Sashe 9
Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin shassheƙar kuka ta ce"dan Allah Yaya Sultan ka samar mana napep, ko kuma ka maidani gida nagaji" harararta ya yi ya ce"ba zan yi ba" daga haka ya ja hannunta suka tsallaka titin. Ci gaba da tafiya suka yi, tana tafe tana gudu-gudu saboda yanda yake tafiya cike da zafin nama. Ana kiran sallar ƙarfe 1:00 na rana suka ƙaraso gaban wani babban masallacin juma'a, kallonta ya yi ya ce"zo ki zauna acan nayi sallah sai mu ci gaba da tafiya" saurin gyaɗa masa kai tayi dan daman neman wajen hutawa take. Sai da ya rakata har wajen data zauna sannan ya ce"kar ki kuskura ki bar nan, kuma kar ki kula kowa" gyaɗa masa kai ta sake yi, ya juya ya nufi cikin masallacin. Lumshe idanunta ta yi ta jingina da kujerar hawaye na zubowa kan kuncinta, iyaka azaba yau Sultan ya gana mata, bata saba tafiya irin haka a ƙasa ba, dan duk inda zasu je kai su ake yi.
Tana nan zaune har aka idar da sallar mutane suka fara fitowa, ta dinga bin su da kallo a ƙoƙarinta na son ganin Sultan, sai dai har bayan mintuna ashirin babu shi babu dalilinsa. Nana ta sauke idanunta kawai ta fashe da kuka, to ko dai tafiya ya yi ya bar ta anan? Wani ɓangare na zuciyarta ya sanar da ita hakan. Kawar da tunanin ta yi dan tasan ba zai tafi ya bar ta ba, ta ci gaba da kallon harabar masallacin tana jiran tsammanin fitowarsa. Ƙarfe 1:43pm ya ƙaraso wajen hannunsa riƙe da wayarsa, sam bata lura dashi ba dan idanunta a rufe suke tana faman hawaye. Ɗan murmushi ya yi sai kuma ya ce
“Nana!”
Da sauri ta ɗago bayan ta buɗe idanunta, kallonsa ta dinga yi amma bata ce komai ba. Gaba ɗaya ta birkice kamar ba ita taci kwalliya ta fito daga gida ba, ɗankwalin kan nata ma tuni ya kwance. Fuska a sake ya ce"kin yi sallah?" Girgiza kanta kawai ta yi, ya ce"but why? Ko baki yin sallar?" ɗago idanunta ta yi suka haɗa ido ta sauke nata ba tare da ta ce komai ba. Sarai ya san da bata sallahr amma ya tambayeta, jin tayi shiru ya sanya ya ce"ina magana da statue ne Nana?"
"Bana yi!"
Ta ce a takaice, murmushi ya yi sai kuma ya ce"alright, tashi mu tafi" dakyar ta miƙe saboda yanda ƙafafunta suka kumbura, ya riƙe hannunta suka bar wajen. Suna fitowa daga gate ɗin taga ya nufi wajen motarsa, ta dinga kallon baƙar motar da ke kyalli, ashe daman da motar ya zo? To ko yanzu aka kawo masa? Ta yi tambayar a zuciyarta..
"Shiga mana"
Maganar Sultan ta katseta. Bata ce komai ba ta buɗe murfin ta shiga front seat tana sauke numfashi, juyawa ya yi ya shiga driver seat sannan ya yiwa motar key ya yi reverse suka bar wajen. Har suka je Gimba road babu wanda ya ce wani abu, Nana sai faman matsa ƙafarta take tana runtse ido, ta gefen ido ya kalleta ba tare da ya ce komai ba. A No.34 state lowcost ya yi parking, daidai wani ƙaton gida, sai a sannan ya juyo ya kalleta ganin yanda take riƙe da ƙafar yasa ya ce"mene ne?" Jin yanda ya yi maganar cike da kulawa ya sanya ta saki jikinta a ɗan shagwaɓe ta ce"Yaya Sultan ƙafata zata cire zafi take min!" Ta ƙare maganar tana yarfe hannu, kallon ƙafafun ya yi sai kuma ya ce"to ko za ki shafa man zafi?" saurin gyaɗa masa kai ta yi, ya zaro kwalbar aboniki daga aljihunsa ya miƙo mata. Karɓa ta yi sai kuma ta ɗago ƙafafun nata tafara janye skirt ɗin, fararen ƙafafunta suka bayyana, Sultan dai sai kallonta yake ba tare da ya ce komai ba. Sai da ta buɗe cealing ɗin jikin kwalbar sannan ta cire murfin, ƙoƙarin shafawa ta fara yi amma sai taji gaba ɗaya ta matsu saboda yanda ta yi da ƙafafun nata, ɗago kanta ta yi ta kalleshi murya a sanyaye ta ce"Yaya ko zaka shafa min?"
"Baki da hannu ne?"
Langwaɓar da kanta ta yi kamar zata yi kuka ta ce"i can't ne" bai sake cewa komai ba ya amshi kwalbar yana kallonta, saurin ɗoro ƙafafun nata ta yi tana shirin sauke su kan cinyarsa, ganin irin kallon da yake mata ya sanya ta ce"can i?" tsaki y yi ya jawo ƙafafun ya ɗora kan cinyarsa sannan ya fara shafa mata man a hankali yana bin ko ina yana shafawa, lumshe idanunta ta yi ta buɗe tana kallonsa, ɗago kansa ya yi ya kalleta ta yi murmushi tana dauke kanta, murmushin shima ya yi ya janye ƙafafun yana girgiza kansa. Sauke skirt ɗinta ta yi ta ɗauki jakarta tana kallonsa ta ce"Yaya na jiraka?" gyaɗa mata kai ya yi ta buɗe motar ta sauka tana ɗaga masa hannu, sai da yaga ta shiga cikin gidan sannan ya sauke zazzafan numfashi, gaba ɗaya ji ya yi wata irin kasala ta rufe shi, ya ɗan jima a wajen kafin ya yiwa motar key ya bar kofar gidan..
****
Nana ta dinga kallon Inteesar tana murmushi ta ce"ina Aunty take?" yarinyar da bazata shige 10yrs ba ta ce"tana ɗakin Daddy" okay Nana ta ce sannan ta gyara zamanta kan sofa ta maida idanunta kan tv inda ake haska wani cartoon a MBC 3, after 5mins sannan Aunty Ramlah ta buɗe ƙofa ta fito, washe baki ta yi tana kallonta ta ce"Nana ce a gidan?" murmushi ta yi tana kallonta ta ce"eh auntie ina yini?" Sai da ta zauna kan kujera sannan ta ce"lafiya kalao, Ya Amma?"
"Tana nan klao Aunty, ta ce na gaisheki." Aunty Ramlah ta mike ta ce"ina amsawa" daga haka ta nufi kitchen, drinks ta kawo mata ta ajiye kan table ta ce"drink it Ina zuwa" okay kawai Nana ta ce, ta juya ta koma kitchen. Kunun aya ta ɗauka ta sha tana lumshe ido, ta gaji sosai kuma ga yunwa da take ji, wayarta ta zaro a jakarta ta kunna taga 3missed calls da wata number, tashi ta yi tana kallon Inteesar ta ce"bari naje toilet" okay ta ce sannan ta nufi hanyar ɗakinta ta shiga. Sai da ta mayar da ƙofar ta rufe sannan ta shiga dialing numbern, ringing biyu aka ɗauka daga ɗaya ɓangaren ya ce
"Nana you keep me waiting"
Ƙasa ta yi da muryarta ta ce"sorry, ina gidan yaushe zaka zo?"
Sir Junaid dake kwance kan gadonsa ya ce"zuwa 4 ya yi?"
Gyaɗa kanta ta yi kamar tana gabansa sai kuma ta ce"Eh nima yanzu nazo, zuwa sannan naci abinci na huta" okay ya ce sannan ta kashe wayar. Ta sauke ajiyar zuciya tana kallon screen ɗin wayar sannan ta juya ta fice daga ɗakin.
Zaune ta sami Aunty Ramlah tana magana da Inteesar, ta ƙarasa ta zauna gefenta ta jingina daga jikinta, murmushi Aunty Ramlah ta yi ta ce"to mage sarkin son jiki, ni kar ki tausheni" a shagwaɓe ta ce"nagaji ne fa, Yaya ne ya sanya nayi tafiya a ƙafa"
"Wane yayan?"
"Yaya Sultan mana" cewar Nana. Aunty Ramlah ta gyaɗa kanta ta ce"shi ne ya kawo ki?" she just nodded her head tana sake narkewa a jikin aunty Ramlah, murmushi ta yi ta ce"to ko dai dashi za'a yi ne Nana?" saurin tashi zaune ta yi tana cewa"Allah ya kiyaye ni bana son sa" yanda ta yi maganar ya sanya Aunty Ramlah dariya sai kuma ta ce"to mene ne aibunsa? Sultan me hankali da nutsuwa, Ni zan iya cewa duk cikin samarin shuwa babu wanda ya kai shi" taɓe baki Nana ta yi ta ce"taɓ! Me zan yi dashi, mugu ne wallahi" harararta Aunty Ramlah ta yi ta ce"to ai duk wannan yanzu ne, kuma kin san ma'anar namiji ya dinga yi miki mugunta?" Shiru Nana ta yi sai kuma ta girgiza kanta, Aunty Ramlah ta gyara zama ta ci gaba da fad'in "idan har ki ka ga kuna zaune da namiji yana miki mugunta ko kuma yana takureki fiye da sauran yan uwanki that's means yana da feeling akan ki, yana sonki ne. Kuma na fahimci haka a gurin Sultan" tura baki Nana ta yi ta ce"nifa Aunty ba haka bane, babu abin da zai haɗani da Yaya Sultan yaje can inda ake sonsa" murmushi kawai ta yi ta ce"ai shikenan, naji watarana kin cemin kina sonsa"
"Har abada ma wallahi" ta ƙare maganar tana tashi daga wajen.
****
Zaune suke cikin parlon kowa ya bada full attention ɗinsa zuwa ga abin da take cewa, Hajiya Babba ta sauke numfashi sannan ta ci gaba da faɗin
"Yanzu na riga da na yanke hukunci akan yanda za'a yi, idan kuma kuna ganin hakan bai yi ba sai a sauya"
Alhaji Kabir ya yi murmushi sannan ya ce"ai babu wani sauyi Hajiya, hakan ma ya yi Allah yasa haka ne mafi alkhairi ya kuma kai mu lokacin" Amin ta ce sannan ta maida idanunta kan Abba ta ce"kai fa Alhaji?" girgiza kai Abba ya yi fuskarsa ɗauke da mabayyanin murmushi ya ce"Alhamdulillah Hajiya, hakan ya yi dai dai, Allah ya kai mu da rai da lafiya ya kuma basu zaman lafiya" duka kowa ya ce Amin. Mama ta ce"to yanzu zuwa yaushe za'a saka kenan?" Hajiya Babba ta gyara zamanta sannan ta ce"ai wannan yana wajensu, ni dai nagama nawa"
Daddyn su Sultan wato Alhaji Kabir ya ce"i think zamu fara magana da yaran sai aji yaushe za'a tsaida, but before that yaushe Arɗo zai dawo? Akwai buƙatar ayi komai a gabansa"
Abba ya jinjina kai sannan ya ce"haka ne, in sha Allah zan masa magana ya sanya rana ya dawo, zaman ya isa haka"
Hajiya Babba ta ce"to wata kila ku yaji maganarku, amma na saka Aliyu ya masa magana ya ce masa wai yana da abubuwan yi ne dayawa acan" murmushi Abba ya yi ya ce"Allah sarki ai yana ƙoƙari sosai, amma duk da haka zai zo in sha Allah" Mama ta ce"Allah ya yarda ya kuma nuna mana" Amin suka ce sannan kowa ya tashi ya watse, Hajiya Babba ta sauke numfashi tana fatan wannan haɗin da ta yi ya zama mai albarka.