← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 125

Sashe 64

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kansa ya yi yana jin wani irin haushinta kamar ya shaƙeta ya ce“kenan saboda son zuciyarki ki ka aikata haka? Saboda ƴar uwarki ta aureshi?”

Shiru ta yi tana kukanta. Ya shiga zagaye ɗakin hannunsa goye a bayansa, can kuma ya tsaya cak yana kallonta daga inda yake ya ce

“Kin cutar da ita shi kuma Allah ya saka mata. Kin hanata auren mijin ƴar uwarki ta kuma auri mijinki. Babu buƙatar a yi miki wani hukunci, iya wannan kaɗai ya isheki ki gane irin abin da ki ka aikata. Ya isheki ki fuskanci Allah na kishin bawansa, tun da kin cutar da ita ne ba akan laifinta ba!”

Sake durƙushewa Zahra ta yi tana ƙara sautin kukanta, tabbas Allah ya nuna mata ishara. Ya kuma sakawa Nana tun a duniya, ta miƙe da kyar tana ci gaba da kuka ta nufi inda yake. Da hannu ya dakatar da ita, idanunsa kamar garwashi saboda jan da suka yi ya ce

“kar ki kuskura! Stay away from me!”

Cikin kuka ta ce“dan Allah ka yi haƙuri, ka yafe min wallahi ba zan sake ba. Na sani na cutar da Nana kuma zan nemi yafiyarta, dan Allah doctor ka yi haƙuri kada ka ce zaka gujeni”

Cije laɓɓansa ya yi yana jin da ace duka ɗabi'arsa ce to babu abin da zai hana shi dukan Zahra. Ya ja dogon numfashi ya sauke yana ƙoƙarin saita kansa ya ce

“ni ki ka yiwa laifi?”

Girgiza masa kai ta yi, ya gyaɗa kansa sannan ya ci gaba da fad'in “to akan me zaki nemi yafiyata?.”

Shiru Zahra ta yi tana kallonsa hawaye sai zuba yake daga fuskarta kamar an buɗe famfo. Ya tako kusa da ita har tana jin sautin fitar numfashinsa ya ce

“Yarinya ce ƙarama. Yarinyar da bata gama sanin ciwon kanta ba, amma ke da girmanki da kuma hankalinki ki ka cuceta, ki ka mata zamba cikin aminci. Ki sani kar ki ɗauka iya hukuncin kenan, idan har Nana bata yafe miki ba to wallahi tallahi kin ji har na rantse babu ni babu ke!”

Manage this pls, I'm not feeling well🙏.

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 39.

Ya ƙare maganar yana jefa mata wani mugun kallo, sunkuyar da kai ta yi tana shessheƙar kuka. Ya ratsa ta gefenta ya fice daga ɗakin kamar zai tashi sama, da idanu Zahra ta bishi sai kuma ta sulale a ƙasa ta rufe bakinta da hannunta tana kuka a hankali. Yana fita apartment ɗin Hajiya Babba ya nufa. Koda ya shiga bai samu kowa a parlon ba, dan haka ya haye sama. A hankali ya murɗa handle ɗin ƙofar, ya hangeta zaune gefen gado tana jan cazbaha a hankali. Numfasawa ya yi sannan ya karasa ciki, Hajiya Babba ta dinga kallonsa har ya zauna a gefenta. Ganin bai ce komai ba ya sanya ta dafa kansa ta ce

“Lafiya dai?”

Madadin ya amsa mata sai kawai taga ya shige jikinta, ya dinga sauke ajiyar zuciya a hankali. Ajiyar zuciyar ita ma ta sauke kafin ta sanya hannunta cikin sumar kansa ta fara hargitsata a hankali. Numfashi ya dinga saukewa yana jin wata nutsuwa ta musamman na saukar masa, ya dinga jin duk ƙunci da damuwar zuciyarsa na narkewa. Sun ɗauki mintuna masu tsayi a haka kafin ta ɗago kansa tana faɗin

“mene ne?”

Girgiza mata kai ya yi dan ya san bashi da hurumin sanar da ita abin da ke damunsa yanzu, dan shi ne wanda ya jawo komai. Ya sauke numfashi kafin ya ce

“bakomai Hajiya”

Kallonsa ta dinga yi sanin ƙarya ba ɗabi'arsa bace yasa ta girgiza kanta ta ce“Abdusammad kenan. Na san halinka fiye da kowa, ko ka manta ni na haifeka? Fuskarka ta nuna akwai damuwa a tare da kai, faɗa min mene ne.”

Ta ƙare maganar tana riƙe hannunsa na dama. Murmusawa ya yi cike da son kawar da zancen ya ce“Hajiya babu komai fa, kawai ina tunani ne akan Nana. Abba ya damu da ita fiye da ƙima, kawai yana sharewa ne, so ina son sanin inda take naje na dawo da ita gida.”

Zazzafan numfashi ta furzar kafin ta ce

“nima da tunanin yarinyar nan nake kwana nake tashi. Duk da ta ɓata mana sunan dangi hakan ba zai sa mu fasa nemanta ba, na tabbata yarinta da rashin jin magana sune suka yi tasiri a tare da ita har taje ta aikata abin da tayi.”

Shiru Abdusammad ya yi dan shi ya san abin da ya faru kuma bashi da niyyar sanar da kowa yanzu har sai sanda yarinyar ta dawo. Dan haka ya jinjina kansa ya ce

“nima i think so.” ya sauke ajiyar zuciya yana miƙewa tsaye ya ce“Allah ya kyauta”

Da Amin ta amsa tana kallonsa ganin ya tashin ta ce“tafiya zaka yi?”

Gyaɗa kansa ya yi ya ce“Eh. Zan je wajen Aliyu ne”

“Tam ka gaishe shi” ta ce tana ci gaba da jan cazbahar hannunta.

****
Da daddare suna zaune a parlon bayan sun gama cin abinci Daddy ya kalli Khadijah da ke kwance jikin Mami ya ce“Mimi je ki kira min Nana” to kawai ta ce sannan ta tashi tana gyara zaman hular sanyin kanta ta nufi upstairs. Miƙewa Adeel ya yi yana danna wayarsa, Daddy ya kalleshi ya ce

“son idan Allah ya kaimu gobe ka fita da wuri zaka yankar mana ticket”

Zare airpode ɗin kunnensa ya yi yana kallonsa ya ce“Daddy wata tafiyar kuma?”

Girgiza kansa ya yi yana murmushi ya ce“a'a zan je Yola ne”

“But ai da ka bari ka huta ko zuwa next week ne”

Adeel ya yi maganar a dame. Daddy ya ce“No dole naje gobe, ba abun da za'a ci gaba da jira bane” Adeel bai ji daɗi ba ganin Daddy na son stressing kansa. amma sanin bai isa ya hana shi ba ya sanya ya ɗaga kafaɗa ya ce

“anyway. Allah ya kaimu lafiya”

Bai kuma tsaya jiran amsarsa ba ya bar parlon. Mami ta bishi da kallo sai kuma ta mai da Idanunta kan Daddyn ta ce“Nima dai har zance ka bari sai next week ɗin” babu yabo babu fallasa ya kalleta ya ce“sai a ci gaba da zama da yarinya bayan ba'a san matsayin da take ba? Iyayenta na faman nemanta”

Girgiza kai Mami ta yi. Ya ce“to kin ga dole ne na mayar da ita ga iyayenta, da ina nan ma ba zan bari ta yi wannan satikan ba” Mami ta numfasa ta ce“Tom shikenan Allah ya kaimu goben lafiya” Dai-dai nan suka dawo parlon. Khadijah ce a gaba sai Nana dake biye da ita, ta zauna a ƙasa tana gyara zaman hijabin jikinta, Girgiza kai Daddy ya yi ya ce

“No! No! Tashi a ƙasa”

A sanyaye ta tashi ta zauna kan kujera idanunta a ƙasa. Khadijah ta koma kusa da shi ta zauna tana jingina da jikinsa wanda ya zame mata dabi'a. Numfasawa Daddy ya yi kafin ya mai da hankalinsa kan Nanar ya fara magana a nutse.

“Nana na kira ki saboda na miki magana akan abin da Khadijah ta faɗa min ɗazu. Garin ya aka yi haka ta faru Khadijah? Mene ya saka ki ka yarda da namiji? Baki san illar dake cikin hakan ba?”

Tuni hawaye suka fara zuba kan kyakkyawar fuskarta. Ta sanya hannunta ta goge cikin shessheƙar kukan ta ce

“Tsautsayi Daddy. Wallahi ban yi tunanin zai min haka ba, kawai na san ina son shi, kuma ina son na aure shi. Amma ban yi tunanin zai iya cutar dani ba, haka ita ma Aunty Zahra ban yi tunanin zata yi amfani dasu wajen cutar dani ba. Na san ban aikata abin da ya dace ba, amma ni na ɗauka hakan da nayi shi ne daidai.”

Ta yi shiru kuka na kwace mata. Girgiza kai Daddy ya yi still looking at her ya ce“ya isa haka. Daina kuka, duk abin da ya faru ya riga da ya faru, ƙaddara ce wadda ba'a guje mata. Duk da kin yi wawta da yarinta amma wannan ba zai zama matsala ba, in sha Allah gobe zan mayar dake gida!”

Da sauri ta ɗago kanta ta kalleshi, sai kuma ta fara girgiza kai tana kuka ta ce“a'a Daddy, dan Allah ka yi haƙuri. Tsoro nake ji, wallahi tsoro nake ji, Yaya Safwan yace sai ya faɗawa kowa idan har na dawo” ta ƙare maganar tana fashewa da kuka. Tashi Mami ta yi ta koma kujerar da take zaune ta riƙeta, Nana ta faɗa jikinta tana sakin wani marayan kuka. Shiru Daddy ya yi yana kallonsu can kuma ya ce“it's enough. In sha Allah gobe zan mayar dake, kuma babu abin da zai faru, ni zan fahimtar dasu”

Cikin kuka Khadijah ta ce“Daddy idan kuma kowa ya ga hotunan fa?”

“To ai dole sai an gani ko nan kusa ko kuma nesa, idan haka ne kin ga ɓoyewar bashi da wani amfani”

Shiru Khadijah ta yi tana sharar hawaye. Ya mai da kallonsa ga Nana ya ce“Zo nan” sakinta Mami ta yi ta miƙe a sanyaye ta koma inda yake, gefensa na hagu ta zauna ya dafata cikin son kwantar mata da hankali ya ce

“Babu abin da zai faru kin ji. Ba zan bari kowa ya taɓa ki ba, ba zan bari su ji haushin ki ba. Amma ai na san kina son ganin Mamarki da Abbanki ko?”

A sanyaye ta gyaɗa masa kai sai kuma ta ce“eh Daddy Ina son na gansu, amma ina tsoron Yaya Safwan da Aunty zahra.”
Chapter 64 · 0% Book details