Sashe 96
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙoƙarin magana take taji ya hankaɗata, Duk yanda Zahra ta so kwatar kanta kasawa ta yi dan ba ƙaramin ƙarfi ya saka mata ba, a dole ta rabu dashi. Bayan ya gama abin da ya yi niyya ya tashi ya fice daga ɗakin ya bar ta a wajen, Ta dinga kuka saboda muguntar da ya yi mata, Baƙin cikin kalmar daya faɗa ta sanyata sake rushewa da kuka. Tana cije laɓɓanta da ƙarfi.
Koda ya koma ɗakinsa bai tarar da Nana ba kuma daman ya san ba zata taɓa zuwa ba, koda kuma yaje kiranta ba zata biyo shi ba,dan haka ya faɗa banɗaki ya yi wanka ya fito ya sauya kaya ya yi kwanciyarsa. Washegari da safe ya kama Saturday, ranar Nana bata da lecture dan haka ko ƙasa bata sakko ba, tana daƙinta a kwance saboda sanyin da ake.
Zahra na zaune kan sofa tana tunanin yanda zata yi, ba zata taɓa bari abin da ya ya mata ya tashi a banza ba. Dan haka ta miƙe ta huce sama, Daƙinta ta shiga ta zauna gefen gadon tana sake maimaita maganar daya faɗa mata, Can dai ta miƙe ta ɗauki veil ɗinta ta yafa sannan ta fito, bata ko tambayeshi ba ta fice daga gidan, After 30mins ta dawo da wata ƙaramar leda. Shiryawa ta yi cikin wata doguwar riga ta abaya nude colour, Ta yi simple make-up a fuskarta sannan ta nufi ɗakin Noor, tana zaune da maid ɗin dake kula da ita suna hira ta shigo. Ta taso da gudu ta rungumeta ta ce
“Ummi"
Murmushi Zahra ta yi ta ɗauketa ta ce“Muje ki raka ni unguwa.”
“Ummi da Abbie zamu je?"
Girgiza mata kai Zahra ta yi ta ce“Abbie na gida za'a bar shi ya huta, dani dake zamu je.”
Tura baki Noor ta yi ta ce“ni na fison har da Abbie” Zahra ta ja kumatunta ta ce“Eh ai gobe dashi zamu je, yau amma mu kaɗai zamu, har da gidansu Afeefa.” washe baki ta yi tana dariya ta ce
“Da gaske Ummi?”
Zahra ta gyaɗa mata kai bayan ta ajiyeta kan kujera. Ta ɗauki ledar data shigo da ita a gefen gadon sannan ta juya ta fita. Kitchen ɗin saman ta shiga ta haɗa coffee kamar yanda ta san zai masa, ta haɗa da hamburger guda biyu a plate. Buɗe ledar ta yi ta dauko wani tablet ta ɓalli guda huɗu ta zuba a coffee ɗin, ta ɗan jira har ya narke sannan ta ɗora a tray ta fita..
Side ɗinsa ta nufa ta murɗa ƙofar parlourn ta shiga, Zaune ta hangeshi kan sofa yana operating system ɗin dake gabansa. Ta yi sallama sannan ta ƙarasa ciki, Ya ɗago fuskarsa ya ɗan kalleta. Murmushi ta sakar masa bayan ta ajiye tray ɗin kan table ɗin gabansa ta ce
“Ina kwana?”
A sanyaye ya amsa, Zahra ta ɗan sunkuyar da kanta ba tare da ta sake cewa komai ba. Shiru parlourn ya ɗauka, Ya ƙarasa abin da yake a system ɗin sannan ya rufe yana kallon ta ya ce
“Lafiya dai?”
Saurin girgiza kanta ta yi ta ce“babu komai, kawai daman ina son zan ɗan fita ne” wani kallon sheƙeke ya yi mata kafin ya ce
“Daman idan zaki fita tambayata ki ke? Bana ce ki dinga tafiyarki ba?”
Murmushi ta yi ta ce“Tom shikenan sai na dawo.”
“Allah ya tsare” Ya ce yana jan mug ɗin dake saman tray ɗin. Miƙewa ta yi tace amin sannan ta juya ta fita tana ɗan leƙensa , Murmushi ya yi bayan ya yi sipping coffee ɗin ya ce
“Ko na zo na raka ki?”
Girgiza masa kai ta yi, sannan ta rufe ƙofar dakin. Ya ɗan yi murmushi shima kafin ya ci gaba da shan coffee ɗin.
Zahra na fita ta koma daƙinta ta zurawa Noor rigar sanyi sannan ta ɗauki jakarta da wayarta suka bar gidan a gaggauce. Yana gama shan coffee ɗin ya tashi ya shige ɗakinsa, Toilet ya faɗa ya wanke bakinsa sannan ya fito ya yi kwanciyarsa.
****
Aunty Khadijah ce zaune kusa da Umma hawaye na zubowa kan fuskarta, Umma ta yi shiru tana kallon ta, can kuma ta kalli Kaddu ta ce“To yanzu mene abun yi?” girgiza kai Kaddu ta yi ta ce“wallahi Umma nima bana ce ba, Khadijah ta yi nisa a cikin sonsa, tun ina ɗaukan abun wasa har ya fara bani tsoro.” Umma ta numfasa tana kallon Anty Khadijah da har sannan bata daina kuka ba ta ce“Khadijah ke kin yarda zaki aure shi?” saurin gyaɗa mata kai ta yi kafin ta ce“Eh umma, wallahi na yarda. Ina son Garba, zan aure shi, daman ba so ki ke nayi aure ba to wallahi zan aure shi!” Jin jina kai Umma ta yi ta ce“To zan yiwa kawunku magana, ki ce masa ya turo magabatansa sai a yi maganar aure.” Aunty Khadijah ta sauke ajiyar zuciya ta shiga goge hawayenta ta ce“Nagode sosai Umma, bari naje na faɗa masa yanzu.” Ta miƙe ba tare da ta jira abin da zasu ce ba ta nufi sama, Da idanu duk suka bita, Kaddu ta girgiza kai ta ce
“Umma ni wallahi bana son auren nan.”
Numfasawa Umma ta yi jiki a sanyaye ta ce“To ya za'a yi Kaddu? Tun da har taga tana sonsa ai babu yanda za'a yi da ita. Khadijah ba yarinya ba ce, ba sabon aure bane balle ace iyaye keda ikon zaɓa mata wanda ya dace da ita. Tana da ikon zabar wanda take so ta zauna dashi” Kaddu ta jinjina kanta jiki a sanyaye ta ce“haka ne, to Allah yasa haka ne yafi alkhairi.” Umma ta numfasa sannan ta ce“Amin Kaddu. Kema ya kamata ki fito da miji ki yi auren ki” sunkuyar da kai ta yi tana murmushi ta ce“ai nima in sha Allah nan bada jimawa ba zan sake auren” Umma ta ce“To Allah yasa, dan zaman haka bashi da wani fa'ida” Kaddu dai bata ce komai ba kanta a ƙasa.
****
Amma ce zaune kan sofa tana kallon Haule dake faman cin gyaɗa, Ta girgiza kanta ta ce“Yanzu gyadar ce zata miki abinci Haule?” kallon ta Haule ta yi, sai kuma ta ce“Amma bana jin yunwa fa. Ɗazu naci abinci wajen Hajiya Babba” Amma ta ce“To shikenan, kin je duba Safwan ɗin?” gyaɗa mata kai ta yi tana ajiye ɓawon gyaɗar kan table ta ce“Eh mun je dasu Maimoon, da sauƙi jikin nasa, dan ma ya gane mu” Amma ta tashi tana ƙoƙarin shiga kitchen dan duba girkin da take ta ce“To Alhamdulillah, Allah ya ƙara sauƙi, mu ma an jima zamu koma.”
“Zan biku Amma”
Ta ce tana marairaice fuska, Harararta Amma ta yi ta ce“ɗazu kin je shi ne zaki sake bin mu? To ba zaki ba.” ta nufi kitchen ba tare da ta jira amsarta ba, Shiru Haule ta yi tana jin babu daɗi a ranta. Har ga Allah tana son sake zuwa ta gan shi, taga wane hali yake, amma ta san tunda Amma ta ce haka ba zata bari taje ba. Tashi ta yi bayan ta kwashe ɓawon gyaɗar a faranti ta nufi waje, a dustbin ɗin dake balcony ta zuba sannan ta dawo parlourn ta ajiye plate ɗin ta nufi ɗakin Nana, tana zuwa ta yi kwanciyarta akan gado tana lumshe ido, nan da nan kuma bacci ya ɗauketa.
****
New York, Lower East side.
Zahra ce zaune kan sofa tana kallon wata baƙar mata wadda ba zata shige shekarunta ba, Murmushi ta yi ta ce“Ke Zahra, to me yasa zaki yi haka?” harararta ta yi ta ce“Lailah ba zaki gane ba, kin san me ya ce min kuwa jiya? Ita yarinya ce ƙarama, ba zai iya yi mata komai ba saboda yana tausayinta sai dai idan ta ƙara girma, kenan ni ce banza wadda ban san ciwon kaina ba? Ni zai dinga yin yanda ya so dani ita kuma ya adanata.”
Murmushi Lailah ta yi ta ce“Gaskiya dai bai kyauta ba, amma kema da baki yi haka ba. Tun da yarinyar ce da gaske, Doctor yana da shekaru ba lallai ta iya ɗauke buƙatarsa ba, ko haka kawai ballantana kin bashi pills gaskiya zai iya cutar da ita.” taɓe baki Zahra ta yi tana kallon Noor da Afeefa dake can ɗaya parlourn suna wasa ta ce“ai so nake ya cutar da itan, yanda iyayenta zasu yi dana sanin bashi aurenta, wallahi ba zan iya zuba ido ina gani yarinya ƙarama ta mulkeni ba, Dole ne na ɗauki mataki akanta, yanda nan gaba idan an ce ya auro wata shi ma ba zai yi gigin yin haka ba.” Lailah ta ce“mazan namu ne sai a hankali, Ban da neman magana mai zai yi da wannan ƙaramar yarinyar? Ni fa ina gano sanda ki ke zuwa da ita Columbia time ɗin baku daɗe da aure ba ki ka ce ƙanwar mijin ki ce, amma ace har ta yi girman da zai aureta? Maza! Maza!”
Cike da ɓacin rai Zahra ta ce“kin gane abin da ke ɓata min rai kenan. Ni da wata aka aura masa ba zan damu ba, amma ya za'a yi ya auri Nana ina raye? Ai idan ma na bari suka zauna lafiya wallahi Allah ba zai bar ni ba.” tuntsirewa da dariya Lailah ta yi kafin ta ce“Ke ƙawata kin iya masifa kema” Zahra ta yi kwafa ta ce“ai in dai mutum ya taboni anan zai gane nima ba haƙuri gareni ba. Ni za'a ci amana?”....
****
Nana na kwance a parlourn ta sai juyi take saboda yunwar data dameta. Ta ɗan ja tsaki sannan ta tashi zaune tana jan hular dake ajiye a saitin kanta ta saka akanta wanda yake a gyare. Tashi tsaye ta yi tana gyara wandon jikinta, wasu up and down English wears ne brown colour a jikinta, ta nufi kitchen ɗin dake parlourn tana tafe kamar iska zai hureta. Tsayawa ta yi a tsakiyar ƙaton kitchen ɗin tana kalle-kalle, Can dai ta nufi store ɗin dake ciki dan duba abin da zata dafa. Kwalin indomie ta buɗe ta ɗauki guda ɗaya sannan ta dawo kitchen ɗin, Ta kunna gas ta ɗaura ruwa cikin ƙaramin tukunya. Dubawa inda take ajiye kwai ta yi taga babu, ta ja dogon tsaki tana dire ƙafarta a ƙasa cike da shagwaɓa ta ce