← Book details Naanah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 125

Sashe 91

Naanah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

****
Safwan ya dinga kallon Siyama ganin yanda ta ɗan haɗe rai, Ya girgiza kansa ya ce

“Ba wai dawowa zata yi ba fa. Kawai dai na faɗa miki ne”

Taɓe baki ta yi ta nemi gefe ɗaya ta zauna tana kallon sa ta ce“Ai saboda ita ka ɗauka da muhimmanci gashi har ta samu ciki a ɗan zaman da ku ka yi tare, amma ni da baka ɗaukeni a bakin komai ba ai gashi ka bar ni sai dai naci na kasayar!”

Safwan ya dinga kallonta da mamaki, can kuma ya ce“Siyama ban gane me ki ke nufi ba? Daman ni ne wanda nake da alhakin samun cikin ki ko rashin sa? Mene nawa a ciki?.”

Tashi tsaye ta yi tana harararsa ta ce“A'a ba kai bane, ya za'a yi ya zama kai daman! Amma ka sani wallahi idan dan ka zalunceni ka ke min haka Allah ba zai bar ka ba. Ai nima matarka ce, kuma nima ina son naga na haihun, amma shi ne ka fifita ƴar uwarka akaina...” Ta bar parlourn da sauri tana kuka, Safwan ya bita da kallo sai kuma ya sunkuyar da kansa yana sauke numfashi. After some minutes kuma ya tashi yabi bayanta. Zaune ya sameta gefen gado sai kuka take a hankali, Ya ƙarasa ciki ya tsaya a zauna akan drawer yana kallon ta ya ce

“Ina son ki gane wannan ba laifina bane Siyama, ban kyamace ki ba, ban guje ki ba. Na ɗauki hakan matsayin ƙaddararmu gaba ɗaya dani dake, amma ki sani ba ni ne wanda ke bada haihuwa ba, tsarin Allah ne. Kuma shi yaga damar ya hukunta Haule ta samu ciki, Shi ne ya yi mata kyautarsa, dan haka ki daina damun kan ki, idan Allah ya so sai ki ga ya sake bamu wasu. Kuma ai a ganina abin da zan haifa kamar naki ne, duk abin da Haule ta haifa karɓarsa zan yi, mu raine shi tare. Kin ga zamu samu ɗa mai lafiya...”

“Ai daman dole ka ce haka, dole ka ce kana son ka samu ɗa mai lafiya. Saboda ni ba zan iya haifar maka ɗan ba, ko kuma baka son irin wanda zan haifa kai da danginka. Shi ne zaka ce min tsarin Allah ne!”

Safwan ya yi shiru yana kallon ta, sam bata fahimci abin da yake nufi ba, dan haka ya taso daga inda yake ya dawo gefenta ya zauna. Hannunta ya riƙe cikin nasa murya a sanyaye ya ce

“Ba haka bane Siyama. Wallahi ko yau Allah ya baki ciki zan yi farin ciki, kamar yanda nayi farin ciki dana Haule. Kuma ai likita ya faɗa mana zamu iya haifar ya'ya wanda basu da cutar, dan haka ki daina damun kan ki dan girman Allah”

Siyama ta sanya ɗayan hannunta ta goge hawayenta, cikin shessheƙar kuka ta ce“Ai shikenan. Allah ya sauketa lafiya.”

Murmushin jin daɗi ya yi dan daman ya san zata fahimce shi ya ce“Amin, Ya bamu wasu Ya'yan.” da amin ta amsa sannan ta ce“muje ka ci abinci.” To kawai ya ce duk da ba yunwa yake ji ba, Ta tashi tana riƙe da hannunsa ta ce“muje to” Ya gyaɗa mata kai bayan ya miƙe tsaye suke fice daga ɗakin.

****
New York, America.

Zahra na zaune tana danna wayarta ya shigo, Sanye yake da pyjames white colour ya ɗaure kansa da ribbon, Ya ƙaraso ciki ya zauna gefen gadon yana kallon ta.

“Sannu da zuwa.”

Ta ce a sanyaye bayan ta ajiye wayar a gefenta. Babu yabo babu fallasa ya ce“Yauwa.” shiru wajen ya ɗauka can kuma ta ce“Ko na kawo maka abinci?” girgiza kansa ya yi yana kallonta ya ce“A'a thank you.”

“But you didn't eat anything fa. Ko dai Nana ta baka abinci?”

Sake girgiza kansa ya yi ya ce“a'a ban ci komai ba, Nana ma bata jin daɗi.” Zahra ta kalleshi a karo na farko ta ce“me ya sameta?” zare ribbon ɗin kansa ya yi ya ce“nothing serious fa, wai cramps ke damunta”

Zahra ta girgiza kanta a sanyaye ta ce“Allah ya sawwaƙe.” Amin kawai ya ce, can kuma ya ce“yau mene ya same ki?” girgiza kanta tayi tana murmushi ta ce“babu komai fa, kawai mood swings ne” Abdusammad ya ɗan taɓe baki sai kuma ya jawota jikinsa ya ce

“shi ne zaki dinga wani shareni?”

Murmushi ta yi tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa ta ce“to ai kai ma sharenin ka yi.” ta ƙare maganar tana shagwaɓe fuska, Ɗago kanta ya yi ya ce“da gaske?” Ta gyaɗa masa kai tana sake narkewa a jikinsa, Murmushi ya yi ya ce“to yanzu zan daina share kin” murmushi ta yi ta ɗago kanta tana kallon sa ta ce“gobe Noor zata tafi school, dan haka da wuri zan tashi.”

Gyaɗa kansa ya yi ya ce“haka ne to dan haka sai ki kwanta da wuri, naga ta damu ta koma da sai ta bari sai ta huta.” Zahra ta ce“wannan ƴar taka mai wutar ciki, ya za'a yi ta jira?” ta ƙare maganar tana murmushi. Dariya ya yi ya ce“Eh ai ke ta gado” Zahra ta ɗan kalleshi da mamaki ta ce“a haba dai ni doctor”

Murmushi ya yi ya ja hancinta ya ce“Eh mana.” Zahra ta maƙale kafaɗa ta ce“a'a sai dai idan kai ta gado wallahi.”

“Ko?”

Ya ce yana ƙoƙarin kwanciya, Ta ɗan yi murmushi sai kuma ta kwanta a gefensa...

Around 2:00 na dare ta buɗe idanunta, Ta tashi zaune ta dakyar saboda ciwon da marar ke mata, ta ɗora hannunta akan mararta tana kuka a hankali. Ta daɗe zaune a wajen kafin ta sauka daga kan gadon dakyar, Ta kunna bedside lamp nan da nan haske ya gauraye ɗakin, kalle-kalle ta dinga yi ganin bata ganshi ba ya sanya ta zura slippers ɗinta ta nufi waje a hankali. Kai tsaye apartment ɗinsa ta nufa, Ta tsaya bakin ƙofar tana murza idanunta wanda har sannan bai gama wartsakewa ba. A hankali ta fara knocking ƙofar tana kiran sunansa, Sai dai har bayan mintuna biyar babu alamar za'a zo a buɗe, Nana ta fashe da sabon kuka tana ɗan buga ƙafafunta, ita kaɗai ta san azabar da take ji. Ta juya ta sauka daga benan, Tsayawa ta yi a wajen tana kallon benan Zahra, lokaci ɗaya kuma ta hau tana tafe tana dafe mararta. Knocking ta dinga yi kamar zata jijjige ƙofar. Abdusammad ya janye Zahra daga jikinsa ya tashi zaune yana kallon ƙofar da mamaki. Itama Zahra buɗe idanunta ta yi dan ba wani nauyin bacci gareta ba,

“Kin ji?”

Ta gyaɗa masa kai tana hamma, bayan ta rufe bakinta ta ce“waye to?”

“Ko Noor ce?” Y tambaya yana sauka daga kan gadon, Zahra ta gyara zamanta tana jiransa. Ya ƙarasa ya buɗe ƙofar. Da mamaki yake kallonta, ganin yanda ta yi tsaye a wajen tana murza idanunta tana kuka, Ya ɗan ware idanunsa kafin ya ce

“Mene ne Nana?”

Cikin kuka ta ce“uncle ni bana son kwana ni kaɗai, kuma cikin ciwo yake min...” ta ƙare maganar tana sakin wani sabon kukan, Zahra ta taso tana kallon sa ta ce

“mene ne?”

Ya ɗan girgiza kansa bayan ya bar jikin ƙofar, Nana ta gani tsaye tana kuka. Ta kalleshi ta ce“Lafiya dai?”

“Uncle ni tsoro nake ji. Ka zo mu tafi tare”

08106608363
Nanameera.*🌹 NAANAH 🌹*

Arewabooks@Nanameera08
Wattpad@Nanameera08.

Page 55.

Daga shi har Zahra suka kalleta, Ta janye hannunta daga idanun tana kallon su sai kuma ta ɗauke kai tana tura baki. Abdusammad ya ce“zo nan.” jiki a sanyaye ta ƙarasa gabansa, Ya sanya hannunsa na dama ya taɓa wuyanta. Zazzaɓi ne sosai a jikinta, Ya ɗan girgiza kansa kafin ya ce“to ki zo ku kwanta da Zahra anan.” A hankali ta kalle shi sai kuma ta sunkuyar da kanta tana maƙale kafaɗa, Zahra ta ɗan yi murmushi ta ce“Kawai doctor kaje.” wani banzan kallo ya watsa mata kafin ya kalli Nana ya ce“koma ki kwanta to. Babu abin da zai same ki” Cikin kuka ta ce“Allah ni ba zan iya kwanciya ni kaɗai ba, Tsoro nakeji. Kuma ai bani da lafiya...” Ta sake fashewa da kuka, Haɗe ransa ya yi in a serious tone ya ce

“koma nace!”

Ganin babu wasa akan fuskarsa ya sanyata ficewa daga ɗakin, Ya mai da ƙofar ya rufe ya koma kan gadon. Zahra ta dinga kallon sa kafin ta ce“amma ka ce bata da lafiya fa, da kaje wajenta.” Bai bata amsa ba ya yi kwanciyarsa, dan ya riga da ya san halin Nana, rashin son zaman lafiya ne kawai irin nata. Zahra bata sake cewa komai ba itama ta koma ta kwanta. Nana ta dinga kallon ƙofar hawaye na sakkowa kan idanunta, Ta juya ta fice daga parlourn ta koma ɓangarenta. Kwanciya ta yi akan gadon ta dinga kuka tana juyi, can kuma ta tashi ta gudu ta nufi banɗaki. Amai ta yi ta wanke bakinta ta dawo ɗakin ta kwanta, ko kaɗan ta kasa bacci sai juyi take tana kuka, tun da ta fara period bata taɓa yin irin wannan ba. Saboda ba'a taɓa barinta babu magani, idan bata yi bacci ba babu wanda zai kwanta a gidan, ko tsakar dare ne sai Abba ya fita ya kai ta asibiti. Ta sake rushewa da kuka tana jin haushin biyoshin da ta yi, tana nan kwance har aka fara kiraye-kirayen sallar asuba a masallacin gidan, ta dinga ƙoƙarin tashi zaune amma ta kasa, daga ƙarshe kuma bacci ya ɗauketa.

Murɗa handle ɗin ƙofar ya yi bakinsa ɗauke da sallama, Ya shigo ciki ya mai da ƙofar ya rufe yana kallon ta, gaba ɗaya ta rufe jikinta da bargo ko kanta ba'a gani. Ya ɗan girgiza kai sannan ya ƙarasa ciki ɗakin, zama ya yi gefen gadon ya sanya hannunsa mai maƙale da counter ya ɗan taɓa ta ya ce

“Ke Nana.”

Shiru bata amsa ba, Ya janye bargon yana kallon ta, ba bacci take ba, amma idanunta a rufe suke sai hawaye dake zubowa ta gefensu. Hannunsa ya kai ya taɓa wuyanta yaji har sannan da zafi sosai, Ya tashi ya fice daga ɗakin ba tare da ya ce komai ba. Bayan kusan mintuna goma ya dawo hannunsa riƙe da wani ƙaramin tray, Ya jawo table ya ajiye sannan ya koma ya zauna yana kallon ta ya ce

“Taso.”
Chapter 91 · 0% Book details