← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 125

Sashe 70

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sunkuyar da kai ta yi tana gyaɗa masa kai, Daman ta san da wannan bayanin tun tuni. Amma ita sam bata masa kallon wanda zata iya aura, a koda yaushe kallon mahaifi take masa. Ɗaukansa take kamar Abbanta, ashe watarana zai iya zuwa ya aureta?.

Miƙewa Abba ya yi yana ɗaukan cazbaharsa ya ce“Idan Allah ya kaimu an jima za'a sadaki da ɗakin mijinki, don haka ina mai miki nasiha da kiji tsoron Allah, ki kasance haske mai haska zuciyar mijinki. Ki zame masa ƙawa kuma abokiyar arziki, dan Allah Nana kada ki bamu kunya.”

Yanda ya yi maganar a tausashe ya sanyata kallonsa, Hawaye na biyo kuncinta ta ce“Tam Abba in sha Allah ba zan baku kunya ba, ba zan bari ku sake kuka dani ba.”

Ta ƙare maganar kuka na kwace mata, Murmushi kawai Abba ya yi sannan ya juya ya fice daga ɗakin, Nana ta bi bayansa da kallo sai kuma ta sake fashewa da kuka, ta faɗa kan gadonta ta shiga rera shi kamar waƙa.

****
Zahra ta dinga kallonsa ganin yanda yake cin abincin hankali kwance, idanun da yaji na yawo a kansa ya sanya ya ɗago kansa, cikin rashin sa'a idanunsu suka sarƙafe da juna. Ta yi saurin janye nata tana ɗaukan mug ɗin tea ɗinta, Ɗan murmushi ya yi sai kuma ya ajiye spoon ɗin hannunsa still looking at her ya ce

“why are you staring at me?”

Yi ta yi kamar bata san me yake nufi ba, ta kalleshi ta ce“magana ka yi doctor?”

Ɗauke kansa ya yi yana murmushi ganin tana shirin raina masa hankali, Zahra ta saci kallonsa ta gefen ido ganin yanda yake murmushi ya sanyata yin murmushin itama. Bai sake bi ta kanta ba har ya kammala breakfast ɗinsa, Ya tashi yana goge bakinsa da tissue ya ce

“To zan fita sai na dawo.”

Tashi itama ta yi tana murmushi ta ce“Tom a dawo lafiya Allah ya tsare hanya.”

Da Amin ya amsa sannan ya juya zai bar wajen, kamar wanda ya tuna wani abun kuma sai ya tsaya cak. Ta ɗan kalleshi sai kuma ta ce“doctor lafiya dai?” juyowa ya yi yana kallonta ya ce“wallahi na kusa mantawa ne. Idan Allah ya kaimu an jima za'a kawo Nana, so get ready please.”

Ji tayi kamar an zare mata lakar jikinta, taji ƙafafunta na neman gagarar ɗaukan gangar jikinta. Numfashinta ya tsaya na wasu sakwanni, Ganin haka yasa Abdusammad cewa

“Lafiya dai?”

Girgiza masa kai ta yi a sanyaye. Ya dinga kallonta ganin yanda ta sunkuyar da kanta, Taku ɗaya ya yi ya koma gabanta, Ya sanya hannunsa ya ɗago kanta. Hawaye ya gani na zuba daga cikin idanunta, Ya ɗan ware idanunsa da mamaki ya ce“Zahra mene haka?”

Saurin goge hawayen ta yi da hannunta tana shessheƙar kuka ta ce“babu komai. Ban sani ba ne”

Ta ƙare maganar tana kirkiro murmushi. Wani irin kallo ya dinga yi mata sai kuma ya ce“Saboda nace miki Nana zata zo ki ke kuka?”

Saurin girgiza masa kai ta yi tana ƙoƙarin ɓoye hawayenta ta ce“A'a doctor, babu komai fa.”

Taɓe baki ya yi dan ya san ƙarya take ya ce“na miki kama da wanda zaki ma karya Zahra?.”

Kallonsa kawai ta yi sai kuma ta sake sunkuyar da kanta kuka na sake tawo mata, ya kalli agogon Rolex ɗin dake maƙale a hannun hagunsa sai kuma ya mai da idanunsa kanta ya ce“But you promised me cewa komai ya shige? Gyaɗa masa kai ta yi ta ce“Eh doctor babu komai Allah ya kawo su.”

“Amin”

Ya amsa a takaice. Sai kuma ya sake cewa“make sure kin shirya kinji. Ki yi kyau abin ki”

Ya ƙare maganar yana jan kumatunta. Murmushin ƙarfin hali ta yi ta ce“In sha Allah I'll” ya yi murmushi sannan ya juya ya bar wajen. Sai da taga ya fice daga parlon sannan ta sulale a ƙasa a hankali, kamar jira take ta fashe da wani raunataccen kuka..

Yana ƙoƙarin shiga mota yaga kiran Papa, Ya tsaya hannunsa ɗaya riƙe da handle ɗin motar ɗayan kuma riƙe da wayarsa ya ɗaga kiran, gaishe shi ya yi amsa sannan ya ce

“Abdusammad ka zo ina nemanka”

Shiru ya yi sai kuma ya ce

“Papa lafiya dai?”

“Lafiya fa. Idan ka zo kaji”

Papa ya bashi amsa kai tsaye, To kawai ya ce sannan ya kashe wayar, Abdusammad ya sauke wayarsa yana mamakin kiran, can kuma ya sauke numfashi ya shige motar.

****
Abdusammad ya girgiza kansa da rashin fahimta ya ce“Papa ban gane abin da ka ke nufi ba.” Gyara zama Papa ya yi kan sofar yana kallonsa ya ce“abin da nake nufi shi ne idan ka san ba zaka iya zama da yarinyar nan ba gara tun yanzu ka saketa!”

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Arewabooks@Nanamera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 43.

Da wani irin mamaki yake kallon Papa can kuma ya ce“But why?” cike da nutsuwa Papa ya ce“saboda baka sonta. Bayan haka ban ga alamun zaka kula da ita ba.”

“Wani abun nayi mata Papa.?”

Girgiza kai Papa ya yi kafin ya ce“ko kaɗan zuwa yanzu babu abin da ka yi mata. Amma alamunka sun nuna nan gaba zaka iya yi mata, Jiya duk ina kallonka kuma naga yanda ka yi, baka shirya zama da yarinyar nan ba. Ko kaɗan baka ji daɗin cewar da aka yi ta tare ba!”. Papa ya ƙare maganar yana jingina da kujerar da yake kai. Numfasawa Abdusammad ya yi dan sai a sannan ya gane inda ya dosa, har ga Allah shi kansa ya sanya bai shirya da karɓar tata ba, amma ya zai yi?. Jin bai ce komai ba ya sanya Papa gyaran murya kafin ya ci gaba da cewa

“Ina son ka dinga tuna abu guda ɗaya, ba yarinyar nan ta ce ka aureta ba. Ba mahaifinta bane, ba tilastaka aka yi ba, kaine ka yi hakan saboda raɗin kan ka. Idan har ka ce zaka cutar da ita a zaman da zaku yi tare to ka sani Allah ba zai bar ka ba, Dan haka da azo ana ɓacin rai daga baya gara kawai ka saketa tun yanzu.”

Papa ya yi shiru yana kallon sa. Ajiyar zuciya Abdusammad ya sauke kafin ya fara magana

“Ni fa ba wai ina jin haushin yarinyar nan bane Papa, na san bata da laifi. Kuma koma tana da shi ai abin da ya wuce ya riga da ya wuce, dan haka babu amfani tado shi. Kawai na kasa yarda ne a ce wai Nana matata ce, na kasa yarda zata shigo gidana ta yi rayuwa dani irin rayuwar miji da mata, bayan yanda na ɗauketa yar ƙaramar ƴata a wancan lokacin.”

Murmushi irin na manya Papa ya yi kafin ya ce“Na gane abin da ka ke nufi, amma ba hujja ba ce. Babu yanda za'a yi ka ce dan kana yi mata kallon ƴa ba zata zama matarka ba watarana, baya da haka ma kasan akwai aure a tsakanin ku. Dan haka ina ganin ka bar wannan tunanin zai fi, sannan kuma kada ka kuskura ka ce zaka yi treating ɗinta a kar yarinya ko ƙarama da ka ke ganinta. Dole ne ka sauke duk wani haƙƙinta da yake kan ka, dole ka bata kulawa irin wadda miji ke bawa matarsa, dole ka saurari matsalarta sannan ka yi mata maganinta.”

Numfasawa ya yi jiki a sanyaye ya ce“Tom Papa in sha Allah.”

“Allah ya yarda ya sanya albarka cikin auren, ya baku zaman lafiya.”

Da Amin ya amsa sannan ya tashi ya masa sallama ya fito.

****
Ƙarfe 9:00 na safe Aunty Ramlah ta sauka a gidan, ta ajiye jakarta tana kallon Amma da ke haɗa wasu turaren wuta ta ce“To amma dan Allah sai a ce yau zata tare? Ina ma laifin a ce gobe fisabilillahi.” ɗan murmushi Amma ta yi ba tare da ta ɗago kanta ba ta ce“to basu ce haka ba Ramlah. Ni yanzu ki tashi ki je idan da abin da zaku yi ku yi, saboda na san tunda aka haɗa sabgar nan da Atta to wallahi ba zata jira ba, tana iya zuwa ta ce dole sai ta tafi da ita.” Tashi Aunty Ramlah ta yi tana murmushi ta ce“Atta ko jaraba” daga haka ta yi dakin Nana da sauri. Bakinta ɗauke da sallama ta tura ƙofar ɗakin, Sai dai turus ta yi a bakin ƙofar saboda Nanar data hango tana kuka a ƙasa ta yi baje-baje sai birgima take. Aunty Ramlah ta saki ƙofar da sauri ta ƙarasa ciki tana faɗin

“Subhanallahi. Nana mene ne haka?”

Ko kallonta bata yi ba sai ma sake ƙara sautin kukan nata da ta yi, Aunty Ramlah ta ɗagota tana kallonta hankali tashe ta ce“baki ji ina miki magana ne? Sai ran ki ya ɓaci tukun”

Ganin yanda ta yi maganar babu wasa a kan fuskarta ya sanya Nana tsagaitawa da kukan. Ta fara sauke numfashi tana shessheƙa a hankali, Zama Aunty Ramlah ta yi a ƙasan tana kallon ta ta ce“Yanzu faɗa min kukan me ki ke?”

“Anty wai uncle zan aura. Uncle fa, Ya za'a yi a ce shi ne mijina...”

Ta ƙare maganar tana sake rushewa da kuka. Girgiza kai Aunty Ramlah ta yi ta ce“a'a ban gane ba Nana, mene ne da uncle ɗin?” ɗauke Hannunta ta yi daga fuskarta cikin son yi mata bayani ko Allah zai sa ita ta fahimceta ta ce

“Anty uncle Abdusammad fa. Kina ganinsa ai kin san Babba ne ko? Kuma fa har mata ce dashi, ni kuma ai yarinya ce, duk su sauran sun yi aurensu da Yara sai ni a aura min tsoho? To dan Allah ba babba bane shi. Ni kuma kalleni fa, Sai a dinga cewa ni ce matarsa?..”

Ta sake fashewa da kuka tana faɗawa jikin Aunty Ramlah. Murmushi Ramlah ta yi sannan ta ce“ke kuma kin fi son ki auri yaro ko? Kin fi son wanda zai nuna miki soyyaya? Wanda ba zai dinga miki faɗa ba ko?.”

Jin ta faɗi abin da take so yasa ta ɗago kanta cikin shessheƙar kukan ta ce
Chapter 70 · 0% Book details