƙasa, hannunsa yakai kan wani ɗan madaidaicin abun saka hoto wanda aƙa ƙawatasa da ado me kyau, ahankali ya ɗago abun tare da juyawa dan hakanan yaji kwaɗayin ganin hoton wanda aka saka acikin abun, sauƙe ganinsa akan hoton dake liƙe ajikin abunne yasashi ɗan zaro idanunsa, lokaci ɗaya kuma ya ƙurawa hoton idanu.
Sanye take cikin wani riga da sket na atamfa me kalan blue, yayinda tasanya hannayenta biyu ta kama waist É—inta, saidai kuma yanayin yanda idanunta ke kallon gefe ne yasa da ka gani zaka fahimci cewa unexpected pic ne aka mata batare ma da saninta ba.
*"LAYLERH..!!"* yaƙira sunanta acikin zuciyarsa wanda take cike da mamakin yanda akayi hoton Laylerh'n yazo ga Maleek, har yayi masa irin wannan karramawar tahanyar sashi a glass me matuƙar tsada da kyau.
"Me hakan yake nufi?." Zuciyarsa tayi masa tambayar da sam bashi da amsarta.
Jin wani tunani na ƙoƙarin ɗarsuwa acikin ransa ne, ya sa yayi saurin girgiza kansa, cikin son watsar da duk wani tunani dake ransa yace.   "Ita ƴar uwarsa ce, saboda haka bai kamata na damu kaina dan naga hotonta aɗakinsa ba, sam ma babu ƙatar hakan."
Da wannan tunanin yayi saurin tattare wajen, tare da gyarasa ya maidashi yanda yake.

Turo ƙofar ɗakin da akayine yasa su maida hankalinsu wajen, ganin Dr.Hafeez ne yasa suka sauƙe ajiyar zuciya, Abbou Kareem ne yayi masa jagora harzuwa inda Maleek ɗin ke kwance.
Wasu ƴan gwaje gwaje Dr.Hafeez ɗin yayiwa Maleek, ganin abun na buƙatar nutsuwa sosai ne yasashi ɗago kai haɗi da cewa.   "Please ko zaku ɗan jira a falo, because hayaniyan ku zai iya ɗan disturbing ɗina wajen yi masa kyakkyawan checking."
Jin abun daya faÉ—ane yasa dukansu suka fita daga É—akin, dan su dama burinsu shine suga ya buÉ—e koda idanunsa ne.
Koda suka fito daga cikin ɗakin, Abbou Jaheed, da kuma Abbou Kareem ne suka nufi cikin gidan, dan dama sun matsu suje su duba jikin Laylerh'n, kasancewar tuni Abbou Jaheed ya tura Dr. Ishaq wato family doctor'nsu saƙo akan yazo ya duba jikin Laylerh'n.
Alhaji Ahmad da Najeeb kuwa waje suka koma dan sallaman baƙin da suka tara, yayinda aka bar Fou'ad shi kaɗai zaune acikin falon Maleek ɗin.

Oum Ayush ce zaune abakin gadon, saikuma Aunty Zee da Teemah wanda suke tsaye agefen Dr. Ishaq wanda yake ƙoƙarin daidaita tafiyar drip ɗin daya ɗaurawa Laylerh'n.
Buɗe ƙofar ɗakin da akayine yasa duk suka juya, ganin su Abbou Jaheed yasa Oum Ayush sauƙe ajiyar zuciya.
Ƙarasowa cikin ɗakin sukayi fuskarsu ɗauke da matsananciyar damuwa, hannu Abbou Jaheed ya sa ya ɗan taɓa goshin Laylerh'n wanda ya ɗau zafi zau kamar wuta, hakanan yaji wani irin matsanancin tausayin Laylerh'n ya kamashi, cikin karyewar zuciyar da ta sameshi ya dubi Dr.Ishaq, asanyaye yace. "Dr. meyake damun ta ne? dan naji jikinta ya ɗauki zafi sosai."
Ajiyar zuciya Dr.Ishaq ya sauƙe, tare da duban Abbou Jaheed din ganin yanda gaba ɗaya hankalinsu ya tashi ne yasa shi ɗanyin guntun murmushi, cikin kulawa yace. "No karku damu bawani serious problem ba ne, kawae dai tana fama ne da matsanancin zazzaɓi, sai kuma yanayin damuwan da tasa aranta yasa jininta hawa, ƙwarai nayi mamaki danaga hakan, domin ƙaramar yarinya kamar Laylerh bana tunanin akwae wata damuwa da har zai iya sawa ta kamu da ciwon hawanjini, agaskiya Alhaji Jaheed ina tunanin ya kamata ace ku bincike ta, domin sanin damuwar dake damunta, dan akasin hakan, zaisa damuwar ta ta ƙara faɗaɗa, wanda kuma hakan zai iyasa ciwon nata yayi worst, idan kuwa haka tafaru gaskia za'a iya samun matsala, saboda ita yarinyace, sometimes ma batasan yanda zata kula da kanta ba."
"Innalillahi Wa'inna Ilaihirraju'oun..!!" Gaba ɗaya suka haɗa baki wajen faɗan haka, saboda ko kusa basu taɓa kawo aransu cewar wai Laylerh zata iya kamuwa da cutar hawan jini ta sanadin damuwa ba, domin kuwa itaɗin yarinyace ƙarama, wanda suke ganin cewa babu wata damuwa da zai kawo naƙasu arayuwarta, musamman ma da ayanzu ne take ƙoƙarin cika 18 years, kuma ayanzu ne suke tsammatawa rayuwarta ƙarin jin daɗi, saboda auren da akayi mata.

Ahankali Abbou Jaheed ya cire hulan dake kansa, tare da zama anan bakin gadon, tuni kuwa zufa ya keto masa, haƙiƙa yau rana ce ta farinciki agaresa, amma kuma gashi tana ƙoƙarin juyewa izuwa ranar riskar damuwarsa, sosai ya kaɗu dajin cewa wae Laylerh'nsa na ɗauke da hawan jini, wannan na nuna alamar cewa kenan bai riƙe amanar da ɗan'uwa da kuma mahaifiyarta suka bashi ba, saboda idan har damuwa zata iya sawa Laylerh ciwon hawan jini, to haƙiƙa hakan na nuna cewar ya gaza bata kulawarsa hundred percent.
Shiru yayi tare dasa hannayensa ya rufe fuskarsa, lallai abun da yakejin tsoro tuntuni shine ke ƙoƙarin faruwa.

Ahankali Abbou Kareem da jin maganar hawanjini'n Laylerh'n yasa shi a shock ya sauƙe ajiar zucia, cikin sanyin da guiwowinsa sukayi yace. "Yanzu Dr.Ishaq menene mafita? sannan kuma ya ake ciki da maganar farfaɗowanta?"
Chapter 50 · 0% Book details