← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 125

Sashe 7

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kanta ta yi ta ce“babu komai” taɓe baki ya yi bai sake bi ta kanta ba har me napep ɗin ya yi parking a bakin estate ɗin. Sauka suka yi ya miƙa masa kuɗin sannan ya nufi ciki, ta dinga bin sa a baya kamar raƙumi da alaka har suka kawo gidansu dan shi ne a farko sannan nasu Sultan, tsayawa ya yi yana kallonta ya ce“tafi gida to” bata ce komai ba ta juya ta nufi ƙofar ta dinga knocking, sai da yaga ta shiga sannan ya yi gaba shi ma.

Amma ta dinga kallonta kafin ta ce“sannu ya jikin?” murya a sanyaye ta ce“da sauƙi” daga haka ta dire ledar akan table ta nufi hanyar ɗakinta. Koda ta shiga ciki zare Abayar dake jikinta ta yi, ta ajiye kan drawer ta kwanta kan gadonta tana sauke numfashi. Duk da yanda ta gaji amma kasa bacci ta yi, tunanin Junaid yaƙi barinta, ko dai ta gwada abin da ya ce mata? Ta dinga saƙa haka aranta har bacci ɓarawo ya saceta. Koda aka yi la'asar Amma ta shigo ta sameta a zaune kan ladduma, hakan yasa bata sake ce mata komai ba ta juya ta fita, haka ta ƙarasa yinin ranar sukuku kamar wadda aka zane, ko wajensu Maimoon da take zuwa kullum bata je ba. Haka ma gurin Hajiya Babba.

Around 8:00 na dare Abba ya shigo ɗakin da kansa, kwance ya sameta ta yi shiru tana tunani, ya zauna gefen gadon ya taɓa fuskarta yana faɗin “ya jikin naki?” tashi tayi zaune sannan ta ce"Abba sannu da zuwa” yawwa ya ce, sannan ya miƙa mata ledar dake hannunsa. Karɓa ta yi t dinga kallon ledar kafin ta sanya hannunta ta buɗe, kwalin waya ta gani ta zaro tana murmushi, iphone 13pro max ce sabuwa, ta saki wani irin ihu tana rungumeshi. Dariya kawai Abba ya yi ya ce“now you are happy ba?” gyaɗa masa kai ta yi tana sake rungumeshin ta ce“thank you so much Abbana, Allah ya biya maka buƙatunka na Alkhairi, ya baka abin da ka ke nema, ya jiƙan iyayenka, ya faranta maka yanda ka ke faranta min”

Murmushin jin daɗi ya yi, wannan shi ne dalilin daya sanya baya gajiya da yiwa tilon ƴar tasa abu, koda abin dole ne akansa idan har ya yi mata sai ta yi masa irin wannan addu'ar. Ya shafa kanta cike da so da ƙauna ya ce“Amin ya hayyu ya Ƙayyum Khadijah, kema Allah ya yi miki albarka” ɗago kanta ta yi tana cewa“Amin Abbana” daga haka ta mayar da kwalin ledar ta sauka daga kan gadon tana faɗin “bari naje na nunawa su Maimoon” murmushi kawai Abba ya yi sannan ya tashi ya fito daga ɗakin, da gudu ta yi waje saboda jikinta har rawa yake taje ta nuna musu wayarta.

Ta kusa kai wa gidan haske ya ɗauke, ko ina na gidan ya yi wani irin duhu, wani irin tsoro taji ya kamata, da alama solar ce ta samu matsala dan su basu san wutar nepa ba. Tun da suka tashi bai fi sau uku ta taɓa ɗaukewa ba, shi ma kuma by mistake ne sai kuma yau. Rasa yanda zata yi tayi, dan duhu na ɗaya daga abin da take tsoro a rayuwarta. Ta dinga juyi a wajen ta kasa gaba ta kasa baya, ledar hannunta ce ta fadi ƙasa ta sunkuyar da sauri tana lalubenta, dakyar ta sameta tana ɗago kanta taji ta a gaban mutum, ihun ta buɗe baki zata yi taji an rufe mata bakin, ya fizgota ta fado jikinsa. Tsabar yanda ta tsorata ya sanya ta sume a wajen daidai nan hasken ya dawo ko ina ya yi tarr dashi.

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Page 5...

Sultan ya dinga kallon fuskarta yana murmushi, sakinta ya yi faɗi a wajen sannan ya buɗe gorar ruwan dake hannunsa ya tsiyaya mata shi tas, a firgice ta buɗe idanunta tana sauke ajiyar zuciya saboda sanyin ruwan data ji. Ganin ƙaton mutum ta yi tsaye akanta fuskarsa babu yabo babu fallasa, sanye yake da ƙananun kaya hannunsa riƙe da empty bottle ɗin sai kuma ledar takeaway. Ganin yanda take kallonsa baki buɗe ya sanya ya ce"kin tashi anan ko sai nabi ta kanki na wuce" tura baki ta yi sannan ta tashi tana kaɗe jikinta murya can ƙasa ta ce"saboda mugunta"

"Me ki ka ce?"

Sultan ya tambayeta yana kafeta da idanu, girgiza kanta ta yi tana ɗaukar ledar wayarta ta ce"ni ba magana nayi ba" daga haka ta juya ta ci gaba tafiya. Da kallo ya bita har ta tura ƙofar ta shiga, ya sauke numfashi sannan ya nufi part ɗin Hajiya Babba. Zaune ta samesu a parlon suna kallo, kusan kowa na gidan yana nan, Maimoon, Juwaira, sai kuma Suhaila. Tana ganinta ta tashi tana cewa"kece da daren nan?" gyaɗa mata kai Nana ta yi sannan ta ce"eh abu nazo nuna miki"

"Na ganki a jiƙe? A wannan sanyin"

Maimoon ta tambayeta ganin yanda take rawar sanyi, kamar zata yi kuka ta ce"to ba Yaya Sultan bane ya watsa min ruwan sanyi" da mamaki Maimoon ta ce"me ki ka masa? Kema ki ci gaba da shiga harkarsa"

Tura baki ta yi tana zama kan sofa ta ce"to ni harkarsa na shiga, kawai fa wuta ce ta ɗauke shi ne naji tsoro ashe shi kuma yana wajen, shi ne ya watsa min ruwa"

Taɓe baki ta yi ta ce"ikon Allah. Me zaki nuna min?"

Ledar hannunta ta miƙa tana washe baki ta ce"Abba ya bani ɗazu"

Maimoon ta buɗe ledar ganin kwalin waya ya sanya ta saki ihu tana dariya ta ce"woww irin wayar Hameeda" gyaɗa mata kai Nana ta yi ta ce"nima haka nace, yanzu ya bani nace bari nazo na nuna miki" .

Maimoon ta dinga juya wayar fuskarta ɗauke da mabayyanin farin ciki ta ce"wallahi na taya ki murna ke kam, daman ni ce nake da waya"

A ɗan dame Nana ta ce"wai har yanzu Yaya Sultan bai bari kin yi waya ba?"

"Wallahi ya hanata, kuma muma ya hana mu"

Juwaira ta bata amsa daga zaunen da take. Kamar su ɗaya da Maimoon sai dai ita ce ƙarama dan Maimoon ta bata wajen 2yrs. Juyawa Maimoon ta yi ta zabga mata harara kana ta ce" dake nake magana da zaki saka min baki?"

Kama bakinta ta yi tana cewa"Allah ya baki haƙuri" daga haka ta ci gaba da kallon da take. Ɗan tsaki Nana ta yi ta ce"yaran nan sun fiye raini wallahi, sai kace mu haka muke yiwa na gaba damu"

Da sauri Juwaira ta kalleta sai dai bata ce komai ba, Maimoon ta yi murmushi tana faɗin"bar ta dai, ni yanzu tashi muje wajensu Hameeda sai a buɗe wayar"

Miƙewa Nana ta yi tana faɗin"muje dan nima na ƙagu na buɗe wayar" okay ta ce sannan ta ware mayafin data ɗaura ta yafashi suka fita suna tafe suna hira har suka kawo apartment ɗin su Hameeda.

Tsayawa suka yi a bakin ƙofar gidan suna kalle-kallen juna, Nana ta ce"after you" harararta Maimoon ta yi ta ce"wallahi ba zan shiga ba, nasani ko Daddy baya nan, kin san dai halin faɗan Mama" Nana ta ce"to me zata magana, daga zuwa wajen Hameeda?"

"Ki fara shiga ke dai"

Haɗe rai ta yi ta ce"to tsoron me nake ji ni, wallahi shigata zan yi" daga haka ta murɗa handle ɗin ta shige, Maimoon ta dinga kallon ƙofar ganin har wajen 2mins bata fito ba ta sauke ajiyar sannan itama ta shiga.

Zaune ta sameta kusa da Mama suna magana, ta ƙarasa ta tsuguna kusa da kujera a sanyaye ta ce"Mama ina yini?" Kakar jira take kuwa ta ce"lafiya Maimuna, wannan shigar fa?" Ta ƙare maganar tana kallonta, Maimoon ta kalli kayan jikinta, riga da wando ne kuma basu wani kama jikinta ba. Jin tayi shiru ya sanya Mama ta sake faɗin "I'm talking to you fa" muryarta na rawa ta ce"na...Nana ta zo tace na rakota nan shiyasa kuma...kuma ban hau sama ba"

Mama ta dinga kallonta babu yabo babu fallasa ta ce"saboda haka ya sanya ki ka fito kamar ƴar arna right? Wato kun dawo daga boarding zaku zo ku dinga yi mana irin wannan halayen ko? To na sake gani" shiru duk suka yi dan daman idan da sabo sun saba da faɗan Mama.

Shiru parlon ya ɗauka na wasu sakwanni, kafin Mama ta rufe littafin dake hannunta ta zare glasses ɗin ta kalli Nana ta ce"baku san hanyar ɗakin nata bane?" Da sauri suka tashi suka bar parlon. Ta bisu da idanu sai kuma ta girgiza kanta a fili ta ce"Allah ya kyauta".

Suna shiga ɗakin Maimoon taja ta tsaya tana sauke numfashi, Hameeda na tsaye jikin dressing mirror tana shafa mai da alama daga wanka ta fito, ta kallesu ganin kamar an koro su ta ce"lafiya dai? Daga ina?" Tskai Nana ta yi ta nemi gefen gado ta zauna. Ta kalleta sai kuma ta kalli Maimoon wadda ke tsaye har sannan tana sauke numfashi sai kawai ta fashe da dariya. Kallonta suka dinga yi, ta ɗaure kanta tana cewa"Mama ce ta muku faɗa right?"

"Ya aka yi ki ka sani?"

Cewar Maimoon a sanyaye, taɓe baki Hameeda ta yi ta ƙaraso ta zauna kan drawer sannan ta ce"Mama fa nace miki, wane bai san halin faɗanta ba"

"Ai wallahi shiyasa nake tsoron zuwa wajenki, ta dinga faɗa" cewar Nana fuska a haɗe, ɗan murmushi Hameeda ta yi ta ce"sorry love, na ganku da dare?" Maimoon ce ta ƙaraso ta miƙa mata ledar tana cewa"waya Abba ya kawowa Nana, shi ne muka zo nuna miki fa" waro idanu ta yi tana karɓa ta ce"woww masha Allah, gaskiya na taya ki murna, ke Nana"

Nana ta ɗan juya Idanunta tana murmushi ta ce"ke dai bari, yau ji nake kamar ba zan iya bacci ba." Hameeda ta ɓare ledar kwalin tana faɗin "sanda zaki yi baki sani ba, ranar da Yaya Hameed ya kawo min wayata haka naji" Maimoon ta ce"ki ka dinga dariya ba, ranar mun kusa haukacewa"

"Yauwa ai har pictures ɗinmu zaki turan dana Aun"
Chapter 7 · 0% Book details