← Book details Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 144

Sashe 59

Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Laylerh kuwa
Jin sauƙar muryarsa acikin kunnuwanta ne, yasa ta rumtse idanunta da ƙarfi, yayinda zuciyarta ta cigaba da wani irin bugawa, tsoron dake kwance acikin zuciyarta ne kuma ya bayyana kansa afili, wanda hakan yasa take jikinta ya soma karkarwa, kamar mejin sanyi.
Sosae abun ke damun zuciarta, dan koda wasa bata taɓa kwana ɗaki ɗaya da wani namiji ba, wannan shine karonta na farko, shi yasa duk takejin kanta afirgice.
Najeeb da yakai ƙololuwa wajen sha'awarta ganin bata amsa masa bane, yasa shi matsowa kusa da ita, harta kai ga ƙirjinsa na gogan bayanta, ɗan rankwafowa kanta yayi tare da sa hannu ya juyo da ita, ya zamana suna fuskantar juna.
"Laylerh!!" 
Akaro na biyu ya sake kiran sunanta, saidai kuma yanayin yanda taji amon muryar tasa ayanzunne yasa ahankali ta soma buɗe idanunta, take kuwa ta sauƙe ganinta acikin idanunsa wanda sukayi ja, wannan yasa ta kasa ɗauke idanunta akansa, ganin yanda gaba ɗaya mood ɗinsa ya sanja.
Ahankali ya ɗan hura mata iskan dake bakinsa akan fuskarta, cikin matsanancin shauƙin daya samu kansa aciki, yasa hannunsa ya shiga shafa gefen fuskarta, ganin yanda jikinta ke rawa ne, yasashi ɗan lumshe idanunsa akasalance yace.  "Tsoro na kikeji?."
Kasa amsa masa tayi, saima wasu irin sabin hawaye ne suka fito daga cikin idanunta.
Yanayin yanda yayi kusa da ita ne kuma yasa numfashinsu gauraya dana juna.
Ahankali bugun zuciyarta ke cigaba da tsananta, take kuwa ta soma ɗan motsa laɓɓan bakinta dake rawa, da'alama so take ta faɗi wani abu dake zuciyarta, amma yanayin yanda bakin nata ke rawa, yasa sirrin dake zuciar nata kasa bayyana.

Tamkar sauƙan ruwa da ɗaukewa, haka gaba ɗaya duk wani tunaninta ya tsaya, alokacin da taji sauƙan bakin Najeeb ɗin akan wuyanta, sanadin hakan kuwa ne yasa duk wani motsi na jikinta dakatawa, harta kuwa numfashinta saida ya tafi hutun wucin gadi.
Ɓangaren Najeeb kuwa daddaɗan ƙamshin dake tashi ajikinta ne yasashi ƙara shigewa jikinta, tare dayi mata wani irin hugging, cikin mahaukacin feelings ɗin daya samu kansa, ya shiga sakar mata wasu irin mahaukatan kisses awuyanta.
Wanda kuma hakan yasa da ƙyar ta iya ƙwato nunfashinta dake ƙoƙarin ɗaukewa gaba ɗaya, samun kanta acikin baƙon yanayin da tayi ne yasa jikinta ya tsananta ɓari, yayinda taji kaman ana buga mata guduma atsakiyar kanta, hannayenta tasa duka biyu ta riƙe kanta da lokaci ɗaya yasoma yi mata wani irin ciwo.
Najeeb kam gaba ɗaya ya soma fita hayyacinsa, saboda lokaci ɗaya ya soma ƙoƙarin manta komae, cikin kuma yanayin daya samu kansa aciki ne, ya ɓalle ƴan ƙananan button ɗin dake jere agaban rigar baccin nata, take kuwa kyawawan breast ɗinta suka bayyana.
Ganin breast ɗin nata afili ne kuma ya ƙara ruɗashi, azafafe yaci gaba da kissing ɗin wuyanta.

Yanayin yanda kanta ke juyawa ne yasa ta runtse idanunta da ƙarfi, wani abune ke ƙoƙarin kutsowa cikin tunaninta, take mummunan yanayin daya rusketa abaya yashiga dawo mata, wanda har yasa taji ajikinta cewar watarana irin haka ya taɓa faruwa da ita.
Ji tayi gaba É—aya duniyar na juya mata, yayinda lokaci É—aya idanunta suka shiga dawo mata da abubuwan da suka faru da ita ashekarun baya da suka wuce.
jikintane ya cigaba da ɓari hartakai ga haƙwaranta na haɗewa waje ɗaya, take wani irin fitinannen tsoro ya shigeta, ahankali ta soma jujjuya kanta da takejin yayi mata nauyi sosae.
Komae da ya wuce ne yashiga dawo mata tamkar alokacinne abubuwan ke faruwa.
Bazata iya jurewa yanayin ba, domin abun yasake dawo mata, yayinda idanunta suka rikide, ba abun da suke gane mata sai lokacin da yake ƙoƙarin keta mata rigar jikinta, hakan yasa ta ƙanƙame jikinta waje ɗaya, tare da sakin wani irin kara, lokaci ɗaya ta soma kiciniyar kwace jikinta daga na Najeeb din.
ƙaran da tayi ne ya dawo da Najeeb hayyacinsa cikin yanayin mamaki ya ɗago kansa ya kalleta, ganin kuma yanda jikinta ke ta ɓari ga kuma gumin dake feso mata ne yasa shi riƙeta da kyau, cikin yanayin mamakin daya shiga yashiga kiran sunanta, saboda ya lura kaman bata cikin hayyacinta.
Kuka me tsanani ta fashe masa dashi tare da soma jijjiga kanta da'alama so take ta ƙwace daga riƙon da yayi mata.
"Laylerh!!"
Yaƙira sunanta da ƙarfi, atunaninsa ko hakan zaisa ta shiga hayyacinta, dan abu takeyi kamar wanda aljanu suka kama.
Sam tayi nisan da bata jin ƙira, kasancewar gaba ɗaya ta fara fita hayyacinta, amatuƙar zauce take haɗe jikinta waje ɗaya, yayinda ta shiga rera masa kuka, tare da soma yaƙushinsa tamkar wanda ta samu gushewar hankali.
Najeeb kuwa ganin yanda take yaƙushin fatarsa da kuma yanda take ƙara jan jikinta bayane yasa shi sakinta, aikuwa dama kamar jira take cikin sauri ta diro daga kan gadon, ganin haka yasa cikin sauri ya cafko hannunta.
Razanannen ƙara ta saka masa tare da soma ƙoƙarin ƙwace hannunta dake cikin nasa, yanayin ruɗewan da yayi ne kuma ya sashi sakin hannun nata batare da ya shiryawa hakan ba,  baya baya ta somayi tare da haɗe hannuwanta biyu waje ɗaya alaman roƙo, matsota da yakeyi ne yasa ta soma girgiza masa kai, cikin wani irin muryar da baisanta da shiba take faɗin. 
"Dan Allah ka ƙyaleni, karka cutar dani dan Allah!!!"
Jin hakane yasa da sauri yakae hannu zae taɓa ta, rumtse idanunta tayi tare da soma ƙiran sunan Maleek, kafun yayi wani yunƙuri kuwa tuni ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice aguje.
Matsanancin mamaki da kuma shock ɗinta ne yasa Najeeb tsayawa kamar statue ya kasa koda motsa ƙafarsa, domin yanayin da yaga Laylerh'n ya matuƙar tsoratar dashi.
Ita kuwa Laylerh cikin matsanancin kuka ta fito daga part É—in nasu, kaitsaye babban falon gidan ta nufa, yanayin yanda take gudu tana kuka ne yasa duk wani wanda baccinsa baiyi nisa sosae ba zai iya jiyo gunjin kukan nata.
Kasancewar kuma ta taho aguje ne yasa tana buga ƙofar falon, ta buɗe nan take.
Atsorace take sosae, hakan yasa gaba ɗaya sautin kukanta ya cika ko ina dake cikin falon, haƙika tashiga tsoron da yasa ko ganin gabanta bata iyawa, duba da irin yanda take ganin abubuwan da suka faru da ita suna dawo mata sabi, wannan yasa ta shiga ruɗu sosae.
Yanayin yanda ta shigo falon aguje ne yasa ta faɗa jikin MALEEK wanda shi kuma alokacin yake koƙarin fita daga cikin falon.
Jin da tayi ta faɗa jikin mutum ne yasa ta ɗago idanunta wanda suka soma dishewa, sauƙe ganinta da tayi akansa ne kuma yasa ta rungumesa ƙam tamkar zata shige cikin jikinsa, kuka ta fashe masa dashi, ahaukace ta soma jijjigasa, bakinta ta buɗe daniyar yin magana, amma gaba ɗaya takasa, saima numfashinta dake ƙoƙarin ɗaukewa.
Ganin hakane yasa shi rungumeta ƙam ajikinsa, kansa ya ɗan soma girgiza mata, kana ahankali ya tura mata ƴar yatsarsa cikin bakinta.
Daidai lokacin kuwa Su Abbou Jaheed  wanda kukan Laylerh'n ya taso su suka karaso cikin falon, wanda kuma hakan yayi daidai da shigowar Najeeb cikin falon.

*4/January/2021*
1/19/21, 8:27 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*Note Edit*

*Chapter 33*

Ƙanƙame jikinsa tayi ƙam yayinda gaba ɗaya jikinta ke rawa , wanda kuma hakan yasa numfashinta soma ɗan carkewa, matsanancin kukan da takeyi ɗinne kuma ya ɗan tsagaita alokacin da ya sanya mata ƴar yatsarsa acikin bakinta.
Maleek kuwa ganin da yayi cewa da gaske ta fita hayyacinta ne yasa shi matseta ajikinsa sosae, duk da cewar hannayenta dake kan ƙirjinsa na yaƙushin fatarsa amma sam baidamu da hakan ba, hasalima ko zafin abun da take masa ɗin baijiba.
Rumtse idanunsa wanda suka kaɗa sukayi jajur yayi, wani irin tafasa yakejin zuciyarsa nayi, yayinda matsanancin tausayin Laylerh'n ke ƙara mamaye zuciyarsa, tabbas yasan me take gujewa, kana kuma me takejin tsoro, saboda ya jima yana gujewa zuwan wannan ranar, ranar da zatasa abun da ya wuce shekarun baya ya kuma dawowa cikin tunanin ta, meyasa Najeeb zai taɓa masa Laylerh'nsa har haka? idan ƙaddara batayi musu adalci ba, Najeeb baikamata yace zai kusanci masa Laylerh'n sa ba, ƙwarai ya tuna abun daya jefa Laylerh'n acikin wannan rikitaccen halin, yanayi da kuma acting ɗinta na yanzu, daidai yake da wanda tayi lokacin baya, lokacin da kwata kwata bayason tunoshi acikin gaba ɗaya tarihin rayuwarsa, domin tuna abun kansawa yaji kaman kansa zai fashe, kasancewar tuna hakan baƙinciki ɓacinrai da kuma ƙunan zuciya ne ke kewayesa.
Shin meye amfaninsa idan har za'a samu wani wanda zai ɗimautar masa da Laylerh akaro na biyu, batare daya ɗau mataki ba, akaron farko wani yaso ketawa Laylerh'n tasa mutumci, gashi kuma ayanzu ma hakan naƙoƙarin faruwa,
Kansa da yayi masa wani irin nauyi ya ɗan soma girgizawa, yayinda kuma idanunsa wanda sukayi jajur suka nemi ƙoƙarin tara masa ruwan hawaye acikinsu.
Jin yanda numfashin Laylerh'n ke fusga da sauri sauri ne, yasa ahankali yasa hannunsa ya shiga shafa bayanta, tare da ɗan soma jijjigata ajikinsa tamkar wata ƙaramar yarinya ƴar shekara 3.
Haƙiƙa tun tana ƙaramarta ajikin mutum ɗaya take samun nutsuwa, komin kukan da take kuwa daya ɗauketa zatayi shiru, wannan mutumin kuwa ba kowa bane face shi, daya zama tamkar shine ma rayuwarta gaba ɗaya.
Aduk kuma sanda tagansa ji take kaman ta tsira daga dukkan wani abun cutarwa, ahankali tasake shigewa jikinsa, tare dasa harshenta ta kanannaɗe yatsarsa dake cikin bakinta, har zuwa yanzu jikinta ɓari yake, yayinda still kuma numfashinta ya kasa daidaita.
Maleek da yaji komae na duniyar ya daina masa daɗi, baƙinciki da ƙunci sun cika zuciyarsa, jin yanda ta ƙara shige masa sosae ne yasashi ɗaura haɓarsa akan watsatstsen gashin kanta dake ta fitar da ƙamshi, tare kuma da sake rungumeta ƙam, domin ayanda yakejin zuciarsa na wani irin tafasa, da ace itadin bata jikinsa to tabbas da zai iya aikata komae, ciki kuwa harda illata Najeeb, wanda sanadinsa ne Laylerh'n ta dawo tamkar wata zautacciya.
Chapter 59 · 0% Book details