Sashe 1
Laylerh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
‡
*Bismillahirrahamanirraheem*
*LAYLERH MALEEK*
*Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Blood Brother, My Happiness, My Sweetheart, nd My Heartbeat (AUWAL) I love you so so much my big bro, wish you quick recovery darlingðŸ‘ðŸ».*
        *FOLLOW ME ON*
              *Wattpad*
           @fatymasardauna
#Firstlove.
*Friday 31/October/2020*
   *(📿Happy Jumma'at Mubarak To All Muslims Ummah, May Allah Bless You And Your Family.🕋)*
*CHAPTER ONE*
*(SOYAYYA wata irin ƙaddarace, da take ɗaure akan wuyan kowa, sannan kuma wata abace da ba'a iya ganin launinta da ido, hakanne ma yasa ba'a iya sauyata, saidai idan taso takan tashi daga sunanta na SO ta koma ƘIYAYYA. Acikin kowani rayuwar ɗan Adam akwai salon ƙaddarori masu tarin yawa, akowacce duniya akuma koda yaushe ƙaddara tana tafiya ne daidai da rayuwa, haka kuma tana rayuwa da mu cikin farinciki ko akasin haka, abu ɗayane yake tafiya acikin zuƙatanmu, shine MURADI, FATA, da kuma son samun ABUNDA ZUCIYA KESO. Sannan kuma babu wani bawa wanda ke iya gujewa ƙaddaransa, Lallai ƙaddararmu tana gudana ajikinmu kamar jini, akowace rana abubuwa mabanbanta suna faruwa, to haka itama ƙaddara takan iya sauyawa ako da yaushe, wannan rayuwar daban take da saura, komai yana cikin zuciya da tunanin LAYLERH MALEEK.)*
 ***    *** ***
Cikin sauri take ƙoƙarin sanya uniform ɗin makarantar ta, sosai take sauri dan tasan idan ta tsaya wasa zatayi latti, wanda zuwa yanzu batasan da wani baki zata fara faɗan excuse ɗinta ba, ga masu gadin makarantar, domin tasan zuwa yanzu suma sungaji da karɓan excuse ɗinta.
Ɗan madaidaicin sket ɗin makarantar nata tasanya, wanda yake da ɗan tattara ajikinsa, wanda idan kasanya sa, zaka jawosa har saman cikinka, dan iyan high waist ɗinnan ne, bayan ta saka sket ɗinne.
Cikin sauri sauri ta zura wata farar rigan long sleeve ajikinta, ahanzarce ta tura rigar acikin sket ɗin, take ta zuge zip ɗin sket ɗin, hakan da tayi ne kuma yasa ba'a ganin ƙasan rigar makarantar nata.
Sauri sauri ta maƙala aninayen dake jere agaban rigar, farin safa ta sanya aƙafafunta, tare da ɗaukan wani toms ɗinta me kalan baƙi ta sanya.
Dayake sket ɗin makarantar tata da kaɗan ya wuce guiwanta, hakan yasa safan da tasa aƙafanta yaɗan taimaka wajen suturta fatar ƙafanta.
Kyawawan fararen idanunta ta É—ago, tare da sauÆ™esu akan agogon bangon dake saÆ™ale jikin bangon É—akin. Â
8:15 am daidai ta gani, jitayi ƙirjinta yayi wani irin bugu, take taji zuciyarta ta karye, shikenan yau ma ta sakeyin latti kamar sauran ranakun, by 8:00 am daidai ake kulle gate ɗin makarantar tasu, da zaran an kulle kuwa babu me shiga, idan kazo late saidai ka koma gida, duk da tasan cewar tana samun alfarmar shiga makarantar daga wajen masu gadi koda an kulle, saidai yau bata tunanin cewa zasu dubeta ma bare har su karɓi roƙonta.
Cikin azama ta zura ɗan madaidaicin hijabin makarantar ajikinta, wanda duka tsayinsa baiwuce guiwan hannunta ba, kallon kanta tayi amadubi, tare da kafe madubin da ido, kyakkyawar fuskarta take kallo ta cikin madubin, sannu ahankali idanunta suka ciko da hawaye, lumshe idanun nata tayi, wanda hakan ya bawa hawayen dake ciki daman gangarowa.
Da sauri ta share hawayen, ta ɗauki Æ™atuwar hand bag dinta ta goya.Â
Text book ɗin ta da tayi assigment acikinsa jiya, wanda ta ɗaurasa bisa kan mirror ta ɗauka, da sauri tafice daga cikin ɗakin.
Koda ta bude ƙofar ɗakin nata ta fito, nan cikin babban falon gidan, da kai tsaye za'a ƙirasa da aljannar duniya ta samu kanta, falo ne tankameme wanda tsarinsa da haɗuwarsa ya zarce misali, kallo ɗaya zakayiwa falon ka tabbatar da cewar mamallakansa ba ƙananan masu arziki bane, saboda wasu irin haɗaɗɗun royal cushions masu uban kyau da tsada da aka ƙawata cikin falon dasu, adon jikin royal cushions ɗin ma kaɗai abun kallo ne,  tsakiyan falon kuwa wani irin haɗaɗɗen lallausan turkish carpet ne a malale, wanda kana takawa ƴan yatsun ƙafanka na lumewa aciki, tsabar laushi, ta cikin falon acan gefe kuwa wani irin ƙawataccen dinning area ne me azabar kyau da tsaruwa, an kewaye gaba ɗaya wajen da haɗaɗɗen decoration me kyau, wasu irin haɗaɗɗun labule kewaye da kowani ƙofa da window dake cikin falon, ga kuma wasu irin flowers masu kyau da aka saka akowani kusurwan falon, wanda sai shinning suke suna ɗaukar ido, still daga
cikin falon kuwa wani irin tangamemen tv plasma ne keta aikin ɓaɓatu shi kaɗai, bayan plasman dake magana shi kaɗai babu wani halitta acikin falon, sai sanyin A/C dake ta busawa.
Kan dinning area' n ta kalla, wayam haka taga saman table ɗin babu ko cokali, bare kuma food flask, da dukkan alama dai yau ɗinma ba'a rage mata break fast agidan ba.
Cikin rashin ƙarfin jiki ta murɗa handle din ƙofar falon ta fita zuwa babban compound ɗin gidan, wanda yayi matuƙar haɗuwa, kanta tsaye ta nufi hanyar babban gate ɗin gidan, sunkuyar da kanta ƙasa tayi, tare da  sanya hannunta duka biyu ta riƙe jakar makarantar dake goye a bayanta.
Ɗahiru me gadi dake tsaye abakin gate ɗin gidan, ganinta yasashi ɗan sakin murmushi cikin kulawa yace.   " *LAYLERH* ƴan mata sarkin makara yau madai amakare za'aje makarantar kenan."
Idanunta ta É—an lumshe tare da jinjina masa kai alaman
"Eh."Â Â
Murmushi ya kumayi tare da cewa.  "To Adawo lafiya Allah ya bada sa'a."  Cikin zazzaÆ™a kuma tattausan muryarta tace. Â
"Ameen Malam ÆŠahiru nagode."Â Â Â Â
Buɗe ƴar ƙaramar ƙofar dake jikin gate din tayi ta fita.
Malam Ɗahiru kuwa binta yayi da kallo yana girgiza kai, cike da matsanancin tausayinta, dan yasan babu makawa yanzu haka ko karyawa batayi ba, kuma haka zata tafi makarantar,  ga kuma motocin da suke ajiye agidan basa aikin komai sunkai guda 7, amma daga cikinsu babu wanda ake bawa umarni ko izinin kai Laylerh'n makaranta, kullum saidai ta fita bakin titi tahau taxi , ranan da bata da kuɗi kuwa saidai ta taka akan sawayenta, wannan dalili yana daga cikin abunda yasa yake matuƙar tausayin yarinyar.
Cikin yanayi naɗan ɗaga ƙafa take tafiya, akan shumfufaɗaɗɗiyar hanyar da ta kewaye unguwar tasu, wanda kowani ƙofar gida akwai titi shumfuɗe agabansa, haka ƙa'idar unguwan tasu take, kasancewarta unguwar masu kuɗi shiyasa, saikayi tafiya me nisa aƙafa baka haɗu da wani ko wata ba, kowa na cikin gidansa akulle, idan ma zaka ga mutane tofa saidai acikin tsala tsalan motocinsu suna wucewa, musamman ma a irin wannan lokacin babu Ragowan ababen hawa akan titin unguwartasu, domin masu tafiya office da makaranta duk sun tafi.
Tafiya take sosai, sai cira ƙafa take burinta baiwuce taganta abbaban gate ɗin da zai fitar da ita daga unguwar tasu ba, dan ananne kaɗai zata iya samun abun hawa.
Sauri take sosai, duk da kasancewar ma babu wani abu na kirki da tasa acikinta tunjiya da dare, gashi yanzuma bata samu arzikin yin break fast ba ta fito.
Saurin da takeyine yasa bata wani ɓata lokaci ba, ta iso ƙofar gate ɗin, me gadin gate ɗinne ya bita da kallo dan idan da sabo ya saba da ganinta kusan kullum, matuƙar akwai makaranta to fa sai yaga wucewanta.
Ɗaga masa gaisuwa tayi sannan tabude ƙofar gate ɗin ta fice.
Samun kanta tayi akan wata sabuwar titi, wanda take akwai ragowan ababen hawa akanta, saidai kuma duk ba motocin haya bane ke kai da kawowa awajen.
Ahankali taÉ—an bubbuga Æ™afafunta tare da ciza laɓɓanta, cikin wata irin murya me sanyi tace.  Â
"Ya Allah Ka taimakeni katuromin abun hawa, yauma na makara, bansan yazanyi ba, nayi missing lectures, gashi by 9:00 muna da test." Â